KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Nana fa’ad En Eesha

????????????????????????
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

[Oct, 2016]

Written by Nana fa’ad En Eesha

Page 48~50

Dukkan su suna zaune Dr Kaysan yafito a Emergency room, yace musu yanxu za canza mata d’aki za kaita VIP, idan an kaita zaku iya shiga ku ganta,suka masa godiya, bayan an kaita d’akin Nurse tazo tace musu yanxu zasu iya shiga, duk suka tashi a guje suka shiga d’akin, bacci take hankalin ta kwance fuskar ta wayam da gani ansan taji jiki, Rumaysa tana zare ido ta nuna ta da hannu tace “Khairiyya”, Mummy ta juya tace “kinsan ta neh Rumaysa”
Rumaysa tace “Eh na santa Mummy kuma kawar Teema ce”, Daddy yace Allah sarki gata kyakkyawa da ita
Hajja ce take ta kallon fuskan, Zil duk hankalin sa a d’age dan kar ta ganeh ta dan yasan Hajja bata da hakuri da mutunci tawani fanni, bayan Hajja ta gama kare wa fuskan ta kallo tace
“Ikon Allah, yarinyan nan dai tana mini kama da wata”, Zilyadeen zuciyan shi ya buga a take yace
“Kedai Hajja ke yanxu idon ki wani karfi neh dashi, wataran abu ja sai kice bak’i”, Hajja tace “Ikon Allah duniya ta 6aci, yanxu matar ka kake fad’a wa haka, lalle kayi sabon amarya dole, Toh ai nafi Rumaysan kyau da gani”, Zilyadeen yace
“Gaskia Hajja kin fita kyau ai shikenan koh”, Hajja ta murkud’a masa baki nidai nana nace lalle kam, Haka su Daddy, Mummy da Zilyadeen suka bar Hajja da Rumaysa a d’akin asibitin………

Ammar
Haka yasha kukan sa yatashi, duk karfin sa yakare, Ummi sai kiransa take a waya amma baya d’auka wa, ya d’auka yace mata mei, karfe biyun dare ya fita a International Hotel d’in, ya sallame sojojin shima yawuce gidan sa, alwala yayi yafara jera nafiloli har aka kira Subh, yana idar da sallan Asuba barci mai nauyi ya kwashe sa…….

  Da misalin karfe bakwai na safe a International Airport maiduguri, Suraj nagani yana sauka a jirgi da Uniform nasa na sojoji, yayi kyau fatar shi tayi fresh, da sajen sa ya kwanta luff a fuskar sa, taku yake na kasaita irin maza masu ji da kansu, Sojoji neh suka kar6a briefcase na hannu sa suka tsara mishi suna "Welcome Sir", bud'e masa owernest kwana na wata mota 4matic Ash sukayi, yashiga ya zauna, driver'n shi yace "Sir ina zan fara kaika, to the office or home"

“Home” Suraj ya basa amsa da cracky voice nasa, Wani babban gida neh a cikin giwa barrack aka kaishi, gidan ya tsaro daidan kud’in sa, bud’e masa kofa a kayi ya fita ya shiga cikin gidan sa, wow ni na furta dan gidan ya had’u ba magana, d’akin sa ya wuce yayi wanka, bayan ya fito a wanka ya saka wando three quarter fara kal da riga shima fari kal mai gajeran hannu, zama yayi a lallausar kujeran parlour nasa, rufe ido yayi yace “KHAIREEYYAH Khairiyya I miss you soooooo much”, bud’e idon sa yayi ya d’auka remot ya kunna TV, yana DSTv channels neh yace bara na kalla NTA, yana juyawa zuwa tashar NTA ya kalla hoton Khairiyya ana nuna wa Missing, baisan lokacin da ya tashi yace “WHAT”, yana zara ido
Khairiyya is missing, no way, yarinyan da dan ita nayi squeezing na dawo Nigeria, na kasa jira shekara d’ayan yayi, Noo Noo, a take ya zare makullin motar sa ya ja motar sa zuwa NTA Maiduguri, yana zuwa aka sara mishi, ya tambaye su tun yaushe ake cigiyar ta, sukace masa sha biyun dare, yace yanxu mai information, akace masa ba wani information sai motar ta da aka gani a International Hotel, yace waye neh ya kawo muku complain, sukace ” wani yayan taneh sunan shi Ammar”, a zuciyan shi dai tun da yasan Alhaji Ibrahim Fu’ad mai Naira ‘yarshi kwaya d’aya dul neh kuma itace Khairiyya, dalilin da yasa ya kara dawowa shineh dan yaji an kulle mahaifin ta a prison, yasan she’s very stubborn zata iya aikata wani abun da shekarun ta bazasu d’auka ba shiyasa ya dawo, kar6an number Ammar yayi, yana ta ringing amma Ammar baya d’auka wa, ya hakura Yace koh bayan minti talatin zai kara dialling

