HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Tana komawa ɗaki ta kalli Furera tace”sis ɗina meke damunki ne naga duk kin rame”.
“hmm bakomai kuma Aunty Hafsat gaskiya kin ƙara kyau wannan wani yaganki seya ɗauka balarabiya ce”.
“hmm kedai bakya rabo da zolaya ki ƙarasa haɗamana kayan bara na saka wannan riga da siket ɗin na atamfar nan naɗan dafa ruwan zafi”.
“toh”.
nanta saka riga da siket ɗin a jikinta sunɗan kamata kaɗan shape ɗin jikinta dukya bayyana ta ɗaura ɗan kwalinta ture kaga tsiya ta fita kitchen tashiga tasamu Ashwariy na ƙoƙarin haɗa abincin dare tace”sannu Mamah da aiki”.
“yauwa ƴata an dawo lafiya”.
“lafiya ƙlau bara naɗan dafa ruwan zafi”.
“a’ah kibari na dafa dakaina ina missing ɗin shiga kitchen”.
“toh shikenan”.
nanta fita tabarta ɗaura tukunya Hafsat tayi ta zuba ruwa tana ƴan waƙe-waƙenta taji wani daddaɗan ƙanshi ya daki hancinta lokaci ɗaya ta lumshe idanunta jitayi kawai an runguneta ta baya jin tattausan hannunsa tayi ya taɓa gefan fuskarta lokaci ɗaya wutarta ta ɗauke waigar da ita yayi suna fuskantar juna yayinda numfashinsu ya haɗe dana juna ya sakarmata kiss a gefan fuskarta lumshe ido tayi lokaci ɗaya ta buɗesa akan F2 da idanunsa suka canza kala sukayi jawur dasu yashiga shinshina wuyanta zuciyarta ce tashiga cewa”lallai Hafsat bakida zuciya kinmanta da kece jahila mara ilimi baƙauya mara tarbiyya karki tsaya kwarjininsa yasa kikasa rama duk abubuwan daya yimiki koba komai kya kwaci ƴancinki a gurinsa yasan kema kinada daraja ba irin matannan bace da suka ruɗe akansa”.
saurin dawowa tayi hayyacinta lokaci ɗaya wani ƙarfi yazomata ta hankaɗeshi tare da cewa”meye haka karka ƙara gisgirin taɓamun jiki da wannan hannun naka mara tsarki wanda ya saba taɓa ƴan bariki watsatsu marasa tarbiyya”.
lumshe ido yayi yayinda yakejin kalamanta namasa ɗaci a zuciyarsa yashiga binta tana baya har takai ƙarshen bango da muryarta kamar zatayi kuka tace”meye hakan nifa banson iskanci”.
murmushin gefan baki yayi har seda beauty point ɗinsa suka lotsa a hankali yace”iskancin zan koyamiki kinga semu zama ɗaya”.
yafaɗa tare dakai hannu ya kashe gas tare da ɗagamata gira ɗaya yakai hannu ta bayanta ya jawota ya haɗe ƙirjinsa da nata wata ajiyar zuciya suka saki a tare yayi saurin haɗe bakinsa da nata yashiga bata kiss bana wasaba seda yayi me isarsa sannan ya saketa jiki na rawa da gudu tabar kitchen ɗin tana cewa”bazan taɓa sonka ba dolenka kabani takardata danni bazan iya zama da mara tarbiyyaba”.
taƙarasa zancenta tana ƙunƙunai dariya F2 yayi tare da cewa”gaskiya komai naki na dabanne I love you my angel saboda ruɗu anmanta da tea ɗin da ake dafawa”.
ya wuce ya tafi yana murmushi yana tino irin taushin leɓenta ɗakin Ammi yashiga bakinsa ɗauke da sallama ƙasa-ƙasa seka kasa kunne zakaji Ammi dake zaune kan sallaya tana lazimice ta kalleshi cikin kulawa tace”lafiya Son”.
“lafiya ƙlau Ammi dama tambayarki zanyi”.
yafaɗa yana sosa ƙeya alamar kunya murmushi Ammi tayi tace”inajinka”.
sauke numfashi yayi sannan yace”Ammi dama Hafsat itace wadda kikace kin nemomin aurenta?”.
“a’ah wacce irin Hafsat kuma ba ita bace waccan tin lokacin dana faɗamaka kace bakasonta akabar zancenta wannan ai itace wadda aka sakamata rana da Hafiz abokin Abdallah meyasa ka tambayeni?”.
lokaci ɗaya jikin F2 yayi sanyi yace”bakomai naɗauka dai itace”.
“ok ko sonta kakene”.
“a’ah tambayadai nayi”.
murmunshinsu na manya Ammi tayi tace”okay”.
Ammi ko a zuciyarta tace”wato kai sarkin girman kai bazakace kana sontaba aiko zaka gane kurenka dan seka gane shayi ruwa ne koda zanbaka matarka yaro”.
nanya miƙe ya fita ba tare dayayiwa Ammi sallamaba yana fita waje yashiga motarsa drivernsa yajasa aka kaishi wani ƙaton mall ya siyo wasu teddy bears fararare masu kwalliyar red da flower rose yashiga mota a zuciyarsa yace”ba Hafiz ba ko wane sena sanarmata da abinda yike zuciyata yau na huta aiba kalar matar data dace dashi bace kalarmuce to amma Ummita meyasa tacemun matata ce kuma ƙila wasa takemun tunda Ammi ba alamar wasa a fuskarta ammafa da harnaji daɗi ashe akwai rina a kaba ba Hafiz ba ko waye bazan janyeba inaji ina gani”.
yayita surutansa a zuciyarsa sannan ya tafi yashiga mota aka jasa.

