KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ammar kasuwa yashiga yayi cefane, su kifi da kaza, dasu tomatoes, komai dai yasiya, Ummi tana zaune tana had’a fruit salad yasame ta yace Ummi ga kayan cefane fa, please kitashi muyi girkin nan da wuri kafun hud’u yayi, Ummi tace
“Nikam na shige su, Toh yanxu Hajiya Ramaadah ta kirani tace kar mu dafa abinci zasu zo dashi”, Ammar ya 6ata rai yace
“Ummi Toh mu ina ruwan mu dasu, ai Khairiyyan muce, mu yaka mata mu dafa mata abinci basu ba”, Ummi ta watsa masa mugun kallo tace
“Toh ba abincin da zan tashi na dafa, Allah ya kawo mini sauki, tunda sunce zasuyi bashikenan ba, maza tashi ka bani wuri na sha iska mara kunya kawai”, haka ya tashi yana kananan maganganu ya nufe kitchen d’in, su kuma gashi basu da masu aikin dafa abinci, haka ya cire kayan sa, ya saka wani daban, ya d’aura apron akai, ya zage ya fara wanke kifin sa wanda already an gyara a wajen, bayan ya wanke tas, ya wanke atarugu dasu tomatoes da albasa ya zuba a blender ya markad’a, ya had’a pepper soup na kifi, bayan nan ya dafa jelof na shinkafa, kajin kam a fridge yasaka dan yagaji, yace sai gobe zai dafa mata shi, bayan ya gama ya zuba komai a food flakes yashiga wanka, bayan ya fito ya shiga d’akin ta ya tattara mata duk kayakin da take bukata, shiri yayi ya fesa designers turaren sa, sai kallon agogon hannun sa yake Rolex mai uban tsada, ji yake lokaci baya tafiya, Allah Allah yake karfe hud’u yayi yaje asibiti ya kalla KIM
Ta 6angaren Captain Suraj ma haka, sayayyan duniyan nan ya mata, su kaji, drinks,ice cream, da kayan shan iska, A can 6angaren Zilyadeen tun karfe uku ya shirya, already ya siya kaji da kifi yace Rumaysa d’aya tayi pepper soup d’aya tayi pepper, yace
“My future wife dan Allah kiyi yayi dad’i please, kar gishiri da barkono suyi yawa, kuma kina gamawa ki shirya mu tafi koh karfe hud’un batayi ba kafun mu iso zatayi”, Ita dai Rumaysa dariya takeyi, irin wannan zumud’in ai yayi yawa, tace Allah sarki yana tausayawa Khairiyya koh dan shi ya buge ta neh
Karfe uku da minti goma Ammar ya dame Ummi su tashi suje asibiti, Ummi tace ita Sam sai karfe hud’u zata bar gida, haka yayi zuciya ya d’auke food flakes nashi yafita a gidan, Ummi kam sai dariya take masa tace lalle akan Khairiyya Ammar yashiga kicin, Karfe uku da rabi yana cikin asibitin, hana sa shiga sukayi, dakyar da rikici suka barsa yashiga, a lokacin Hajja da Khairiyya suna nan ta6a hira, Zainab tana kwance tayi bacci, yashiga da sallama Hajja ta amsa, Khairiyya duba agogon jikin bango tayi taga hud’u ma baiyi ba, tace
“Ammar ya kashiga karfe hud’u baiyi ba”, yayi dariya yace
“Kuji yarinyan nan fa, ance miki ni wasa neh”, ta murkud’a masa baki, suka gaisa da Hajja, Hajja tace
“Khair anya Ammar ba da biyu ba”, Khairiyya ta had’e fuska tace
“Hajja wai ni sau nawa zan gaya miki yayana neh and nothing else”, Hajja tayi dariya tace toh bari muji ta bakin sa, ta juya wajen Ammar tace
“Shin ni kai kana sonta neh”, Ammar dariya ma maganar ta basa yace
“Kai Hajja, mei zanyi da ita, kanwata ce fah”, yana mai jin kunya, wajen Zainab yaje ya bubbuga ta da kafa yace
“Keeee tashi, kinzo kina yiwa mutaneh bacci a asibiti, toh mei amfanin zaman ki”, Zainab ta tashi tace kaga yaya Ammar ina bacci na zaka zo ka tada ni, Ammar yace
“Ehh na tashe ki d’in, stupid”, Hajja tace
“Haba Ammar, daka barta ai, mei ka kawo haka a food flakes”, yana murmushi yace
“Kifi neh da jollof rice”, Hajja tace
“Irin wannan wahalan haka, toh miko mini”, ya mika mata ta zubawa Khairiyya a plate, tace
“Kici Khair kinji, ki samu karfin jiki, baki son cin abinci wollah”, Khairiyya ta kar6a ta saka pepper soup d’in kifin a bakin, a take ta fusgar dashi, tace
“Ammar mei wannan, wa ya dafa”, Hajja ma ta karba ta ta6a, itama da kyar ta had’iye, Ammar yace
“Nii na girka”, duk suka kwashe da dariya, Khairiyya tace
“Ammar waya saka ka dole , haba “, suna cikin masa dariya saiga Rumaysa, Zilyadeen da Suraj duk suka shigo lokaci d’aya da kaya nik’i niki a hannu, Khairiyya tace
“Rumaysa zo kiyi tasting pepper soup na Mr Ammar, the chief Cook”
Rumaysa ta ta6a tace
“Kai nikam ya mini dad’i sosai”, duk suka kwashe da dariya banda Ammar
Duk suka gaishe da Khairiyya ya jiki ta ansa da sauki, Rumaysa tace
“Khairiyya ga abincin da yayana Zilyadeen yace na had’o miki”, Khairiyya ta d’aga ido ta kalla Zil tace
“Nagode”, Rumaysa ta zuba mata fried rice da pepper chicken, Captain Suraj ya mika mata ice cream yace tasha karya narke, haka taci abincin su Zilyadeen da ice cream na Suraj sai santi takeyi….. Bayan ta gama ci duk suka zauna hira sai Ammar yace shi zaije masallaci yayi sallah sai ya wuce yana da aikin yi
Bayan awa d’aya sai ga Ummi da mummy suma sun shigo, Suraj da Zilyadeen suka tashi sukace suna da abunyi zasu wuce, Khairiyya ji tayi kamar kar Zilyadeen ya tafi dan bata gaji da kallon sa ba
Bayan sati d’aya
Haka nan duk suna d’awainiya da ita na sati d’aya ba wanda ya nuna alaman gaxawa, kowa dai kullum nuna kokarin sa yake
Kusan Karfe biyar da rabi duk suna zaune ana hiran duniya docter yashigo d’akin ya duba Khairiyya, yace komai is set kuma nan da sati biyu hannun zai had’u da yake kariyan ba sosai baneh, kuma za sallame su yanxu, after two weeks suzo ayi X-ray
Duk suka masa godiya, ya rubuta takardan sallama, bayan nan Hajja ta dage sam Khairiyya zata bisu su zasu gama jinyar ta, haka Ummi ba yadda ta iya ta amince mata, Khairiyya kam dad’i kamar tayi yaya zasu na kwana da Zilyadeen a gida d’aya

