HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Suna tashi Badamasi yace”sakarai kawai kalli yadda yaketa tsuma yarinyar data tafi tana zubarmana da k’imar gidanmu”.
“eyi ai wannan shegiyar matar tasa ta mori boka gaskiya yakamata ta d’auki mataki bakaga yadda take wani b’ob’oye hannu a cikin hujabi k’ilama abun kunya ta kwaso”.
“Wlh kuwa gaskiya muje mu sami Iya asan yadda za’ai haka kurum”.
nan sukaita gulmace-gulmacensu .
Cikin fara’ah Bappa ya amshesu suka gaisa bayan sun gaisa principal yayi bayanin fad’uwar da Hafsat tayi a makaranta har karayar data samu da zuwa asibitin da sukai sosai Bappa yayita godiya sun juya zasu tafi Principal yace”au namanta Malam Ibrahim in Allah yakaimu ranar Asabar munada musabak’ar Jiha da za’ah gudanar a fitar da Wanda ze wakilci k’asa gashi Kuma wannan abu yafaru ya za’ai kenan gashi dai Hafsat itace zata wakilci jiharmu ta Kano “.
murmushi Bappah yayi tare da cewa”Allah yakaimu lafiya Malam insha Allahu zatazo ai abunma yazoda sauk’i ba’ah k’afa bane setaje d’in “.
“nagode Malam Ibrahim sunce a kula da bata magani nanda sati biyu zata iya warkewa”.
“bakomai insha Allahu za’ah kula muma Kuma zamu yimata irin namu na Fulani”.
“to Masha Allah semun dawo k’ara dubata”.
nansukai sallama suka tafi bin bayan Hafsat yayi data dad’e da shigewa yayi tunkafin su fara magana yana mamakin yadda tak’i nunamasa.
Yana shiga ya tadda matan gidan na gulma be tsaya kulasuba ya nufi b’angarensu yana shiga ya taddata tana nunawa su Ummita magungunanta da M. Jalaludeen yabata zama yayi tare da cewa”sannu kinji d’iyar Bappanta yanzu nan ashe karyewa kikai amma na tambayeki kikai shiru”.
murmushi tayi tare da rife fuskarta da d’ayan hannun tace”saboda banason hankalinka ya tashi shiyasa”.
murmushi yayi tare da cewa”toh Allah yayimuku albarka ki kula da bata magani sosai Malamansu sunce jibi za’ai wannan karatun Kuma banason d’iyar Bappanta ta fad’i inason d’iyata ta kawowa garinnan canji wa’inda suke mata wata fassara sugane jahilcine kawai ke damunsu”.
“toh”.
Suna wannan zancen sukaji muryar Iyah akansu tace”aradu kayi kad’an nagaji da irin wannan cin
da suke mu’amala ke ki kiyayeni ki fita idona inrife inta shanyeka ni bata shanyeniba kikoma gurin bokanki kice ni ban shanyuba maga inda zatan nagani kaiba abun kunyarka bane ace gobe za’ah kawo kayan k’anneta ita tana zaune a gida ba Wanda ya tab’a cewa yana sonta saboda ansan dadin da take a birni nagaji naga inda zata fita nagani”.
“kiyi hak’uri Iyah wlh …….”.
be k’arasaba ta dakar dashi da hannu tare da cewa”na yanke hukunci sannan Kuma ke duk abinda kike ciki ki fitar da miji cikin wa’inda kike dandin dasu dan wannan Karan tare nakeson a had’a inkuma baki fitarba nizan fita wajan gari insamomiki da kaina Dan a garinnan ba wanda ze yadda ya aureki yasan ke ragowar wani ce”.
tana gama fad’ar haka ta fice fuuu tanata fad’a koda su Lantana sukaji duk abinda Iyah tace kowa murna ta kamashi so suke suga yadda za’ai ta nemo miji.
Wasu hawayene masu zafi suka zubo a idon Hafsat sharemata Ummita tayi tare da cewa”haba shalelena kidena kuka watarana se labari kiyi hak’uri insha Allahu watarana se Iyah tayi alfahari dake”.
Bappah ko bak’aramin tausayi Hafsat tabashiba yace”kiyi shiru kinji d’iyar Albarkana kije kici abincinki “.
“toh Bappana Yayah muje dakanan nayimaka k’arin karatun”.
“Toh muje”.
nansuka tafi zuciyar kowa ba dad’i suna fita Bappah yakalli Ummita da bata tab’a samun kalma me dad’iba itada ‘yayanta daka bakin mahaifiyarsaba cikeda tausayi yace”kiyi hak’uri da abinda mahaifiyata take muku ba…..”.
saurin rifemasa baki tayi da hannu tare da cewa”kadena bani hak’uri mahaifiyarmu ce baki d’aya kuma ta isa damune kawai meyasa baka gajiya da bada hak’uri ne gobe kaje birni kasamu Malamansu ka nunamusu bata samu sauk’iba su samu me musu karatu tunda wuri”.
jawota jikinsa yayi tare da cewa”Allah yayimiki Albarka ya zakice inje ince bazataba gaskiya bazan iyaba na rigada na amsamusu Zan san yadda zanyi ki kwantar da hankalinku”.
“banason ka b’atama Iyah rai Dan Allah kabarta kayi yadda tace d’in “.
nanya nunamata toh sukaita hirarsu har akayi magariba.
B’angarensu M. Jalaludeen suna komawa ana tashin d’alubai yana fita daga mota ya hangi su Billy a bakin k’ofar office d’insa da alama shi suke jira k’arasawa yayi gurinsu cikin nutsuwa kallon fuskarsu yayi duk damuwa murmushi ya sakarmusu tare da cewa”ku kwantar da hankalinku manyan k’awayenmu karaya kawai tasamu insha Allahu gobe zamuje daku da wasu daga cikin d’alibai ku gaida ita”.
