KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan tasha kukan ta tafara dariya ita kad'ai kamar wata sabuwar kamo, tace wlhy wlhy Rumaysa kin ta6o ruwan dafa kanki da kanki, Rumaysah kin ta6o tsuliyar dodo, zan nuna miki Wacece Khairiyya, yanxu nafara kwad'ayin zama tare dake a matsayin kishiya ta, dariya take kamar wata zararriya, ita kad'ai tasan abunda take shiryawa a ranta, Zainab ce ta shigo d'akin da sauri tace

“KIM lafian ki kuwa”, Khairiyya ji tayi yau tana son hira da zainab, tunda suke basu ta6a minti talatin mei kyau suna hira batare da sunyi fad’a ba, dan masu karatu na fad’a muku a baya Zainab ustaziyace kuma tana son fad’an gaskia koh da gaskian zai 6ata maka rai, Zainab tace
“Answer me please KIM mei yake damun ki haka”, Khairiyya ta zauna tabata lbrn abun da yafaru daga farko har karshe, tana fad’a tana kuka tana dariya, can you imagine Zaynab Rumaysa har tana da bakin da zata ce mini wai Allah kad’ai yasan mei nake aikatawa ni kad’ai a babban gida, mei take nufi kenan, so take tace mini ni yar iska ce, kuma ina shaye shaye, ama drug addict, but anan nasan batayi karye ba, na yarda, kuma harda cewa ita d’in Yar Gida ce ni kuma bare ce, zan nuna mata cewa Bare tana zuwa tafi yar cikin gida walawa da samun waje, zan nuna mata cewa…. “, bata karasar da maganar ba Zaynab ta rufe mata bakin ta tace
“KIM karki afka babban kuskure a rayuwar ki, karki 6ata rayuwar ki akan wata daban, Khairiyya aure ba abun wasa baneh, da zakibi shawara ta kawai ki manta da Zilyadeen da Rumaysa, ki shafe su a babin rayuwar ki, da zakibi shawara ta zance miki Khairiyya a duk duniyan nan ba namijin da yake sonki kamar Sur a’a AMMAR, Khairiyya nasan dacewa Ammar yana sonki yana kaunar ki amma ke sam baya gaban ki, kin d’auke shi as a brother neh kawai, but try and give him a chance KIM”, Khairiyya tace
“If only zan iya but I just can’t, he’s a brother to mee and nothing else, idan kinga ban aura Zilyadeen ba toh ban cika Khairiyya ba, Zaynab kinsan ni farin sani, banjin son auren Zilyadeen amma ina sha’awar shiga cikin gidan sa badan komai ba sai dan Rumaysa, I really wannan show her my true colour, she must regret what she told me”, Zaynab ta girgiza kanta ta kama hannun Tace “Khairiyya kenan, lemme advice idan har kina son kanki Toh Khairiyya karki fara, Khairiyya karki fara, idan ma bakison Ammar why not SURAJ, Khairiyya just don’t try that, you are young and beautiful don’t ruin your life, kuma zan kira Yaya Ammar na fad’a masa abunda kike shirin aikatawa, Abba da daddy suna zuwa zan sanar dasu, barama kiga na kira Yaya Ammar tun yanxu”ta d’auka wayar ta dan kiran Ammar Khairiyya bata dakatar da itaba dan tana son jin muryan sa, tace
“Zaynab sa mana a loudspeaker “, Zaynab ta saka a loudspeaker yana ringing, Ammar ya d’auka wayan yace
“Yarrr swt ustaziyas Sis yakike”
“Lau Mallam”, yayi dariya yace yau kuma nineh Mallam, lalle yarinyan nan yanxu kin raina ni dan kinga bana kusa koh”, Zaynab tace
“Yaya Ammar kasan mei yafaru, kayiwa Khairiyya fad’a”
“Mei Khairiyya tayi”, zuciyan sa yana mei bugawa, Zaynab ta basa lbrn duk abunda yafaru, yace yanxu ina KIM d’in take, Zaynab tace gata nan tana jinka, Khairiyya a take ta kar6a wayan, tacewa zaynab tashi kibar d’akin nan idan mun gama wayan zan kiraki, Zaynab tana dariya tafita a d’akin tace kudai kuka sani, Zaynab tana fita a d’akin Khairiyya tace
“Yarrrr I miss you alot alot alot, infact more than alot”, Ammar shuru yayi baice komai ba, dan har ransa da brain da Jinin sa yaji maganar ta, ba karya shima yayi missing nata sosai
Yace “I miss you more JAAN”, kawai sai Khairiyya ta fashe da kuka tace
“Bawani Mr Ego, bakayi missing nawa ba, I called you several times but you ain’t picking my calls, ba ranar da bana tunanin ka, I miss you sooo very much please come back soon”, Ammar yafi minti biyu kan yace
“Don’t worry KIM, zan dawo very Soon”, sunfi awa d’aya suna waya yana bata shawara yace mata
“KIM kar iya ruining life naki akan wata Rumaysa, you know what’s best for you”, bayan yabata shawarwari tace
“Nagode Ammar, thanks alot, In Shaa Allah zanyi yadda kace, na fasa auren Zilyadeen, ka tayani addu’a Allah za6a mini Mafi alkhairi, thanks” a zuciyar cewa take auren Zil kam kamar nayi
“Never say thanks and sorry KIM, kin manta I am your best friend, what are friends for? “Cewar Ammar
Tayi dariya tace “and you will always be my best friend bye, and take care please, kar matan can su saka maka ido, you know I dont like it idan mata suna falling maka” yayi dariya yace nasani KIM, bye ya katse wayan
A can Russia Ammar neh rike da waya a hannun sa, yace In Shaa Allah KIM, KE TAWA CE

