KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Zubewa a kasa tayi ta fashe da kuka, kuka take sosai kamar wanda ranta zai fita, kusan awa d’aya tana kuka ba tsayawa atake kuma naga ta d’auka papers d’in ta duba saman, UMTH tagani, bud’e ido tayi tana tunani, can kuma sai ta kara fashewa da kuka tana bubbuga kafan ta, bayan tayi kuka ta kara duba papers d’in sai kuma ta fashe da dariya, dariya take kamar wata sabuwar kamu, tana dariya tana hawaye, idan tayi dariya sai kuma ta fashe da kuka, tashiwa tayi ta d’au wayan ta da sauri

Nana fa’ad En Eesha

????????????????????

07034419520

????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

Thanks soo much E’eeshmal????????????

4 masu son novel din daga farko
www.narhnah.mywapblog.com

[Page 64]

 A take tayi dialing number Kamalu badd, ajiye wayan tayi akan dressing mirror tana safa da marwa a cikin d'akin wayan kuma yana loudspeaker yana ringing, har ta katse bai d'auka wayan ba, wayan ya kara dialing da kanshi da yake yana automatic dial, ringing d'aya biyu Kamalu badd ya d'auka wayan yace

“Hello hajiya, ranki dad’e ina gaisuwa kaina a kasa”, wani dogon tsoki taja tace
“Kayi sa’a Kamalu badd, had it been bakayi picking call d’ina ba da sai na saka guys sun fasa mini your stupid water melon (meaning har6e mishi kai), har kai ka’isa nakira ka a waya kaki receiving call d’ina, who the hell do you think you are”, bayan ta gama masifan ta Kamalu badd yace
“Haba hajia kinsan bazan miki haka ba, bakida labari an kulle ni a cell neh”
“Mtseww wannan kai ta shafa, zaka iya tuna Doctor Umar”
“Kut! Likita Umar zakice Hajia” Sai ya fashe da dariya yacigaba “Haba hajia ai bana manta mutane, na isa na manta da likita Umar, tab ai bazan ta6a manta dashi ba haka zalika shima bazai manta da mu ba”, Khairiyya tace
“Gooood, very good, yanxu kana ina”
“Ina cikin gari hajia, yanxu haka ina benishek”
“Mtswww ka cika shirme Ka shigo Maiduguri yanxu yanxun nan, ka nema mini doctor umar, duk inda yake ka kira ka sanar dani”
Kamalu badd yace
“Toh hajia angama, yanxu ma ina hanya”, Khairiyya ta katse wayan abun ta, wardrobes nata taje ta bud’e su tana kallo daga sama har kasa, kayaki neh makil aciki koh boutique albarka, taja wani dogon tsoki tace
“Gosh yanxu wani kaya zan saka, hannun ta tasa a kanta gashinta ya tarwase ya sauko ya rufe mata fuskan ta, ta kara jan wani dogon tsoki ta maida gashin baya, tace yau zanyi shigan ba mutunci, wani dogon skirt yar kanti ta d’auka, sai wani vest armless red, da wani black coat na mata ta d’aura a kai, zama tayi a gaban mirror ta tsara kwalliya, make-up kit nata kawai abun kallo neh ya cika dressing mirror ta, ta kai kusan awa d’aya ta painting face nata dan yafi karfin ace kwalliya sai dai painting dan ni kaina nagaji da jiran ta gama make-up d’in na d’auka biro na da takarda ta nafita a gidan na tara napep dan ya kaini gidan su Zilyadeen

