KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

 Zilyadeen neh a gaban iyayen sa ya sunkuyar da kai kamar munafiki, duk iyayen sunyi shuru, can daddy yace

“Zil bawai muna hanaka abun da Allah ya halatta baneh, dududu auren ka sati biyu neh kacal, kayi hakuri mana zuwa nan da wata shida but idan dai kai ka nace yanxu kake so Toh sai da yaddan Rumaysa, idan Rumaysa bata yarda ba dole ka hakura, but koh yau Rumaysa ta amince toh gobe zamuje gidan su yarinyan”
“Daddy banda matsala da mata ta nasan zata amince” daddy yace toh shikenan ai kaje ku tattauna, yanxu ka tashi ka kaini airport inada meeting a Abuja, Zil yace toh Daddy muje…

Suraj neh zaune da Khairiyya suna hira, Abba yazo wucewa Suraj ya durkusa har kasa ya gaishe shi, Abba yace ku samei ni a falo ina son magana da ku, duk suka mara masa baya suka shiga falo, Suraj ya zauna a kasan carpet, Khairiyya da Abba suna kan cushin, Abba yayi yayi dashi akan yahau kan kujera amma Suraj yaki yace
“Abba nan ma yayi wollah karkaji komai”, Abba yayi murmushi yace toh shikenan as you wish, ya gyara murya, yace
“Abun da yasa na kiraku shine kai Suraj na yaba da hankalin sosai, idan har dagaske kana son Khairiyya Toh ka turo magabatan ka dan ayi maganar auren ku”, Suraj dad’i yaji sosai kamar a zuba masa ruwa a kasa yasha, yace da murya kasa kasa
“In Shaa Allah Abba ina zuwa gidan zanyi wa mahaifana magana”
Abba yace toh ”Madallah hakan ai yafi”, Abba yabasu waje dan su cigaba da hiran su, Khairiyya duk hankalin ta a jagule, ta rasa mei yake mata dad’i, shikam Suraj sai murna yake yanata wage hakora, can ya mata sallama, d’an rakiyan da ta saba yimasa batayi ba…..

Da daddare misalin karfe goma da rabi Zilyadeen yana zaune tare da Rumaysa sai zuba masa shagwa6a takeyi ita a dole ya tsifa mata kitson kanta, da kyar ya iya tsefe gudu uku yayi nishi yace 

“Wify Wlhy nagaji, kinji yadda hannuna yake zuga kuwa, gobe zan kira mei kitso ta tsefa ta kitsa miki”, Rumaysa ta turo baki tace
“Husby ni gaskia kai nake son kamini”, da kyar ya lalashe ta ta hakura, bayan sun koma d’aki sunyi wanka sun kwanta a kan gado, Zilyadeen ya rungume ta tabaya yace
“Wify nah I soooo much love you, I love you alot”, Rumaysa itama ta rungume shi sosai tace
“I love you more Nural Hayat, words can explain how much I love you, you mean everything to me my heart, ina sonka sosai sosai”, yayi murmushi yana shafa dogon brown gashin kanta mei kyali da tsantsi yace
“Prove to me that you love me JAAN”
“Wani irin proving kake so, ai tun ranar da nashigo gidan ka nayi proving maka how much I love you”, Zilyadeen yaja hancin ta yace i know dearest, inaso ki mini proving ta wani hanya daban, Rumaysa tace
“Just say anything da kakeso na maka, I promise zan maka idan bai sa6a wa addini ba husby nah” tayi masa kiss akan lips, Zilyadeen ya sake runguman ta gam yace
“You sooo sweet durlin, sooo sweet like honey, no more than honey”, tayi dariya tace
“Are you sure more than honey, fad’a gaskia husby”, yana mai shafan gashin ta yace
“Ki yarda dani JAAN, u r more sweet than honey”, ta rungume sa sosai tana mei shafa bayan sa, Zil yace
“Rumaysa inason ki sosai, yanxu muyi question and answer, zan na tambayar ki questions kina bani answer akan Islam”, Rumaysa tace
“Toh Mr lecturer yau kuma”, yace Sosai ma kuwa, let me start, number one question Auren mata sama da d’aya haram neh koh halal”, Rumaysa ji tayi zuciyan ta ya buga tace
“Ba haramun baneh, hasalima Sunnah neh”, yace Yawwa Good, kinci 1st question, tambaya na biyu shineh matan annabi S.A.W guda nawa ya aura”
“Annabi S.A.W ya aura mata goma sha d’aya” good answer cewar Zil, akwai wacce baya so aciki? Rumaysa tace
“Duk yana son su kuma yana adalci tsakanin su”, Zilyadeen yayi kabbara yace
“Wow ashe matata fa ba laifi”, Rumaysa dai murmushi tayi but zuciyan ta yana bugawa
[28/10 5:01 AM] Nana Fa’ad: Ya rungume ta sosai yace “laifi neh idan mijin ki zai kara aure”, ji tayi zuciyan ta ya buga, atake tafara jan jikin ta, muryan ta yana rawa tace
“Kabar wasa husby, I hate this type of joke”, ya rike ta gam yace
“Honey I am not joking, I mean what I said”, ya rike hannun ta gam cikin nasa yace
“But that those not mean bana son ki, Rumaysa kinfi kowa sanin inason ki, so na hak’ika, kinfi kowa sanin ina kaunar, you know that Zil love’s you sooo very much, kisani not that bana sonki shiyasa nake son kara aure, inason ki sosai Rumaysa kema kinsan da haka, kuma inason Khairiyya ma sosai, idan dagaske kina so nah Rumaysa ki amince na aura Khairiyya, na miki alkawari zanyi adalci tsakanin ku kinji Wify”, hannun ta taja daga nasa da karfi tana girgiza kanta hawaye sai zuba yake tace
“Ka bani kunya, ka bani mamaki, dududu auren mu sati nawa neh, sati biyu neh fa kacal shine har zaka zo mini da maganar kara aure, I never expect this from you Zil, you stoop sooo low, but kasani wlhy wlhy saidai kaza6a tsakanin Ni da Ita, karkace yanxu ni matar kace sai yadda kayi dani, wlh ko kad’an, a yanxu kam at my age banyi shirin zama da kishiya ba, the decision is yours Rumaysa koh Khairiyya”, tana mei shirin bar masa d’akin ya kama rigan ta ya durkusa har kasa yace
“Kar muyi haka dake JAAN, prove to me that you love me, Dan Allah kiyarda dani, bawai ina nufin bana sonki baneh ke kinfi kowa sanin cewa ina sonki, ni mei kaunar kine”jan kayan ta tayi tace
“Daman maza haka suke, hmmmm namiji kenan, namiji namiji neh, shikenan ka latsa mangoro, ka gama amfani dani na sati biyu zaka wurgar dani a kwandon shara, toh wlhy baka isa ba, kasani inda raina toh wlh bazan ta6a bari ka aura Khairiyya ba”, taja wani dogon tsoki tabar wajen, Zil ya rasa mei yake masa dad’i, ya bita d’akin ta amma kofan a rufe yake

