HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Amsar kyaututukan tayi cikin girmamawa da ladabi su Billy suka amsa ta juya da nufin tafiya taji muryar M. Jalaludeen yace”zakiyi jawabin godiya “.
juyawa tayi ta amshi loudspeaker cikin girmamawa a hannunshi d’aga lulu eyes d’inta da zatayi karaf idanunsu ya sauka cikin na juna saurin k’asa tayi da idanunta nan taji wani iri ganin jama’ah yasa M. Jalaludeen yin k’asa da murya yadda babu meji ko ita inbanda suna kusa bazatasan meyaceba yace”Congratulation my ???? sure I love you with all my heart”.
jin wani sanyi tayi yana ratsa zuciyarta Wanda bata tab’ajin irinsaba domin ganin abun nashi takeyi Kamar a mafarki itada bame sonta a garinsu Amma wai ita har ake fad’ama kalmomi masu tsada tana wannan tinanin taji ance” jiranki akeyi Hafiza Hafsat”.

Murya na rawa ta fara magana nanta fashe da kukan farinciki dakyar ta gama taje mik’amasa ya wani yimata wani kallo Wanda Habibah dake lura dasu jitayi wasu hawaye masu zafi sun zubomata tace”Jamilah gaskiya dole muyi maganinta domin idan na cigaba da kallonta zan iya had’iyar zuciya in mutu bazan iya jurar ganinta da My Husband to be d’inaba”.
ta k’arasa maganarta tare da fashewa da wani kukan bak’in ciki janta jikinta tayi tare da cewa”kiyi hak’uri nayimiki alk’awarin zata gane kurenta kinji k’awata kidena kuka kinga yanzu hankalin mutane kanmu zeyo in aka gane”.
nan tayita lallashinta har tayi shiru(niko Real eeshow nace kinada aiki indai lallai abinda yayi kikeso lallai kema se kinyi).

4:00pm
Suna idar da sallah Billy tace”Zully wai yau bazamuga mazajen namu bane naga Kamar bakizo da system d’in takiba nifa yanzu Kuma so nake naga new update”.
waro ido waje Zully tayi tare da cewa”wlh na manta saboda wannan abun farin cikin daya samemu nazo da ita man ai kema kinsan dole musha kallo ke nifa har hasaso kyawawan ‘ya’yan da zamu haifa nake wlh”.
“nima haka baki labarine kawai banyiba domin ni har mafarkin F2 nakeyi wai gamu a lambun soyayya yasha fulawowi da kyawawan ‘ya’yanmu munata Shan k’auna”.
dariya Hafsat tayi sosai harda rik’e ciki tace”gaskiya ina tinanin semun had’u mun muku ruk’iya domin kunfara samun matsala “.
“bamuda time d’inki bud’omana mud’an gani mu wuce”.
“toh”.
nanta budemusu hotunan F2 ne kala-kala shiga tayi ganinsa tayi zaune ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yayi parking d’in gashinsa sekace wata mace ga uban sark’ok’o ga wata blue black d’in riga armless inda dantsensa sunsha tatuu me hoton scorpion ga d’ankunne a kunnensa se wandon jeans black three quarter yana Danna system d’insa.

D’aga idonda Hafsat zatayi tayi ido hud’uda hoton jitayi wata muguwar fad’uwar gaba ta ziyarceta dakyar ta iya d’auke idonta a kansa tace”a uzubillahi”.
a zuciyarta suko mutanen se wani jin dad’i sukeyi abunsu sukaita gani .

Tazo futa kenan daga get M. Jalaludeen na Shirin shigowa tsayawa tayi ya wuce yafutota yayi da hannu yace”zona kaiki gida”.
girgiza kai tayi alamar a’ah wani kallo data watsamata ne yasata hawa suka tafi yasa kyaututukan suna cikin tafiya M. Jalaludeen yayi gyaran murya tare da cewa”My Heart congratulations once again bansamu nayimikiba saboda mutane Allah Kuma yabaki sa’ar ta jaharma”.
cikin muryarta me sanyashi cikin wani condition tace”nagode Malam Aida temakon Allah danaku na zama “.
nandai sukaita hirarsu har suka isa getso ta sauka a kwanar D’annafada sukai sallama ta nufi rugarsu ta rumada.

Tana isa k’ofar gidansu Kamar kullum suna nan zaune wucesu tayi sunata habaice-habaicensu haka ta wuce tashiga se binta suke da ido ganin ledojin data wuce dasu seda takai b’angarensu Ummita na binta da kallo sannan ta gaida mutanen gidan sannan takoma zama tayi ta fara nunawa Ummita wani farincikine ya ziyarci Ummita tace”Allah yayimiki Albarka insha Allahu sekin zama abar kwatance a rugar nan ki dad’a dagewa ki cikamun mafarkina da burina kinji d’iyar Albarka”.
“toh Ummita wannan shaddar Yayah Zan bawa da Bappi mukuma mu d’inka atamfofin ko”.
Lantana cikin sauri ta nufi b’angaren Iyah har tana cikin tuntub’e gamuwa sukai da Iyah tana Shirin futowa daga k’ofa harta kusa tureta Iyah sarkin masiface tace”lafiya Lantana”.
“Iyah inafa lafiya yanzu yarinyar nan ta dawo daga yawon dandinta da uban kaya anya Iyako ba satosu tayiba har wani cewa take zata bawa Bappin Idi shadda me kamar madubi “.
“ainima abinda Tsahare dillaliya tagama fad’amun kenan aradu tayi kad’an bara Iron yazo”.
ana haka sukaji muryar Bappi a b’angaren su Ummita cikin sauri suka nufi b’angaren nan Iyah taita sababi Koda Bappi ya fad’amata cewa tayi”da’allah sakaren banza shanyayye kawai rufemun baki”.
nan taita sababinta.