Zilyadeen zaune a d’akin sa yana duba lecture note a personal computer shi, Rumaysa tashigo d’akin tasha kwalliya da wani mini skirt da half top a jikin ta purple, Masha Allah ba laifi ya amshe jikin ta, yana d’aga kai ya kalle ta a take ya saukar da kansa, durkusa wa Rumaysa tayi har kasa tana hawaye tace
“Husby dan Allah dan Annabi ka yafe mini, ina matukar sonka shiyasa nake masifan kishin ka, but yanxu na sauko, kayi hakuri Nural Hayat d’ina, please” tana hawaye, shi kuwa koh kallon ta baiyi ba yacigaba da danne dannen sa akan personal computer sa, Rumaysa ta kama hannun sa tace
“Nurul Hayat na yarda, na amince zan zauna da Khairiyya a matsayin abokiyar zama, na amince ka aura Khairiyya”, wani kallo ya mata yacigaba da aikin sa yace
“Please you are disturbing me can’t you see i’m busy”, Rumaysa tana hawaye tace
“Haba Nurul Hayat, ya kakeso nayi da rayuwa ta, hawan jini ai sai yakamani, so kake zuciya ta ta buga, you know I love you sooo much, I love you Nurul Hayat, fushin ka ba karamin tashin hankali yake sakani ba, wlh Allah nayarda ka aura Khairiyya, kuma nayi alkawari zan zauna da ita da zuciya d’aya, zan zauna da ita tsakani da Allah”, sai ta fashe da kuka, Zilyadeen ya tausayi ainun, d’ago ta yayi ya rungume ta, yana shafa bayan ta yace
“Shhh wify, please stop crying, kinsan bani son kallon ki kina zub da hawayen ki, I also love you very much, but ai yanxu is too late, Khairiyya auren ta saura two weeks”, a take Rumaysa ta raba jikin ta da nasa tana kallon sa tace
“Are you serious husby, waye zai aure ta, Ammar”, Zilyadeen ya girgiza kansa yace
“General Suraj”, Rumaysa tace
“Allah sarki, but karka damu kanka, idan Khairiyya matar kace toh tabbas saika aure ta”, Zilyadeen yana mei shafa fuskan ta yace
“Zanyi missing Khairiyya, but ki saka ni addu’a Allah kawo wata mei kama da Khairiyya, ni koh mei irin voice nata ma”, Rumaysa ta d’an bugesa a chest yace “wshh wify da zafi”, ta tura bakin ta tace bawani addu’a da zan maka, ya rungume ta yana dariya, daga nan aka canza salo nidai nana fa’ad naja doguwar bak’in hijabi nah na bar musu gidan na kara tsaida napep dan ya kaini gidan su Khairiyya na d’auko muku rohuta

 Khairiyya tayi shirin ta tsaf, komai in black tayi har takalmi Nick heel black, ta toshe sexy eyes nata da black sunshade glass, Kiran Kamalu badd tayi tace

“Kamalu naga message naka are you sure yana Barwee”, Kamalu yace
“Yana Barwee hajiya ta bayan building wajen garden”, Khairiyya tace yawwa good, ka samei ni a gida bayan 2hours, ta katse wayan…… fisgan motar ta tayi Ferari black ta bar gidan sai Barwee Maid, tana shiga tayi parking motar ta tawuce bayan building d’in wajen garden, hango Doctor Umar tayi yana shan cigarette da wata yarinya tana facing d’ayan side d’in bata samu ganin fuskar wacece ba, da tafiyan ta mai d’aukar hankali har ta iso wajen, tana zuwa ta masa wani lallausar murmushi tace
“Weldone Umar, Weldone”, tana tafa hannu, Doctor Umar shima yana murmushin mugunta yace
“Thank you KIM”, ta zauna a kujera sai tajuya taga yarinyan da suke tare, to her own Suprise taga Munay the beauty, Khairiyya ta kara fashewa da dariya tace
“Weldone Munay, you really impress me”, Munay ma tana murmushi tace
“Suprise Suprise Suprise”

Masu karatu Thanks all for reading, Kunsan ina zuwa school that’s why watarana bana posting sometimes kuma ina pages kad’an please bear with me

Mabcie tace na cika jan rai ???????????????? Sorry dear kinsan ya school yake…. Much Lurv????????????????

Nana fa’ad En Eesha

[11/22, 11:49 PM] ‪+234 806 524 6449‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Nov, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 65]