     Ranar Saturday da misalin karfe goma aka d'aura auren ZILYADEEN USMAN ABDALLAH DA RUMAYSA A SADAKI SISIN GOLD GUDA GOMA







    Nana fa'ad En Eesha

????????????????????????
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

[Oct, 2016]

 Written by Nana fa'ad En Eesha

{Page 58}

    A ranar Khairiyya tana cikin kunci Rumaysa kuma tana cikin farin ciki, Anyi aure lafia, ba'ayi wani events ba sabida ango Zilyadeen bayaso, daga walima sai walima shima dan Rumaysa ta nace dole sai anyi, a daren Ranar akakai amarya gidan ta, gida neh madaidaici da d'aki uku parlour biyu,kitchen biyu,  komai na gidan unique cos mostly kayan ordering akayi daga turai..... 
Misalin karfe goma na dare Zilyadeen yashigo cikin d'akin Rumaysa da leda a hannu, ya zauna kusa da ita yace Amarya bata laifi koh ta kashe d'an masu gida, itadai Rumaysa fuskan ta rufe da gyale sai sautin kukan ta kawai akeji, dakyar ya lalashe ta taci kaza da drinks daya kawo, bayan sun gama ci ya sakata wanka da alwala shima yayi, bayan nan sukayi sallah suka gode wa Allah daya nuna musu wannan ranar, daga nan Zilyadeen ya fara canza salo, dole Rumaysa tabada kai bori yahau, a daren ranar ya mata alkawari kala kala, daban daban dan Rumaysa tafitar dashi a hankalin sa, a cikin alkawarin harda Ni Mijin mace d'aya neh Rumaysa, bai saurara mata ba har sanda bakin ta ya mutu dan kuka sai sauke numfashi kawai take, nidai nace ya'isa haka naja Eesha muka bar musu d'akin..... 

