HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

AFTER 9 MONTH
Abubuwa da yawa sun faru cikiko harda auren Aunty Zahra da Sarki Muhammad da auren 5DBCP gabaki ɗayansu da auren Fatimah da Al’ameen da Abdallah da Billy wanda gabaki ɗayansu F2 ne ya ɗauki nauyin komaina bikin gabaki ɗaya a cikin masarautar yayi musu katafaren estate haɗaɗɗe suka zauna Hafsat ke sakkowa daga stairs ɗin jirgi da turtsetsen cikinta wanda haihuwa ko yauko gobe taƙara zama babbar mace tayi wani fresh da ita tana sakkowa tashiga ɗaya daga cikin motocin da sukaje ɗaukarta suka nufi masarautar kano suna isa sukayi parking F2 dakanshi ya tarbeta ya rungumeta ba tare daya damu da jama’ar dake gurin ba yakama hannunta suka nufi part ɗin Ammi suna shiga suka tadda Aunty Zahra’uh da Abbuh a part ɗin ƙarasawa sukayi Hafsat tana ƙoƙarin duƙawa ta gaidasu Ammi tace”a’ah haba daughter inake ina tsugunno a irin wannan yanayin da kike ciki zauna ma gaisa a haka basekin wahal da kankiba”.
“toh Ammi ina yininku”.
“lafiya ƙlau ya fama”.
“Alhamdulillah Aunty”.
“masha Allah kuje part ɗinku kiɗan huta “.
“toh”.
F2 yafaɗa tare da miƙewa Hafsat na miƙewa taji mararta ta riƙe cije leɓenta na ƙasa tayi tare da dafa cikin tace”ah wayyo Ammi cikina”.
saurin kamata Ammi da Aunty Zahra’uh sukayi nan wani farin ruwa ya fara zuba tsorata F2 yayi yace”Ammi haihuwa ce bara na tafi da ita asibitina nayimata komai”.
hararshi Ammi tayi suka shigar da ita wani ɗaki dake falon lokacin har ciwon yafara cin ƙarfinta nan Aunty Zahra’uh tasa jakadiya a sanarwa da doctor ɗin masarauta ba’ah jimaba suka taho tare nan akashiga temakamata amma shiru se baƙar wuya da taketasha F2 ko yako kasa zaman fada yakoma part ɗinshi ba abinda yike se nafila yana faɗawa Allah har bayan isha’ih ba haihuwa bayan ya idar da sallah ko naɗe sallayar be tsaya yayiba ya fita cikin sauri ya nufi part ɗin Ammi duk inda ya wuce se gaidashi akeyi bemasan anayiba saboda tsananin tashin hankali yana shiga yaga Ammi na fitowa haɗe rai yayi tare da niyyar wuceta yaji tace”ina zakane”.
“Ammi dan Allah kibarni naga matata bakiji yadda nikejiba haƙurina ya ƙare zan ɗauketa intafi da ita inmata c.s dan bazan iya jurar ganinta a wannan halinba”.
yana gama faɗin haka ya wuce Ammi batayi ƙoƙarin hanashiba yana shiga ya wuce kan bed ɗinda aka ɗorata yaga lokaci ɗaya ta fita hayyacinta wani irin takaicin likitocin ne yakama F2 yace”kuna aikin me zaku kashemun mata wallahi indai narasa matata kaf sena kasheku kuna ganin jini ya ɓallemata amma kukasa sawa a sanar dani ku fita ku bani guri aikin banza kawai”.
yaƙarasa zancensa cike da masifa fita sukayi suka barshi dagashi se ita ciro hanky yayi ya sharemata gumi yashiga yimata dabaru har jinin ya tsaya sannan yashiga bata temakon gaggawa cikin muryar jikata tace”My king “.
komawa yayi daidai kanta yana kallonta buɗemasa hannu tayi ya rungumeta lokaci ɗaya haihuwa tazo suna rungume da juna F2 sejin ƙarar kukan baby yayi saurin sakinta yayi tare da waigawa meze gani baby waigawa yayi gurin Hafsat yaga ta sume ɗaukar Baby boy ɗin yayi ya miƙawa Ammi dake shigowa yashiga gyara matarsa seda yayimata komai sannan yayimata allurar bacci ya fita ya ɗauki babyn da har anyimasa wanka ɗaukarsa yayi tare da kara bakinsa a kunnen baby yayimasa kiran sallah bayan ya gama ya kafawa babyn ido kamarsu ɗaya da Hafsat murmushi yayi ya miƙawa Ammi kafi kace me ko ina yasa matar sarki Farouk ta haihu
Ranar suna aka sakawa yaro suna Aliyu(Haidar) mejego se shiga take tana fita cikin tsadaddun kaya ita da babynta se son barka domin F2 da 5DBCP sun kashe nera dasu Ammi.

BAYAN SHEKARU GOMA

Wasu haɗaɗun couples nagani ke shiga wani hall megirma koda na matsa kusa senaga ashesu Hafsat ne da F2 da wasu kyawawan yara kamar ƴaƴan larabawa su uku biyu mata ɗaya namiji zama sukayi akan kujeru basu daɗe da zamaba m.c yace”munason ganin Aliyu Farouk Muhammad yazo ya buɗemata gurin taronnan da karatun Alqur’ani megirma kafin azo afara bada gift”.
murmushi Hafsat tayi tace”tashi kaje ɗan albarka”.
“toh Ummuh”.
nan yaron cikin nutsuwa yaƙarasa ya zauna yafara karanta suratul Muhammad F2 ne ya raɗawa Hafsat a kunne”gaskiya zuciyata keɗin ta dabance kyan ɗa ya gaji ubansa toni nawa ɗan gadar Umminsa yayi haƙiƙa keɗin HASKEN RAYUWATA wanda baze taɓa disashewa ba inasonki abar ƙaunata”.
murmushi Hafsat tayi tare da sakarmasa kiss aka kirasu suka ansarwa yaronsu kyauta zuwa da yayi na ɗaya a gasar karatun Alqur’ani megirma.

Tamat bi hamdullah abinda muka faɗa ba daidaiba Allah ka yafemana kajiƙanmu kayimana gafara kasa mucika da imani Allah kasa muyi amfani da abinda mukaji muyi koyi dashi.

Jinjinar bangirma ga babban Yayah Itz Bashir M bala da Officer Zubair Abdullahi da Abdullahi Mustapha da Senior Kebie Skt da groups ɗina ina godiya sosai da haɗinkan da kuka bani Allah yabarmu tare semun haɗu a cikin sabon litattafina mesuna………………… shiɗin na daban ne domin salonsa na daban ne gobe in Allah yakaimu zan sakeshi.

Sister idan kin karanta kiyomun comments a duk inda kike ina yinki koda banganiba kiyimun share much love. ????????????

Daga Alƙamun ƴar Mutanen Gwarzo._✍️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56

Leave a Reply

Back to top button