Alhaji Abdullahi (Daddy, mahaifin Zilyadeen) a parlour yana kallon News kawai yaga hoton Khairiyya ana neman ta, kiran Zilyadeen yayi yazo ya kalla ana nuna Khairiyya a Tv, da sauri suka d'auka number da aka bayar wanda za'akira idan an samei ta, Zilyadeen yace Daddy bara na kira nasan yanxu dole suna cikin tashin hankali, kiran Ammar sukayi amma duk da haka shuru bai d'auka ba, Zilyadeen yace anya lafia, but zan kara kira

Da misalin karfe takwas na safe Khairiyya ta farfado, sai kallon d’akin takeyi, ta rasa mei yakawo ta asibiti, Rumaysa tana ganin Khairiyya ta bud’e ido tazo kusa da Khairiyya tana mata murmushi tace “Khairiyya sannu koh”, Khairiyya ma ta maida mata da murmushin tace “Yawwa Rumaysa”,
Rumaysa tace “na d’auka baza ki ganeh ni ba ai”
Khairiyya tayi murmushi da kyar tace “na’isa ace bazan ganeh kiba, kuma kullum sai munyi hiran ki da Teema ai”, muryan Hajja neh ya tsaida su tace
“Kajimun ja’irar yarinya, kinsa mara lafiya a gaba kina ta zuba, haba mana kekuma, keda yakamata ki taimaka mata ta wanke baki ki had’a mata shayi tasha amma kika sata a gaba kina zuba”
“Kai Hajja ba yanxu ta tashi ba, sannu fa nake ce mata” cewar Rumaysa

“Kin raina ni ai, kin ganni tsohuwa kin d’auka kunne na baya aiki bana ji, toh har yanxu garau nake yar bakin ciki”, duk daurewan Khairiyya sanda tayi dariya, Rumaysa zata bar wajen Khairiyya ta rike hannun ta tace
“Rumaysa ya akayi nazo nan wajen”
“Saidai kiyi hakuri Khairiyya accident neh wlhy yaya na neh yana tafiya ya buge ki”, Khairiyya ji tayi zuciyan ta ya buga, accident ta fad’a a zuciyan ta, toh ya akayi hakan ta faru, ta kasa tuna komai, tace a zuciyan ta abun da zata iya tunawa last jiya shineh taje gidan Ammar, ta wuce International Hotel, sai ordering abincin da tayi, shine kad’ai abun da ta iya tunawa, Rumaysa tace
“Karki damu yaya na zaizo in next 30mins haka, hope kin yafe shi”, Khairiyya tace
“Haba Rumaysa ai tsautsayi neh, it can happen to anyone, qaddara ai bata wuce ranan ta”, Rumaysa tace
“Haka neh kam Khairiyya, bari na kawo miki roba ki wanke bakin ki”, Khairiyya tayi yunkurin tashiwa taga duk hannun ta a d’aure bata lura bama sai yanxu, da sauri ta d’aga kai ta kalla Rumaysa tace
“What happen to my hand, mei yasame hannu nah”, Rumaysa tace so sorry dear kin samu karaya but you don’t have to worry the doctor said in next 3weeks zai had’u, In Shaa Allah nan da wata uku k’ashin zai had’u sai ki dage da cin KZ
Hajja tace “yanxu Rumaysa ba zuba surutu kikeyi ba koh kallon ta kike yi dan iskanci, kin raina ni koh ai banga laifin kiba laifin Zil nagani”, haka Hajja ta kawo mata Sabuwar brush da toothpaste (makilin), ta taimaka mata ta wanke bakin ta, sannan ta had’a mata shayi da bornvita ba madara(kunsa masu karaya ba’a basu madara), Khairiyya sai kallon tsohuwar take tana cin goron ta, itadai Hajja tana bata dariya, kuma kamar ba yau tafara kallon taba, a zuciyar ta cewa take the face looks familiar (kedai kullum), Rumaysa ta taimaka mata ta zauna

