HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Hafsat duƙawa tayi har ƙasa ta ƙara gaidashi cikin girmamawa amsawa yayi cikin farinciki yace”gaskiya Son dole a canza sabon biki bazeyiwu ace ina raye ba’ayi wani shagali a bikin ɗanaba”.
“toh Abbah aidama bata tareba tana hannun Hajjo”.
“toh shikenan jibi se ayi dan a ranar zanyi murabus a naɗaka sarauta”.
Ammi cetace”masha Allah,Allah na godemaka daka nunamun wannan rana yanzu komai zezama labari”.
“wlh kuwa aminyata Allah ya kiyayemu da mummunar ƙaddara”.
“Ameen”.
suna cikin hirarsu kowa cikeda farinciki wayar Aunty Zahra’uh tayi ƙara tana ganin mijinta ne tayi murmushi tace”Hajjo ƙilafa harya ƙaraso”.
“toh masha Allah ɗagamana to”.
“toh”.
nanta ɗaga cikin farinciki tace”salamu Alaikum”.
“wa’alaki salam Hajiya kice matar Captain Shuraim ko”.
jinba muryarshi bace yasata cewa”eh nice ya akayi”.
“Allah yayimasa rasuwa sanadin suna sama gabaki ɗaya iskar saman tazama acidic wato Carbon (II) oxide lokaci ɗaya ta canza gabaki ɗaya mutanen jirgin sun mutu”.
sakin wayar tayi tare da fashewa da matsanancin kuka tace”Innah lillahi wa’innah ilaihirraji’un shikenan na rasa mijina”.
kallonta kowa yayi nan Hajjo ta ɗauki wayar takira anan pilot ɗinda yakira yashidamata komai sosai ta tausayawa ƴarta domin tasan irin sonda takeyiwa mijinta nan tashiga rarrashinta suka ɗunguma harsu Ammi aka tafi gidan Aunty Zahra’uh zaman makoki sanadin haka aka ɗaga tarewar Hafsat da naɗin F2 se anyi arba’in.
*BAYAN KWANA ARBA’IN *
Abubuwa da yawa sun faru cikiko harda F2 daya canza lokaci ɗaya tin randa Hafsat tayimasa maganar abubuwan da yike aikatawa ya dena komai yasaka tilor ya ɗinkamasa manya kaya haɗaɗɗu ya aje se bayan anyi araba’in sannan yaje aka yimasa aski aka barmishi ƴar suma kaɗan yaje aka gogemasa duk tatoo ɗinda yike jikinsa gefe guda kuma Hajjo nata jiƙa amarya Hafsat da magunguna ƴan asali yanzuma haka zaune yike yana shafa yana gamawa ya gyara gashin kansa ya buɗe drowers ɗinsa yaga manyan kayansa kala-kala murmushi yayi yakai hannu kan wata gizna ash colour ya ɗauka ya ɗaura akan gado sannan yakoma ya ɗauki agogo ash da takalmi cikin takalman daya caccanza ya ɗakko ash ya aje saka manyan kayan yayi a karo na farko daya furta”gaskiya Hafsat bansan dame zan godemikiba haƙiƙa keɗin HASKEN RAYUWATA ce inasonki ina ƙaunarki”.
yaƙarasa sakawa yasaka malun-malun yaƙarasa gaban madubi anan yaga baƙaramin kyau yayiba yayi murmushi ya feshe jikinsa da daɗaɗan perfumes ɗinsa ya fita danso yike yau Hafsat tasan yaji faɗan data yimasa.
A main falon Hajjo yasameta tana zaune da alama ta dawo daga makarantar gidan sarautarsu Hajjo datake koyawa yara karatu tindaga nesa ya hangeta ta jingina da jikin kujera ta limshe idanunta jakarta a gefanta murmushi yayi yaƙarasa sakkowa daga stairs ɗin ya zauna kusa da ita daddaɗan kamshin turarensa ne yasa ta buɗe ido sukayi ido huɗu da F2 cikin manyan kaya a fili ta furta “wow amma gaskiya kayi kyau yanzu kai dan Allah bakaji daɗin jikinka ba kamar wani sabon ango”.
dariya yayi me sauti yace”angone man tinda gobe za’ah kawomunke cikin gidana My Angel nima sakkowa nayi na nunamiki kwalliyata dominki akayita tonima aɗan koyamun karatun”.
“aiko nagode sosai kayi kyau sosai inajinka jiya kana rangaɗa karatun Alqur’ani jinayi kamar karka dena wlh sede inriƙa koyamaka litattafai suma wanda baka iyaba waikai ya akayi kayi karatu haka nifa wlh lokacin da ƙawata Billy da Zully suke yomana download ɗin Update ɗin hotunanku wallahi kallon arna nike muku musamman danaji tace dangerous ne nifa a tinanina ko sallah bakwayi musamman kaida kake saka nakelace da earing harda wani parking”.
dariya F2 yayi sosai harda riƙe ciki yace”kuma bakisan wani abuba ba abinda bamayi saboda a cikinmu ba wanda be sauke Alqur’ani megirma ba kawaidai muna yin duk abinda mukeyine saboda mu ɓata sunan Familynmu musamman yadda naga Abbuhna yayiwa Ummihna kafin ta rasu shiya hassalani akankifa Angel nafara tinanin wata ɗiya mace tin randa naganki domin nida ganin soyayya nike maɓa lokacine”.