 Misalin karfe goma sha d'ayan dare Khairiyya akan gado sai juye juye take ta kasa bacci, bud'e kofan d'akin ta akayi da sauri ta tashi ganin Abba neh, tace  Abba lafia, Abba yana murmushi yace lafia kalau baby nah, ya zauna akan gadon ta, yace

” baby nah sorry banji ta bakin kiba nace Suraj ya tura da iyayen sa, tun time da nace yaturo da mahaifan sa naga kamar baki so ba, a tunani nah murna zakiyi sai naga sa6anin haka, baby khair bakya son shi neh, don’t hide anything to me kifad’a mini gaskia”, hawaye sharr a fuskan ta tace
“Abba bawai bana son yaya Suraj baneh, kawai dai akwai wanda nake so na aura neh, had it been bana son waccan ba abun da zaisa na ki Suraj, but Zil neh kad’ai wanda nake son spending the rest of my life with”, Abba yana goge mata hawayen ta yace
“Ki daina kuka baby nah, ai wannan ba matsala baneh, bazan miki abun da bakya so ba, bazan ta6a miki auren dole ba, kinsan ai mei ya rabamu da Ammin ki, dalilin AUREN DOLE, kiyi shuru baby nah, kima wanda kikeso magana akan inason ganin sa, sannan idan Suraj yazo I know abun da zan fad’a masa kinji, kiyi shuru”
Khairiyya ta rungume Abban ta tace nagode Abba, I love you soo much, In Shaa Allah zan masa magana gobe, kuma a goben zaka gansa, Abba yayi murmushi yace ba komai Baby nah Allah kaimu goben
Daga Zil har Rumaysa kwana sukayi idon su biyu, da asuba tana idar da sallah a lokacin Zil ya tafi masallaci bai dawo ba ta d’au makullin motar ta tabar gidan, direct gidan su ta wuce, tana shiga cikin gidan ta wuce part na mummy direct, a lokacin mummy ta idar da sallah tana addu’a, bayan ta idar mummy tace
“Rumaysa lafia naganki da asuba haka, ina mijin ki”, kawai Rumaysa ta fashe da kuka tace
“Mummy yanxu Zil baya so nah baya kauna ta”
“Shhhh rufe mini baki Rumaysa, mei sa kika ce haka”, Mummy tacewa Rumaysa ki mini dalla dalla yadda zan fahimta, Rumaysa ta zub da hawaye tace
”Mummy aure Zil yake so ya kara, kwata kwata auren mu fa sati biyu neh mummy shineh har yana maganan kara wani auren”sai kuma ta fashe da kukan, mummy tace
“Share hawayen ki Rumaysa, duk wata macen da mijin ta yace mata zai kara aure suna cikin amarci toh gaskia abun ba dad’i, koh nice za’a mini haka a aure na sati biyu I will feel thesame or more than what you re felling now, idan ba da yardan ki ba toh Zil bai isa ya kara aure ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button