Firgit ya tashi a bacci, duba agogon wayar sa yayi yaga 98missed calls, duk wayar sa ya d'au zafi battery ma yakusan mutuwa, kira neh ya sake shigowa, ya d'auka yace

“Hello”, can kuma yace “Thank you very much tana Teaching Hospital koh, In Shaa Allah zamu had’u nagode sosai”, koh wanke fuskar sa baiyi ba balle wanka ya d’au key na motar sa, shiga motar sa yayi ya fisge ta, gudu sosai yake kamar wani mai Race, nan da minti biyar har ya iso TH, number d’akin da aka gaya masa yafara nema, babban asibiti neh ya kasa samuwa sanda wani security ya taimaka masa, bud’e kofan yayi ya kai idonsa zuwa kan gado, Khairiyya ce zaune tana shan Tea da pepper soup na kaza wanda Hajja ta sakata gaba ala dole sai tacinye, kawai gani sukayi mutum a kansu, baisan lokacin da ya zo gaban Khairiyya ba ya kama hannun ta yana kuka yana cewa
“KIM Alhamdulillah, bansan ina zansa kaina idan ban ganki ba, hankali na duk ya d’aga ya tashi”
Kara tasake ”washhhhh Ammar you are hurting me, akwai zafi”, baisan lokacin da ya janye hannun saba, shida yashigo baima lura da d’aurin hannun taba, bud’e baki yayi yace
“Mei yasamei hannun ki KIM”, da muryan shagwa6a tana ture baki tace “Accident Ammar”

“Ayyah so sorry dear”, yana maganan duk hankalin sa a tashe, Rumaysa da Hajja bud’e baki sukayi suna kallon su, Hajja tace
“Wannan mijin kineh”, Khairiyya ta zare ido tana kallon Hajja tace
“Haba Hajja wannan fa yayana neh”, Hajja tace
“Aww gaskia akwai kama kam”, Khairiyya tace “kai Hajja taya kike had’a ni da wannan ugly face d’in, pig face with caterpillar eyebrow”, Hajja ta bud’e baki tace
“Mei kuma catofila”, duk sukayi dariya Rumaysa tace “caterpillar ba’ace miki catofila ba”, tooh ni ina nasan muku, idan zagi nah kukayi naji dadi nagode sosai amma ban yafe ba..
Duk suka bud’e baki suna dariya, Ammar yace
“Khairiyya ce ta zage ki ba muba”, Hajja tace ku kuka sani ni bara na sha iskan Allah a waje na bature ya ishe ni, ta fita a d’akin, Rumaysa ma tace “Toh bara na baku iska”, Khairiyya tace
“Rumaysa mei kike nufi zaki bamu iska, yi zamanki ai na fad’a miki yayana neh”, Ammar yace
“Jike Rumaysa sai na nemi ki”, Rumaysa tana dariya tace “kindai ji kunya Khairiyya har kina wani denying”
Khairiyya ta juya tana kallon Ammar tace “idan na warke i’ill bury you alive”, Rumaysa tana dariya ta bar musu d’akin..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button