HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Ruƙayya na fita layin ta haɗu da Goje jikinsa na ɓari kamar mazari harda hawaye wujiga-wujiga dashi kama haɓa tayi tace”lafiya Goje naga duk kafita hayyacinka ko wani abun ne yafaru naga har kuka kakeyi”.
“inafa lafiya Ruƙayya wannan aikin dana yimuku na matarnan data mutu yanata sani a tasku yanzu haka banida komai duk shagunana sun ƙone anrasa meke haddasa wutar hakanan ake ganin wutar kuma bata taɓa shagon kowa se nawa danaje gurin wani Sheikh seyike tambayata menikeyi nabashi labarin rayuwata anan ne yike shedamun abinda kuka sakani nayiwa Gimbiya Khadija ke bibiyata inyi gaggawar zuwa nabawa yaranta haƙuri shine kawai zansamu salama nakuma faɗamusu ƙarya nike ga tsinanniyar data sakani gaskiya Ruƙayya kun kwareni yanzu matsiyacina nike banida ko sisi komai nawa ya ƙone yauma bansan inda zan kwanaba”.
sauke numfashi Ruƙayya tayi tace”gaskiyane Goje nima rannan ta kaini bango ta turani gurin boka Matsatsaku na anso mata magani akan ɗanta a hanyar dawowa nayi Accident aka kaini Asibiti likita ya kirata ya sanarmata dandanan segata tana zuwa yike shedamata da za’ah yimun aiki a ƙafata na million uku tabada kuɗin buɗar bakin matar nan setace bata dasu kasanta da son kanta se babban ɗan gimbiya Khadija ne ya biyamun Farouk nikuma na rasa dame zan rama kawai rannan seta kirani tace najemata gurin boka wata dabara ta faɗomun na amsamata to yanzu na anso mata maganin na kawomata kabari se nanda kwana bakwai zata gane kurenta kazo muje mubasu haƙuri ko ma samu rahamar ubangijinmu temakon da yaron yayimun ne yasa na dawo hanya na gane na tafka babban kuskure shine nima danaje gurin bokan na yanke shawarar temakon yaron da mahaifinsa daga sharrin wannan makirar matar”.
“toh Ruƙayya Allah yakaimu semuje muyita tuba ga mahaliccinmu”.
“hakane rana itayau ɗin mayi waya”.
“toh”.
nansuka rabu kan zasu haɗu bayan sati ɗaya.
BAYAN KWANA BAKWAI
F2 duk ya fita hayyacinsa bashida burin daya wuce yaga Hafsat ganin ba alamar ganinta yasashi yanke shawarar tafiya yaje ya sanarda 5DBCP halinda yike ciki cikin shirinsa na tafiya ya nufi part ɗin Ammi ganin bata falo harya juya wata kuyanga tace”ranka shidaɗe tana ɗakinta”.
“okay”.
ya wuce ya nufi bedroom ɗinta samunta yayi akan sallaya tana lazimi da alama dai walaha ta idar zama yayi gefan gado yana jiranta tana ƙarasa murmushinta tace”Son ina zuwa haka naga ansha kwalliya”.
cikin sanyaya murya wadda ke nunida yana cikin tsananin damuwa yace”zankoma U.k zanyi wani aiki idan nasamu lokaci zan zo naganku”.
“toh Allah ya tsare Allah kuma yasa dagaske kake zaka riƙa zuwa”.
“zanzo insha Allahu Ammi”.
“toh Magajin Malam tinda kazo kaje kun gaisa da mahaifinka kuwa?”.
lokaci ɗaya yanayinsa ya canza yace”a’ah banjeba”.
“okay to yanzu idanka fita ka biya ka gaidashi”.
“toh”.
yafaɗa a daƙile ya tafi yana fita be biya yagaida Maimartaba ba kawai yahau mota aka nufi airport dashi tashiga jirginsu Pilot ɗinne yace”Oga ina zamuyi”.
jiyayi kawai bakinsa ya furta” muje Adamawa nayi sallama semu wuce”.
“okay sir”.
nansuka nufi Adamawa.
Suna isa ya sauka yashiga motar wani abokinsa suka nufi masarautarsu Hajjo suna isa sukayi parking suka tafi part ɗin Barkindon Adamawa samunsa sukayi yana zaune a haɗaɗɗen falonsa kashingiɗe yana lazumi zama yayi kusa dashi tare da cewa”tsoho me ran ƙarfe anata lazumi kenan kaida kaƙi ka tunkiyi ƙasa kabarmu mu sake ko”.
dariya yayi tare da cewa”kaikuma meran roba”.
