KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

  Zilyadeen yana dawowa daga masallaci yashiga cikin gidan sa direct d'akin Rumaysa ya wuce, da mamakin sa yaga a bud'e, a ransa cewa yake koh ta sauko neh daga fushin da takeyi, zama yayi a kujira yana jira ta fito a ban d'aki shi duk a tunanin sa tana ciki, ya kusan minti talatin baiga tafito ba a take ya tashi ya bud'e kofan toilet d'in yaga empty, gidan kaf ya duba bata ciki, ya fita wajen Isa mai gadi yace

“Kaga fitan iyalina “, Isa mai gadi yace
“Naga fitan ta Oga, ni na bud’e mata gate ma ta fita”, ji yayi hankalin sa ya tashi, da sauri shima yace bud’e mun gate, da gudu ya d’au key na motar sa shima ya fita a gidan, gidan su direct ya wuce, yana horn mai gadi ya bud’e masa kofa yashiga ya hango motar Rumaysa, yana shiga yaga falon ba kowa empty ya wuce part na mummy direct, shigan sa yayi sallama, duk suka d’aga kai suka kalle sa, ya zauna a kasa ya gaishe da mummy, yace
“Ina kwana mummy”, mummy tace
“Ban gansa ba kaji, wato kai baka da mutunci kana son ja mana magana a idon duniya koh, yaushe ma aka daura muku aure da Rumaysa da har zakace kanason kara wani auren ehhh, kuma fa kai kace kana son Rumaysa bawai auren dole aka muku ba, toh wlhy let me tell you something, idan Rumaysa bata amince da auren nan bato sai dai kaima ka hakura”, Zilyadeen jikin sa yana 6ari yace
“Mummy this is not fear, ku mini rai, inaso na aura Khairiyya bawai dan bana son Rumaysa baneh, a’a ko kad’an ina son Rumaysa Mummy kuma ina son Khairiyya “, Mummy tace
“Toh ka za6a d’aya, KHAIREEYYAH KOH RUMAYSA”
“Duka mummy, duk ina sonsu”, yazo har gaban Rumaysa yace
“Rumaysa please kiyarda dani”, Mummy ce ta katse shi tace
“Karka 6ata lokacin ka, baza ka ta6a auren Khairiyya ba muddin Rumaysa bata amince ba, that’s FINAL”

NI NANA BAN HAIHU BA, NAJI ANA CEWA NA HAIHU, KOH AURE BANDA BALLE MAGANAR HAIHUWA, AISHA KABIR BATAGARAWA MUGUWAR MAKARYACIYA CE???????????????????????????????? ita ta muku karyan nan, Sorry Wlhy ina zuwa school ban samu time ba shiyasa kukaji ni shuru but zaku jini har zuwa Sunday In Shaa Allah  ????????????????????????

incase kunyi clash da typing errors???????????? ba time 4 me to edit….. Thanks all

Nana fa’ad En Eesha

www.narhnah.mywapblog.com
????????????????????????
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

[Oct, 2016]

 Written by Nana fa'ad En Eesha

I dedicated this page to Tawan JJ (Aisha kabir batagarawa) ILY????????????

{Page 59}

   Mummy tace "maza tashi kubar mini gida", Zil duk jikin sa yayi sanyi, Rumaysa  ta tashi ta fita, tun kan yabar cikin gidan yaji karan motar ta alaman ta tafi kenan, kasa driving  motar yayi ya zauna kawai a ciki, shineh baija motar ba sai kusan bayan minti arba'in, direct gidan sa ya wuce, yana shiga yafara jin kamshin girkin Rumaysa, kitchen yashiga yaga tana ta faman  girki, tana ganin sa ta masa murmushi tace

