KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan Zilyadeen ya tafi Khairiyya tashiga wajen Abban ta, akan sallaya tagansa yana addu’a, bayan ya idar yace
“Baby yane har ya tafi”, Khairiyya tace Eh Abba yatafi, Khairiyya ta zauna ta basa lbrn duk abun da sukayi da Zil, Abba ya numfasa kan yace
“Khairiyya naso kiyi karatu, koh da part 3 kikai, amma tunda kin nuna mini auren kikeso shikenan, nasan tun farko shineh a ranki shi kike so shi kike burin aura, but kisani aure ba abun wasa baneh amma tunda you re very sure auren kikeso kuma Zil kikeso ki aure shikenan, kice masa ya turo da mutanen sa and ki fad’a masa dalilin da Suraj ya fasa auren ki”, Khairiyya ta kama hannun Abban ta tace
“Abba nah ngd, no words da zanyi using na maka godiya, Allah bar mini kai Abba, Zil mutumin kirki neh, shi neh namijin da a duniya zucita tafara so”( umm su KIM ba kunya)
Abba yayi murmushi yace
“Baby ki sani you are my only child, idan ban miki ba ma wa zanyi, I love you”, Khairiyya ta rungume Abban ta tana hawaye yana bubbuga bayan ta yana cewa yi shuru my daughter

Zilyadeen gidan su direct ya wuce, yayi sa’a both Daddy da Mummy suna gida,bayan sun gaisa ya kawo musu maganan Khairiyya, Daddy yace
“Toh meisa shi soldier ya fasa”, Zil yace
“Daddy wai kawai dan before tana d’an ta6a abu”, Daddy yace ta6a abu kamar ya bangane ba, Zil yana sosa keya yace
“Before tana d’an ta6a syrups amma yanxu batayi daddy, ta shiryu sosai kuma inason ta a haka, koh tanayi ai daddy naga jahadi zanyi, zan sakata a hanya na addinin musulunci”, Daddy ya numfasa kan yace
“Matar kafa ta amince”, Zil yana murmushi yace
“Ai daddy munriga mun gama da ita tayarda ta amince”, Daddy yace toh shikenan ka fad’a musu gobe In Shaa Allah zamuzo, Zil sai zuba godiya yake baki har kunne ya tashi ya tafi, yana shiga motar sa Khairiyya ta kirasa a waya tace
“Guess what”, da zumud’in jin abun da zatace yace
“All ears baby”, tayi murmushi wanda yaji sautin ya lumshe ido tace
“Abba yace katuro”, wani hamdala yayi yace
“Kema guess what”, tace “What” da sauri, yace
“Daddy sukace gobe zasu zo maganar auren mu”, itama hamdan tayi tace
“Wow Allah kaimu, bara na sanar da Abba tun yanxu”, kyat ta katse wayan, yana murmushi yana kallon wayan sa, muryan ta kad’ai yana saka shi a cikin nishad’i ya rungume wayan yace “I love you sooooo much Khair, Mahal na Mahal kitab KIM(I love you da Philippines)”

????????????????????

Nana fa’ad En Eesha
[11/22, 11:49 PM] ‪+234 806 524 6449‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Nov, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 67]

Da gudu tashiga d’akin Abban ta taje ta sanar dashi abun da Zil ya fad’a akan gobe iyayen sa zasu zo, yace
“Allah kaimu goben Khairiyya, Idan alkhairi neh Allah ya tabbatar idan kuma sharri neh Allah watsar”, Khairiyya tace
“Ameen Abba nagode”

Da daddare Khairiyya ta kwanta bacci abu kamar wasa bacci yaki zuwa ba wanda take tunani ya tsaya mata a rai kamar Suraj, juye juye take akan gado amma bacci yaki zuwa mata, tashiwa tayi tayi alwala tafara jero nafiloli ba adadi, addu’a sosai takeyi wa Suraj Allah basa mace tagari, itama Allah za6a mata miji mafi alkhairi da ita..

