KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

 Ammar neh a International Airport na maiduguri, ga jakan sa a hannu, idon sa fari ya koma kala jaa, yana jin son Khairiyya koh wani 6angaren jikin sa, ina sonki Khairiyya, ban ta6a Son wata d'iya mace haka ba, I soo much love you Khairiyya, Inda Raina zan aure ki Khairiyya, zan kula da ke, I promise to take care of you, I promise to do anything for you Khairiyya, you mean the world to me   *AMKHAIR*... daidai lokacin aka kira sunan sa a masa screening ya shiga jirgi

Khairiyya tana fita Teema ta kirata tace mata
“Khairiyya kizo Mph3 yanxu prof balla zai shiga”, Khairiyya ta amsa da toh ta wuce hall da Teema ta fad’a mata, lecture na awa biyu neh amma ba abun da take fahimta sai tunanin Ammar zilyadeen da Suraj…..

     Daidai karfe biyu zasu fita a makarantar Teema zata kaita gida Zilyadeen yana ta kiranta  a waya taki ta d'auka, sai kuma call nah captain Suraj yashiga, ta d'auka tace

“Hello soja”, yace KIM d beauty ina cikin school naku fa kina ina neh, tace
“Ina science complex ta wajen parking space na mph”, yace ohk ganinan zuwa, bayan kamar minti biyar sai gashi yazo, suka gaisa da Teema, Teema tana ta zolayar sa, Khairiyya ta shiga cikin motar Suraj, tace musu idan ka gama ka samei ni, bayan ya gama da Teema yashiga motar ya fisga, tuki yake a natse yace
“KIM har yanxu baki bani amsa ta ba, kusan wata d’aya kenan, KIM ina kaunar ki ina masifan sonki, please dan Allah mei a zuciyar ki”, ji tayi zuciyan ta yana bugawa, ta rasa mei zata ce mishi, ita yanxu ta fidda rai akan Zilyadeen bawai dan bata sonshi ba, gudun fitinan Rumaysa take, Ammar kuma tana sonshi neh a zaman yayan ta, Suraj kuma harga Allah bata ta6a jin sonsa a ranta ta ba, ina sonshi shima as a brother, kamar yadda nake son Ammmar, kai inaaaa Son Ammmar daban neh I can’t compare it with any other one, Toh mei Suraj ya rasa, yana da ilimi, hankali, addini,uwa uba kyau, bata san lokacin da tace
“Yaya Suraj karka ji komai, Abba na yana zuwa zan fad’a masa”, wow nagode Khairiyya, daman ina ji a jikinah ke tawa ce, inason ki KIM, Inda raina ke matata ce SUKHAIR

Kunji ni shuru wlhy school ya sakani a gaba, kullum busy.... 

 Toh masu karatu, soyayyan wa kuke so kugani

ZILKHAIR or AMKHAIR koh SUKHAIR

 FOR comments 
          07034419520

Nana fa’ad En Eesha

????????????????????

  www.narhnah.mywapblog.com

[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

Page 55

     _*You will never understand how much you mean to me. You found interest in me after all i've done to you when we barely met. I acted as a complete jerk. I was very disrespectful towards you but you still gave me a chance when I asked for. You have shown me that even the person who has made the most horrible mistakes can be loved. You brought out the side of me that I believed I had already lost*_...... tana hawaye sosai, duk ba wanda ya lura da Rumaysa na wajen, Khairiyya ta cigaba da cewa

