KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan sati biyu

Khairiyya ta samu sauki sosai ba abun da yake damun ta, sai memory ta da tayi loosing neh har yanxu bai dawo ba daman suma basu saka a rai zai dawo yanxu ba, Doctors sun gama duba ta har an rubuta musu takardan sallama, Abba ya siya musu gida a New Delhi d’in kusa da Asibitin, Doctors sun sallame su akan za su na kawo Khairiyya for check up after every 3weeks

Gida neh mai kyau 3 bedroom sai parlour biyu, da kitchen, Ammar ya d’auka d’aki d’aya, sai Khairiyya da Zaynab ma d’aki d’aya, da wata mei aikin su mei suna Priya, bayan kwana uku Zaynab ma ta koma Nigeria, daga Ammar sai Khairiyya da kuma Priya, Priya tana kwana da KIM a d’aki d’aya Bayan tafiyan Zaynab Khairiyya ba aikin ta sai kallon Indian Film da tsokanan Ammar, ta maida shi kamar wani kakan ta
Zaune take a parlour tana kallon Sanam Teri Kasam ga handkerchief kusa da ita sai faman hawaye take tana sharewa, daga baya kawai sai ta fashe da kuka, Ammar dake zaune a can gefe yace
“Ke mu mei wannan, zan kashe Tv fa”, Khairiyya ta juya ta kalle sa tace
“Ammar kaga yadda ake soyayya, hmm shin Ammar kasan ya SO yake dan ni gaskia ummm na manta”, take yaji zuciyan sa ya buga ya tashi yashiga d’aki abun sa ya barta ta cigaba da kallon film ta

Da daddare Ammar yana zaune a parlour kawai sai ya fara jin gidan na waren konewan abu , da gudu yashiga cikin gidan yana kiran sunan Khairiyya, yana duba kitchen kawai sai ya ganta, kitchen d’in duk hayaki sai tari take ga wuk’a da albasa a hannu, da gudu ya kashe gas cooker ya fitar da ita a kitchen yace
“KIM mei wannan, so kike ki kona gidan” tace
“Abinci nake so na girka”, ransa ya 6aci yace
“Are you stupid, are you out of your senses, idan yunwa kikeji ba sai ki fad’a na kaiki kici abinci ba”, Khairiyya tana hawaye tace
“Bana jin yunwa, m just trying to cook for you, kullum sai kana santin abincin Priya kana cewa wow wow nice cook, nima shiyasa yau nake so na maka Ammar”, tausayin ta yaji sosai yace
“Ba sai kinyi stressing kanki ba KIM, meisa kike son kiga na yaba ki”, ta d’aga kai sama kamar tana tunani tace
“I don’t know why, all what I know shineh ina jin wani iri duk lokacin da kake yabon abincin priya, nima inaso naji kana cewa wow wow KIM”, Ammar yace
“Haba taya zaki had’a kanki da Priya, you mean alot to me, I like you KIM”, tace
“More than priya”, yaja tsoki yace
“More than Priya, far more than her”, Khairiyya tayi murmushi, yace kije ki canza kayan ki muje muci abinci, da gudu ta hau sama ta canza kayan ta, wani restaurant ya kaisu suka ci abinci, bayan sun dawo gida around sha d’ayan dare Ammar yace
“Hope kinyi isha’i before mu fita”, Khairiyya ta d’aga kanta tace Nayi, yace Yawwa Good gurl yanxu kije ki kwanta, kamasa Khairiyya tayi tace
“Ina tsoro Ammar, kasan da Priya nake kwana gashi bata nan sai dai mu kwana tare”, haka suka tayi dashi da kyar ya bita d’akin ta ya kwantar da ita akan gado shima ya nema dogon kujera can nesa da ita ya kwanta but suna facing juna, Khairiyya ta kalle sa tace
“Ammar tell me a story”, Ammar ya zare idon sa yace
“Story kuma KIM”, Khairiyya tace eh kuma sam sai ya bata story before tayi bacci, tace
“Nifa bana iya bacci ba tare da an bani story ba”, Ammar yaja tsoki yace yau sai dai kiyi hakuri mai baki bata nan
Kawai sai ta fashe masa da kuka tana bubbuga kafan ta, Ammar yace “shikenan yi shuru kiji”

Once Upon a time, there was a handsome caterpillar
Khairiyya tayi dariya tace Ammar caterpillar kuma, Yace shhh let me finish please, Khairiyya tace
“Ohk Monster”, yacigaba

