HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

AFTER 3MONTH
Abubuwa da yawa sun faru cikiko harda shaƙuwa me ƙarfi data shiga tsakanin F2 da Ummita dakuma kammala aikin Hajjinsu Zaune suke a jirgi Fatimah tace”Aunty Hafsat bakiji yadda nikejin wani sanyiba na zan tafi gida inga Ummitana wlh”.
“hmm nima haka wlh duk na gaji da garinnan kawai so nike naganni a gida”.
nan sukaita hirarsu har jirginsu ya sauka suna fita suka hau motocin dasu Abdallah sukazo ɗaukarsu dasu suka fara tafiya Abdallah yace”wai gaskiya karatu ba daɗe Aunty Hafsat kingako yadda kuka rame kuwa karma bunburu taji labari kallarta duk yadda ta faɗa”.
murmush Al’ameen yayi tare da cewa”wacece bunburu kuma aiba bunburu anan ko Teemana”.
ƙasa Fatimah tayi saboda kunyar Al’ameen dakyar ta iya cewa”wlh kuwa ƙila dai Billynsa ce bunburun”.
dariya gabaki ɗaya suka fashe da ita Hafsat tace”gaskiya kuna shagalinku wlh ni wata irin yunwa nikeji”.
“kaji kai me karemusu tokaji dai abinda sukace wai yunwa sukeji tinkafin mu ƙarasa”.
“nagani na yarda amma ni banda gimbiyata”.
yaƙarasa zancensa tare da kallon Fatimah ta mirrior sunata hirarsu har suka ƙarasa suna yin ƙoƙarin parking motocin F2 na shigowa suma parking space suka nufa gaban Hafsat ne yabada damm jikinta yahau rawa a zuciyarta tace”to waini ina ruwana dashine da har zanji wani iri idan naganshi”.
wata zuciyar ce tace”kiyi kamar baki ganshiba kiyi harkokinki yadda kikeyi”.
nanta buɗe murfin motar ta fita Fatimah ma fita tayi suka jera Hafsat na kwance niƙab ɗin fuskarta F2 dake magana dasu Abdallah ne ya kafeta da ido ta cikin glass ko ƙiftawa bayayi gani yayi tana kwancewa ɗan kwalin doguwar rigarta ya zame dogon gashinta yafara bayyana waigawar da zatayi taga wayam ba Fatimah hangarta tayi gurinsu F2 suna murnar haɗuwa da sukayi taɓe baki Hafsat tayi tare da cewa”kace gurin wancan mara tarbiyyar kika tafi kenan”.
ɗaga kafaɗa tayi alamar meye ruwanta ta shige cikin gida.
F2 ko tin fitowarta ya kafeta da sexy eyes ɗinsa dake manne cikin glass su Fatimah na lura dashi Abdallah ya kalli Fatimah yace”ƴar ƙanwata gwara da kikazo da ƙawar nan taki wlh naji daɗi yanzu zan kira Hafiz na faɗamasa tare kukazo da amaryar tasa”.
wani irin tuƙuƙin baƙincikine ya turniƙe F2 yaja wani tsaki yace”sweetheart mushiga cikiko?”.
“toh Hamma”.
yayi gaba a zuciyarsa yace”idan na tsaya jin wannan kalaman yaronnan se zuciyata tayi bundiga”.
ya juya yayi gaba Fatimah ta suka haɗa ido da Abdallah sukayi dariya sannan sukabi bayansa Hafsat na shiga ta samusu Ammi duk a falo rungumeta tayi Ammi tace”nayi missing ɗinki daughter”.
“nima haka Ammina ina yini”.
“lafiya ƙlau daughter ya karatu”.
“Alhamdulillah”.
Aunty Fido ce tace”wato daughter anga Ammi mu anmanta damu zan kamakine zaki dawo hutu lokacin basu Ammi maga yadda za’ayi inkulaki”.
dariya Hafsat tayi tace”ayi haƙuri Aunty Fido tuba nike ina yininku”.
“lafiya ƙlau ya karatu”.
“Alhamdulillah Ummita koki kulani”.
tafaɗa cikeda shagwaɓa F2 dake shigowa ne mamaki ya kasheshi a zuciyarsa yace”Abdallah kuma yace ƙawar Fatimah naga kuma se shagwaɓa takeyiwa su Momy baradai muji”.
yana wannan zancen yaji Ummita tace”ni yanzu mijinkine ɗana bakeba tin wuri kitafi ki nemi Momynki ko Farouk?”.
ƙara shiga tinani F2 yayi a zuciyarsa yace”innalillahi wa’innah ilaihir raji’un dama tanada aure to wanene mijin nata inko hakane bansan irin halinda zan tsinci kainaba”.
jiyayi Ummita tace”kaikuma Son ina maka maganar matarka bata girma kayi shiru dani ko bayanta kaima kabi”.
ƙaƙalo murmushi yayi tare da cewa”a’ah Ummita na nina isa na goyi bayanta bayan inadake”.
yafaɗa tare da sakin wani murmushi yaƙarasa kusa da Ummita ya zauna tare da zame glass ɗin fuskarshi yasaki wani ƙasaitaccen murmushi yashiga gaida su Ummita ansawa sukayi Hafsat ko tin shigowarshi falon ta ɗauki wayarta tashiga dannawa tana chart ɗinta dasu Billy tana zabga murmushi Ummita ce tace”keeeh bakiga mijinki bane koki gaidashi banason sakarci”.
cono ɗan ƙaramin bakinta tayi kamar batason yin magana tace”ina yini”.
seda yaja lokaci cikin yanga yace”lafiya ƙlau ya school”.
wani takaicinsa ne yakama Hafsat ta miƙe tare da cewa”Aunty yunwa nikeji”.
