KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Ammar ya matso kusa da Khairiyya yace “kinji ana fad’a an d’auka ni mijin ki neh kuma muna kama”, dogon tsoki Khairiyya taja tace
“Allah sawwaka na zama matar ka, mei zanyi da kai, miji nagari nake addu’a Allah ya bani”, maganar ta mata masa rai, ya had’a fuska yace
“Allah baki”, taga ransa ya 6aci da d’ayan hannun ta taja gashin sa tace
“Don’t feel bad Ammar, ba wata mace da zata k’ika dan kana da kyau, ga uwa uba hankali, you’re from respectful family and you’ve a good personality, kana da ilimi sosai na addini but kana aiki da wasu kabar wasu, just kayi kokari kana aiki da duk ilimin ka, kasan ance nobody is perfect but idan kafara aiki da iliminka nasan and I am sure you’ll be perfect kuma ba wata mace a nan kasar Nigeria bance kasar waje ba da zata k’i ka”, sosai yaji maganan a ransa, cewa yake a zuciyar sa
“Ina sonki Khairiyya, ina matukar sonki, bazan iya rayuwa babu keba, m addicted to you”, zuba mata ido yayi yana kallon ta, taga kallon ba na karewa baneh ta hura masa iska a ido tace
“Stop staring at me Ammar, karka cinye ni please”, yace “Allah sawwaka, naga mata kyawawa wanda suka fiki kyau yarinya”, Khairiyya tace
“Ahakan kuma ka zuba ido kana kallo nah”, fankan d’akin duk ya baza mata dogon gashin ta yana rufe mata, hannun ta kuma d’aya an d’aure, tace
“Ammar please ka kama nini gashina yana damuna”, Ammar yace “Toh naji hajia amma ni hakan ma kinfi kyau”
“Please banson wulakanci yana shiga mini ido”

☆☆☆☆☆☆☆
Captain Suraj da tambaya har yasan inda Khairiyya take, da yake babban soja neh baisha wahala ba aka basa duk details na Khairiyya, har ya iso d’akin, zai shiga kenan Rumaysa ta tsaida shi tace
“Ammm Soja wa kake nema dan nan d’akin Sister na neh i’m sure you re mistaken”, da shike yanxu uniform neh a jikin sa, bud’an bakin da zaiyi yace
“Ba nan baneh d’akin Khairiyya, idan nan neh toh ni mijin da zata aura neh”, Rumaysa mamaki neh yacika ta, da kyar ta bud’e baki dan yamata kwarjini tace “ehh nan neh”, bud’e kofan d’akin yayi yashiga, daidai lokacin Ammar yana d’aure mata gashin ta da ribbon , tana jin sallamar Captain Suraj ta d’aga kai ta kalle sa, bata san lokacin da tayi ihu ba

So masu karatu wa kuka ga ya dace da ita, who do you think is best for her
Zilyadeen, Ammar or Suraj

Nana fa’ad En Eesha

????????????????????????

07034419520
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

[Oct, 2016]

    Written by Nana fa'ad En Eesha 

Page 51~52

   Khairiyya tace "what,am i dreaming or what, Ammar idan mafarki nake please ka tashe ni, Captain Suraj kaine a gari lalle kam yau za'ayi ruwan sama da kankara"tana wage hakora, Suraj ya d'au kujera yazauna agaban gadon,kallon ta yake, ta kara masa kyau sosai gashi duk bakin ciki ya cikasa, waye haka yake kama mata gashi da ribbon yace