 _*You're the Man I wish to live the rest of my life with*_

Sai ta fashe da kuka tana gama fad’an haka, Zilyadeen ya d’auke handkerchief fari ya share mata hawayen ta dashi, yace
“KIM, kin furta mini almost all abun da nake son…… “, bai karasa maganar da yake son fad’i ba Rumaysa ta fara tafi, tace lallai namiji namiji neh, Hausawa daman sun fad’a, idan ka d’au na miji Uba toh tabbas zaka mutu maraya.., Namiji ba d’an goyo baneh, idan zaka goye sa ka goye sa da kitse, idan kitsen ta narke ya fad’a kasa, Lallai Zilyadeen, ka nuna mini asalin ka yau, ka manta yadda ka ringa bina for the past three years, shekaru uku kana roka nah nayarda da kai, kana So nah, baka ta6a Son mace bayan ni ba, baka san So ba sai a kaina, amma a sati uku kacal wata ta canza ma tunanin ka, sati uku kacal ka manta soyayyan da kamini na shekaru, a sati uku har zuciyar ka zata iya son wata d’iya mace, ka bani kunya, ka bada ni, ka sani INDA RAINA to wlhy Allah bazan zauna da Khairiyya zaman kishiya ba, ka sani sai dai ka za6a tsakanin RUMAYSA KOH KHAIREEYYAH…….
Ta shiga gida da gudu tana kuka sosai, Khairiyya ta kasa fahimtar komai, Zilyadeen yace
“Khairiyya kishigo mota mu tafi”, tana so tayi magana yace “shhhhhh just kishiga mota na kaiki gida”, ta shiga cikin motar suka bar haraban gidan, tafiya suke kowa da abun da yake sakawa a ransa har suka iso gidan su Ammar, suna shiga cikin filin gidan Ammar kuma zai fita, Ammar koh tsayawa baiyi ba ya fisga motar shi da karfi ya fice a gidan, Zilyadeen yace
“Khairiyya ki saurare ni da kunnen basira, idan nace bana sonki bana kaunar ki Toh na miki karya, ina son ki Khairiyya but bazan 6oye miki ba, nafison Rumaysa fiye da ke, fiye da koh wace mace a duniya bayan mahaifiya ta, tun lokacin da Rumaysa tazo duniya nake sonta, kuma har yau har gobe, til ma last breath… Ban ta6a sawa a raina zanso wata d’iya mace a duniya nan ba bayan Rumaysa, sai gashi kwatsam na kamu da sonki, I also wish to live the rest of my life with you but only idan Rumaysa ta amince, idan bata amince ba dole muyi hakuri da juna Khairiyya, daman a duniyan nan there are things we don’t want to happen but have to accept, things that we don’t want to know but have to learn and people we can’t leave without but have to let go, so muyi hakuri Khairiyya, Auran mu nida Rumaysa nan da wata biyu neh, idan har ta amince sai a had’a ku gaba d’aya, ki sani kar kice na daina son Rumaysa nafara son kine, koh kad’an ba haka baneh, soyayyan Rumaysa har yanxu ba abun da ya ragu a ciki, sai kinji ni a waya”, ta bud’e motar ta fita da gudu tashiga gida, tana shiga cikin gidan d’akin ta direct ta wuce ta kwanta a kan gado tafara kuka kamar wanda aka mata mutuwa
Ummi ce tashigo d’akin tace
“KIM mei yafaru, mei yake damun kune”, Khairiyya batace komai ba ta rungume Ummi tana kuka mai tsuma rai, Ummi sai lallashin ta take tana cewa Khairiyya duniyan nan sai hakuri, every time you get upset at something, ask yourself if you were to die tomorrow, was it worth wasting your time being angry, Khairiyya life is short, duk abun da kikaga ya same bawa to kisani tun can daman Allah ya rubuta zai faru dashi, no one can escape from his or her destiny, nothing can change your destiny except Du’a to Allah, ki kwantar da hankalin ki…….. Haka Ummi ta lallashe ta har ta samu tayi shuru

      Yana shiga cikin gidan d'akin Rumaysa ya wuce direct, a kasa yaganta tana kuka sosai, ya zauna kusa da ita yace 

“Haba Rumaysa, ni da nake kallon ki mei ilimi da sanin yakamata, kar ki bani kunya mana”, ta juya ta watsa masa kallo tace
“awww dole ka fad’a haka ai, tun baka aure taba ka fara kirana nah da jahila “
“Yaushe na kiraki da suna jahila kuma Rumaysa “
“Toh mei kake nufi da cewa bani da ilimi, jahila kenan ai, kuma ka sani Usman, Wlhy Allah saidai ka za6a koh ni koh Khairiyya”, zare idon sa yayi yace
“Haba future wife, har zaki iya barwa wata daban Nural Hayat naki ita kad’ai”
“Sosai ma kuwa idan baka sani ba, zan iya zama da wata daban amma ba khair ba, the decision is yours Zil, koh ni koh ita”
“Rumaysa kinsan ina sonki, kuma bazan 6oye miki ba inason Khairiyya, kar kishi ya rufe miki ido Rumaysa, nayi alkawari zanyi adalci tsakanin ku”
“Toh Wlhy na hakura da kai Zilyadeen, kaje ka aure ta”, tafita tabar masa d’akin gaba d’aya

