KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kwana biyu Teema ta kira Khairiyya akan suna da departmental lectures Computer Programming by 8:00 am, a ranar tun sallan asuba bata koma bacci ba, tana idar wa tashiga wanka, bayan ta fito ta zauna a gaban mirror tafara tsara kwalliya,bayan ta gama ta bud’e wardrobe nata dan duba kayan da zata saka, anan ma ba karamin 6ata lokaci tayiba wajen duba kayan da zata saka ba, atlast habbaya baki ta saka tayi rolling da gyale baki, ba karamin kyau tayi ba dan daman abaya yana kar6an ta sosai, ita bata gama ba sai karfe takwas, tace What! Har time yayi, fita tayi dinning dan cin breakfast amma mei, sai taga Indomie da chips, kiran Dije tafara kamar wanda bakin ta zai tsinke tace
“Dije wannan wani irin rashin hankali neh, bakisan University ba d’aya yake da Secondary school ba, ai inacin wannan before na isa makarantar abinci zaiyi digesting mtseww, ki kawo mini pizza da shawarma Mota” ta fita tabar Dije a tsaye a wajen
“Ranar da kikayi aure zamuga idonki ai ” cewar Dije

 Ita bata isa Makarantar ba sai Karfe Tara, ahaka ba karamin gudu tayi ba, bayan tayi parking Motar ta tace

“Ohhh Emmm Geee, yanxu inaneh lecture venue d’in, mtsww matsala nah da university ko wani lecture da venue da za’ayi(ajin da za koyar)”, d’aukar wayar ta tayi ta duba venue da za’ayi lecture’n dan d’azu Teema ta tura mata, Yaa Allah yanxu inaneh ETF04, wata yarinya tagani tana wuce wa ta tambaye ta tace
“Please sis inane ETF04”
Yarinya ta mata kwatance, Khairiyya ta mata godiya, da tambaye dai haka har ta isa bakin ajin, Tusa kai tayi tashiga, sai kwas kwas na takalmin ta wanda yaja hankalin kowa, ga makeup da tayi ga kyau, ga uwa uba kamshin turaren ta da tun shigan ta class d’in ya d’auka da kamshin perfumes nata, duk class d’in tsit yayi kamar grave yard, daidai ta samu kujera zata zauna taji husky cracky Voice yace
“Heaea You get out of my class”
Khairiyya juyawa tayi dan ta tabbatar koh da ita malamin yakeyi, d’aga idon da zatayi ya had’u da nashi duk suka shiga shock
Fuskar yarinyan da bazai ta6a mantawa ba, yarinyan da taci mutuncin Hajja nah, yarinyan da tasaka yan ta’adda suka mini duka, yarinya yar maye..
Itama ido ta kura mishi, tabbas kamar tasanshi wani wajen, kuma ta ta6a kallon shi da Sabir, ohhhh that cute guy with Sabir
“Can’t you hear me, I said get out of my class”
Tabbas yaci sa’a he’s cute, da ba abun da zai hanani yi masa rashin mutunci, Bayan VC babban abokin Abba neh ai saidai a canza mini department badai su koreni a makarantar ba, but you are lucky, your cute face save you….

 Tana tafiyar ta mai d'aukan hankali ta fita a class d'in, shiga motar ta tayi ta kunna AC tana tunanin Face na malamin, mtsw wai ina na sanshi neh, wayan tane yafara ringing ya dawo da ita daga doguwar tunanin da ta fad'a, wata number tagani wanda ba na Nigeria ba, ta d'auka tace hello

Nidai nana bansan mei akace mata ba naga tafara hawaye tana kuka tana cewa
“No No No, please stop kidding me, this can’t be possible, how? No please”, wani kuka ta sake mai karfi tana cewa
“Yaa Allah help me, idan bacci nake na tashi”

Yanxu kuka fara karanta labarin *KHAIRIYYA* 


 Nana fa'ad En Eesha 

????????????????????????
[11/8, 9:29 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

   *[Sept, 2016]*


        Written by Nana fa'ad En Eesha????

Page 37~40

Khairiyya tasa Kwal6an a baki ta kur6a, a take ta fusgar dashi tace Ammar mei wannan, can I say its sour or bitter neh, I can’t take it, bazan iya sha ba Ammar
Ammar yace “zaki iya, ki gwada just try it you can”, ta saka a bakin ta tarufe ido da kyar tasha quarter(kwata), tana gama sha batafi minti biyu ba tafara maganganu daga baya bacci mai karfi yayi awon gaba da ita

