KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Nasan akwai typing errors so please kuyi hakuri

  Nana fa'ad En Eesha 

????????????????????????
[11/8, 9:29 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

   *[Sept, 2016]*


        Written by Nana fa'ad En Eesha????

Page 31~32

  Fita tayi ta samei Suraj a guest room (d'akin baki), Kallon ta yake kamar wanda zai cinye ta, zama tayi suka gaisa, sai duk kuma sukayi shuru, Khairiyya tace Suraj ya bakaci komai ba, yace naci fa i'm ohk Alhamdulillah, can we go, Khairiyya tace Sure why not

Suka jero zuwa parking slot, Khairiyya tace “na d’au motana neh or zamuje da naka”
“Let’s go with mine”
Khairiyya tace “ohk toh shikenan”
Suka shiga motar, wow ni nana nace sun dace, Suraj ya juya wajen Khairiyya yace
“Ina muka nufa”
Khairiyya tace “Barwee”, Suraj yace Barwee fa kikace, tace “Yeah i know”, Suraj yace ohk toh

 Wani babban had'adden Hotel neh wanda tun a nisa zakaga wuta yana blinking an rubuta Barwee, hotel neh da wajen shakatawa, suna parking motar su, suka nema kujera suka zauna kusa da pool suka zauna, sukayi ordering drinks da snacks, sunaci bawanda yake cewa kala, sai can Khairiyya tace

“Mei sa all the time kana nan shuru, baka magana koh dai haka soldiers suke, but I am sure akwai something that you soldiers like alot”
Suraj yace mei kenan, Khairiyya tace idan naci mei zaka bani, Suraj yace “anything u want, idan baifi karfi nah ba”
“Promise me” cewar khairiyya
Suraj yace “I promise”, Khairiyya tayi murmushi tace
“Wow Good, abun da sojoji suka fiso en almost all soldiers are addicted to Gurls and Drink/Drugs I mean kayan maye”
Kallon ta yake da mamaki, wato mutaneh suna kallon ko wani soja yana da neman mata da shan abun kenan, why do people think bad about us, kafin yace wani abu tace
“Don’t feel bad bazan guje kaba” ta kashe mishi ido, tacigaba
“You know we have something in common” ta juya tana kalle kalle koh akwai wanda yake jinsu koh kallon su taga kowa yana harkan gabansa, ta matso da fuskan ta daf kusa dashi tace masa ahankali
“I also Drink, get drunk, but I don’t smoke, kawai syrup en wasu Tablets nakesha, so tell me, nasan you smoke cigarettes,Indian Hemp, koh kana shan Tequila, vodka, Champagne, etc, ta kara masa wink (kashe masa ido) wannen kake sha……
Kallon ta yake da mamaki, yarinya wanda batafi shekaru goma sha bakwai ba amma tasan duk wayannan kayan mayen, young en beautiful haka, ya d’auka rashin ji neh kad’ai da ita ashe har tana shaye shaye, toh ina mahaifiyar ta take tabar ta tana shaye shaye, this is too bad
Khairiyya taga yayi shuru ta ta6asa tace
“Heyy don’t feel bad and don’t be shy, your secrets are safe so tell me ba komai” ta masa wink
“I don’t drink en I don’t smoke, kuma bana neman mata”
Bud’e baki Khairiyya tayi tana kallon sa, tace “be serious yarr, why are you pretending, I know habits na soldiers”
Da husky voice nasa yace mata ” i’m serious, bazan miki karya ba, duk abun da kika lissafa bana koh d’aya daga ciki”
“But ai duk abun dana lissafo ansan aikin sojoji neh, suna son mata dason shaye shaye” cewar khairiyya
“Not all soldiers drink, smoke or su womanizers Khairiyya, bai kamata kuna mana kallo dukan mu haka muke ba, I agree 50/50 sunayin haka but not all”
“No bawani rabi, kace kusan duka sojoji haka suke, but nayarda dakai, but naji haushin fad’a maka da nayi ina shan abu, after all ma Syrup neh ai kawai ba wani abu big deal ba”
“Khairiyya dont say that, baki san watarana zaki iya zarce wa ba, tell me why do u take syrups”
Khairiyya taji batason maganan kwata kwata, dan it’s a secret baza taso ta gayawa a stranger ba, atake tace
“You promise me idan nayi guessing zaka mini duk abun da nace koh”
Suraj yace “of course zan miki but ai bakici ba, kinyi misunderstanding na sojoji but ki fad’a mei kikeso”
A take ta matsar da kujeran ta kusa dashi tace “Yawwa koh kai fa” gefe da gefe ta duba koh akwai mei jinsu, tace “matso da kunnen ka wanna tell u something kar ajimu”
“Khairiyya mene haka da har sai kin mini whispering, just tell me ba wanda zai jimu”, Khairiyya tace “No sai a kunne”, Haka dai ya matso da kunnen sa kusa da ita, matso wa tayi daf kusa da kunnen shi tace da hankali
“Do you have a Gun or Pistol with you”
Zare ido yayi dan ba karamin mamakin tambayan ta yayi ba, yace “WHAT, mei kikace? “
Khairiyya tace idan baka jin turanci mei kyau what I mean is that “akwai bindiga a jikinka”
“Mei zakiyi dashi” Suraj ya tambaye ta da mamaki a fuskan sa, he just can’t believe abun da take tambayar sa, toh ma mei zatayi dashi..
Khairiyya tace “Lahh nothing much fa, inaso muyi threatening wani yaro neh wlhy ya dame ni, wai shi a dole so nah yake, he can kill and die for me, inaso na sani if he really mean those words, kagane ai ” ta kashe mishi ido
“What nonsense, but badani ba, I can’t do that, wannan ai yaran taneh”
Khairiyya ta 6ata rai tace “kasan karya alkawari yana d’aya daga cikin alamomin munafukai”
“Just say it directly ni munafiki neh koh”
“Nifa ba haka nake nufi ba Suraj, kawai dai baka kyauta mini ba, you are boring, I just want you to enjoy koh sau d’aya neh yau”
Suraj yace “Toh shikenan ina Yaron yake”, Khairiyya tace “Wow kokai fa, lemme call him, d’aukan wayan ta tayi dan kiran Sabir taga ya mata 7missed calls ma,murmushi tayi tace yau naka yakare, kiran number wayan shi tayi, yana fara ringing Sabir ya d’auka yace
“Haba mss hot kullum idan an kiraki sai kinga dama kike picking”
Khairiyya tace “Haba my heart yanxu kana ina”
Sabir yace inata gate na biyu
“Toh kazo wajen pool muna jiran ka”
“Toh shikenan” cewar Sabir, ba’afi minti biyu ba sai gashi ya iso, tab Sabir shadda yasaka har da hula kamar wanda zaizo gaishe da siriki
Suka gaisa da Suraj, bayan sun gaisa Suraj yayi ordering abinci ma Sabir, Sun d’an ta6a hira kadan Khairiyya ta fara ta6a Suraj da kafa da kafan ta, Suraj tsab yaganeh abun da take nufi, bayan sunyi hira ya tambaye sa maganar karatunshi and everything, Suraj yace dan Allah muje motarka ina son magana da kai, Sabir yace toh ba komai bismillah, suna shiga Motar Sabir Suraj ya cire d’an wani karamin bindiga ya saka a goshin Sabir