This handsome caterpillar had everything in life he could wish for. Green leaves to eat all day, green branches & ground to crawl on, green skies & green friends he could enjoy. And then he started to notice that everything was green. Different shades of green & all around him was green
Khairiyya abun ya d’aure mata kai ta kasa fahimtar koh kalla d’aya, tace
“Ammar Even the Sun”, Ammar ya d’aga mata kai yace
Even the Sun KIM, He survived but he never really lived. Green was suffocating him. Green was his prison. Green to him was black, it was darkness. So he crawled on the green grass, searching without knowing he was searching
Khairiyya ta zare idonta tace
“Weird Ammar, what was he searching for, mei yake nema”
Ammar ya tashi daga kan kujeran da yake kwance yana kallon ta, yace
“Colour”
Wani dogon tsoki Khairiyya taja tace Nifa ban ganeh kan storyn nan ba, it’s so complicated, so confusing, kawai yana neman colour, yayi mei da colour, mtsww boring story I swear, Ammar yayi murmushi yace
“Naji boring story ai sai kiyi bacci tunda kinji story”, ya tashi ya tofa mata addu’a, shima ya koma kan kujeran da yake dan bacci

Nigeria

Suraj da Munay neh durkushe a gaban Zaynab suna rok’on ta Allah da Annabi akan ta gaya musu inda Khairiyya take, Zaynab ta tausaya musu sosai dan for the past wata takwas kullum sai Suraj da Zil sunzo suna rok’an su information inda Khairiyya take, Zaynab tace
“Yaya Suraj tana India, New Delhi”

????????????????????????

Nana fa’ad En Eesha
[11/22, 11:49 PM] ‪+234 806 524 6449‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Nov, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 70]

Zaynab ta basa address na inda suke zaune a India, Suraj da Munay suka ringa zuba godiya, zasu fita a gate kenan sai ga Zil shima yashigo gidan, gaisawa kawai sukayi Suraj suka fita a gate d’in Zil kuma yashigo cikin gidan, Ummi ya samu a falo bayan sun gaisa da Ummi yata rok’on Ummi akan ta gaya masa inda Khairiyya take, Ummi tace
“Saidai kayi hakuri Zil dan mahaifin ta yace kar a fad’a wa kowa inda yarsa take”, haka yagaji da magiya ya tashi ya tafi, yana tafiya Ummi ta kwala wa zaynab kira, Zaynab ta amsa ta fito a d’akinta ta durkusa, Ummi tace
“Karki kuskura ki fad’a musu inda Khairiyya take komai rintsi kinji”, Zaynab taji zuciyan ta ya tsinke cos already ta fad’a wa Suraj, tace Toh Ummi In Shaa Allah

Bayan kwana hud’u a India

Khairiyya ce zaune a gaban Tv tana kallon Indian Film as usual Dilwale, bata da aiki daman kullum daga Ammar yana koya mata karatun Al Qur’an sai kuma kallo, Ammar ya ajiye duk wasu aikin shi yana kula da ita, tun ana aiko mishi yazo har suka gaji aka tura masa sunyi firing nasa, Yana aiki a wani company dake Russia, Knock da Khairiyya taji da gudu ta tashi tana Ihu
“Yehhhh Zaynab ta dawo”, da shike sunyi waya da Zaynab tana mata wasa tana hanya, Ammar shi kuwa kallon ta yakeyi kawai, bud’e kofan da zatayi yayi ido hud’u da Suraj, da sauri ta koma baya, dafe kanta tayi dan yana tsara mata sosai, zata fad’i kenan Suraj ya cafko ta, dai dai nan Ammar yazo wajen, ganin Suraj rik’e da KIM ransa ya 6aci sosai, da sauri ya raba Khairiyya s jikin Suraj, yace
“How dare you touch her”, Suraj yace
“Sorry bro naga zata fad’i neh”, Ammar ya masa tsawa yace
“And so bloody what idan zata fad’i, don’t you ever think of touching her with your filthy phalanges” cak Ammar ya d’auke ta sai d’aki, bayan ya dirata akan gado ya koma parlour yaga Suraj a tsaye, Ammar yace masa
“Please dan Allah kabar mini gida, har yanxu batayi recovering memory ta ba”, Suraj yace
“Karka damu, ba abun da zan fad’a mata or anything kawai inaso na ganta and kuma ta saba da ni neh please”, Ammar yace shi fa sam bai yadda ba, dole Suraj ya bar masa gida, bayan ya kore Suraj ya koma d’akin Khairiyya, yazo bakin gadon yace
“KIM are you ok”, ta d’aga kanta, tace
“Ammar waye wancan, seems like I know him”, Ammar yace
“KIM kar kiyi stressing brain naki baki sanshi ba, he’s my friend and kuma wannan shine karon farko da yazo gidan nan”, Khairiyya tace
“No nasanshi koh a dreams nah”, Ammar yace shhh KIM kwanta kiyi bacci, tace Ammar film d’in fa, Ammar yace Film sai gobe na yau ya isa, Khairiyya ta tura baki tace but yanxu fa safe neh, Ammar yace
“I know nace sai gobe koh”, Khairiyya ta tura bakin ta tace toh mei kama da Monster

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button