Ta 6angaren Suraj shima kasa baccin yayi, bai ta6a jin son wata mace a duniya kamar KIM ba, yana son ta yana tsananin sonta, zubar da hawaye yake yana rok’a mata gafara awajen Allah, bayan ya idar yana kuka yana cewa KIM bansan haka kike ba, I tot abunki a shaye shaye ya tsaya ashe harda bin maza, why KIM, why, Allah gafarta miki KIM Allah ina rokan ka kashire mini son Khairiyya a zuciya ta, bayan ya gama surucen sa ya d’auka Al Qur’ani yana karantawa

Bayan ta idar ta kunna wayan ta, Ammar neh ya fad’o mata akai, message tafara typing kamar haka
Mr Ego, bazan ta6a gajiya wajen kiran ka da tura maka messages ba, I miss you sooo much, in need of your prayers dear General Suraj auren bazai yi dashi ba, ya janye aure na

Russia

Ammar neh kwance a d’akin sa da cardigan a jikinsa blue, hannun sa akan kirjin sa da duk alamun zuciyan sa na rad’ad’i, ya ramei yayi duhu bakin sa a bushe, jin shigowar message yayi a wayan sa daman wayar sa na kusa dashi, bud’e wa yayi ya karanta message d’in, abun ya basa mamaki sosai, ya kasa ganeh kansa murna zaiyi koh tayata bak’in ciki, a take yayi replying mata kamar haka
KIM how comes, why, what happen
Zuciyan sa yana mai bugawa, hannun sa rike da wayan yana jiran ta tayi reply, ba’afi seconds talatin ba tayi reply kamar haka
Wai ni Khairiyya HIV positive, ganin message d’in sai ya fashe da dariya, da sauri ya mata reply kamar haka
Like seriously, LOL KIM, funny…….. waya fad’a masa haka, ta masa reply
Wani Fake stupid likita, barsa Ammar zan koya masa hankali, kasan I love irin wannan games d’in, Ammar yayi dariya sosai, rabon sa da dariya har ya manta, ya mata reply
Don’t worry dear every disappointed is a blessing, Khairiyya ta masa reply kamar haka
ni kuwa nasan da haka, cox now zan aura wanda zuciya ta keso, Wato Zilyadeen, what do u think, yana gama reading ya rik’e kirjin sa sabida rad’ad’in da zuciyan sa ke masa, reply da baiyi ba kenan, wani message neh ya karo shigowa Khairiyya ya bud’e
Why Silent hot jerk, Ammar yana gama reading msg d’in yayi offing na wayan sa gaba d’aya, yace I wish you all the best KIM, Allah baki mijin dazai kula dake har the end of your life….. wannan kenan

Nigeria

a gurguje pls

Zilyadeen sun gama komai da Rumaysa ta amince tana taya sa murna a fili amma bai kai har cikin zuci ba, an gama komai daga sadaqi har kayan toshi, Ummi (Maman Ammar) ita take shirya Khairiyya dan yanxu Khairiyya ma a gidan take, Abba kuma yana can Dubai had’owa Khairiyya kayan d’aki da kitchen, Khairiyya tasha gyaran amare tayi kyau abunta saura kwana uku a d’aura aura, sunyi kiran Ammar amma shi koh d’aga wayan bayayi amma ya tura musu message akan zaizo