“toh kije dining aiga abincinku can Fatimah ku wuce kuci kuma favorite food ɗinku aka yimuku.
“wow Aunty kice zamuci da yawa kenan Aunty Hafsat ko a U.k bata wani cin abinci tinda mukaje waiba daɗi”.
“toh ai yanzu sekuje kuci”.
nansuka tafi Hafsat ko se cika take tana batsewa ta wuce dining Ummita ce takalli Farouk tace”mushiga ɗaki ko Son muyi hirarmu”.
“eh Ummitana domin akwai magana”.
“toh muje”.
nansuka shiga bedroon ɗinda Ummita take suna tafiya Aunty Fido tace”gaskiya Ammi da akwai matsala yanzufa kamarya gane matarsace”.
“eh to idan ya gane basemun barshi ya gantaba tinda yau duk zamu ɗunguma mutafi 9ja kawai se Hajjo ki wuce da ita gidanki kinga ai ze ta nemanta ba tare daya san inda takeba”.
“aiko Aminiyata kin kawo shawara kamar yadda ya wulaƙantata dole shima seya gane kurensa wlh”.
nansuka yanke shawarar yin haka.
Suna shiga suka zauna gefan gado Ummita tace”Son inajinka faɗamun maganar”.
sosa ƙeya yayi cikin inda-inda yace”amm dama abinda ban ganeba dama Hafsat matata ce?”.
murmushinsu na manya Ummita tayi haɗe da cewa”eh matarka ce wadda Ammi ta nemamaka aurenta dama baka sani bane?”.
a zuciyarsa yace”Alhamdulillah Allah na godemaka aida nasan irin wannan matar Ammi ta auramun da tini ina 9ja na huta da ciwon marar nan dake damuna ƙilama inada yarinya yanzu a ciki”.
wata zuciyarce tace”to ammafa kamar akwai matsala ta ina zaka fara da ita Hafsat ɗin naga se wani shashshamaka ƙanshi takeyi gaskiyane Ammi dole dana kiraki kibani shawara kice ƙila da akwai abinda ya taɓa haɗamu amma kuma ni ai ba abinda ya taɓa haɗani da Hafsat sede Ammi dana yiwa wannan maganganun ina ganin kamar Hafsat bata saniba”.
yana cikin zancen zuciya yaji Ummita tace”Son lafiya ka shiga duniyar tinani haka”.
wani ƙasaitaccen murmushi ya saki tare da cewa”Mum bakomai bara naje na dawo”.
“toh seka dawo”.
nanya miƙe ya fita samu yayi ba kowa a falo saɓanin da akwaisu Ammi da Hajjo zama yayi ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana smiling Fatimah dake laɓe ce ta fito kamar zata wuce tace”Hammana lafiya naga kana murmushi”.
“bakomai sweetheart wani abun kika gani zubomun Jus”.
“toh Hamma “.
tafaɗa tana aje wayarta a kusa dashi ta tafi bayan tafiyarta kiran Al’ameen yashigo wayar kallon wayar yayi ya miƙa hannunsa ya jawota tana tsinkewa yaga wani haɗaɗen hoton Hafsat tasha wanka akan screen ɗin wayar murmushin gefan baki yayi yakai wayar daidai bakinsa ya sakarmata kiss ya buɗe wayar yashiga galery ɗin Fatimah duk ya tura hotunan Hafsat a wayarsa yana gamawa kiran Hafsat na shigowa wayar Fatimah ganin hotonta nanya haddace number ya aje wayar Abdallah dasu Fatimah dariya sosai sukasha sannan Fatimah tace”gashi Yayah kayi haƙuri na daɗe ko”.
ansa yayi tare da ƙara haɗe girar sama data ƙasa yana mazurai shi ala dole me aji sakkowa Hafsat tayi daga ita se ƴar riga mara hannu da ɗan wando iya guiwa ba tare data kula da F2 dake falonba cikin masifa take cewa”Fatimah! Fatimah!! waike meyasa kikeda delay ne kinsanfa anjuma zamu………”.
maƙalewa maganar tayi sakamakon ganin F2 da tayi shiko F2 yana cikin shan lemonsa yana ganinta a haka ya shaƙe yashiga tari Hafsat ko se lokacin ta lura da kayan jikinta ta wani dake tace”Fatimah bakya kyautamun kinja na fito a haka ƴan sa ido suna kallemun jikina”.
taƙarasa maganarta cike da takaicin F2 Fatimah ko dariya ke cinta ganin yadda F2 daka ganin Hafsat ya shaƙe Hafsat kuma nata uwar masifa dakyar ta danne dariyarta tace”sorry Aunty dama Yah Abdallah ne yace infaɗamiki ki turamasa da hotunanki”.
“toh”.
tafaɗa a takaice ta juya ta shige ɗaki F2 ko dakyar ya dena tari idanunsa suka kaɗa sukayi ja kishi na cinsa a zuciya yashiga danna wayarsa kamar gaske.