“ina lokacin dakacewa Fatimah ku haɗu a Orphanage ɗinka nayi mamaki sosai anan nafara tunanin toya akayi kakeyin aikin Allah haka kana wannan shigar”.
dariya sosai yayi wayarsa tayi ƙara dubawa yayi yaga sunan Adam yana yawo akan screen ɗin wayar ɗauka yayi tare da cewa”hello Adam”.
“na’am bro gamu a ƙofar gidan Hajjo”.
“okay to ku shigo”.
“toh”.
nanya kashe gani yayi lokaci ɗaya yanayin Hafsat ya canza lokaci ɗaya kallonta yayi yace”lafiya My Angel naga yanayinki duk ya canza”.
“kawaidai banason wa’innan abokannan nakane saboda kasan aboki yana bada gudunmawa gurin canza abokinsa kumani wlh banasonka dasu saboda da mutumin arziƙi akeson abota”.
murmushi kawai yayimata wani haushine yakamata ta miƙe cikin sauri tana niyyar hayewa sama taji ance”amaryarmu kunyarmu akejine?”.
tsayawa Hafsat tayi ta juya cikin jin kunya tace”a’ah da Qur’ani zanje na aje”.
tafaɗa tare da satar kallonsu mezata gani gabaki ɗayansu sun haɗe cikin gizna irinta F2 har hula da takalmi wani sanyi taji ya mamayemata zuciya ta duƙa tace”ina yininku”.
haɗa baki sukayi gurin cewa”lafiya ƙlau ya shirye-shiryen biki Hafsat ba abinda zamucemiki se godiya haƙiƙa keɗin HASKEN RAYUWARMU CE kin tunashemu lokacin da muje cikin ɓata mun manta da ba’ah gyara ɓarna da ɓarna muka shagala mukayita aikata san ranmu bama aiki da ilimunmu mungode sosai “.
“lafiya ƙlau bakomai nikeda godiya naji daɗin ganin kundawo cikin hayyacinku Allah zamu godema bara naje “.
“toh sekin dawo”.
nanta shige sukuma suka zauna suka shiga tsare-tsarensu na biki.
4:00pm
Zazzaune suke a gurin walima anata wa’azi akan aure bayan angama aka buƙaci babbar aminiyar amarya dasu ansarmata kyauta Zully ce ta tashi taje ta ansarwa Hafsat nan aka shigaci ana sha kowa cikin farinciki.
Ƙarfe takwas daidai Hafsat ce zaune me kwalliya na tsaramata kwalliya bayan angamamata tasa wata haɗaɗɗiyar gown fara sol da head red takalmi da pos red baƙaramin kyau tayiba seda sukayi hotuna sannan Hafsat ta zauna ana turamata a wayarta su Fatimah dasu Zully suka shigo cikin shirinsu farin material da head blue black se pos ɗinsu blue black Billy cetace”toh amarya kitashi muje mukaiki motar ango mu tafi saboda duk ankwashe mutane saura mu ƙawayenki daku”.
“toh muje”.
nanta miƙe suka tafi seda suka rakata haɗaɗɗiyar Roice-roice fara sol suka buɗemata tashiga suka mayar suka rife aka jasu.
Tana shiga mota ƙanshin turarenta ya bul-bule ko ina lokaci ɗaya F2 yaji tsigar jikinsa ta miƙe inda wata muguwar sha’awarshi ta motsa lokaci ɗaya sexy eyes ɗinsa suka canza kala lumshe ido yayi sakamakon mararshi data murɗamishi ya buɗesu akan Hafsat da duk takejin rigar jikinta a takure kuma kamar tsirara kai hannu yayi ya jawota jikinsa yace”ba…magana…ma…ko My Jewel”.
yadda yike maganarne yayi mugun bawa Hafsat tsoro a zuciyarta tace”wayyo Allah kardai maganar Billy tazama gaskiya Farouk naci zeyi naga idonshi ya canza lokaci ɗaya se nishi yike kace zansha wahala”.
duk wannan zancen datake F2 najinta dariya yayi sejitayi yace”ƙarasa bani labarin abinda friend ɗin tamu tace inji danni indai akankine banida sauƙi zakijini sosai yarinya saboda friend ɗina sesunsha wahala”.
saurin dawowa tayi daga tinain data tafi tasa hannu ta rife fuskarta tana dariya shima dariyar yayi suka cigaba da soyewarsu har suka isa gurin dinner ɗin buɗemasa akayi yafito sannan ya zaga ya buɗemata ya saƙala hannunsa ta hips ɗinta ya rungumeta suka fara tafiya ƙawayen amarya na takemusu baya ba abinda kake gani a gurin se hasken cameras har suka isa gurin da aka tanaza dominsu suka zauna aka shiga gabatar da dinner cikin kwanciyar hankali da lumana can na hangi Fans ɗin ZANJIRATA, NABARWA ZUCIYATA, HAƊIN ALLAH,BAR RAINA ALLURA, HASKEN RAYUWATA, KAYIMUN HALACCI, NAYI NADAMA, KARAGAR MULKI suna cashewa inda su Zully da Billy ƙirji kamar ze ɓalle dan rawa su Ammi nata zubarda nera.