KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

  Zaynab tana shiryawa Khairiyya kayan ta a jaka karami Khairiyya kuma tana tattara gaba d'aya fake results da Doctor Umar yayi, basufi twenty minutes ba suka gama had'a komai Zaynab takai Khairiyya airport.. 

Tayi sa’a jirgi zai tashi in next 40mins, tabiya su kud’i suka bata ticket, Zaynab tajira har 40mins jirgin su Khairiyya ya d’aga zuwa Abj, Zaynab tashiga motar ta kenan taga Suraj, bata san lokacin da tafita a motar tasamei shi ba, Sallama ta masa, d’ago da sexy eyes nasa ya kalleta, ganin zaynab ce yayi murmushi yace
“Ahhh malama Zainab kece”, Zaynab tayi murmushi tace
“Nice Our soldier, kwana biyu”, yace “Wlhy kalau”
Wayan tane yafara ringing ta kalla Ummi ce take kira, da sauri tayi picking call d’in tace
“Ummi gani nan yanxu zanzo”, ta katse wayan, da sauri ta mika masa wayan tace
“Can I have your digits so that muna gaisawa”, General Suraj yace
“Sure why not”, ya kar6a ya latsa number sa ya mika mata wayar ta, dialing tayi a wajen yashiga, tace
“Please save my number”, yayi murmushi yace
“Sure I will”, tace masa bye ta tashiga motar ta, ta madubin motan sa sai kallon sa take, ba karamin rama yayi ba, tayi murmushi tace “You are my 1st love”

Abuja

Khairiyya ta sauka lafia, already daman Abban yana airport yana jiran ta yace ai zama bai kamasu ba sai suje office na abokin sa, Fedral government Office dake Abuja sukaje, bayan sun shiga office d’in suka gaisa, mutumin babba neh a wajen, Alhaji mantawali kenan, abokin Abba neh sosai tun suna kanana, Alhaji mantawali yace
“Alhaji mai naira ya naga kamar ranka a 6ace seems like you ain’t in a good mood”, Abba yace
“Wlhy kuwa, cire fake results d’in gaba d’aya yayi ya nuna wa Alhaji mantawali, Alhaji mantawali was shocked
Yace “wannan results d’in gaskia neh or what”, Abba ya basa lbrn duk abun da yafaru, Alhaji mantawali yace
“How dare him do that, wannan kuma Doctor, yau dinnan za tura masa wasik’an sallama, duk inda yaje a Nigeria da sunan neman aiki baza mu bashi ba”, Alhaji mantawali ya kar6a duk details din, Yace
“But yanxu dole mu kira doctor ya mata test”, Abba yace “ba matsala akira doctor”, Alhaji mantawali yayi waya bayan minti biyar sai ga doctor, Doctor yad’an d’iba jinin ta kad’an, already daman yazo da HIV STRIP da buffer solution, cikin 15mins ya nuna result ba red line a test that shows that she’s negative, Doctor ya rubuta result ya basu

bayan sun d’an tattauna suka masa sallama suka tafi, direct gidan su na Maitama suka wuce, bayan sunyi sallah sunyi wanka sukaci abinci, Khairiyya tana zub da hawaye Abba yace
“No need 4 you to worry my dear, kuma baza muyi convincing nashi akan you re HIV negative ba, Allah zai kawo miki wanda ya fishi, Khairiyya tana kuka tace
“Abba ya zakayi da abokan ka da zasu zo auren, next tomorrow neh fa Abba”, Abba yace
“Karki damu baby nah kinji”, Khairiyya ta rungume Abba tace
“I am soo sorry Abba”, Abba yace ba komai bby nah

Washehari a Maid

Wanda ya kasance ranar jumma’a, Doctor Umar yana office yana duba patients aka aiko masa da MD yana neman sa, bayan ya gama da patient d’in yafita zuwa office na Medical Director, bayan ya zauna M.D. ya mika masa letter, Doctor Umar hannun sa yana rawa ya kar6a yace
“Sir wannan fa”, M.D yace
“Ammm wannan letter neh anyi firing naka a aiki dalilin fake results da kayi”, Doctor Umar baisan lokacin da ya tashi a kujeran da yake zaune ba yace
“What”, da sauri ya bud’e letter ya karanta, hawaye yake Sosai ya aza hannu akan sa
A daddafe ya isa office nasa, yana shiga ya zube a kasa yafara kuka sosai kamar karamin yaro, cewa yake
“KIM KENEN, KIM THE KIM, because of you I lost my wife and kuma because of you na rasa my job, why Khairiyya why, I swear bazan barki haka ba, I swear you must regret abun da kika mun” tashiwa yayi ya tattara kayan sa na office d’in kaf yafita, motar sa yashiga ya d’auka wayan sa yayi dialing number Khairiyya, a lokacin Khairiyya tana bacci cox tagaji sosai dawowan su daga Abuja kenan, ringing na wayan ta neh ya damei ta, picking tayi ba tare da ta duba kan screen ba, a take ta tashi jin muryan doctor umar, yace
“Khairiyya kenan, kizo downtown na hanyan Lagos street in next 15mins ki samei ni or nasaka boys d’ina su zuba petur a gidan Uncle Hisham, Allah sarki Zainab gashi ita kad’ai neh a gida, na baki 15mins”, Khairiyya batasan lokacin da ta tashi ta zura Hijabin taba ta d’auka key na motar ta, dan tasan halin Doctor Umar tsaf zai iya aikata abun da yafad’a

