HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Cikin shiri tashiga ɗakin Hafsat daketa ɓoye-ɓoye Hafsat na ganinta tayi ƙasa da kanta dariya Hajjo tayi tace”Daughter dole ki ɓoye fuskarki man tunda kun gama zabgamana rashin kunyarku a tsakar gida ki shirya mutafi Kano sauri nikeyi”.
“toh Hajjo bara nasaka hijab ɗina”.
“toh yi sauri”.
nanta saka hijab ɗinta tanata ƙasa da kanta har suka fito falo gurinsu Abdallah ba wanda ta iya kalla haka suka ɗunguma suka shiga motocin da zasu kaisu Airport suka shiga Hafsat zata shiga motar Hajjo kenan Hajjo tace”wuce kitafi motar mijinki dan bazaki jawomunshi kuzo ku kashemun idoba”.
cono ɗan ƙaramin bakinta tayi tace”kai Hajjo ni bani da wani miji”.
“eyi bakida miji shiyasa harda yimana kuka wayyo mijina ze mutu Hajjo kin ɓacemun da gani ko sena yanke wannan bakin naki kamar na sheda”.
wucewa tayi tana cunkule rai tana ƙunƙunai harta isa motar da yike zata buɗe driver ya buɗemata shiga tayi tana ƙunƙunai shikuma ya rife yajasu F2 dake zaune ya lumshe ido kamar me bacci yanajinta tanata ƙunƙunanta tana zama yaji wani daddaɗan ƙamshin turarenta ya bigi hancinsa haka yasa ya buɗe idonsa ya saukesu a cikin nata da itama shi take kalla saurin ƙasa tayi da oily eyes ɗinta daketa maiƙo murmushi yayi ganin kunyarsa takeji hakan yabasa damar ƙaremata kallo yashiga duniyar tinani yaji ƙunƙunanta tana cewa”haka kurum aka turoni gurin wanda ba abinda ya iya sesa ido da kallon jaraba”.
dariya yayi a zuciyarsa ba zato sejinta tayi a jikinsa ya zame hijab ɗin jikinta yashiga shinshina bayan wuyanta jikinta ne yashiga rawa kamar ɗan mazari murya na rawa tace”dan Allah kayi haƴuri wlh bazan sakeba na tuba”.
yadda tayi maganar yakusa bashi dariya seya dake yace”bake mara kunyaba to yanzu ba wani hukunci da zan riƙa yimiki wa’innan abubuwan zan rinƙa yimiki a matsayin hukunci”.
murya kamar zatayi kuka tace”aibama zan sakeyimaka rashin kunyaba”.
dariya tabashi har seda ya dara hakan yasa Hafsat ta shagala da kallonsa ba zato taji yace”kyau nayimikine naga irin wannan kallon haka kinga wa’innan friends ɗin nawa inasonsu ki kulamun dasu sosai”.
yafaɗa yana nuna Boobs ɗinta wata irin kunyace takama Hafsat tayi saurin rife gurin da sauri tayi ƙasa da kanta ta zame jikinta a nashi ta zauna shiko ɗan gogan ko a jikinsa yayi mursisi abinsa kamar bashine yayi maganarba shirune ya biyo baya tsakaninsu yayinda kowannensu yashiga duniyar tinani har suka isa suka fita ba wanda yacewa kowa komai suka shiga jirgi se mimmiƙar da hijabinta take dayaɗan fara squeezing Hajjo dai na ganin ikon Allah nansuka zauna a kujera kusa data juna.

Suna isa Kano suka shiga motocin da Ammi ta aiko su ɗaukesu suka nufi masarutar suna isa sukayi parking Hafsat cikin tsiwa ta kalli F2 ta wani haɗe rai tace”gaskiya bazan iya zama da mutum me irin shigar ƴan iskaba kamar wani mace mutum harda wani ɗan kunne da sarƙa ga wani ɗan iskan zane-zane a jiki kamar kwarya ga gashi har wani kitseshi akeyi ga sittira in antashi sakata ƙirji a waje haba ina baze yiwuba ƴaƴana su tashi suga mahaifinsu wani iri haba ina ina mai baka shawara wannan rayuwar da kakeyi bata ɗan musulmi bace ai ita rayuwa kafin ayi dakai kakeyi da kanka koba danni ba ka temaka kadena wannan rayuwar koba komai ka mutunta addininka da asalinka kayi haƙuri gaskiya nike faɗamaka matsawar kana so nasoka irin sonda zakayi mamakinsa toh ka gyara rayuwarka ka fuskanci lahirarka na tabbatar Ummih da tana raye bazataji daɗiba dan Allah Farouk ka canza halayenka kayi haƙuri dan Allah karkace nayimaka rashin kunya gaskiya nike faɗamaka”.
sosai yaji kalamanta dukda idanunsa a rife yike zaka ɗauka bayajinta ta buɗe murfin ƙofa ta fita sauke numfashi yayi me zafi sannan ya furzar da iska me zafi ya buɗe motar ya tafi falon baƙi inda yaga su Hajjo sun shiga.

