KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Hijabin ta tasaka tabi bayan Abban ta, tun kan tashiga parlour shi taji maganganun mutaneh, da Sallama tashiga falon kanta a kasa, waje ta nema ta zauna kusa da Abban ta, bayan ta zauna ta gaishe su gaba d’aya suka amsa mata, Abba yace
“Khairiyya kingan su nan, Iyayen Suraj neh”, ji tayi zuciyan ta ya tsananta da bugawa, Abba yacigaba da cewa
“Sunzo mini da wani mummunar labari Khairiyya,Yaushe last had’uwar ki da Suraj kuma mei yafad’a miki”, Khairiyya kanta yana kasa sai hawaye zub zub zub yake sauka muryan ta yana shaking tace
“D’azu da safe Abba, yazo mini da maganar cewa yafasa aure nah”, sai ta fashe da kuka, wajen sautin kukan ta kawai akeji, kuma ba wanda yace mata kala, bayan tayi mei isarta tayi shuru sai shashshaki take Abba yace
“Mei dalilin da zaice ya fasa auren”, Khairiyya still tana zub da hawaye tace
“Ce masa akayi inada HIV”, Abba yayi murmushi ya d’aga kai ya kalle Abbu yace
“Shine dalilin dazai ce yafasa auren, ba komai ba sai kun damei kanku ba”, Abbu yace
“Ai maganar gaskia muke so musani”
“Tunda mei auren ta yace ya fasa ai shikenan, ya juya wajen Khairiyya wanda take durkushe a wajen take kuka yace
“Tashi mushiga Yata kinji”, ya d’aga ta ya rike hannun ta daidai zasu fita a kofan falon yace musu
“Idan kun gama cin naman da shan drinks d’in ga kofan fita”, suka fice kayan su, d’akin shi yakaita direct ya zaunar da ita yana ta lallashin ta, yace
“Khairiyya waye yamiki sharrin nan”, Khairiyya tana kuka tace
“Doctor Umar”
“Mei alakan ki dashi”
“Abba is a long story idan ni da kai re both free zan fad’a maka”, Abba yace
“Ohk toh, but ki sani ya afka banban kuskure a rayuwar sa, yana zaman qualified doctor zaiyi false result, har Abuja zanje ayi firing nasa, kuma every hospital a Nigeria suki d’aukan sa aiki”, Khairiyya tace
“Noo Abba, kar mu masa haka please mubar sa da Allah, yayi na farko but idan ya kuskura ya sake for the second time Toh ni da kaina will teach him a lesson”, Abba da kyar ya hakura, Khairiyya ta koma d’akin ta idon ta duk a kumbure tasha kuka, Teema tana ganinta ta tashi tace Khairiyya lafia, Khairiyya bata san lokacin da ta zube a carpet ta kara fashe wa da kuka ba, tace
“Teema Suraj ya fasa aure nah”, Teema taja wani dogon tsoki tace
“Mei yasa wai”, Khairiyya tace mata da tsawa kije ki tambaye sa mana, Teema tace
“One man poison is another man’s food, ai ke gaba ma takaiki, yanxu zaki samu ki aure wanda ranki yake so”Khairiyya ta watsa mata mugun kallo tace
“Waye kenan”, Teema tana murmushi ta kashe mata ido d’aya tace
“Dan uwana mana, Yaya Zilyadeen”, wani fusgar da iska Khairiyya tayi ta zauna akan cushin tace
“Idan nace miki bana son Zil toh na miki karya, inason Zil but Suraj yana da qualities da nake Son namiji yazama yana dashi, yana da qualities da maza few neh suke dashi a duniya, Allah sarki Suraj Allah baka mace tagari, daman tun asali baka dace dani ba, you deserve someone better”, Teema ta harare ta tace
“Banza ke kika sani, kinga tafiya ta dan an kusan kiran Magrib yanxu”, Teema ta d’au jakan ta tace bye Khairiyya, Khairiyya tace nima zanzo kinji ki ajiye mini biski da miyan kuka, Teema ta harare ta tace
“Yar rainin sense, sau kike kice kullum idan kinzo gidan mu biski da miyan kuka mukeyi”, Khairiyya tayi dariya tace kedai sai nazo

Teema tana fita a gidan su Khairiyya gidan Zilyadeen direct ta wuce, tana shiga daidai lokacin zaije sallah Magrib, Zil yace

“Teema ana kiran Sallah ke kuma kina yawo, kina zaman mace”, Teema ta gaishe shi tace
“Umm yaya Zil nazo maka da wani albishir”, yaja tsoki yace
“Shineh baza ki iya bari sai gobe ba”, tace
“Noo I can’t wait Yaya, yanxu daga gidan su Khairiyya nake,kaji wani abun mamaki an fasa auren ta da General Suraj”

????????????????????????????

