HASKEN RAYUWATA COMPLETE HAUSA NOVELS

Washe gari da sassafe Bappah yashiga d’aki yace”Hafsat tashi ki shirya ki rakani unguwa yanzu zamu dawo”.
“toh”.
nanta tashi ta shirya hartasa tsofaffin kayanta Bappah yace”kisaka na sallah mana gidan abokina zamu”.
“toh”.
nanta saka ta zabga hijab suka fito kacib’is sukayi da Ummita kallon Bappah tayi da mamaki tace”inakuma zaku da sanyin safiyar nan”.
“zamuje dawane yanzu zamu dawo”.
“toh amma karku dad’e dan kasan Iyah tahanata fita.
bata kawo komaiba har suka fice daga gidan ba tare da kowa ya gansuba suka hau mashin suka nufi Gwarzo.
Suna isa ya sauketa a bakin get d’in makarantar suka shiga suka gaisa da Malamai yabawa M. Jalaludeen amanarta ya juya sukuma suka d’unguma suka nufi Abuja suna zuwa suka tarar har anfara gabatar da musabak’a zama sukai kafin a Kira jihar Kano d’aukar Qur’ani tayi tad’an k’ara dubawa segashi ankirata dukda karayar hannunta ba abinda ya sauya sema wani farinciki datake cikin nutsuwa ta isa inda zatai karatun ta zauna aka fara jawomata tafara rera k’ira’ah shiru ne ya d’auki Hall d’in ba abinda kakeji se muryarta harda masu lumshe Ido seda akaimata ja uku sannan ta yarfa tangimi aka Kuma jejjefomata tambayoyi ta amsa sannan ta tashi suna gamawa akace se gobe in Allah ya kaimu za’ah fad’i sakamako a gidan redios dasu television nan suka juyo gida .
Suna isa ta sauka ta tadda Iyah a tsakar gida da Bappah da Ummita tanata masifa jiki a sanyaye ta k’arasa ta tsugunna wani k’ulutun bak’in cikine yak’ara turnik’e Iyah tace”dama na fad’amuku ta fidda miji tak’iko to yanzu dakaina zan zab”omata Dan bazanje gidan biki a rik’a nunaniba wlh tayi barikin a gidanta”.
nan taita masifa hartayi tagama ba Wanda yace da ita uffan.
Washe gari Iyah na zaune a d’akinta tana cin d’umamen tuwo taji sallamar wata mata wadda suke ganin tafi kowa wayewa a garin sakamakon tana zuwa birni tanayin ‘yan sare-sarenta amsa mata tayi shiga Hansai tayi tare da cewa”k’awata yanaga kamar kina cikin damuwa Allah dai yasa lafiya”.
“ba dole ki ganni cikin damuwaba ace kamata Hansai waini jikata kezuwa birni dandi nakuma ceta fiddo miji tak’i “.
“kwantar da hankalinki akwai wani yaro dayace insamarmasa mata meze hana mu had’a tunda ba’ah garinnan yakeba Kuma kinga yarinyar dukda ta zubarda k’imarta ai tana da kyau kinga shikenan a rirrifa ayi da wuri”.
“da gaske Hansai Kuma kina ganin ba matsala”.
“wlh babu kedai kawai ki tara yaranki ki sanar musu”.
“toh ba matsala aini nama rigada na yanke hukunci kicemishi nabashi ita ya turo rana ita yau a d’auramusu aure tare danasu Furera kobe shuryaba nabashi kyauta”.
“toh bara in shirya idan nashiga garin nasanarmasa”.
“toh yimaza Dan Allah karki bari yagane ya fasa”.
“Toh”.
nan Hansai ta fita tana mai sakin wani murmushi wanda ita kad’ai tasan ma’anarsa Kiran Lantana Iyah tayi tasata takiramata su Bappah nanta kiramatasu ta rab’e taji mezatacrmus.
Kallonsu Iyah tayi tare da cewa”dama ba wani abubane yasa na tarakuba se akanka kai Iro “.
“munajinki Iyah”.
“nayiwa Hafsatu miji kuma wannan ba shawara nake bakaba umarnine dan wlh muddin ka hana akai wannan auren sena tsinemaka dan bazan bari inzuba mata ido duniya nata zaginaba”.
lokaci d’aya hankalin Bappah yayi mugun tashi kamar zeyi kuka yace!!!!
Votes and Comments
Plz share
_*Daga Alk’alamin ‘yar mu???? *HASKEN RAYUWATA*
MALLAKIN
REAL EESHOW
HOME Of QUALITIES WRITERS ASSOCIATION
DUNIYAR LITTATAFAN HAUSA TV
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQvSubscribe and share
PAGE 1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣
"Iyah dan Allah kiyi hak'uri Hafsat duka nawa take da za'amata haka kuma ma ni yanzu banida ko biyar d'inda zammata kayan d'aki Iyah kiduba ki gani wlh Hafsat yarinyace".
cikin masifa Iyah tace”kaga Iro ka fita a idona in rife dama waya fad’amaka ko kana dasu Zan bari kayimata wani abun ai daka ita se halinta da ‘yar tabarma za’ah kaita idan canma taje tanamusu karuwancin da uwarta take sata tasan ba kyaleta zasuyiba dan haka kama fitar da rai inkaga ba’ayi aurennanba to banida rai Kuma ko banida rai kabari akak’i ban yafemakaba ina laifi ma da aka samu wanda yake sonta domin ni namayi mamakin da yace yanasonta k”ila kyalkyal banza yagani dan haka fara shirin biki daka yau”.