Sauke numfashi sukayi gabaki d’aya tare da cewa”Alhamdulillah Malam mungode sosai”.
“bakomai “.
nansukaimasa sallama suna juyawa suka hangi su Habibah anata fara’ah k’arasawa sukai Billy tace”anyi asara duk hassadar mutum nagaba yayi gaba na baya se labari Hafsat ta tseremiki yadda kikaso kassarata Allah be nufaba ta Allah ba takiba”.
“sakarai kawai jahilar banza”.
suka ruga da gudu kwafa Habibah tayi tare da cewa”Jamilah gaskiya dole mu koyawa yarancan hankali suma”.
“dole kuwa har ita ‘yar gogar tasu”.
nansuka tafi suma.
Sosai sukayi nishi sanadiyyar gudun da sukasha seda suka gama sannan Billy tace”kinsanko a tsorace na iya fad’an hakan kuwa ina fad’a gabana na dukan uku-uku domin kartawarfamun mari da wannan hannun nata”.
“nima haka wlh naso na fad’awa Malam sena fasa se Hafsat ta dawo masan yadda zamuyi da ita”.
“gwara da biki fad’aba saboda wannan uztaziyar inda kin fad’a setamu tafi zafi bata da zance na wa’azin hak’uri”.
“wlh kuwa”.
nan suka tafi.
Zaune take a d’akin Ummita ta aje hannunta kan fulo tashiga duniyar tinani taji an tab’ata firgigit tayi alamar ta tsorata ganin Ummita tayi akanta d’aukeda kwaryar a hannun dakuma ledar maganinta ajewa Ummita tayi tare dafata tace”meyake damun d’iyata”.
murmushi ta k’ak’alo tare da cewa”bakomai Ummitana hannuna ne kawai yakemun d’an zugi”.
murmushi manya Ummita tayi tare da cewa”ban yaddaba d’iyar kirki akwai abunda ke damunki”.
“Allah ba komai Ummitana”.
“ban yaddaba saboda ban tab’a ganin d’iyata a cikin damuwaba irin haka kodai kan musabak’ar da Iyah ta hanane in itace ki dena damun kanki rabon mutum baya tab’a wucemasa in Allah ya k’addara zakiyi sekiga da kanta tace ki tafi kicire komai a ranki kinji d’iyata insha Allah wannan ilimin dakikai seya amfaneki koda bayan ba raina nidai abinda nakeso dake kicigaba da hak’uri zakiga ribarsa insha Allahu kinji tashi kisha fura kusha maganinki”.
“toh Ummitana insha Allahu zan could gaba amma nida banida saurayi a ina Zan nemosa”.
tak’arasa zancen cikeda damuwa murmushi Ummita tayi tare da dafa kwantaccen gashinta tace”Allah shiyasan yadda zeyi damu yayimana jagora yasa Alkhairi a ciki kinji”.
“toh”.
nansukaita hirarsu har seda Ummita ta tabbatar ta fita a damuwa suna tsaka da hira sega Bappah da zugar Malamai dasu Billy jan Ilajonta tayi sama ta rife yalwataccen gashinta shimfid’amusu tarbama tayi tare da yimusu marhabun Hafsat dake kusa da Ummita ko d’aga ido takasayi ido a k’asa ta gaidasu bayan sun gaisa suka aje ledoji Malamai suka fita inda M. Jalaludeen nataso su had’a ido amma tak’i bashi damar hakan har suka fita akabarsu Billy bayan kowa yafita Billy tace”sannu yak’arfin jiki “.
“da sauk’i nayi missing dinku”.
“muma haka kinsan wani abu ashe tsinannar Habibah ce taja kika fad’i k’ila dan karkije musabak’ar nan da za’ai gobene”.
“hmm kuya akai kukasan hakan”.
“alama muka gani”.
“kurik’a kyautatawa mutum zato my hearts d’ina”.
“kingani ko to da mun fad’amasa da haushinmu zataji”.
suna cikin hira sukaji anata bud’a lek’awa Billy tayi ta hango mutane d’aukeda riyo na kayan jarirai guda biyar dawowa tayi tace”haihuwa akaimuku ne naga ankawo kayayyaki a riyo”.
“a’ah kayansu Furera aka kawo dasu Hassana”.
“name wai?”.
“Aure man”.
“au waiku a riyo aka kawo kayan lefe tab kuma guda nawa”.
“eh guda d’aya man da nawa za’ah kawo”.
“tab Allah ya kyauta mudai M. Jalaludeen baze kawo a riyoba a akwatuna ze kawo har sha biyuma”.
murmushi Hafsat tayi tare da cewa”hmmm bakwa raboda abin dariya Allah yakaimu”.
“ameen danmu idan aka tashi kawo namu da F2 a jirgi za’ah kawo”.
nansukaita hira har suka tashi zasu fita tafi rakata suna zuwa tsakar gida sukaji Larai nace”ayiriri yara sunyi goshi wasuko sede yawon bariki bako mashinshini ayi zuwan zomo kasuwa aci da gudu a koma da gudu”.
Zully ceta kalli Hafsat tace”au a gidan nakuma baki tsiraba”.
saurin rifemata baki Hafsat tayi tare da cewa”yishiru matar Yayan Bappah ce”.
nansuka fita tundaga nesa ta k’arewa M . Jalaludeen kallo a zuciyarta tana cewa”dama ka bayyana kanka ga iyayena danaji dad’i”.
tanata sak’enta har suka isa suka shiga motar ta juya.