Khairiyya tace “wow Munay kin burge, but don’t you ever think wannan small thing d’in zaiyi surprising d’ina, ain’t suprise gurl, but lemme ask you something”, Munay tace inajin ki, Khairiyya ta gyara zama ta zuba Ribena drink dake gabanta tayi sipping kad’an tace
“Kina taimakawa Umar neh or kina da your own reason da kikayi haka”, Munay ta girgiza kanta tace
“I am not helping Doctor Umar, inada my own reason da nayi haka”, Khairiyya tayi dariya tace
“You love him right”, Munay itama tayi dariya tace
“I love his money da power/position shi”, Khairiyya ta girgiza kanta tace
“Toh ke har yanxu karamar yarinya ce, baki kai kizama enemy nah ba, baki kai muna competition dake ba, koh kad’an ke ba class d’ina bace, at 1st na d’auka ke wata babban yarinya ce, sai yanxu na rena ki na raina wayon ki, is better kiyi giveup tun yanxu Munay dan wlh Allah bazaki iya ja dani ba, da kince Son shi kike da bazan raina kiba cos ance everything is fair in love and war, but da kikace dan kud’in shi da matsayin shi naji na raina ki sosai”, Munay ta fashe da dariya tace
“A ganin ki ba, mu zuba mu gani mana”, Khairiyya tace
“Kinyi kadan na zuba dake yarinya, In Shaa Allah bazaki aura Suraj ba koda ni ban aure sa ba, sabida Suraj mutum neh mei hankali, baiyi deserving cheap slut like you ba, he deserve someone better, someone better than ni kaina”, Munay tace toh ki hana idan har ke kin cika Khairiyya Ibrahim Muhammad fu’ad mai naira, Khairiyya tace “hmmmm bani da time naki”
Munay the beauty ranta idan yayi dubu ya 6aci, d’aukan jakan ta tayi tabar musu wajen,bayan ta tafi Khairiyya ta juya kanta wajen doctor Umar, tace
“Doctor Umar kenan, ka bani kunya tunda kana jaa da kanwar bayanka, tun ranar da kace sai kaga bayana, sai ka caka mini wuka a ciki tun ranar nake jiran ka, na d’auka ka hakura ashe baka hakura ba, yanxu muna 1:1, inada 1 kana da one, acikin 7days duk wanda yake da 2 toh yayi winning”, Doctor Umar yace
“7days ai yayi yawa, Khairiyya kamar yadda na ta6a gaya miki sai na kashe ki da hannu nah toh yanxu na janye, idan na kashe ki nine da asara, gaba d’aya zunubin ki za’a d’aura mini, the best thing da zanyi nayi revenge shineh na saka miki kunci a rayuwar ki har abada, duk wani d’a namijin da zaizo da sunan zai aure ki sai na hana sa, sai na raba ki da masoyan ki kaf kamar yadda kika rabani da matata, wanda har duniya ta kare bazan ta6a samun irinta ba, wanda nake son ta fiye da komai a rayuwa ta”
Khairiyya tace “halinka neh ya rabaka da ita bani ba”, ta tashi ta d’au jakan ta tace
“The game begins now, bye”, ta tafi, Doctor Umar yayi murmushi yace “har yanxu ke yarinya ce”, ya cigaba da shan cigarette nasa, Khairiyya gida ta wuce direct, tana zuwa bakin gate ta kalla motor su Kamalu badd, ganin motar ta suka sauka a motar su itama ta sauka a nata motar, Kamalu badd yace
“Hajia an gaishe ki”, Khairiyya tace yawwa, Doctor Umar yana son yayi revenge akan abun da muka masa”, Kamalu badd yace
“Hmmm shi asu wa, ai lokacin ma sa’a yaci”, Khairiyya tayi murmushi tace
“Zan neme ku daga yanxu zuwa dare”, duk suka ce “Toh shikenan hajia”, Khairiyya tashiga motar ta ta danna horn mai gadi ya bud’e gate, da gudu ta shiga gidan, tana shiga cikin haraban gidan taci karo da Teema, Teema tace
“Yanxu nake shirin bar miki gida uwar yawo”, Khairiyya tace
“Yanxu ma zaki iya tafiya ai”
Teema taja tsoki tace “ki koreni yar rainin hankali kawai”, Motoci neh har uku suka danno kansu cikin gidan, daga ciki har da motar Abba, Khairiyya tace
“Teema kinga mushiga ciki”, taja hannun ta suka shiga cikin side na Khairiyya, bayan sun zauna Teema taci tasha Khairiyya kuma tana buga game a wayar ta dan tana fashen sallah, Teema tace
“Wai ni KIM yaushe Mr handsome zai dawo neh”, Khairiyya ta d’aga kai ta watsa mata kallo tace
“Waye kuma Mr handsome ni ban sanshi ba”, Teema tace
“Haba KIM, Toh Yaya Ammar, the handsome guy on earth”, Khairiyya ta wani ja dogon tsoki tace
“Nima ban sani ba, ga number wayan sa ki kirasa ki tambaye sa”, ta mika mata wayar, da sauri Teema ta kar6a wayar tayi copying number Ammar tace “Thanks besty”, Khairiyya ta kar6a wayan batace kala ba, game take da wayan ta amma sam hankalin ta baya kan game d’in tana tunanin Suraj, ita bata ta6a tsammanin abun zai damei ta haka ba, bata ta6a jin tana kaunar sa ba amma taji bak’in cikin fasa auren da yayi, Teema ce ta katse mata tunanin ta tace
“KIM Wlhy dafa yanxu mun zama yan uwa, kinga kin aure yaya Zilyadeen ni kuma na aure AMMAR”, Khairiyya ta kara jan wani dogon tsoki tace toh malama ya ishe ki haka please, bata karasa maganar ba Abba ya bud’e kofan parlour ta, Teema ta durkusa har kasa ta gaishe shi ya amsa mata yana mai fara’a yace wa Khairiyya
“Baby ki saka hijabin ki kisamei ni a parlour”, Khairiyya ji tayi zuciyan ta ya buga tace Toh Abba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button