idon Bappah sun kad’a sunyi ja ya bud’e baki ze magana Yayansa Shafi’u ya d’agamasa hannu tare da cewa”karka sake sakamana baki domin wannan shawara da Iyah ta yanke tayi bazamu bari azo har gida a b’atamana zuri’ah ba ka shirya Asabar za’ah d’aura bandama an shanyeka yaza’ai ka zuba ido kana kallon yarinya me shekaru irin wannan a gida tana yawon sakarci to baze yiwu ba”.
shiru Bappah yayi Iya tace”ka tashi kaban guri sokon namiji wanda baida katab’us a gidansa”.
jiki a sanyaye ya tashi ya fita bayan ya tafi Badamasi yace”aiko Iyah gwara da kikai haka inba hakaba se anje an kwasomana abun gori har mu mutu baze dena bummuba”.
“eyi ai shiyasa nayi haka nima anje anko dudubawa amare katakwaye gurin Nasiru kuwa yacemun ya gama”.
“A’ah yaushe ya gamane”.
“eh d’azu ya aiko”.
“toh bamuje”.
nansuka tafi.
A daddafe ya k’arasa b’angarensu yana zuwa ya zauna sharaf Ummita dake jan carbice tana lazumice a tsorace ta kalleshi tare da cewa”lafiya Bappan Hafsat naga kashigo a irin wannan yanayin meyafaru “.
cikin damuwa murya a sanyaye yace”Iyah ta zab’ama Hafsat miji kuma tace muddum in nahana aurennan seta tsinemun”.
“toh seme dan kakarta ta zab’a mata miji ai abun alfarinmunema kuma Iyah bazata tab’a zab’amata wanda ze cutar da rayuwartaba ni banga abin b’acin rai ananba a ganina inbanda abunka”.
“ya zakice haka memakon kinemomin mafita sekice haka bafa asan yaronba ta cemun d’an ciranine k’ilama iyayensa zasu aura mai ita Allah dai yasa ba gagararre bane danni bazan b’ata kud’ina insai wasu kayan d’akiba ita Iyar data jajiboshi tayimata”.
“hmm kana bani mamaki Bappan Hafsat ai komai ka gani muk’addarine daga Allah kadena tashin hankalinka Allah yasa Albarka yabasu zaman lafiya da zuri’ah ta gari”.
sauke numfashi Bappah yayi cikeda tausayin matar tasa da ‘yayansa yace”bakomai Allah ya tabbatar mana da Alkhairi amma ni Hafsat nakeji koya zata amshi abun”.
“Ameen mijina haka nakeson naji kana cewa ka kwantar da hankalinka ba wani abunda ze faru Hafsat yarinyace me biyayya ba abinda ze gagara da izinin Allah”.
murmushi Bappah yayi yana k’arajin k’aunar matartasa nabi tako ina na jikinsa.
Hafsat dake shirin shigowa d’akin taji duk abinda ya faru ta share d’an guntun hawayenta tausayin iyayenta nabi ta ko ina na jikinta juyawa tayi zata nufi d’aki sega Lantana Itada Hanne ‘yarta tana wak’a tana cewa”Hanne azo a fara shirye-shirye dan tunda ank’ak’aba me bak’in jini a cikin bikinnan dole mu tashi tsaye kar a shafamiki saboda tsabar bak’in jini da dandin da ake zuwa seda akayi gwanjanta sannan aka samu wani masaki ya taya shima dan besan ciki fanko bace dabe d’aukaba”.
murmushi Hafsat tayi ta shige d’aki sukuma suka wuce.
Sallama akayi Ummita ta lek’a ganinsu Billy ne yasata cewa”a’ah su Bilkisu ne sannunku da zuwa”.
“yauwa Ummita”.
nansuka gaidata tayimusu jagora har d’akin Hafsat samunta sukai tana sallah zama sukai Ummita na Shirin juyawa Zully tace”Ummita tare muke dasu shugaban makarantarmu suna waje da Bappah wai kije inji Bappah”.
“toh Zaliha “.
nanta fita abinta Hafsat nayin sallama suka rungumeta harsun kusa fama mata hannu suka had’a baki wurin cewa”albishirinki sweetheart ke kikazo ta d’aya kinga yadda gari ya d’auka kuwa ko ina kaje zancen da akeyi kenan jiya aka sanar da daddare”.
hararsu Hafsat tayi tare da cewa”kudai bakwa raboda tsokana kuga yadda ‘yan meduguri suka zubarda k’ira’ah kuce ni kwayi kwa gama k’aryarku”.
“sweetheart wlh dagaske muke kuma ‘yar nan kinci kujerun Makkah guda ukuma da kyauttutuna manya da million biyu da sauran abubuwa”.
“Dan Allah dagaske kuke ko wasa”.
“wlh dagaske mukeyi jiya da ana fad’a jinayi kamar nayi tsintsu nazo nan na fad’amiki”.
wasu hawayen farin cikine suka zubomata nantake tayi sujjudushshukur tayi godiya ga Allah sukaita murna.