Shi kuma Doctor Umar bayan ya gama waya da Khairiyya ya danna number wani, yace
“Ka duba mini da wani mota zata fita dashi”, ya katse wayan, ya kara dialling wani number yace
“Be ready any moment zata iya zuwa”, ya katse wayan, yana katse wayan call yashigo da sauri ya d’auka yace
“Ohk toh naji”, ya katse wayan ya kara dialing number da yakira na biyu yace
“Da Mercedes C60 ash colour, kayi yadda nace”, ya katse wayan yana murmushi yana zub da hawaye

Khairiyya ce tana tuk'i da gudu cikin mota Mercedes C60 sai gudu take, already tana hanyan Lagos street d'in, wata babbar Mota Daf yake binta a baya bumper to bumper, kan kace kwa6o babbar motar ta buge ta, wata babbar Mota Daf irinta ta ture ta tun daga kan bridge har kasa sai cikin ruwa

????????????????????

Nana fa’ad En Eesha
[11/22, 11:49 PM] ‪+234 806 524 6449‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Nov, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 68]

Mutaneh sun taro a bakin ruwa ana kokarin cire Khairiyya, duk wannan abun da yafaru a gaban idon Munay sabida tana gefen wani shopping mall abun yafaru kuma ta hango Khairiyya b4 the incidence har sunyi ido hud'u da ita, gaba kad'an neh motar ta buge KIM, ba karamin firgita tayiba, jikin ta yana kakkarwa da sauri ta d'au wayan ta takira Suraj, yana picking call d'in tace

“Yaya Suraj, kazo hanyan Lagos street, Khairiyya”, tana fad’a tana kuka sosai, itama da gudu ta sauko har kasa wajen kogin, Duk wahalan sauka da nesa bata jiba, gudu take tana fad’iwa tana tuntu6e har ta sauka akan bridge d’in

Maza neh sun taro but sun kasa cire Khairiyya sabida motar ta matse da ita a ciki kuma kofar bata bud’uwa, Munay zubewa tayi awajen tana Kuka kamar wanda za’a kasheta, hango Suraj da tayi da gudu taje ta kamashi tana cewa
“Yaya Suraj Khairiyya, idan ta mutu bansan ina zan sa kaina ba, nashiga Uku yaya Suraj, na munafurce Khairiyya, Khairiyya kiyafe mini please dan Allah Khairiyya, Yaya Suraj Khairiyya batada HIV sharri muka mata, ka gafarta mini Yaya Suraj”, tana gama fad’an haka taga Suraj baida niyan komai sai kallo tsaban ya rikice, da gudu Munay ta koma bakin kogin zata shiga wasu mata suka kamata, Munay sai bubbuge su take ita a dole su barta tashiga cikin ruwa, kuka take sosai tana cewa Dan Allah Khairiyya karki tafi, I wronged you, ki yafe mini Khairiyya, Khairiyyahhhhh
Da kyar aka rike Munay wanda ta birkice musu dan kuka, dan idon ta yaganeh mata duk abun da yafaru, Motoci manya har biyu suka buge ta, Suraj shima dirshin yayi a kasa ya rushe da kuka, Kuka yake sosai kamar karamin yaro, shima sai cewa yake
“Khairiyya I need you, please karki tafi ki barni, I am so sorry, very sorry for not trusting you, I love you Khairiyya, I love you more than my own life, you mean alot to me KIM, you mean alot K-h-a-i-r-i-y-y-a (emphasizing the name)

Da kyar aka d’aga motar, aka samu aka cire ta a cikin motar akayi rushing nata NAKOWA HOSPITAL, direct emergency aka kaita, ba tare da 6ata lokaci ba doctors suka taru akan ta dan treatment…

After 5hours, Bayan awa biyar

Abba neh yashigo asibitin hankalin shi a tashe, wata nurse yagani da gudu yasamei ta yace
“Where is my daughter”, da karfi, Nurse d’in tace
“Calm down sir, please calm down, wace daughter ka kake magana”
“Daughters nawa daman nake dasu a duniya ehhh”, bai gama magana ba yaji an rungume sa ta baya, juyawan da zaiyi kawai yayi four eyes da AMMAR, Ammar kuka yake sosai sosai, rungume Abba yayi yace
“Abba KIM, MY KIM, MY QUEEN, MY HEART, MY LOVE, MY LIFE, MY HAPPINESS, MY DREAM, MY COLOUR, MY SUNSHINE”, duk maganan nan baisan yana fitowa a bakin sa ba, wani doctor neh ya fito yace
“Ina mahaifin ta”, Abba yace gani nan da sauri, Doctor yace
“Ka bini to my office”, Abba duk jikin sa yayi sanyi ya bisa office nasa, bayan sun zauna Doctor yace
“You don’t have to worry Sir, karka damu, but I will advice you ka kaita Taj Mahal Delhi Hospital wanda yake India, Cox gaskia ta samu internal Injury sosai, ta bugu a kanta which I am very sure zata iya loosing memory nata da kuma m sorry to say both gaba d’aya kidney nata sun samu injury wanda idan ba’a iya anyi wani abu akai ba dole a mata Kidney Transplant

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button