“Nurul Hayat welcome, kayi hakuri in next 15mins zan gama breakfast d’in kaji”, mamaki neh ya cikasa, “ohk” kawai yace ya fita a kitchen d’in. D’akin sa yaje yayi wanka, bayan ya gama parlour yaje ya zauna ya kunna TV, shigowar text message yaji a wayan sa, take ya bud’e dan ganin sunan Khairiyya
so sorry dear I know it’s too early to call or send you a message, but i just can’t wait zuwa anjima because i’m super excited, you know why?, Abba yana son ganin ka, In Shaa Allah zamu kasance tare har karshen rayuwar mu…… Please kazo around 11:30 haka, I miss you
Sa hannun sa yayi a gashin kansa yace Yaa Allah help me, Rumaysa ce ta ta6ashi tace
“Husby your breakfast is ready, kazo dinning”, Zil yace noo ki kawo mini anan, Rumaysa tace ohk toh… Rumaysa ta kawo masa abinci suka zauna suka ci, mamakin ta kawai yakeyi, bayan d’axu ta gama masa rigima yanxu kuma tana pretending kamar ba abunda yafaru, bayan sun gama cin abincin ta kwasa plates ta kai kitchen ta wanke, cikin minti goma ta gama ta fito ta samei shi a parlour yana zaune, ta zauna kusa dashi ta shafa fuskan shi tace
“I am so sorry husby, nasan na 6ata maka rai”, Zilyadeen yayi murmushi yace
“Ba komai wify, yawuce… yanxu Khairiyya ta tura mini message akan Abban ta yana son ganina, Rumaysa I need your help please, you’re my hope please dan Allah ki amince na aura Khairiyya, ki amince naje na samei Abban ta nace masa Eh inaso na aure ta”, Rumaysa atake tafara zub da hawaye tace
“Zilyadeen zan iya maka komai a duniya, but I am so sorry bazan iya amincewa ka aura Khairiyya, not now, today koh in next one thousand years to come neh”, Zilyadeen ransa idan yayi dubu ya 6aci, yace
“Rumaysa wannan wani irin kishi neh, why are so selfish, wannan ba halin ki baneh, kin ban kunya kin bani mamaki, tirrrr da halinki “, Ya fita yabar mata gidan gaba d’aya, zubewa tayi a kasa tafara kuka sosai, cewa take Ina sonka Zil, I love you, Ba macen da daga auren ta sati biyu taji mijin ta na maganan kishiya bataji kishi ba,bataji yadda nakeji ba, m very sorry Zil, forgive meeeee, haka tayi kuka mai isarta,kanta sai sarawa yake, tashiwa tayi tasha Panadol ta kwanta, batafi minti biyar da kwanciya ba bacci ya d’au ke ta……