Ammar ya fita ya rufe mata kofa, washe gari bata tashi a bacci ba sai kusan karfe shad’ayan rana dan tana fashin Sallah, ta tashi da mugun ciwon kai, da kyar ta iya wanka tasaka kayan ta, fita tayi parlour ta gaishe da Ummi (mamar Ammar), Ummi tace
“Khairiyya ga abincin ki a dinning”,
“Toh Ummi Thanks”, Khairiyya taje dinning, cokali biyu kawai taci ta tashi, d’akin Ammar tashiga, zaune yake a gaban computer suna Video call da Baban shi (Uncle Hisham), Khairiyya ta zauna itama tana tambayan Uncle Hisham Abban ta, Uncle Hisham yace
“Khairiyya karki damu yanxu haka zanje wajen lawyer shi musamu muyi solving matsalan, da yardan Allah zai fito”, Khairiyya tana share hawayen ta tace
“Kawo please try your possible best dan Allah”
“Karki damu Khairiyya, jini nah ne dole nayi trying best d’ina, I promise you zai fito soon” cewar Uncle Hisham
“Thanks kuma dan Allah idan kaje wajen Abba nah ka kirani, I really wanna talk to him”
“Karki damu, nan da minti goma shabiyar zan kiraki dan yanxu zan shiga wajen shi ina gaban prison din, bye and take care” yayi hanging video call d’in
Hawaye tafara, Ammar neh ya zauna agaban ta yana share mata hawaye yace
“Stop crying Kim, komai mai wucewa neh”, tace
“Ammar baza ka ganeh baneh, I soo much love my dad, he’s my life my everything”, tashiwa Ammar yayi ya bud’e fridge, gaba d’aya daga sama har kasa kwala6en giya neh, d’auko champagne yayi da cup yamika mata,yace
“Drink this”, ta karba kenan sai wayan Ammar yafara ringing, yace Daddy nakira nah wait karki sha, d’auka wayan yayi yace
“Hello Daddy”, Uncle Hisham yace give the phone to khairiyya, Ammar ya mikawa Khairiyya wayan ta kar6a, jin muryan Abba tayi a dashe, Abban ta na ce mata
“Hello Khairiyya yar baba, karkiji komai, very soon zan fita a prison, just take care of yourself kuma ki mini alkawari baza ki daina zuwa makaranta ba, ki mini alkawari you will be strong, ki mini alkawari baza kina kuka ba, promise me zaki zauna gidan Uncle Hisham kafin nazo”
Tana hawaye tace “I promise you Abba, na maka alkawari”
Abba yace “Good baby nah,Nasan kunada lectures yau so ki shirya ki tafi makaranta dont let this issue affect you, bye take care”yayi hanging call d’in, yana hanging ta fashe da kuka, kuka takeyi kamar wanda ana yanka mata fatan jikin ta, Ammar ya bata hakuri amma ina takiyin shuru, wayar ta tad’auka ta kira Teema, Teema tana d’auka wa Khairiyya tace
” Teema akwai lectures neh” “Eh akwai na computer programming, lecture na malamin jiya da ya koreki,Khairiyya jiya mei yafaru neh, an miki rasuwa neh”
Khairiyya tace “mtsww kinji ki, idan rasuwa aka mini zan kiraki neh har na tambaya koh akwai lectures ko babu mtws, what time neh the lecture”
Teema tace “by 2:00pm”, “ohk toh sai nazo” cewar khairiyya ta katse wayan…..
Ammar yace “are you sure Khairiyya zaki iya zuwa school”, tace
“Zan iya Ammar, trust me”, d’aukan giyan da yabata tayi ta 6oye cikin rigan ta dan kar Ummi tagani, d’akin ta tashiga tasaka kayan ta English wears, riga top mei dogon hannu blue da skirt wanda saman a matse sai kasan ya bud’e bak’i, takalmi mai uban tsaye ta d’auka shima bak’i tasaka, ta d’au giyan ta tasaka a katon jakar ta tafita, karfe d’aya da rabi tana cikin makarantar, duk tarasa mei yake mata dad’i, kiran Teema tayi tace
“Teema inane lecture venue d’in”
“Class na jiya, ETF04, kina ina nazo na samei ki” cewar Teema
“Nifa bana cikin makarantar, kedai sai mun had’u a class” ta katse wayan
Bud’e kwal6an giyan tayi ta tusa a bakin ta, rufe idonta tayi ta damke dan sam abun ba dad’i, tasha kad’an, ji tayi ba abun da yake damun ta kuma, bata ankara ba har karfe biyu da rabi yayi, what! Haka time yake gudu, motar ta taja har gaban class da zasuyi lecture, d’aukan giyan ta tayi ta kwankwad’a har kusan rabi, sai wani jiri takeji komai kallon sa bibbiyu take, fita tayi a motar da kwal6an giyan ta a hannu, tana tafiya a dume har tashiga cikin class d’in, tana shiga class d’in tayi tuntu6e ta fad’i dan dogon takalmin ta, kassssss kwal6an ya fashe, gaba d’aya kallo ya koma kanta, da kyar ta iya tashiwa, Teema tazo dan ta taimaka mata tace
“I am ok Teema karki damu” cikin muryan maye, Muryan Malamin su Zilyadeen neh da tsawa yace