“hhh antashi lafiya”.
“lafiya ƙlau ya mutanen gidan naku”.
“lafiya ƙlau ina tsohuwar take”.
“tana lafiya baka biya ta part ɗinta bane”.
“eh kaina fara zuwa na gaisar”.
“kace na ciri tuta “.
“eyi”.
nansuka gaisa da Abdul’jalal suka ɗanyi hira sannan sukayimasa sallama suka tafi sosai Barkidon Adamawa yaji daɗin ganin yau jikansane hadda dariya.
Suna shiga part ɗin Hajjo ba kowa se masu aiki dake gyaran ɗakunan zama sukayi a falo harya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya kalli gurin wani corridor wanda glass aka saka a rife gurin amma idan mutum yanason shaƙatawa yana iya zuwa gurin ya zauna gani yayi kamar mutum a gurin hakan yasashi tashi bugun zuciyarsa yashiga ƙaruwa harya isa gurin yana buɗa labule ya hangeta tasha wankan doguwar rigar material pink ba ɗanwali akanta gashinnan yasha gyara ta ɗora ƙafa kan kujerar dake passing ɗinta ta ɗaura system kan cinyarta tanata danne-dannenta kunnenta kuma ta tosheshi da earpiece wani irin sanyine ya luluɓeshi a hankali ya mayar da labulen yakoma ya zauna ya shiga wayarsa ya tura message 10mins aka kirashi ba tare daya ɗaukaba yace”Abduljalal ina zuwa”.
“okay seka dawo”.
nanya tafi be daɗeba ya shigo hannunsa ɗauka da wata jaka ya wuce ya buɗe labulen a hankali ya zuge ya shiga ya mayar ya rife ba zato taga mutum yayi kneeldown a gabanta hannunsa riƙeda rose flower yace”Hafsat inasonki ina ƙaunar bazan iya rayuwa inbabukeba ki tausayawa rayuwata in narasaki banajin zan cigaba da rayuwa kisoni koda rabin sonda nikemikine tin randa nafara ɗora idona a kanki naji duk duniya banida wani burin daya wuce naganni gani gaki a inuwa ɗaya akanki nasan tinani akan mace dan Allah kisoni kona samu sukuni a rayuwata”.
Tinda yafara magana ta tsaya take kallonsa a cikin ranta tana cewa”Allah na godemaka daka nunamun ranarda Farouk duk ajinsa ya zubar ya duƙamun
amma gaskiya niɗin me sa’ace wow jinike kamar nayi rawa dan daɗi ammafa idan nabada kai bori yahau da wuri ze rainani seya gane kurensa dan seyasan yacemun baƙauya jahila mara ilimi mara tarbiyya dole ne ya fuskanci hukunci”.
a fili kuma takai hannu ta anshi flower kamar abun arziƙi wani daɗine ya mamaye zuciyar F2 bazato kawai se gani yayi ta jefar da flower ta taketa ta mutsutsuketa cikin masifa tace!!!!!!
Votes and Comments
Plz share to others
_*Daga Alƙamun ƴar Muta???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME OF QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
PAGE 5️⃣3⃣➡5⃣4⃣
"Bana sonka bana ƙaunarka bana ƙaunar me ƙaunarkama mezakayi da jahila mara ilimi mara tarbiyya baƙauya to bari infaɗamaka F2 kake kowa bazan taɓa sonkaba na tsaneka igiyar aurenama dake kanka seka sakeni dan baka yimunba mara tarbiyya kawai a irin wannan shigar ta banza da kakeyi ko ina sonka sena dena tinwuri kaje ka nemi wayayya me ilimi ƴar birni irinka ka aura danni ba kalar matar daya kamata ka aura bace".
zata wuce fuuu ya kama gefan rigarta cikin kuka yashiga cewa”Hafsat kiyi haƙuri dukda kince bakya sona ni ina sonki ina ƙaunar ina fatan mu rayu da juna bazan sakekiba koda zan mutu da sanki bazan taɓa sakinkiba danaga wannan ranar gwara naga ranar mutuwata inasonki dan Allah kiyi haƙuri danasan ke Ammi ta auramun da bazan miki hakaba kitemakeni”.
su Abdallah dasu Fatimah dake ganin abinda yafarune jin kalaman Hafsat sukayi kamar ta daɓamusu wuƙa dukda abinda tacemasa sukaga beyi zuciyaba yakuma yimata magana wani tausayinsa ne ya kamasu Abdallah yace”Sweetheart yakamata muje mu taya Hammah bada haƙuri saboda ni a yanzu tausayi yike bani wlh”.