Nana fa’ad En Eesha
[11/22, 11:49 PM] ‪+234 806 524 6449‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Nov, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 66]

Zilyadeen zare idon sa yayi, yace
“Teema kishiga ciki kiyi sallah kici abinci yanxu zanje sallah”, Teema ta kashe masa ido tace “Toh Yaya asani a addu’a na aure Ammar”, Yayi dariya kad’an yace
“Silly gurl”, ya fita ita kuma tashige gidan, da tashiga cikin gidan Rumaysa tana Sallah Teema itama tayi alwala dan gabatar da Sallah, Bayan Teema ta idar da Sallah Rumaysa tace
“Ke mei yakawo ki gida nah da Magrib d’innan”, Teema tana sosa kanta tace
“Wlhy wucewa nake kuma fitsari ya matse ni nace bara na tsaya”, wayan ta neh yafara ringing taga Mum, ta d’auka tun kan mahaifiyar ta tayi magana tace
“Mum ina gidan Rumaysa fa yanxu zanzo”, kat ta katse wayan, Rumaysa ta harare ta tace Yar yawo kawai kinyi asara, bara na zuba mana abinci, daidai nan Zilyadeen yashiga d’akin yace
“Wani abinci kuma, yarinyan da ake neman ta a gida, maza tashi na kaiki gida yanxu yanxun nan”, Rumaysa tace
“Husby da Motarta tazo fa”, ya sosa keya yace
“Eh nasani ai, sai kace bakisan halin Teema da yawo ba, zanbi bayan ta neh har sai naga tashiga cikin gida tukun, yanxu Mum takirani tana mini complaining d’inna, maza tashi muje”, Teema sai dariya take ciki ciki ta d’au jakar ta suka fita, kowa yashiga motar sa suka bar gidan, sanda sukayi nesa tukun suka tsaida motar su, Zilyadeen yafita a motar sa yashiga na Teema, Teema kawai ta fashe da dariya tace
“Kai yaya haka kake”, ya 6ata rai yace
“Kinga bana son raini, just tell taya kika san an fasa auren Khairiyya”, Teema tayi dariya ta basa labarin duk abun da tasani, duk abun da taji kuma yafaru a idon ta, shi kanshi Zilyadeen was shocked, yasan Suraj yana matuwar son Khairiyya toh mei dalilin da zaisa yafasa auren, yace
“Teema ngd sosai”, yafita a motar taja motar ta, shima Zilyadeen yashiga nasa motar, zama yayi yana tunani na kusan minti talatin tukun yaja motar sa sai zuwa gidan su Khairiyya, baisha wahala a bakin gate ba Cox mai gadin yasanshi, kan ya fita a motar ya fesa perfumes nashi masu dad’in gaske, ya samei Haule a waje tana waya yace ta masa sallama da Khairiyya please, Haule ta amsa mishi da Toh, ta kaisa guest room tayi serving nashi su drinks da snacks……

Daidai lokacin Abba da Khairiyya suna zaune a parlour sa, sai lallashin ta yake, Abba yace