Washegari da safe Khairiyya da Zaynab suka je gidan Alhaji Ibrahim Muhammad fu'ad , khairiyya tana shiga cikin gidan taga ko'ina kura, ranta idan yayi dubu ya 6aci, ihun kiran sunan Haule, Indo da Dije tafara, sai gasu nan a gaban ta, ta watsa musu kallo tace

“Wannan wani irin iskanci neh, wato dan kunga bana gidan shineh kuka bar gidan haka, daga ku kalla TV sai ku dafa abinci kuci koh” duk dai basu tsaman Khairiyya zata musu zuwan bazata ba, ihu tayi tace
“Ina tambayar ku kuka mini shuru, lalle ku d’in nan, Toh yanxu ku d’au tsintsiya ku share da mopping gidan nan tas, daga kan d’aki na har na Abba, toilets na gidan nan gaba d’aya ku wanke su tas, idan gidan nan banga yana kyale yana shinning batoh a bakin aikin ku,ku tashi ku bani waje”, duk suka tashi a take suka bar wajen, Zaynab tace
“Haba Khairiyya wannan fa bai kamata ba, baki ganin sun girme kine”
“Dan sun girme ni sai mei, ina biyan su nake, kinsan nawa nake biyan su every month kuwa mtswww”, Khairiyya da Zaynab suma suka canza kaya riga da wando suka zage suna aiki, su Haule sai mamaki suke yau hajiya Khairiyya dakanta tana aiki, ikon God

A gurguje pls

_International Airport Maiduguri_

Ranar monday da misalin karfe hud'u na yamma Khairiyya nagani da Ummi da kuma Zainab acikin airport, sai duba agogo suke duk hankalin su a jagule, Khairiyya sai aikin jan tsoki take, karan jirgin da taji kamar zai toshe mata brain yadawo da ita daga tunanin da tafad'a, ba'afi minti talatin ba wani dogo farin mutum mai kyaun gaske wanda a kalla bazai wuce arba'in da takwas ba tare da Uncle Hisham dukkan su rike da akwati a hannu, Khairiyya da gudu taje ta rungume mutumin tace Abba nah I miss you so much tana kuka, shima ya rungume ta yace I missed you more my baby, haka ta kankamei shi shi sanda Ummi tace 

“Haba Khairiyya ai kya bari yasha iska” duk sukayi dariya, Uncle Hisham yace
“KIM kinga Abban ki shine koh gaisuwan nan babu”, Khairiyya tace “so sorry uncle”, yayi dariya yace nidai kam nayi fushi Gaskia…. Gidan Uncle Hisham suka wuce, bayan sunyi wanka sun ci abinci sun huta Abba yace zai tafi gidan sa, Uncle Hisham yayi yayi dashi ya tsaya amma yace shi sam a gidan sa yake son kwana, haka Abba da Khairiyya suka shiga mota suka dawo gida, masu aiki sai zuwa kwasan gaisuwa suke, yau maigidan Oga ya dawo gida after two years, Abba da Khairiyya sunkai karfe biyun dare suna hira, Abba yace
“Baby nah yanxu fa karfe biyu kiyi sallah ki kwanta bacci koh”, Khairiyya tace eh kaima bara na barka ka huta, gudnyt Abba nah. … yace gudnyt babynah

   Sati d'aya shar ana cin Amarci, tun ranar da aka d'aura masa aure da Rumaysa bai kira Khairiyya ba, Khairiyya ranta yayi mugun 6aci takira sa ranar auren sa ta masa congrat amma baiyi picking call d'in ba kuma bai kirata ba tace wato dan yayi aure shineh harya manta dani, lalle kam zanyi maganin sa

Suraj kuma tun ranar da Abba yazo kullum yana sintirin zuwa gidan, haka har suka saba da Abba sosai har zama suke suyi hira, Abba yana kaunar yaron sosai idan Suraj yayi kwana biyu baizo gidan ba har Abba yana kiransa a waya yaji koh lafia, sosai suka saba dashi, yanxu ma Khairiyya ta sake da Suraj sosai, duk mai kaunar Abban ta toh itama tana kaunar sa…… Ammar har yau bai kirata ba, ta kar6a number wayansa a wajen zaynab idan takira sa baya picking call d’in, Ammar yayi mugun 6ata mata rai, wani dogon tsoki taja tace Ammar zanyi maganin ka, Khairiyya zaka wulakanta koh, d’au wayar ta tayi ta turawa Ammar text message kamar haka
mtswwwwwwww GO TO HELL, JERK

