KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan Khairiyya ta fita a office nashi yaji sam abun da yamata bai kyauta ba, but she deserve that yace, yacigaba da harkan sa hankalin sa kwance, bai koma gida ba sai karfe shida

Yana zuwa gida Rumaysa tayi serving nasa abinci, ci yake hankalin sa kwance yana ta kallon kyakkyawan fuskan ta, bayan ya gama ci ya fita sallan Magrib, bai dawo gida ba sanda ya idar da isha’i kusan misalin karfe takwas da rabi, bayan ya dawo ya kira Rumaysa a waya yace “ki fito ina parlour”, sanda taci kwalliya tafito, ni dai nana nace ikon Allah kwalliya ma da daddare, su soyayya manja
Bayan ta fito suka zauna suna hiran su ta masoya, basu an karaba har karfe goma da rabi tayi, wayar sa neh yafara ringing, dubawa yayi yaga Daddy, ya d’auka wayan yace
“Hello daddy”, naji yace Daddy ya zaka mana surprise haka, toh yanxu zanzo, ya katse wayan
Juyawa yayi yana kallon Rumaysa yace “kinsan daddy wai surprise yamana, yanxu jirgin su ya iso wai naje na dauke shi a airport kuma kar na fad’a wa Mummy”, Rumaysa tace “ahh lalle ya mana zuwan suprise kam, yanxu tashi to kaje”, Yace Toh my love
Ya tashi ya d’au key na motar sa, yace “My love sai nadawo “, Rumaysa tana murmushi tace Allah kawo ku lafia, ya fice a gidan yana wangale hakora dan dad’i, yana bala’in son Rumaysa, yana tunanin ta yana driving

Firgit ta tashi a bacci dalilin mugun mafarki da tayi, kusan karfe goma da rabin dare kenan, dan ma tana fashin Sallah, abubuwa neh suka sake dawo mata sabuwa fil dalilin mafarkin da tayi, cewa tayi
“Yaa Allah I love him soo much, idan zilyadeen ya mini haka bansan ina zan saka raina ba”, yunwa neh sosai ya addabeta, kiran waya tayi a kawo mata abinci a d’akin ta, bayan an kawo mata da kyar ta iyaci, maganganun Zilyadeen neh yadawo mata a kanta, batasan lokacin da ta d’auka kwal6an giya har biyu ta bud’e, fita tayi a hotel d’in gaba d’aya, tana tafiya tana shan champagne da Hernesy (masu karatu idan baza ku manta farkon page d’in ba bara na tuna muku)
Tafiya take a buge akan titi kamar zata fad’i kasa, ga bottle (kwal6an)na Hernesy a hannun ta na dama, bottle na champagne a hannun ta na hagu, idan ta kur6a Hernesy ta kur6a champagne, da dare misalin karfe sha d’ayan dare a garin maiduguri, wani mota neh yazo da gudu yana mata horn amma inaa hankalin ta baya jikinta, kwass motar ya kwashe ta tafad’i a kasa

BACK TO ASALIN LABARIN

Ya fito a motar sa a rikice, tunda yake bai ta6a buge wani d’an Adam koh dabba ba, wajen yarinyar ya nufa ya d’aga ta cak, daidai yazo gaban motar sa yayin da wutan gaban motar ta haska su zai saka ta a motar shi ya kalla fuskan atake ya zare idon sa yace KHAIREEYYAH

