KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Tafiyan minti ishirin sukayi sai gasu a cikin gidan Alhaji Abdullahi, duk da madai gidan su Khairiyya yafi wannan kyau amma sai yabata wani sha’awa, har wani kanshin Zilyadeen takeji tun daga bakin gate, sai wani lumshe ido takeyi, d’akin Rumaysa aka ajiye mata kayan ta, duk suka mata sallama, Suraj yace
“KIM In Shaa Allah zanzo gobe kinji, take care of yourself koh”, wani bak’in ciki da Zilyadeen da Ammar yacikasu, shi Zilyadeen ya kasa ganeh kansa, meisa yake kishin Khairiyya, Ammar kam kala baice ba yacewa Ummi da Zainab su samei shi cikin mota
Bayan duk an watse Rumaysa ta had’a wa Khairiyya ruwan wanka, bayan ta fito tayi sallah, Hira sukayi sosai da Khairiyya, suna cikin Hira wayan Rumaysa ya fara ringing, Yana kusa da Khairiyya, Khairiyya ta d’auka tace
“auuu su soyayya manja, har ana saving number da Nurul Hayat, kice mun kusa shan baki”, Rumaysa murmushi kawai tayi tafita a d’akin, Khairiyya abun sha’awa ya bata, ita a rayuwar ta batasan mei saurayi bama, bata kula su, duk wanda yace yana sonta toh haushin sa zata faraji, gashi a yau tana son Zilyadeen, amma shikuwa bata gaban sa, hannun daman ta tasa a gashin ta tace “wayyo Allah ya zanyi da son wannan bawan Allah, Allah kasa shima ya soni kamar yadda nake sonsa”
Bayan Rumaysa ta fita a d’akin ta wuce side na Zilyadeen, zaune ta tardashi, tayi sallama ya amsa yana murmushi yace
“Amarya ta idan ban neme kiba wato ke baza ki nemeni ba koh”, tana murmushi tattare da kunya tace
“Haba na’isa my future husband, ai ban isa ba”
“Ya bakuwar mu, hope kina kula da ita mei kyau, kin san koh sauro d’aya banso ya cije ta, duk abun da take so ki mana kinji swt”, nan take taji mugun kishi ta had’a rai, tace
“Kasan a duniyan nan banso kana nunawa koh wace d’iya mace kulawa sama da ni, I can sense that you are so very protective of her, kana nuna mata care more than me, please karka sa na fara kishin ta, kasan dai ina kaunar ka more than my life itself, shiyasa nake masifan kishin ka, ina kaunar Khairiyya ma sosai, amma akan ka zan iya rufe ido na…. ), bata karasa maganar ba yace
“Haba my future wife, wannan wani irin magana neh, kinsan ba wata mace a gaba nah idan ba keba, ki daina fad’an haka, don’t misunderstand me please, i care for her sabida dalilin buge ta da nayi, if not nothing else “
Rumaysa tace ohh better, haka suka d’anyi hira, yace yanxu ki koma kar Khairiyya tace an barta ita kad’ai, tace toh future husby
Rumaysa ta tarar da Khairiyya tana waya, bayan ta gama tace
“Keda yaya Ammar neh”, ta ja tsoki tace
“Aa nida Captain Suraj neh, Yana ma gaishe ki”, Rumaysa tace
“Wa yaga lovebirds, ai ni da fari na d’auka ke da Ammar neh, sai daga baya naganeh shakuwa neh kawai, ashe ke da soja neh”, Khairiyya ta wani 6ata rai tace
“Kamar ya nida Soja”, Rumaysa ta harare ta tace
“Mtsww banza ai kin fini sani”, Khairiyya ta juya ta rike hannun ta tace
“No Allah bansan komai ba”, Toh shikenan tunda baki sani ba, yanxu tashi muje muci dinner a parlor, haka duk suka had’u a dinning, suka zauna suna cin abinci, Khairiyya dai kusa da Rumaysa ta zauna, tana opposite da Zilyadeen, haka suke cin abincin da hankali, Khairiyya kasa cin abun kirki tayi, dan gani take kamar Zilyadeen yana kallon ta, shikam sai kallon su duka biyu yake, anan ya kare musu kallo, Tabbas Khairiyya tana da kyau duk da ma ita d’in ba fara bace, Rumaysa kuma fara ce sol amma Khairiyya tafita kyau. Bayan sun gama ci Mummy tace suje da sauran abincin d’akin su koh anjima zasu bukata, sukace toh
Suna shiga sukayi wanka sukayi sallar isha’i suka kwanta kan gado, Rumaysa ta juya tana kallon Khairiyya wanda itama ta kwanta ta lumshe ido tace
“Khairiyya acikin Ammar da Suraj wa kika fi so”, Khairiyya ta bud’e ido tace