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤
Zilyadeen yayi kiran Khairiyya a waya har ya gaji amma bata picking call nashi, yanxu wani mugun haushin sa takeji, tun da yayi aure bai kirata ba sai kusan bayan sati biyu, ta 6angaren Zilyadeen kuma hankalin sa neh ya tashi da Khairiyya bata picking call nasa, d’aukar mota yayi sai gidan su Ammar, yaje ya durkusa har kasa ya gaishe da Ummi lokacin tana tare da Uncle Hisham, yace Khairiyya lafiya kuwa ina kiranta bata d’aukan wayata, Ummi tayi murmushi tace
“Lafia kalau wlh Zil, kasan Abban ta yadawo so bata cikin hankalin ta Kasan yadda takeson Abban ta yanxu tana gidan su itada zaynab”, yayi musu godiya yatafi akan zaije ya samei ta a wajen, bayan tafiyar sa Uncle Hisham yake tambayar Ummi yace
“Wannan kuma waye haka”
“Zilyadeen lecturer nasu khair, kuma shi ya buge ta lokacin da muka ce maka tayi accident”
Uncle Hisham yace “ayyah Allah sa dai lafia”, Ummi tayi murmushi tace lafia kalau ai sun saba sosai wlhy
[26/10 6:38 PM] Nana Fa’ad: Tun abakin gate securities suka hana sa shiga gidan, yana ta kiran Khairiyya amma stil bata picking na wayan, daga baya ya tura mata message text yace
please ina bakin gate na gidan ku en securities sun hana ni shiga, please kifito
A lokacin daidai tafito a wanka sunyi akan Suraj zaizo da yamma taga shigowar message na Zilyadeen, zura hijabi tayi takira Haule tace
”Inada bako a gate please yashigo ciki, ki ajiye sa a guest room kuma kiyi serving nasa before na fito”, Haule tace “angama hajiya”
Zilyadeen yana cikin motar sa yaga an bud’e masa gate yashigo ciki, sai bin gidan yake da kallo, irin gidan da a rayuwar sa bai ta6a shiga irin sa a nigeria ba, yasan su Khairiyya sun fisu kud’i, kyau ma ba magana sun fisu dan su Ammar da zaynab da ya sani a family ma kad’ai ya ishesa, duk kyaun zuriyan su yasan su Khairiyya sun fisu, ya kara tabbatar wa kansa lalle fa Khairiyya tana mishi Son gaskia, Allah neh ya had’a jinin su… suka gaisa da haule
Haule takaishi guest room tayi serving nashi su drinks da snacks.. Khairiyya bata gama shiri ba sai kusan bayan awa d’aya da rabi, koh wani minti goma Zilyadeen yana duba tsadadden agogon hannun sa Ikia, da sallama tashigo d’akin, Yaa salaam ya furta a ransa, yau tafito Khairiyyan ta na da, tasha kwalliya kamar wata professional make-up artist neh ta mata makeup, kan ta yasha d’aurin d’ankwali, atamfa super wax blue da touches yellow neh a jikin ta d’inkin riga da skirt wanda ya zauna das a jikin ta, da gyale light yellow da touches brown, ba karamin kyau tayi ba,sai zuba kamshi takeyi, tana zuwa ta zauna a kujera ta had’a rai, kasa furta komai yayi sai kallon ta yakeyi kusan minti goma, Khairiyya tace
“Idan bakada abun fad’a toh ni inada abunyi a cikin gida”, he was so suprise, Khairiyya da take sonsa neh itace take masa haka, da kyar ya had’eye miyau bakin sa ya sauka akan kujeran yazo gaban ta yace
“Mss beauty m soo very sorry, nasan nayi kuskuren share kin da nayi, please kiyafe mini”, haka ya mata dad’in bakin da kalamai masu zaqin karshe har ta sauko daga fishin da takeyi suka sha hiran su, dazai tafi yace
“Khairiyya yanxu wajen mummy zan wuce akan maganar aure nah dake, In Shaa Allah ke tawa ce khair, inason ki sosai”, Khairiyya ma tayi murmushi tace
“I love you also”, suka rabu suna mei kewar junan su… (nothing so dangerous like love)

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button