Yace “You can kill and die for my sis koh”
Atake jikin Sabir ya fara 6ari, sai zufa yakeyi yace
“Wlhy inason ta but baikai da mutuwa ba”
Suraj yayi ready da bindigan kamar wanda zai har6a, atake Sabir yace
“Bana sonta, wacece Khairiyya, ni banma santa ba”
Suraj kam cikin shi yacika fal da dariya amma ya rike, Khairiyya ce tace
“Haba Sabir kamanta kace You can kill and die for me, let’s prove it to him, idan yakashe ka nima nakashe kaina” ta juya wajen Suraj tana zubar da hawaye kamar dagaske tace
“Yaya wai meyasa duk saurayin dana kawoshi wajen ka sai ka kashe shi, shin baka so nayi aure neh koh kana da dalilin yin haka, I swear idan har ka kashe Sabir nima zan kashe kaina, wannan alkawari na maka, duk samari nah kana kashe su toh wannan idan ka kashe shi tabbas zaka rasani, rasani na har abada, ka kashe shi Yaya Suraj Nima sai na kashe kaina”
Suraj yace “haka kikace koh, toh bari mugani idan na kashe shi koh zaki iya kashi kanki”, setin kan Sabir yayi da bindiga, yace “Say your last prayer”
Jikin Sabir yana 6ari yace”Wlhy bana sonta, ban ma santa ba, yau nafara kallon ta”, Suraj yace “What! baka santa ba”
“Bansan taba, asalima yau nafara kallon ta”
Suraj yace toh tunda haka neh kasira, kafin na kirga goma kabar cikin hotel nan kuma koh a hanya kaganta kayi kamar baka santa ba, kayi deleting number ta a wayar ka, tun kafun Suraj yafara kirgawa ya fisga motar sa yabar haraban Barwee Hotel….
Shiga Mota Suraj yayi Itama Khairiyya tashiga, dariya suka fara kamar wasu zararru, Suraj yace
“Khairiyya you tooooo much”
“I know yaya Suraj” ta kashe masa ido suka kara 6arke da dariya, haka har suka isa gida yayi dropping nata suna dariya, Suraj neh yafara tsaida dariyar sa yana Kallon ta tana dariya, azuciyar sa yace
“Wow ita komai mata kyau yake, she’s funny en pretty”
Sanda tayi dariya mei isarta tayi shuru, kallon juna suka fara na kusan minti biyu Khairiyya ta d’auke kanta, da wata murya wanda baisan shima yana dashi ba yace
“Khairiyya I really wanna tell you something but I think this is not the right time”
“Yaya Suraj why do u think this is not the right time, mei kake so ka fad’a mini tell me now”
Suraj yace “NoPp surprise neh, yanxu antura ni course a Iraq but In Shaa Allah idan nadawo zakiji”
“Har Iraq Captain Suraj, how many months zakayi”
“12 months, that’s one year kenan”
Khairiyya ta bud’e idon ta tace “har shekara d’aya is too much yarr, m gonna miss you alot”
Suraj kasa believing abun da kunnen shi yaji, azuciyar sa cewa yake wow itama zatayi missing d’ina, kura mata ido yayi yace
“Are you sure you will miss me”
Khairiyya ta kashe masa ido tace “ofcourse I will miss you, alot alot ma”
Ba karamin dad’i yajiba yana murmushi yace
“Thanks alot dear, please take care of yourself for me”
“Khairiyya tace sure I will and thanks for your time”
Haka suka rabu suna mei kewar junansu kamar wanda karsu rabu, ita kanta Khairiyya taji ba dad’i.. Tana shiga d’aki ta fada akan gado tace Captain Suraj m gonna miss you alot, you are like a brother yarr please come back soon…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button