“Khairiyya you are still young, kina da future agaba sosai, ni fasa auren da yayi sam bai damen ba, a duniyan nan idan mijin ki neh toh dole ki aure sa, idan kuma ba mijin ki baneh duk yadda akayi, duk yadda kuka kai da son junan ku toh fa aure nan baza ayi shiba, kiyi hakuri Baby nasan tun farko bashi kike so ba, kinga inason sa neh shiyasa kika yarda amma nasan ba koh d’igon sonsa a zuciyar ki, yanxu kika fara makaranta baby you have a long way to go, advice da zan baki shineh kiyi karatu sosai kinji”, Khairiyya tace
“In Shaa Allah Abba”, Abba yace
“Nifa abun da yafi damuna shineh Invitation cards da nayi da wuri na saka aka rarraba ma friends dina both na outside the country da wanda suke cikin Nigeria cos daman zanyi tafiya nan zuwa sati d’aya bazan samu time ba nace gwara nayi na huta, kuma ga abun da yazo yafaru” daidai nan Haule ta musu sallama, bayan sun amsa tace
“Khairiyya ana sallama dake”, ji tayi zuciyan ta ya buga tace
“Waye”, Haule tace Zilyadeen, Khairiyya tace
“Jeki kice masa bazan fito ba”, Abba yace
“Haba yar nan,ai haka bashida da kyau, maza tashi ki shirya kisamei shi, kikasan koh kawai yazo ku gaisa neh”, Khairiyya tana ture baki ta tashi ta zuru wata doguwar hijabin ta tafita, tun kan tashiga guest room d’in take jin kamshin turaren sa, lumshe idon ta tayi zuciyan ta yana har6awa dan ita a tunanin ta bata ta6a son wani d’a namiji kamar yadda takeson Zil ba, da sallama tashiga ya amsa mata, idon sa kyar a kanta, waje ta nema ta zauna amma har yanxu bai daina kallon taba, har tafara jin kunya irin kallon da yake watsa mata, kallo neh daya kunce abubuwa iri iri daban daman, bayan ya gama kashe mata jiki da kallon sa yace
“Nazo neh namiki congrat auren ki saura 11days koh, Allah kaimu na miki murna sosai, nazo neh da nawa contribution d’in dan zanyi tafiya before auren nace bara na kawo nawa contribution d’in”, cire check yayi a aljihun sa ya fitar da biro yafara rubutu ya mik’a mata, kar6a tayi taga check na 500, 000 thousand
Zilyadeen yace “Sorry Khair nasan kinfi karfin haka but that’s what I can afford, Allah bada zaman lafia, ki sani har abada bazan ta6a mantawa dake ba, kullum ina kara jinki a raina, dake nake kwana dake nake tashi I still love you Khair, I love you soo much, amma yanxu zakiyi aure, dole na cire sonki a cikin raina Khair, ki tayani da addu’a dan nasan heart d’ina zata iya tarwashe wa”, Khairiyya hawaye take sosai, taji wani sabon sonsa yashiga mata rai, batasan lokacin da tace
“Suraj ya fasa aure nah“, wani murmushi Zil yayi daman abun da yake jira ta furta kenan, zama yayi dirshin a kasa a kan carpet yace
“What, Why, Suraj d’in”, Khairiyya ta d’aga kanta alaman Eh shi d’in, Zil yace
“Kai Suraj baiyi ba, ai duk abun da ya had’a ku baici ace yafasa auren ba, ni da nake masa kallo mutum mai hankali mei tunani, mutum da yasan yakamata, mutum mei riko da addini, ashe ba haka baneh”, ya matso kusa da Khairiyya yace
“Khairiyya In Shaa Allah baza kiji kunya a idon duniya ba saidai shi yaji kunya, karki damu already daman Rumaysa ta amince na aure ki sai kuma zaki aure Suraj, yanxu tunda ba auren ku ai shikenan sai a d’aura a daidai ranar, In Shaa Allah keda Abba bazaku ji kunya ba, bai isa ya kunyata ku a idon duniya ba, share hawayen ki Khairiyya kinji”, da dad’in bakin sa, su sweet words yasa har Khairiyya ta amince, daman Zilyadeen akwai shi da dad’in baki kuma da d’acin magana…. A duniya idan akwai mutumin da maganar sa yake tasiri a jikinta yake shiga kanta kai tsaye bai wuce Zil ba, hakan nan ya ringa expressing feelings nasa yana gaya mata how much he loves her and how much he misses her. Khairiyya tace
“Yaya Zil baka tambaye ni dalilin dayasa ya fasa auren ba”, Zil yace
“Shhhhh Khair, I trust you completely, I trust you with all my life, you don’t have to tell me anything”, Khairiyya tayi murmushi tace Thanks alot, Thanks for trusting me, Zil yace No thanks tsakani nah dake, You mean alot to me and I can do anything for you baby… wannan kenan masu karatu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button