Zilyadeen neh yana tuki a motar sa wata mota corolla S yake ta binsa abaya sai horn ake danna masa, Zilyadeen ya samu waje yayi parking motar shi, yana kallo ta mirror na kofan sa waye yake masa horn haka, Wani chocolate guy mai moderate height yafito a motar, ba kowa baneh illa Doctor Umar
Docter Umar ya sauka a motar shi yazo wajen inda zil yayi parking, Zil ma yafito a motar sa, Doctor Umar ya mika wa Zil hannu suka gaisa, Zil yace
“Your face looks familiar, sorry please ina nasan ka”, Doctor Umar yana murmushi yace
“Maybe a University Teaching Hospital”, Zil yace
“Ohhh kai doctor koh, maybe a wajen na sanka, So hope all is fine”, Doctor Umar yace
“Malam Zilyadeen, kai d’an uwana neh bazan so wani abu yasamei ka ba, Love for your brother what you love for yourself, Laa yu’u minu ahdakum hatta yuhibbul akhee ma yu hibbul li nafsii”
Zil yace “Na’am wannan haka yake”, Doctor Umar ya gyara tsayuwan shi yace
“Ni doctor na Khairiyya neh a asibiti, sorry but I have to tell you this, Khairiyya tana da HIV, here re her reports”, ya mik’a masa wasu papers, Zil hannun sa yana rawa ya kar6a, yana duba su d’aya bayan d’aya, papers neh na result na HIV, ga sunan ta da komai duk informations dai akai
Docter Umar yace “Shin kasan dalilin da Suraj yafasa auren ta, wannan shineh reason da Suraj yafasa auren ta, I am not saying all this things dan ka fasa auren, No kawai inaso ka sani neh, if kana so ma ka bincika da kanka, na barka lafia”, ya barsa a wajen in dilemma, sai kallon papers d’in yake, da karfi yaja motar sa sai gidan su Khairiyya, cikin gidan direct yashiga zuciyan sa yana har6awa,ba kowa a gidan sai masu aiki, suna tambayan sa koh lafia yace musu Khairiyya ta aiko sa, d’akin ta ya nema yafara bincike, tun daga kan wardrobe, drawers komai, ya bud’e wani karamin kit red colour mai kyau, zare ido yafara, ba komai baneh a cikin kit d’in sai receipt na asibiti da drugs, he was more than shock, a daddafe yabar gidan, da kyar ya iya driving motar zuwa gidan su Uncle Hisham, a lokacin Khairiyya tana tare da Zaynab suna hira a garden yayin da wata mata take mata dilka, ya tambaya mei aikin gidan inda khairiyya take, mai aikin ta fad’a masa ba sallama yaje wajen ya watsa mata papers d’in a fuska yace
“Khairiyya mei wannan, I can’t believe this”, Khairiyya hannun ta yana rawa ta d’auka paper d’aya tafara reading, all kamar na Suraj da sauri ta kalle Zil wanda ya gama fita a hayyacin sa tace
“I can explain, let me explain pls”
“Explain what Khair, explaine what, kin cuce ni Allah ya isa tsakani na dake, auren kuma an fasa, na bar muku duk wasu abubuwan da muka kawo” ya barta a wajen
Yana barin wajen ta fashe da kuka, yi take sosai kamar wanda aka mata mutuwa, cewa take
“Umar kayi na farko na barka toh wlhy yanxu baka isa ba” Su Ummi da Zainab sai hakuri suke bata amma ina taki tayi shuru, daidai lokacin Abban ta yakira ta, da sauri tayi picking call d’in, Abba neh yafara magana yace
“Baby nah nashigo Nigeria, yanxu ina Abuja, but zuwa 2hours jirgin mu zai tashi zuwa maid, ya shirye shirye”, kawai sai ta fashe mishi da kuka tace
“Abba Zilyadeen shima ya fasa auren”
“What, kinsan mei kike fad’a kuwa”
“Abba wlhy, duk aikin Umar neh, Doctor Umar”, Abba ya sauke numfashi mai nauyi yace
“Thank God ina cikin Abuja, do you know what will happen, kije airport if akwai jirgin da zaije Abuja and any available space koh nawa neh kud’in sa ki hau kizo, kice musu you are my daughter, any amount kawai if akwai space kizo ki samei ni a Abuja, and kuma kizo da gaba d’aya fake results d’in kinji baby ki daina kuka”, Khairiyya tace
“Ohk Abba, bye”, ta katse wayan, Khairiyya ta samei Ummi tace
“Zanje airport yanxu Abba yace nasamei shi a Abuja”, Ummi tace Hope dai lafia, Khairiyya tace lafia kalau Ummi karki damu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button