HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

nan M. Shamsu yafara jawomata suratul Nisa’ih tashiga reromasa cikin zazzak’ar muryarta me sace zuciyar me sauraro har ya dakatar da ita bemata gyara ko d’ayaba nan M. Jalaludeen shima yajamata suratul Maryam nanma tayi bako gyara d’aya sannan aka kawomata suratul Lukman tayi tangimi nanma tayi sosai harseda sukaji Kamar karta dena sannan akaimata tambayoyi ta amsa sannan aka sallameta ta koma ta zauna nan akaita kira kowa yayi sannan a fitar da sakamakon M. Jalaludeen yafara addu’ah sannan yace”zamu fad’i sakamako insha Allah yanzu saboda gobe had’a first position suyi suma a fitar da gwani”.
nan yan aji aka shiga tafi murmushi yayi tare da satar kallon Hafsat da cikinta ya d’uri ruwa yayi sannan ya k’ara had’e rai yace”wadda tayi na talatin da bakwai itace”.
sekuma yayi shiru nan kowa yayi tsit dariya yayi sannan yacigaba da magana yace”shine Abdulmumin Abubakar”.
nan akai kabbara sannan yacigaba da Kira har yazo kan goma ba’ah fad’isu Hafsat ba nan yacigaba da Kira ana shida aka kira Billy ana biyar aka kira Zully nanya cigaba da Kira har yazo kan na biyu wadda mutane suke zaton Hafsat ce ko Habibah katsam yace”Habibah mukhtar Bala ce tayi na biyu sekuma gwarzuwarmu Hafsat Ibrahim itace tazo ta d’aya”.
yak’arasa maganarsa yana mai fad’ad’a murmushinsa ihu class d’in aka d’auka dan ba k’aramin son Hafsat sekeba nan Billy suka rungume Hafsat suka shiga murna abinsu.
B’angaren Habibah ko M. Jalaludeen na gama fad’a taji wani k’ullutun bak’in ciki ya tsayamata jitayi Kamar ta kwarma ihu tayi kotaji dad’i a zuciyarta jitayi wani hawayen bak’in ciki ya zubo sharr dafata Jamila k’awarta tayi tare da cewa”dama nasan wlh bazasuyi adalciba ita zasuba ki share hawayenki kar a gane Muna cikin damuwa dole muyi maganinta”.
ta k’arasa zancenta tare da sharema k’awarta hawaye ba tare da kowa ya luraba suka fice aiko karaf a idon Zully tab’a Billy tayi da sauri tare da cewa”kingafa ‘yan bak’in ciki sede a mutu domin insha Allahu sweetheart itace zataci na makarantama”.
“insha Allahu kuwa a hakadai za’ah k’are tayaya mutumko zeci gaba yana hassada”.
nan dai sukaita habaicinsu ‘yan class nata murna.
Ana tashi ta nufi titi sa’ah ta had’uda wani mutum d’an arzik’i zeyi hanyar getso nan ya tsaya dakyar tahau dan Ummita ta hanata shiga motar daba ta hayaba Koda sukaje ya sauketa kwanar d’annafada ta k’arasa a k’afa har rugarsu Kamar yadda ta saba a k’ofar gidansu ta samisu Furera anata gulmar da aka saba tazo gabda zata wucesu taji Bara’atu na cewa”bakuga yau har wani murmushi akeyiba anyi kasuwa gurin dadin da akayi kenan”.
tanajinsu dukda bataji dad’in abinda sukace mataba amma ba abinda ya canza daga annurin fuskarta Tana isa Kamar kullum ta wuce gurin bishiya tayiwa matan k’annan Bappinta sannu tabiya d’akin Iyah dan tayimata sannu tana zuwa ta tarar da tanacin tsire duk’awa har k’asa ta gaida ita murya a dak’ile tace”lafiya ga kaya nan ki kwashesu ki wankomunsu mikomata Furera”.
kallon Furera tayi da se zunb’ura baki takeyi suna had’a ido tace”to mayya meye kike kallona “.
“yiki bata dan karta cinyemun danba bata tsirennan zanyiba”.
murmushi kawai Hafsat tayi tare da cewa a zuciyarta”nidai ba Wanda ze b’atamun rai Dan yau ina cikin farin ciki”.
tana wannan maganar taji an watsamata kaya saurin dawowa tayi daga zancen zucin da takeyi ta kwashe ta nufi b’angarensu Tana shiga ta samu yayanta Aminu da Ummita suna zaune suna hira k’arasawa tayi da kaya ta aje toshe hanci Aminu yayi tare da cewa”kedai anyi sakarai wlh wato har yau baki dena amso wa’innan kayan garadan masu fitsarin kwanceba ko”.
dak’uwa Ummita tayimasa tare da cewa”kaidai Aminu bakajin magana Ina ruwanka watarana se labari mahak’urci mawadaci insha Allahu Mamana seta zama abin kwatance naga kina farinciki meya farune tawan”.
murmushi Hafsat tayi tare da k’arasawa ta aje kayan gefe dukda gajiyar da takeji taje ta k’arasa gurinsu Ummita tabasu labarin nasarar data samu suna wannan Bappi ya shigo nan sukaita murna bayan magariba tana idar da sallah ta wuce rafi ta wanke kayan ta shanyasu ta koma gida abinta.