7:52am
Tashiga makaranta cikin takun nutsuwa wucewa tayi class tana shiga!!!!!

kuyi hak'uri da jina da kukai shiru kunsan Ina school abun ne se a hankali sekunamun uzuri

More Votes and Comments
More typing
Plz share

_*Daga Alk’alamin’yar muta???? *HASKEN RAYUWATA*

MALLAKIN
REAL EESHOW

HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION

DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
http://ww.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dLOe_AqkiQ
Subscribe and share

PAGE 0️⃣9️⃣➡️1️⃣0️⃣

    Ta tarar da M. Nura yana musu k'arin karatun  Umdatul Ahkam bakinta d'auke da sallama ta shiga ta wuce seat d'in su ta zauna harta zauna M. Nura ya watsamata wani kallo ko tsayawa yayi yakai karatun beba yace"koma gaban allo kitsaya ga laifin makara gana rashin sallama  saboda kin maida mutane 'yan iska ".

murya na rawa Kamar zatayi kuka tace”wlh Malam nayi sallama “.
“rufemun baki yarinyar da ko ganin mutane bakyayi da gashi sekace bamune sillar zamanki kome kika zamaba”.
Billy da Zully ne suka had’a baki gurin cewa”Malam wlh tayi kawai dai bakaji bane kana karatu”.
“rufemun baki sakarkaru kawai Kona tambayeku”.
“ba tayiba Malam dama haka takeyi”.
cewar Habibah dake murmushin k’eta itada aminiyarta
shiru sukai ban ‘yan class suka had’a baki sukace”Malam tayi sallama wlh kawai dai bakajibane”.
ganin zasu harbo jirginsane yasashi cewa”koma ki zauna Kuma Banda surutu”.
ba tayi mamakin abinda yayimataba ta koma ta zauna ya cigaba da yimusu karatun.

Yana fita Zully tace “wannan mutumin wato ta nan ya b’ullo kenan tunda kince ba soyayya aka turokiba bara yatsaneki kenan “.
“eyi ba mahaukaci bane nifa na tsanesa wlh”.
“nima haka wlh”.
“zunibima kuke ragemasa saboda bemasan kunayiba wai kunu a wani gida kuzo muyi muraji’ah”.
“Toh uztaziya sarkin wa’azi”.
nan suka cigaba da karatunsu .

Ana futowa break suna Shirin tashi sega wata yarinya tana shigowa k’arasawa tayi har gaban seat d’insu tace”Ina yininku Aunty Hafsat tazo inji M Jalaludeen “.
” Lafiya k’lau to kicemasa gani nan”.
nanta tafi kallon juna su Billy sukayi tare da cewa”Hafsat mufa bamu gane tsakaninki da M. Jalaludeen ba kodai angamu da an dace ne?”.
damm gaban Hafsat yabayar murya na rawa had’ida marairaicewa tace” bakomai tsakanina dashi kawai dai mutunci ne ke tsakaninmu”.
wata dariya suka shek’e seda sukai me isarsu sannan Billy tace”Hafsat ashe yadda muka d’aukeki ba haka kika d’aukemuba banga abun b’oyemanaba mu amma muke iya fad’a miki komai namu dake bamu da wayau muma zamu dena mu tsaya a matsayinmu”.
ta k’arasa zancenta cikin fushi murya na rawa Kamar zatayi kuka tace” Billy kuyi hak’uri ba wai b’oyemuku nayiba saboda yace karna fad’awa kowa yazama sirri tsakanina dashi har seya gama n.y.s.c d’insa shiyasama ban fad’amukuba kuyi hak’uri Dan Allah kuyi hak’uri k’awayena na gari inkuka juyamun baya dawa zanyi rayuwa”.
ta k’arasa zancenta da kuka rungumeta sukai tare da cewa”mun hak’ura kinji Sweetheart kidena kuka kingako yadda yake jifanki da wani shu’umin kallo a Assembly kuwa shiyasama muka gane”.
murmushi tayi tare da cewa” ‘yan sa ido kawai saboda sa ido har kuka lura to Dan Allah mu b’oye zancennan”.
“ai dama hakan za’ai muje mu rakaki kai ammafa a makarantar nan tamu ana son maso wani wlh”.
“Wlh kuwa sosaima”.
nan suka nufi office d’insa suka tsaya jiranta a kusa da windown office d’in b’angaren Habibah da Jamila ma suna ganin sun fita sukabi bayansu suka zagaya ta bayan window d’in office d’in wai don suga me sukajeyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56Next page

Leave a Reply

Back to top button