KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan ta gama shiri Ammar yayi sallama ya shigo d’akin, Khairiyya tace
Ammar please mei good news d’in
“Ke wace irin sister ce, haka kike kiran suna nah direct ba koh yaya or broh, kinsan shekaru nawa na baki kuwa, you are now eighteen nikuma twenty seven just calculate shekaru nawa na baki”
“Koh ma nawa neh ni dai Ammar zan kiraka bazan sakaya ba ehee” ta murkud’a masa baki, yace Good yanxu sai kitashi mutafi gida ai, kinsan yanxu karfe Tara fa, one two tashi mu tafi, Khairiyya tace “toh naji Mr Ego”
Ta shirya suka shiga motar ta suka dawo gida, Ummi da Zainab neh a parlour suna kallon Mbc bollywood, ana wani film Kick na Salman Khan da Jacqueline Fernandez, Ummi kallon su take ranta a 6ace tace
“Daga ina kuke, ke Khairiyya inata ta kiran number ki bakya picking, kai kuma tun da kace mini kana tare da Khairiyya ka kashe wayar ka”
“Ummi na kaita gida neh ta kwaso wasu kayakin ta” cewar Ammar
“Bayan daga gidan natashi, inji masu aikin ta bata je ba, nidai shawaran da zan baku shineh kudai na ke6ewa ku kadai, idan namiji da mace suka had’u toh the next abu shaid’an neh, na yarda da kai Ammar nasan baza kayiwa kanwar ka komai ba, amma hmmm bakusan sharrin shayd’an ba, please ku kiyaye”
“Toh Ummi mungode” cewar Khairiyya
“Ummi ama damn hungry ina food please” cewar Ammar
“Yana dinning” cewar Zainab (kanwar Ammar, yarinya yar shekara goma sha bakwai ustaziya ce sosai, shiyasa Khairiyya bata kulata dan koman ta wa’azi, Khairiyya takan cewa idan inason wa’azi naje post office a tura mini mana nazauna tana ji)
Ammar yace “Yawwa KIM, ki kawo mana d’aki na muci”, bud’e baki Ummi da Zainab sukayi
Ummi tace “Toh kuci mana a dinning mei har sai takai d’akin ka”
“Ummi dinning is not comfortable, please Ummi mei haka”
Ummi tace “inaga Abba yana zuwa zance a aurar daku mu huta, idan kunyi aure kwayi komai”
Kallon juna Ammar suka fara da Khairiyya wanda cikin su yacika da dariya, Ammar yace
“Kai Ummi, Khairiyya she’s just a sis, and she will be the last candidate dazan aura”
Ummi tace “kudai kuka sani”, Ammar yace come on Khairiyya inajin yunwa kije kiyi wanka nima zanyi, na baki nan da minti goma sha biyar please
Khairiyya tace “naji Ammar”, ta wuce d’akin ta shima ya wuce tasa
Bayan 30mins Khairiyya tafito, riga da wando neh na bacci a jikin ta, ta d’aura kanta da dan kwali, dinning taje ta d’auko su food flakes da plate ta wuce d’akin Ammar, zaune yake yana karatun Al Qur’ani, Khairiyya ta zauna tana sauraron muryan sa mai dad’in gaske, bayan yakai karshen aya ya dakatar, yace Yawwa Khairiyya please serve me m very hungry
Khairiyya tace “kaidai son ci kamar gara”, tayi serving nashi, bayan sun gama ci cikin su yayi dam kawai Khairiyya ta fashe da dariya tace
“Kai Ummi ma dai, wai aure, aure nida AMMAR, tab idan na aure ka ai Ammar mei yaran mu zasu zama, TANTIRAI zasu zama”, ta fashe da wani dariyan, taciga da cewa “both of us bamujin magana, gashi muna shan abu, gwara ni bana kula maza but what about you Ammar, you are a playboy”
Shima dariya yayi yace
“Kim wollah you will be the last candidate to marry, da zan aura, kai ban ta6a imagining ni dake azaman miji da mata ba”
“Last kace Ammar, last din ma kacire cos babu ma” cewar Khairiyya
Ammar yace”Just shutup, ke idan kin samei ni ki godewa Allah
No one can deny my attractive looks and one look from me can melt any gurls inside, not to brag but no one can resist me. Lots of gurls chase over me for my looks but mostly for my money
Khairiyya tace “Mr Ego keep talking” , duk suka fashe da dariya, Ammar yace
“KIM naji kince Mr lecturer i love you so much who is that”, jin zuciyan ta tayi yayi dummm, atake tafara tuna abun da tayi a maranta, take tafara hawaye tace
“Nashiga uku Ammar, I embarrassed him in front of everyone, yanxu nasan ya tsane ni, yazanyi Ammar, Tunda nake ban ta6ajin son wani kamar shi ba, tell me Ammar what will I do now”, Ammar jin zuciyan sa yayi kwata kwata ba dad’i, baisan dalilin dayasa ransa ya 6aci ba
Khairiyya tace “I must go to his office na basa hakuri gobe In Shaa Allah,koh Ammar? “