 Khairiyya yini tayi ranar bataci komai ba, Ummi tayi tayi da ita amma kii taki ci, Zainab ce tashigo d'akin Khairiyya ta zauna kusa da ita, ta shafa fuskan Khairiyya tace

“KIM nasan mei yake damun ki, and I know it’s very painful, abun da yakama daga ni, Ke, yaya Ammar, yaya Suraj duk muna Son masu wani”, da sauri Khairiyya ta juya ta kalle ta tace
“Zainab ban ganeh ba, mei kike nufi, Ke kuma wa kike so haka, har akwai wani d’a namiji da zai ce baya sonki, duk kamun kanki, duk ilimin ki, kina dressing yadda addinin musulunci ta tsara mana, duk kyaun ki, bazan 6oye miki ba kaf family mu a yarinya budurwa banga wacce take da kyau irinki ba”
Murmushi Zainab tayi tace kinsan kowa da irin kyaun sa, maybe kallon tsoro kike min, dogon tsoki Khairiyya taja tace
“Kee a nawa kike da zan miki kallon tsoro, yanxu tell me something, mei kike nufi da kema kina son masu wani, wa kike so Zainab, who do you love”, Zainab tayi murmushi mei ciwo tace Khairiyya no need na fad’a miki cox bazaki magance mini matsalan ba, only prayers zai magance mini matsala ta Khairiyya, kema ina rok’on ki kidage da addu’a, ba komai muke so a duniyan nan alkhairi baneh, ki ringa addu’a idan alkhairi neh Allah tabbatar idan kuma ba alkhairi baneh Allah watsar”, Khairiyya ta rike hannun ta tace Ngd kwarai dagaske Zainab, Zainab tayi murmushi ta rungume Khairiyya tace never say sorry and thanks, what are friends for……..

Suraj a kullum sai yazo gidan su Ammar sunyi hira da Khairiyya, ita har yanxu batajin tana sonsa amma ta saba dashi sosai, ranar da baizo ba zata kirashi a waya taji koh lafia, Zilyadeen neh kad'ai a ranta, idan ta tuna da Rumaysa sai taji zuciyan ta na bugawa, ita yadda ta tsara rayuwar ta ba kishiya, mugun kishin Rumaysa take a halin yanxu, a kullum sai Zilyadeen ya kirata a waya sun gaisa duk da madai basa hiran kirki, Ammar kuma bai kara shiga tsabgar taba, ba abun da yake shiga tsakanin sa da Khairiyya sai gaisuwa, ba karamin damun Khairiyya abun yake ba, a ranar ba kowa a gida daga ita sai Ammar, da hankali ta bud'e d'akin sa tashiga, kwance yake akan gado, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin damuwa, yayi duhu ya rame, gashin kansa yayi tsayi har yafi na Eesha tsowo ba gyara, zama tayi a gefen gadon tace

“Yaya Ammmar”, a hankali ya bud’e idonsa wanda yake a lumshe yace “menene”, tana mai zub da hawaye tace
“I can’t help it Ammar, zuciya ta zata iya bugawa idan kacigaba da shareni, zan iya jure kowa a duniyan nan apart from my Abba, kowa ya shareni Ammar a duniyan nan bazai damen ba but You Ammar bazan iyaba, please Ammar, kasani you are the only brother da nake dashi, I am sooo sorry Ammar kayafe mini, nayi babban kuskure dana ce maka ka tsane ni, I am sooo sorry Ammar kadai na fushi dani”, Ammar sauka yayi akan gado yazo daf kusa da ita yana hawaye kamar mace, kasa furta komai yayi na kusan minti biyar kan yace
“Ba komai Khairiyya, ni yakamata na baki hakuri, na 6ata miki rayuwar ki, sam baki dace da mutum iri nah ba Khairiyya, but ki sani KIM ina son ki, So na hakika, ina kaunar ki, bazan ta6a iya daina sonki ba, dake nake bacci dake nake tashi, your love runs through my blood, you are my everything, you are my life, you are my world, Zuciyata tana dab da bugawa KIM, but bakomai, Allah baki Zilyadeen”, yana gama fad’an haka ya fita a gidan gaba d’aya, kuka ta fashe dashi, a take taji Zilyadeen ya fice mata a ranta, ta rasa ganeh kanta yanxu, ta rasa ganeh wa zuciyan ta yake so… Zil neh, Suraj neh koh Ammar

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button