Hafsat ko a gigice ta shiga ɗakinsu Fatimah dake zaune tana wayace tace”lafiya Aunty kika shigo kamar wani ya biyoki”.
waigawa Hafsat tayi taga ba F2 a ziciyarta tace”gaskiya mutuminnan bashida kunya Allah ya isana bakina bara naje nayi brush yasamun wannan ƙazamun bakinnasa da yasha gwagwarmayar ƴan bariki”.
ko takan zancen Fatimah batabiba tashiga toilet tayita yin brush tana hawaye tana yiwa F2 Allah ya isa seda tayi brush 4 sannan ta fito tana Allah ya isa ta wucesu Fatimah shinshina kayanta tayi taji ƙanshin turarensa sukeyi jitayi wani irin takaicinsa yaƙara kamata ta wuce gurin drower ta ƙarasa ta cire kayanta tana tsaki ta canza wata gown tana cikin yafa mayafin rigar Aunty Fido ta shigo kallonsu tayi tare da cewa”kuna nan kuna hira sunfita fa ku ake jira”.
“toh Aunty”.
nansuka fita har bakin mota Aunty Fido ta rakasu suka hau suka tafi.

Da kayan ya fita a hannunsa saboda saitine se kyalli sukeyi yashiga main falon gidan yana ƴan waige-waige baiga kowaba hakan yasa ya aje kayan a gefan labule yadda bame gani ya haye sama Aunty Fido dake kwance kamar bacci takece tayi murmushi ta miƙe ta duba abubuwan daya shigo dasu tace”wato dai mutumin andai gama kamuwa shine harda siyo flower ina jiyemaka dan yanzu zaka gane kurenka”.
tana wannan zancen taji kamar yana tahowa hakan yasata saurin komawa ta kwanta kallonta yayi yaga tana nan a yadda yabarta hakan yasashi ɗaukar kayansa ya fita yasaka a mota dariya sosai yabawa Aunty Fido ya dawo yaƙara shan kunu yace”Aunty ina Ammi takene”.
Aunty Fido miƙewa tayi zaune tare da yin hamma kamar me bacci tace”sun tafi 9ja kasan jibi za’ayi walimar nan nima gobe zan tafi shiyasa ma nabadasu Anun aka tafi dasu”.
“ok”.
a zuciyarsa yace”aiko zuwa 9ja yakamani dan yau a darennan sena faɗamiki sirrin zuciyata Hafsat dukda wancan sakaran Hafiz ɗin na niyyar yimun kutse dolene nayimasa hankali wlh”.
seda yaɗan daɗe sannan ya miƙe tare da cewa”zan wuce Aunty”.
“ina badai U.k ba daiko”.
“can zan koma”.
“bazaka walimar bane”.
“eh inada patient ne”.
“okay tom shikenan”.
nan yayimata sallama yafita yashiga mota driver ne yace”ranka shidaɗe ina mukayi?”.
a taƙaice yace”Airport”.
“toh”.
nanya jasu suka tafi suna zuwa yashiga Jet ɗin 5DBCP ya nufi 9ja.

Suna isa Aunty Fido takira Ammi tasanarmata da komai dariya Ammi tayi tace”ai zega tsiya yanzuma haka ma Hafsat tana Adamawa kafin ya ganta zesha wuya”.
“yauwa Ammi ammafa ni harya fara bani tausayi harda ƴar flowers ɗinsa”.
“hmm kinga Firddausi karki karyamun budget domin so nike ta dalikinta yasamu HASKEN RAYUWARSHI koba komai ze natsu”.
“toh Ammi se anjuma”.
nansukayi sallama takashe wayar Ammi takira Hajjo ta sanarmata da komai suka shiga tsara komai da komai.

Suna isowa 9ja Jet ɗinsa na sauka yafara sauka daga matattakalar jirgin shaƙar iska yayi ya lumshe ido ya buɗesu yayinda abubuwa da yawa suka dinga faɗomasa a ransa sauka yaƙarasa yi yashiga motar abokinsa doctor Fu’ad suka nufi masarautarsu!!!!!!

Dan Allah idan kin karanta kiyi sharing zuwa groups ɗinda kike banida lafiya bazan iya share ba wannan dakyar na ƙarasashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button