Typing errors, no time to edit pls

Nana fa'ad En Eesha

????????????????????
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

   *[Sept, 2016]*


        Written by Nana fa'ad En Eesha????

Page 45~46

Ammar ya numfasa kan yace
“Khairiyya do you think is right kije office nasa”, Khairiyya tace Ammar I really wanna apologize to him, abun da na masa ba dad’i, and I know now ya tsane ni, bazan iya ganin wanda nake kauna, wanda nake tsananin so ya tsane ni ba Ammar
Ammar yace “ohk as you wish, but please Khairiyya ki kama kanki, ke mace ce, kuma ansan mata da kamun kai please”
Wani kama kai, ai yanxu koh mei nayi bazai kara gani nah da daraja ba, kawai zan basa hakuri neh cos ina feeling guilty”, Ammar yace “alright toh Allah kaimu gobe”
Khairiyya tace yawwa Ammar what’s the good news
“The good news, emmm Abba will be free soon, an kama manager shi daya saka cocaine d’in but manager still deny cewa bashi yasaka ba, but ana working akai In Shaa Allah nan da sati biyu zai fito”, Khairiyya ta share hawayen ta tace I pray so Ammar, ina feeling incomplete without my Abba
Ammar yace “Don’t worry KIM, everything will be over soon”, bayan sun gama hiran su Khairiyya ta koma d’akin ta dan bacci……. Ammar kuma kasa bacci yayi yace “Gosh what’s wrong with me, mei yake damu nane”, sam yaji jikin sa ba dad’i, fridge yaje ya d’auka champagne yasha, sanda ya shanye tas yacire kwal6an a bakin sa, rad’ad’in da yake ji a ransa har yanxu bai ragu ba, fita yayi kitchen ya d’auka wuka yadawo d’akin sa dashi, wuk’an ya d’auka ya yanka hannun shi kad’an, kallon jinin jikinsa yayi yana sauka, zafin yanka da yayi yasaka shi jin dama dama, daga baya ya nema tsumma ya d’aure wajen, sai kuma bacci 6arawo daya sace shi