 *12:30 pm*

Abba zaune da Khairiyya a parlour, Abba sai duba agogon sa yake yace Baby na baki masa magana akan inason ganin sa baneh, Khairiyya tace
“Wlhy Abba na tura masa text message, har ya nuna mini delivered, Toh bansan koh ya gani ba”, Abba yace
“Why not ki kirasa, inada very important meeting by 1:30, call him now please”, Khairiyya ta d’au wayar ta takira sa kusan 5miss calls but baiyi picking ba, tace
“Abba baya picking call d’in fa” duk hankalin ta a tashe, Abba yace
“Idan baizo ba in next 10mins gaskia ni zan wuce”, text neh ya shigo wayan ta atake ta duba, taga Zil
kiyi hakuri Khair, I can’t make it, so sorry for the disappointment… Rumaysa taki ta amince na aure ki, kuma parents nawa sunyi sai only if idan ta yarda. But In Shaa Allah I will try my possible best to convince her, very sorry Khair… Bye
Hawaye tafara, Abba yace “Khairiyya mei yafaru”, shuru tayi batace komai ba, kar6an wayan ta Abba yayi yakaranta message d’in tsab, Abba yace
“Baby nah what was he trying to say, I just can’t getrit, kimini dalla dalla, wacece Rumaysa”, Khairiyya tana share hawayen ta tace
“His wife Abba”, What! Abba yayi exclaiming, yacigaba
“Daman yana da mata shineh baki sanar da ni ba, mtswww Rubbish”, duk sanyin falon yana zufa, cire babban rigan sa yayi ya ajiye a gefe, falon shuru sai sautin kukan Khairiyya, Abba a rayuwar sa baison ganin Khairiyya tana zub da hawaye, har cikin ransa yakeji, yayi cooling voice nasa yace
“Mamanah I know that kina son shi sosai, I can’t say kidaina son shi cos bani da right ma na fad’a miki haka, but kiyi tunani mei kyau, bance karki aura mei mata ba all what m saying shineh kiyi addu’a Allah za6a miki mafi alkhairi, if you can wait har sai matar sa ta amince ba matsala”, Khairiyya ta rike rigan sa tace
“Abba wlhy na hakura, Suraj zan aura, Wlhy na hakura da Zilyadeen
Abba yace “shhhh baby nah, aure ba’a masa haka, kar kiyi auren huce takaici, you are still young baby nah, ki nutsu and choose a life partner”, Khairiyya tace
“I trust Suraj, bawai dan Zil ya mini haka baneh na za6a Suraj, a’a Suraj koh ba komai ina kaunar sa, inajin shi kamar jini nah”, Abba yace
“Toh shikenan madallah, wipe your tears my dear, muta addu’a Allah za6a miki mafi alkhairi”

~~~

Gidan su SURAJ

Gida neh babba a cikin anguwan Fori, ya had’u iyakan had’uwa. A parlour wani dattijo dogo chocolate colour, yana da dogon hanci da idonsa daidai ba manya ba zaune a lallausar kujera, sai gefen sa wata farar mata amma da gani hasken na kanti neh (bleaching) wanda baza ta wuce shekaru arba’in da bakwai ba, doguwa ce itama, tanada manya manya ido, bud’addan hanci da bakin ta madaidaici baida girma
Suraj kuma zaune akan carpet, kansa a kasa. Suraj yace
“Abu yarinya sunan ta Khairiyya yar gidan Alhaji Ibrahim Muhammad fu’ad mai naira”, bud’e baki matar tayi tace
“Anyi Yaron nan kasan mei kake fad’a kuwa, yar gidan Fu’ad mai naira guda”, Suraj yayi murmushi yace
“Haba Mami, yar shi ce ta cikinsa”, Mami ta zare ido tace
“Ina kai ina yarinyan Mai naira, ai tafi karfin ka”, Abu neh ya katse ta yace
“Haba Saude ya kike magana haka, ai mace bata fin karfin namiji, kai kuma Suraj ka sanar da mahaifin yarinyan zamuzo sati mai zuwa In Shaa Allah”, Suraj yana Sosa keya had’e da murmushi yace
“Nagode Abu, ni zan fita office”, Abu yace toh sai kadawo, ya tashi yafita a falon, Abu yace
“Maman Munay nizan fita”, tace “Toh Alhaji sai kadawo Allah kiyaye hanya”, ya amsa da Ameen ya fice a gidan, yana fita a falon wata yarinya wacce bazatafi shekaru ishirin da d’aya ba tafito daga d’aki, doguwace baka tana kama da Abu sosai, hancin su iri d’aya dogo tsit kamar pencil, da bakin ta irin nasa karami sai idon ta dara dara irin na mahaifiyar ta Mami, Kyakkyawa ce sosai yayin da kyaun ta yake rud’an ta. zama tayi akan kujera tana tura baki tace
“Mami ya kuka kare”, Mami tace zo nan daughter nah munay d baby, my baby last, yarinya kyakkyawa kin wanda ya rasa, yarinya auto, yarin…. bata karasa ba yarinyan (munay) tace
“Kai Mami ya’isa haka please, just tell me wacece yarinyan da yaya Suraj yake so, wacece yarinyan da ta sace zuciyan wanda nake so nake kauna fiyeda komai a rayuwa ta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button