“Kai Rumaysa, yanxu mei ya kawo maganar nan, ke tell me who is Nural Hayat, wanda naga d’axu ya kiraki a waya”, Rumaysa tace
“Hmmm shineh mijin da zan aura In Shaa Allah nan da wata biyu, ina sonsa ina kaunar sa, I love him more than words can say, karki damu watarana zan had’a ki dashi, but fa zaki sha mamaki, you’ll be suprise I know idan kin ganshi”, Khairiyya tace
“Su manja iyayen soyayya, Toh ni maganar gaskia bazan 6oye miki ba, bana son Suraj da Ammar, na d’auke su like brothers, kuma a cikin su ba wanda ya ta6a furta mini So, Ammar yana cewa yana So nah, but ba irin son da kike tunani baneh, So irin na yaya da kanwa neh. Akwai wani da nake Son shi sosai, amma shi sam bana gabansa, bansan ya zanyi ya soni ba Rumaysa, amma ina sonshi, Sonshi sosai kamar rai nah, ban ta6a Son wani mahaluki kamar shi ba, please ki taimaka mini, I need you to advice me”, Rumaysa ta bud’e baki tana kallon Khairiyya da take zubar da hawaye akan namiji, duk kyaunta, duk class nata, duk arzikin ta, lalle so banzan abu neh, tace
“Khairiyya idan har dagaske kike you need my advice, shawaran da zan baki shineh ki cire sonsa a zuciyar ki, tunda dai ya nuna miki bai kaunar ki, mei sa baxa kiso mei sonki ba, Suraj yana sonki, Ammar zan iya rantse miki da Allah shima yana sonki, ki za6a a cikin su ki aura Khairiyya, ki manta da mutumin da baya sonki”, Khairiyya ta tashi ta rike hannun Rumaysa gam, tana hawaye sosai tace
“Baxan iya son kowa ba wollah Rumaysa, shi kad’ai nake so, shi kad’ai zuciya ta ta aminta dashi, my life will be worthless without him, my life will be shattered without him, He mean everything to me, I can’t live without him, I think of him every moment of my life”, Rumaysa ta numfasa, tace
“Lalle abun naki fa sai addu’a Khairiyya, abun da zakiyi yanxu shineh kisan his likes and dislikes, abun da yake So da wanda baya so, kiyi duk abun da kikaga zai ja hankalin sa gareki, kina sallan dare da azumin Monday and Thursday, kina rok’on Allah idan alkhairi neh Allah tabbatar, idan ba alkhairi baneh Allah watsar dashi”, Khairiyya ta rufe wa Rumaysa baki da hannun ta, tace
“Ki daina fadin idan ba alkhairi baneh Rumaysa, ni nasan alkhairi neh, nagode da shawaran da kika bani, Allah bar zumunci, nagode sosai, by the time da zaki san wanda nake so haka sai kinfi kowa murna “, Rumaysa ta buge ta na wasa tace
“Ai idan kina so kiga murna ta toh fa sai Ammar, yaro ga kyau, gaskia ya had’u karshe, kullum sai Teema ta mini hiran sa, nace mata kwalelen ta, Ammar na Khairiyya neh, Ammar mijin mace d’aya neh kuma itace Khairiyya kamar yadda Nurul Hayat d’ina yake Mijin mace d’aya”, dogon tsoki Khairiyya taja tace
“Malama sai kiyi tayi ai, kinga kwanciya ta”, ta juya ta kwanta abunta, daidai ta kwanta taji message yashigo wayar ta, dubawa tayi taga Captain Suraj
Baby please do take care of yourself, I miss you, Murmushi tayi ta masa reply
I ‘ll dear, I miss you too
Tana ajiye wayan taji yana ringing daman a vibration ta saka, Private number tagani, taja wani dogon tsoki tace Wlhy na tsana a kirani da private number, bazan d’auka bama, Rumaysa tace
“Haba mana ki d’auka mana kikasan koh mistake neh, nima sometimes waya na shiga private, sai dai a tambaye ni ya nasa waya ta a private”
kara kira akayi na biyu Khairiyya ta d’auka, tana ta cewa hello amma shuru ba’ayi magana ba, tace “wannan wani irin iskanci neh an kirani kuma anyi shuru mtseww” ta katse wayan, Rumaysa sai dariya tace kai Khairiyya kekam baki da hakuri koh kad’an, bata ajiye wayan ba text message yashigo, baro2 sunan Ammar-Ego tayi saving
I’ve been thinking about you alot… More than alot, infact, wani dogon tsoki taja ta mishi reply kamar haka
wow good job Mr Ego, please bacci zanyi so don’t disturb

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button