BAYAN KWANA BIYU
Zaune suke a class suna hira sega wata Malama ta shigo shiru sukayi tace”kufita Assembly”.
amsawa sukayi ta fice kallon Hafsat Billy tayi tare da cewa”insha Allahu Mrs Ahmad kece da nasara “.
murmushi Hafsat tayi tare da cewa”wlh kidena cemun wani Mrs Ahmad banaso Allah dai yasa ngd bestyna”.
“mu ai inkika cemun Mrs F2 dad’i zanji sosai dan k’ila har kyauta zan baki”.
“Wlh “.
dukda tana cikin tinanin taci hakan be hanata darawaba saboda k’awayena nata sun zurma sosai a zuciyarta tace”Allah ya shiryamunku”.
jitayi Billy ta katseta ta hanyar cewa”mufita insha Allahu makarantarmu keda nasara infara ganin sweetheart a duniya ana karatu”.
“Amin “.
nan suka wuce abinsu.
Shirune ya d’auki gurin filin Assemblyn inda gaban Hafsat keta faman dukan uku-uku principal ne ya kalli d’alibai tare da cewa”Alhamdulillah ala kulli halin ina tinanin kowa yasan ankara da hazik’ar d’alibarmu Hafsat Ibrahim a cikin musabak’ar da aka gudanar ta makarantu inda za’ah fitar da Wanda ze wakilci jiha ko to ina mai sanar daku cewa!!!!!!
More Votes and Comments
More typing
Plz share
Daga Alk’alamin ‘yar mutanen mutanen Gwarzo???? HASKEN RAYUWATA
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
http://ww.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dLOe_AqkiQ
PAGE 0️⃣7️⃣➡️0️⃣8️⃣
"Gwarzuwar d'alibarmu hazik'a Allah yabata nasarar samun matakin farko wato ina nufin ita tazo ta farko a cikin musabak'ar".
Kabbara gurin yad’auka had’eda murna da farinciki Hafsat ko wani hawayen farin cikine suka zubomata k’ara rungumeta Zully tayi tare da cewa”Sweetheart ba kuka ya kamata kiyiba murna ya kamata kiyi Zaki wakilci jahar Kano kigodema Allah da wannan baiwa da yayimiki”.
kai ta gyad’amata cikin muryar kuka tace”Billy kukan farinciki nakeyi da irin ni’imar da Allah yayimun abinda ban tab’a zataba hak’ik’a kud’in k’awayene nagari masu k’arfafawa mutum guiwa idan yana cikin karyewar zuciya Allah yabarmu tare”.
ta k’arasa tare da sakin hawayen farinciki Zully cetayi murmushi tare da cewa”Hafsat ai anrigada anzama d’aya Mrs Ahmad”.
jitayi wata dariya tazomata seda ta dara sannan tace”kudai kuna fama wlh Allah ya shiryamunku”.
“Ameen wlh kina bamu mamaki irin yadda kika maidamu sakarkaru kika sani ko Allah ya kawo silar had’uwarmu Kuma ai abun na Allah ne”.
Hafsat ganin k’awayen nata sunyi nisa basajin kira yasata cewa”aini zanfi kowa farin ciki saboda aminaina zasuyi sanadiyyar shiryuwuwar Dan Adam zuwa ta farkin Allah”.
wani dad’ine ya mamaye zukatan su Billy suna niyyar magana sukaji ana Kiran Hafsat Assembly zata amshi kyaututunanta nanta tafi abunta cikin nutsuwa abinta.
Habibah dake tsaye tana jin nasarar da Hafsat ta samu taji wani abu ya tsayamata ga Kuma ‘yan makaranta da suka d’auki kabbara ganin irin tarin masoyan da Hafsat take dashine yasata jin wani jiri Jamilah ce tayi saurin rik’eta tare da cewa”gaskiya wannan ‘yar iskar yarinyar ta cimu wasa dole musan abinyi domin bazamu zuba ido Muna gani ta tafi wannan musabak’ar ba dole mu d’auki mataki “.
“nimadai abinda nake gani kenan domin bazan bari duk burin danaci akan masoyina da rayuwata tazo ta ruguzamun ba to Amma ke me kike ganin yakamata muyi akanta”.
murmushi Jamilah tayi tare da cewa”matso da kunnenki kiji yadda za’ai”.
“toh”.
nanta matsa ta rad’amata wata magana wadda nima kaina Real eeshow bansan me suke cewaba murmushi Habibah tayi tare da cewa”aiko wannan yayi wlh yanzu yaushe zamu yi”.
“A’ah kibari se gobe intazo makaranta”.
nan sukaita kissufa irin muguntar da zasuyi mata.