“nima haka wlh bakaji yadda naji tausayinsa ba saboda yadda su Hajjo ke gara kansa ko My Al’ameen”.
“wlh kuwa Sweetheart ɗina muyi wani abun”.
nansuka shiga corridor ɗin suma.
Hafsat na ƙoƙarin fisge rigarta kenan taji F2 yafara tari harda jini ya dafe gefen zuciyarsa luuuu yafaɗi ƙasa da gudu tayi kansa kafinsu Abdallah su ƙarasa tashiga jijjigashi tana kuka tana cewa”wlh ƙarya nike maka Farouk inasonka nima bazan iya rayuwa inbakaba kawai na rama abinda kayimun ne inka mutu nima mutuwa zanyi ku temakamun wayyo Allah na in narasaka nima mutuwa zanyi nashiga ukuna kutemakamun Abdallah”.
tana faɗa tana kuka tana aikin jijjigashi ganin haka bazemataba yasa ta kara kunnenta daidai saitin zuciyarsa taji shiru kuka ta sake fashewa dashi tayi saurin haɗe bakinta da nashi tana zuƙo numfashi Abdallah ne yayi hanzarin ɗakko ruwa ihun da Hafsat keyine yafito dasu Hajjo da sauran mutan gidan yayyafamishi ruwa Abdallah yayi be motsa ba hakan yaƙara bawa Hafsat tsoro tana kuka tana zuƙomasa numfashi idanta ya rife tana kai bakinta da niyyar zuƙomasa taji caraf yakama harshenta yashiga tsotsa kamar wanda yasamu lolipop tayi ta janye harshenta yaƙi bata dama tinowa datayi dasu Abdallah yasa hankalinta ya tashi dakyar ta zame bakinta a nashi tare da kaimasa duka ya goce a kunyace ta miƙe ba tare data kalli kowaba ta gyara rigarta cikin kunya saɗaf-saɗaf ta wuce dariya tabawa kowa na gurin haɗe rai F2 kamar bashine yagama kissin ɗintaba ya tashi zaune tare da dafe goshinsa yace”wash Abbuh na”.
mamakine yakama kowa na gurin saboda a sanin da kowa yayiwa F2 bayako gaida mahaifinsa Hajjo ce tace”Abbuh kuma “.
“eh Hajjo shi nikeson gani yanzu”.
“toh ka kirashi”.
Hajjo ta faɗa tana niyyar juyawa wayarta tayi ƙara ɗauka tayi tare da cewa”aminiyata yanzu Farouk ya faɗi mu munɗaukama wani abun ne yasameshi sekuma mukaji ya ambaci mahaifinsa abun yabamu mamaki”.
“aimuma yau munga abin mamaki saboda abinda nakira na faɗamiki kenan muma anan Muhammad be daɗe da farfaɗowaba shima yana miƙewa daga fada zeshiga gida ya yanke jiki ya faɗi ba abinda yike faɗi se Khadija da Farouk abun mamakinma neman Khadija yikeyi da dayanda za’ayi ki sanarwa da Maimartaba kuzo dan abun ba lafiya kuzo a zauna akwai abubuwa da zamu tattauna domin yanzu Muhammad alamu sun nuna ba’ah cikin hayyacinsa yikeba wlh”.
“toh shikenan bara na sanarma Maimartaba tinda ga jirginsu Farouku semu taho”.
“toh nagode”.
“yauwa bara na kira Zahra’u ta shiryomu taho saboda kinga ita Sa’adatu basu daɗe da tarewaba”.
“yauwa hakanma yayi”.
nanta kashe ta kira Aunty Zahra’uh bugu ɗaya ta ɗaga bayan sun gaisa tace”Idan Captain yana nan ki tambayeshi kiɗan rakani masarautar Kano yanzu Ammi takirani akwai matsala”.
“toh Hajjo bayanan bara na kirashi na sanarmasa kinsandai baze hanaba “.
“toh shikenan kiyi sauri a jirginsu Farouku zamu muje mu dawo yanzu nima zanje in sanarwa Abbih ɗinku”.
“toh”.
nanta kashe cikin sauri ta nufi part ɗin Barkindon Adamawa samunsa tayi a kashingiɗe yana karanta daily trust ƙarasawa tayi gurinsa cikin sauri ta zauna zare medical glass ɗin fuskarshi yayi tare da cewa”abar ƙaunata lafiya”.
nanta warwaremishi yadda sukayi da Ammi murmushi yayi yace”toh Allah dai yasa lafiya kije ku tafi”.
“toh nagode mijina abin alfaharina”.
nanta tashi taje ɗaki ta shiga shiri.