Washe gari da safe Khairiyya ta shirya zuwa makaranta, material ash da light purple neh d’inkin riga da skirt, hijabi naga ta saka shima light purple (daman Kim tana saka hijabi bayan na yin sallah), tayi light makeup, ba karamin kyau hijabin ya mata ba, ta d’au dogon takalmin ta, itakam bata rabuwa da heels, falo taje ta gaishe da Ummi, tace Ummi zan tafi school, Ummi tace “ai na dauka yau bazaki ba, yanxu fa karfe sha biyu, toh Allah kiyaye hanya Khairiyya kuma please banda gudu akan titi, Khairiyya tace In Shaa Allah Ummi, balle ma ai ni bana gudu akan hanya, gudu ai sai Ammar
Ummi tace kudai kuka sani kunfi kusa
Khairiyya ta d’au motar ta sai university of Maiduguri, tana zuwa tayi parking motar ta tawuce department na computer science, neman office nashi tafara tana bin office na wajen d’aya bayan d’aya dashike koh wani office akwai sunan malami a rubuce, can taga Mr Zilyadeen a 5th door….
Zilyadeen yana zaune yana editing handout da zai bawa students nashi yaji an masa knock yace “come in”
Da hankali ta bud’e kofar tashiga tayi sallama, d’aga kai yayi ya kalle ta, koh kad’an baiyi mamakin ganin ta ba, ta mishi kyau ainun, a zuciyar shi cewa yake Mashaa Allah, ya nuna mata kujera yace “you can seat”
Mamaki abun yabata, ita duk a zaton ta koran ta zaiyi, koran ma koran kare, da hankali ta zauna, duk sukayi shuru ta kasa bud’e baki tayi magana shikuma ya cigaba da aikin da yakeyi, can kusan bayan minti biyar ya d’aga kai ya kalle ta yace
“If u don’t have anything to say you can leave”, jin zuciyan ta tayi bugun ya tsanan ta, dakyar ta iya bud’e baki tace
“Dan Allah kayi hakuri abun da na maka a class jiya, I was drunk bansan mei nake ba, sorry for the embarrassment”, ajiye biron hannun shi yayi yace
“Why do you drink, bazan yarda dake ba idan kika ce mini sabida mahaifin ki yana prison, the 1st time da na ganki a buge kike, kuma is almost six months back, kin manta ni, how can you forget my face so quick, idan kin manta ni toh ni bazan ta6a manta kiba, I hate you the very 1st time I set my eyes on you, how can you forget that so easily, kin manta a Nedd Grocery, kin buge My grandma kika ce mata ke wace irin bahuwar tsohuwa ce, bakya kallo neh ehh tsohuwa, kin manta ni, ni da kika saka wasu yan ta’adda suka mini duka, kamata yayi ace dakika shigo nan kice na yafe miki laifukan da kika mini not laifin da kika mun, zan iya yafe miki na jiya, but I cant forgive you abun da kika yiwa Hajja, kakata, wanda nake sonta fiye da kaina, now just get out of my office before I loose my temper”, zata durkusa yace mata cikin tsawa
“I said get out”, tashiwa tayi tana goge hawayen ta tafita a office d’in, zama tayi a motar ta, wayar ta tad’auka ta kira Ummi tace
“Ummi yau a gidan mu zan kwana, inaso na had’a kayaki na gaba d’aya,daga gobe a wajen ku zan fara kwana”
Ummi tace “koh kefa Khairiyya, toh ai da kinsa an kwashe miki kayakin”
“No Ummi bazasu kwashe mini yadda nake so baneh, baza su san abubuwan da nake bukata ba, idan na tashi a makaranta anjima zan je gida, gobe da sassafe zan dawo”
“Ohk toh shikenan, zan sa Ammar yaje ya tayaki kwasan kayan, sai ya tayaki kwana ma, but Khairiyya ya naji muryar ki haka anya lafia”, Khairiyya ta kwakulo murmushi tace haba Ummi kalau nake, yanxu zan shiga lecture bye, ta katse wayan
Fisgan motar ta tayi ta wuce gidan Ammar wanda yakai ta lokacin, horn da karfi tayi mei gadi ya bud’e mata gate, Ammar ma baya gidan, bud’e fridge tayi ta kwasa kwal6an giya guda biyar tasaka a motar ta, fisgan motar tayi sai International Hotel, ta biya kud’in d’aki na kwana d’aya, tana shigan d’akin ta zube akan gado tafara kuka mai tsuma zuciya, ta rasa mei yake mata dad’i, ga Abba yana prison, ga Ammi bata damu da harkan ta da Abban taba, ga son Zilyadeen, da wanne zanji dashi Yaa Rabbi
Bud’e kwal6a tayi ta saka a bakin ta sanda tasha rabi tukun ta cire a bakin ta, ta kara tusa kwal6an a bakin ta sanda ta shanye tas tukun tacire shi a bakin ta, wani bacci mei nauyi neh ya d’auke ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button