Nana fa’ad En Eesha

????????????????????????
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

   *[Oct, 2016]*


        Written by Nana fa'ad En Eesha

Page 47

Da hankali ya kwantar da ita a gadon bayan motan,Fisgan motar yayi yana gudu sosai akan titi harya iso Teaching Hospital Maiduguri, ya d’auke ta cak yashigar da ita, atake sukayi admitting nata a Emergency, wata Nurse ce tafito tace
“Sai dai kayi hakuri it’s a police case (yan sanda), dole sai kaje police station sunzo anyi signing sun sheda, kuma kagaya musu ya akayi hatsarin ya faru”, Zilyadeen yace “What nonsense, this is bullshit, ya za’ayi nakawo mutum ba lafia rai a hannun Allah kuna maganan police station, why are you people so heartless, wlhy ba police station da zanje kuma dole ku dubata ku mata aiki”, da tsawa yake maganar, wani likita neh yafito yace mei yake faruwa neh, suna had’a ido da Zilyadeen likitan yace “ahhh sheik Zil kana duniya”
Zilyadeen yace “Dr Kaysan please wannan ba lokacin magana baneh na kawo patient kuma wai dole sai nakai report police station, this is not fair at all”, Dr Kaysan yace karka damu Zil zan dubata ba matsala, atake yasaka Nurse d’in tabisa suka shiga cikin Emergency inda aka ajiye Khairiyya
Duk hankalin sa ya tashi, ya manta da Daddy dayace yazo ya d’auke sa a airport, kiran daddy neh yasa ya tuna yace “ohhh shit”, d’aukar wayar yayi yace
“I’m soo sorry Daddy, wlhy na buge wata yarinya a hanya yanzo haka an rike ta a TH”, bansan mei daddy yace masaba naji yace
“Ohk Toh shikenan Daddy sai kazo”, haka ya ringa zirga zirga acikin asibitin, wata nurse ce tafito a cikin d’akin da ake duba Khairiyya, da sauri Zilyadeen yasamei ta yace
“How is she”, Nurse d’in tace “you don’t have to worry ba wani ciwo sosai taji ba kuma In Shaa Allah zata warke”
Zilyadeen yace “please ki fada mini mei yasamei ta”, Nurse d’in tace “Hannun ta neh ya karye sai kuma some minor injuries kaidai ka kwantar da hankalin ka”, Zilyadeen yamata godiya
Can bayan kamar minti talatin saiga Daddy, Mummy, Rumaysa da Hajja (Kakar Zil) sun shigo asibitin suma dai duk hankalin su a tashe, bayan sun zauna da Zilyadeen suka d’an tattauna, Daddy yace toh yanxu wa za’a bari ya kwana a asibitin, Zilyadeen yace
“Daddy tunda fault d’ina neh zan kwana, ban san ku wahala”, Daddy ce
“A’a baza ayi haka ba kai namiji neh idan wani abun yatashi baza ka iya taimaka mata ba”, Hajja tace
“Toh Alhaji ni ai sai na kwana”, Daddy ya kalleta yace “kema ai ba’abun da zaki iya mata”, Hajja ta 6ata rai tace
“Lalle Abdullahi, mei kake nufi kenan, so kake kace na tsufa bazan iya kula da ita ba ehh, kaji kafa, har yanxu garau nake, inaga ma nafi ka karfi”, tana magana tana taunar goro, Rumaysa tace
“Kinga Hajja zan taya ki kwana kinji”, Hajja tace toh kishiyata uwar shishshigi toh sai mu kwana”, Daddy yace
“Toh shikenan Hajja, sai ku kwana da Rumaysa”, Zilyadeen dai baiso Daddy ya amince Hajja ta kwana ba dan karta ganeh Khairiyya, dan yasan idan ta ganeh ta toh akwai matsala……..

Tun lokacin da Ammar yaje gidan sa mai gadi yace masa ai kanwar sa tazo ta fita, shiga gidan yayi ya bud’e fridge nasa yaga ba kwal6a har biyar, a take hankalin sa ya tashi, bai zauna ba ya d’auke motar sa yaje gida, yana zuwa gida ya tambaye Ummi koh Khairiyya tadawo dukda ma bai ga motar taba, Ummi tace “ai Khairiyya yau a gida zata kwana, nace mata ma zakaje ka tayata kwasan kayakin ta”, hankalin sa duk ya d’aga,fita yayi ya fisga motar sa gudu yake sosai kamar wanda zai tashi sama har yakai gidan ta, tun a bakin gate baba mai gadi yace Khairiyya bata shigo gidan ba, hankalin sa neh gaba d’aya ya tashi, tun karfe shida na yamma yake neman ta har karfe sha biyun dare, idan ka gansa zaka rantse ba Ammar da kasani baneh d’an gayu mai ji da kyaun sa, komai ya tsaya masa cak, ya neme ta ko ina bai ganta ba, hannun sa yasa a gashin sa dogo bak’i mai tsansi yace
“Idan wani abu yasamei Khairiyya bazan ta6a yafe wa kaina ba, ni na koya mata shaye shaye, Yaa Allah ka taimaka mini kar wani abu yasamei ta, kar wani mugu ya lalata mata rayuwa, kar ta had’u da masu yankan kai”, zama yayi dirshin a kasa akan hanya yana kuka kamar wani karamin yaro, cewa yake
“Na cuce ki Khairiyya na cuce kaina, I will never forgive myself if something bad happen to you, Khairiyya bansan ina sonki ina kaunar ki ba sai yau, idan na rasaki kamar na rasa rayuwa ta neh, my life will be shattered without you”, kuka yake sosai, Ammar mei kyankyami mai tsafta shineh ya zauna dirshin a kasa, a kasan ma kusa da bola koh tsoron Jinnu bayayi, yaga kukan bazai taimake saba atake ya tashi ya wuce NTA, ya bada hoton ta da yake dashi a wallet nasa yace duk wanda yasan inda take zai basa tukuici,masu aiki a NTA sukace yayi hakuri yanxu dare yayi gobe da asuba zasu saka as breaking news yayi hakuri, yace shi sam fa tun yanxu afara nunata, a take suka sakata a News..
ya saka boys maza yabasu number motar ta da kalan sa duk wanda yaga motar shima yana da tukuici babba, Kusan karfe d’aya yana yawo a garin maiduguri da sojoji yana duba Khairiyya amma shuru babu labari, can wayar sa tayi ringing, ya d’auka yasa a loudspeaker dan sojojin suji, akace
“Hello Oga an samu motar fa, kazo International Hotel”, baisan lokacin da ya fisga motar shi yana gudu sojoji suna bin bayan sa har zuwa International Hotel, motar ta yagani, a take yashiga reception yace aduba masa list yana neman Khairiyya Ibrahim, atake suka duba masa sukace “sir room 44”, da gudu gudu har ya iso d’akin ya bankaje kofan, yaga kwal6a uku baiga biyu ba, toilet ya bud’e yaga wayam bata ciki, cikin d’akin ya koma yaga jakan ta akan gado, d’aukan jakan ta yayi ya runguma yafara Kuka kamar karamin yaro yana cewa “Where are you Kim, dan Allah kiyafe mini”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button