Samun Maimartaba sukayi a tsaye yakai-yakawo gurin yayi shiru kowa yana sauraren Goje da yike basu labarin abinda dukya faru dashi da sharrin da sukayiwa gimbiya Khadija yaƙara da cewa”dan Allah ku yafemun inbaku yafemunba bansan yadda zanyi da rayuwata ku temakeni kuyimun rai”.
Ruƙayyama zayyanemusu duk abinda suka aikata itada Fulani Zainaba taƙara da cewa”nima Maimartaba a shirye nike dana anshi hukunci daidai da abinda na aikata “.
Fulani Zainaba daketa gumi ce ta fashe da kuka tace”wlh ƙarya takemun mijina so take ta haɗani dakai wannan matar ba mutuniyar arziƙi bace”.
wani mugun kallon Maimartaba ya makamata tare da cewa”idan bakiyimun shiruba senazo nan na karyamiki wuya tsinanniya karya shiyasa banji daɗin haɗani aure da akayi dakeba dandai biyayyar mahaifi kuma Allah yagani Zainaba kin cutar da rayuwata dani Allah ya isa bazan taɓa yafemikiba kuma da kike cewa ba mutuniyar arziƙi bace keɗin itance “.
yaƙarasa zancensa tare da fashewa da kuka Ammi ma miƙewa tayi tabawa Maimartaba labarin abubuwan da suka faru tinkan gimbiya Khadija ta rasu har zuwa lokacin data rasu da rashin zuwa kaita da yayi wani kuka Sarki Muhammad ya fashe dashi yace”shikenan hankalinki ya kwanta tabarmiki duniyar tsinanna me halin karnuka”.
jisukayi Fulani Zainaba ta fashe da dariya tana cewa”kace ta mutu Allah ta mutu hhhhh ta mutu”.
tana faɗa tana soshe-soshe tana dariya nan tashiga faɗin irin miyagun abubuwan datayita aikatawa a cikin masarautar ganin alamun hauka a tattare da ita yasa Maimartaba yasa aka tafi da ita gidan mahaukata tanata cisgar gashin gabanta tana ci lokaci ɗaya tashiga yin wani mugun wari wanda bazakace ga irinsaba (Yah Allah ka kiyayemu da aikin danasani ka karemu da faɗawa irin wannan rayuwar ta zuwa gurin boka duk meyi ƙarshensa baze taɓa yin kyauba sannan gakuma rashin ansar sallar mutum harta kwana arba’in mutum yayi zuwan zomo kasuwa Allah ka karemu da karewarka ka kare gabanmu da bayanmu dan alfarmar sayyidissadati ).

Sosai sarki Muhammad yike risgar kuka jin munanan abubuwan da Fulani Zainaba tayi ta rabashi da matarsa farincikinsa sosai yabawa kowa na gurin tausayi suka share ƴan kwallolinsu F2 dake laɓe yaji komai ne ya share hawayensa yashiga sarki Muhammad na ganinsa ya miƙe tare da buɗemasa hannu alamar yaje kallon Hafsat yayi yaga shitake kalla ganin bashi da niyyar tafiya yasata ɗagamasa kai alamar yaje hakan yasa da gudu ya ƙarasa ya rungume Abbuhnsa suka fashe da wani marayan kuka a tare kowa na gurin seda yayi hawaye su Maryam ko duk kunyar abinda mahaifiyarsu tayi ta damesu jinsu suke kamar mujiya a gurin seda sukayi kuka me isarsu sannan Maimartaba yace”ku tafi mun yafemuku Ruƙayya”.
“mungode ranka shidaɗe”.
nansu F2 suma suka yafemusu sannan suka tafi bayan tafiyarsu Sarki Muhammad ya kalli F2 cikeda so da ƙauna yace”Son ni banga surukar tawaba baka nunamun itaba”.
jin abinda sarki Muhammad yace yasa Hafsat saurin yin ƙasa da kanta kallonta F2 yayi yace”Abbuh gata can”.
“masha Allah daughter Allah ya sanya Alkhairi”.
“Ameen”.
“kukuma mekuke jira da bazaku rungume mahaifinku muji ɗumin junaba”.
rungumeshi sukayi yayinda sukeji ƙaunar mahaifinsu tana yawo a cikin zuciyarsu inda sarki Muhammad yakejin kamarya haɗiye yaransa dan farinciki tsayawa su Maryam da jikinsu ya gama yin sanyi sukayi a tinaninsu bandasu hakan yasa sarki Muhammad cewa”ku bazakuzo bane kuji ɗumin nawaba”.
suma ƙarasawa sukayi suka rungumeshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button