“Teema help her get out of my class now”, Khairiyya ta tashi da kyar taje daf kusa dashi, warin giyan duk ya damei shi ya kid’imeshi ya cika masa hanci, toshe hancin sa yayi da hannun sa, Khairiyya tace
“Mr handsome, I like you soo much, the 1st time da na ganka tare da Sabir naji nafara sonka, but fa karka ce kyaun kaneh ya rinjaye ni sam ba haka baneh, my cousin brother Ammmmar, Yaya Ammar yafika kyau, yana da ten packs, hard chest,da gashin sa bak’i dogo kamar na Ceth Rollins infact komai but bana sonshi, but you I don’t know why I just like you”,tana maganan duk a buge, cikin maye, hannun ta tad’aga zata shafa fuskan shi ya wanke ta da mari, yace
“Are you Insane, are you out of your senses, don’t you dare ever think of touching me you filthy wretch with your filthy hand, so disgusting”, ya fita yabar class d’in gaba d’aya, da kyar Teema taja ta tasaka ta a Mota, driving nata tayi zuwa gidan da takaita jiya(gidan su Ammar) daidai tazo gaban gate zatayi horn wata mota kirar BeenzS600 neh tazo itama zata shiga gidan, Ammar neh a ciki, a take ya fita a motar dan yaga ba Khairiyya bace ke jan motar, tsayar da Teema yayi, yace
“What happen to her”, Ammar yana tambayen ta amma ta kasa basa amsa, kallon sa take kamar wanda zata cinye shi, tsoki yaja ya daka mata tsawa yace
“Will you stop staring at me and answer me”, atake ta firgita tace
“Umm sorry wlhy she was drunk”, Ammar yace
“Sauka daga motar” ta sauka kamar yadda ya bukata, ya mika mata makullin motar sa yace kibini a baya, shi kuma ya shiga motar Khairiyya yaja, wani mansion gida yakaisu a anguwar Polo, Teema sai kalle kalle take dan tun da take bata ta6a ganin gida karami da ya tsaru irin wannan ba, har tafara dreaming ita da Ammar a gidan, Ammar ya d’auka Khairiyya cak yakaita cikin gidan, sai surutun da ba kai takeyi tana cewa da muryan maye
“Ammar ina son Abba, inason son ka, inason Mr lecturer, kasan sunan Mr lecturer mu, sunan shi Zilyadeen, wow unique name kakeji not like sunan ka Ammar saika ce sunan Almajirai, but fa kafisa kyau ka fisa had’uwa amma shima kat neh, Abba na yana zuwa gidan zance ya aura mini Zilyadeen, Ina So…. “, bata karasa ba tafara amai, duk jikin sa ta 6ata mishi da amai, saiyi takeyi, sanda ta zubar da abin cikin ta tass a jikin sa, Ammar yacewa Teema wanda ta shagala da kallon sa batasan ma Khairiyya na amai ba
“please ga d’aki can, ki wanke mata jikin ta, akwai towel a wajen ta cire kayan jikin ta, idan ta cire sai ki kawo na wanke”, Teema tace “Toh”
Teema tajata d’akin, ta mika mata towel, Khairiyya ta cire riganta ta shiga toilet, Teema ta kunna mata shower ta fita, koh second goma batayi ba a toilet ta fita ta kwanta a kasa sai bacci
Teema ta fito tasamei Ammar yana waya, bayan ya gama tace
“Khairiyya tayi bacci ni zan tafi, ga kayan ta”, ta mika masa
“Thank you soo much Teema, please duk ranar da tasha abu nan zaki na kawo ta karki kaita gida kinji”
“Ohk toh”, sai kuma ta tsaya tana kallon sa, yace
“Kina bukatar wani abu neh”
“No I just need your number so that na kiraka naji lafiyar Khairiyya ” cewar Teema
“Ohk toh ba matsala”, ya bata number ta tafi
Khairiyya bata tashi a bacci ba sai kusan karfe takwas, tashiwa tayi ta ganta da towel a jiki, ta kasa tuna abun da yafaru da ita, kanta yayi zafi, Ammar neh ya shiga d’akin, ido ta ware zuciyan ta yana bugawa tace
“What happen Ammar, mei ka mini, mei yafaru, nan inane?”
Wani murmushin mugunta yayi yace
“Ohhh baby you sweet like zuma, kai more than Zuma”
Zama tayi dirshin a kasa tana kuka tace
“Ammar ka cuce ni, bazan.. “, bata karasa ba yace
“Heaea Woman stop, fyad’e shineh abun da bazan ta6a yiwa mace ba, I can’t rape a gurl, have u seen this body (yana nuna mata jikin shi), mata su suke kawo kansu wajena, har wasu suna cewa zasu biya ni, lots of gurls chase over me for my look, mei zanyi da ke abeg ki tashi ki saka kayan ki mutafi gida”
Khairiyya tace Keep talking Mr Ego, taja tsoki
Ammar yace “Nine Mr Ego koh naji ai nakai neh maza tashi mu tafi, kuma akwai good news sai munje gida zan fada miki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button