 Typing errors koh, sorry ba time

Nana fa'ad En Eesha 

????????????????????????
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

Page 53

 Ammar baiso hakan ba, duk ransa a jagule, shi kwata kwata baison KIM ta kwana gida d'aya da Zilyadeen, sai wani kumbure kumbure yakeyi, mugun kallon da Ummi ta watsa masa yasa yabar d'akin, Rumaysa kam sai murna take ta samu abokiyar hira, haka aka tattara duk kayan wajen aka kai mota, Hajja tacewa Khairiyya 

“Khair ke kishiga motar Ammar abokin fad’an ki sai ku bimu a baya tunda ba sanin gidan kukayi ba”, itadai Khairiyya bata so haka ba, ta so ace mota d’aya zata shiga da Zilyadeen, Captain Suraj ma yaso da ance tashiga motar sa, Hajja tajuya wajen Zainab kanwar Ammar tace
“Zee ke da Ummi da mummy kushiga Motar soja ni da kishiyata motar mijin mu zamu shiga”, Ummi tayi murmushi tace toh Hajja ai Suraj ma d’an mu neh, duk suka shiga motar
Zilyadeen yana gaba sai Suraj sai na Ammar shineh na karshe, sai hiran sa yake da Rumaysan shi baya koh jin kunyan Hajja, itadai sai Allah wadai take da halin sa, tace yaro ba kunya, itadai Rumaysa sai dariya
Suraj yana jan Mota Zainab tana gefen sa, sai wani kallon sa take a sace, zuciyan tane yake bugawa idan ta kallesa, shiko tukin sa yake baima san tanayi ba….. Awajen su Ammar kuma shine da Khairiyya a mota, ita duk ta matso su iso gidan, kallon ta yake with so much tenderness in his eyes, ita ko sai murna take zata je gidan masoyin ta, wanda take So kamar ranta, Ammar shi kuwa hankalin sa kwata nakan driving sauran na kanta, a zuciyar shi cewa yake
I dated, I hung out, there was never anyone I was even close to being serious with, and I was fine with that.. looking at her made me see my world differently, I was 27 old boy who was given everything in life but never really loved anything.. looking at her, I see a whole world possibilities and I love them all,kiiiiiii yaja buriki ganin ya kusan buge wani tsoho, Khairiyya tace “
Subha’nallah haba Ammar, kaiwai kana tuki baka kallon gaban ka, saura kad’an ka buge mutumin can fa mtsww”, Kallon ta yayi kawai ya girgiza kansa, yace
“Ya naga kina murna, koh irin ki nuna bakison gidan dan ni”
“Mtswww I am so excited Ammar, ban san dalili ba”, dogon tsoki yaja yace sai ki tayi ai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button