“Sai yau KIM, jiya na dawo daga kasar da aka turani course, sai yau nashigo Maiduguri, ina shigo wa naje gidana na kunna TV nagan hoton ki an saka missing, shine nafito neman ki”, Khairiyya ta zare ido ta bud’e baki with soo much suprise on her face tace
“Yaya Suraj hoto nah a TV kuma missing”, tana fad’an haka ta juya wajen Ammar tana kallon sa, tsab tasan shi ya aikata, Khairiyya tace
“Yaya Ammar haba dai, basai kajira gari ta waye ba, kawai ka kama kasaka hoto nah a Tele6ijin gaskia baka kyauta mini ba”, Shiko Ammar koh kulata baiyi ba yana gama d’aure mata gashin ta ya nema gyale ya rufe mata gashin ta dashi, duk bakin ciki da kishi ya rufe sa anga gashin KIM nasa, Khairiyya taga bashida niyan kulata tace wa Suraj
“You are so nice, thanks for the care, naji dad’i sosai, gaskia gwara da kadawo cox nayi missing naka sosai”, zo kuga dad’i a wajen Suraj, yana wage hakora yace
“Nazo nima sabida ke, I miss you more, da naga hoton ki missing har hankali na ya d’aga, I don’t wanna loose you”, Khairiyya tayi murmushin jin dad’i, ita tana kaunar duk mai sonta, tace “Nagode Captain Suraj Allah bar kauna”, sanda cikin Ammar yayi kululuu da jin maganar ta, ranshi yayi mummunar 6aciwa, Sallama akayi, suka amsa tukun aka bud’e d’akin
Zilyadeen, mummy, Hajja da Rumaysa neh suka shigo d’akin, Zilyadeen sanda yaji zuciyan sa ta buga (nidai nana nace OMG kamar ina kallon Clash of the titans )
Khairiyya kam zuciyan tane yake bugawa, koh dai shine yayan Rumaysa da ya buge ta, Suka gaisa dasu mummy, mummy tace
“Khairiyya ga mutuminki da ya buge ki”, zuciyan ta ya tsanan ta da bugawa, Muryan shi naji yace
“Khairiyya ya jiki”, da voice nasa mai narkar da zuciyan ta, Khairiyya tace
“Dasauki”, da tsiririn muryan wanda Ammar baisan ta dashi ba, atake ya juya ya kalle ta, tana da zak’in murya amma yadda ta amsa shi daban neh, sai wani kunya kunya takeji, ana hira bata magana sai murmushi, Suraj kam yana jin dad’i Khairiyya ta canza hali baisan da biyu baneh
Ammar ya kira Ummi yace suna asibiti, Ummi tace toh yanxu zatazo, ba’afi minti goma sha biyar ba sai ga Ummi da Zainab
Ummi da mummy kallon juna suka fara, Ummi ta nuna ta da yatsa tace sis Ramaadah kece wannan, Mummy ta rungume ta tace nice Aysher, mummy tace lalle yanxu shekaru nawa da rabuwa, tun muna secondary school, ikon Allah kenan (mummy da Ummi sunyi makaranta d’aya da suke yara GGSS BAMA da ke cikin borno)
Ummi tace ai Khairiyya yata ce, mummy tace Allah sarki ikon Allah kenan,Mummy tace sai hakuri fa, Ummi tace abu Allah ya qaddara zai faru, ai ba komai, duk suka gaigaisa, haka dai d’akin yacika dam mummy da Ummi suna hiran makarantar su,ana shan dariya, Rumaysa tana satan kallon Zilyadeen, Ammar da Suraj suna satan kallon Khairiyya, Zilyadeen ya kalla Rumaysa ya kalla Khairiyya, idan Khairiyya ta had’a ido da Zilyadeen sai ta sunkuyar da kai tana murmushi, idan ta had’a ido da Suraj sai ta kashe masa ido d’aya, idan ta had’a ido da Ammar sai ta murkud’a masa baki tayi nuni da hannun ta irin ya da zafin kallo haka…..
Haka nan dai Nurses suka kore su sutafi saidai suzo karfe hud’u visiting hours, Ammar yace zai zauna, Ummi ta harare sa tace
“Kajika fa, nidai zan zauna”, Hajja tace sam ita bata yarda ba, Ita zata zauna da Khairiyya responsibility nasu neh, haka Hajja ta dage, Rumaysa ma tace toh zasu zauna tare da Hajja, Ummi tace baza ayi haka ba, Zainab zata zauna da Hajja, akayi shawara akan Zainab da Hajja zasu na kula da Khairiyya
Haka duk suka fita a d’akin akabar Hajja, Khairiyya da Zainab… daga nan Khairiyya tayi bacci su Hajja da Zainab kuma suna ta hira Zainab tana ta shan dariya….
Bayan su Zilyadeen sun koma gida, Mummy tayi gaba ta barsu, rike hijabin Rumaysa yayi yace
“Haba my future wife, jiya na wahala baki kwana a gidan ba, yau kuma wai zaki kara zama, koh muryan ki bakiso naji neh, bakisan nayi missing naki ba”, Rumaysa ta wani rufe fuska da hannun ta tace
“Inaso mana Nurul hayat, nima nayi missing naka”, tana gama fad’an haka tayi gudu tabar sa awajen yana wage hakora, yace “Rumaysa ina matukar kaunar ki, I love you sooo love, tun ranar da kika zo duniya nafara sonki kuma bazan ta6a iya daina sonki ba, I love you to the square root of infinity”, yana gama fad’an haka ya tuna da Khairiyya, yaji kansa ya d’au zafi gaba d’aya, ya furta
“Khairiyyahhhhh, meisa nake tunanin ki neh, I think of you every moment, whyyyy”…. masu karatu yaci ace zuwa yanxu kunsan wacece Khairiyya, wanene Zilyadeen da kuma Suraj, toh lemme start with Zil, zan fara da Zilyadeen

 Wanene Zilyadeen

Alhaji Dahir Abdulqadir shuwa asalin d’an maiduguri neh Shuwa, da matar sa Hajia Jamila (hajja) wanda aka musu auren dangi kuma Allah yasa suka zauna lafia, bayan shekara d’aya da auren su Allah ya basu haihuwa suka haifa yaro kyakkyawa dashi suka saka masa suna Abdullahi (Daddy), daga nan sai basu kara haihuwa ba har sun cire rai sai bayan shekaru goma sha biyu kwatsam Hajia Jamila ta samu wani cikin, murna a wajen su kamar mei, bayan wata tara Hajja ta haifa yar ta aka rad’a mata suna Fatime dagan nan kuma basu kara haihuwa ba a lokacin Abdullahi ya gama secondary, bayan yayi candy yace shi sam a BUK zai cigaba da karatunsa, da kyar dai Suka yarda suka barsa, ya samu admission a Political science, a lokacin da yana part 4 aji na karshe a jami’a ya had’u da Ramaadah itama yar Maiduguri,a lokacin hajiya Ramaadah tana zaune a gidan kakar ta a kano, da shike iyayen ta duk sun rasu a hatsarin mota daga hanyan su kano zuwa maiduguri, sai take zama da kakar ta kano bayan ta gama secondary a Bama wanda yake cikin Maiduguri tukun iyayen ta suka rasu.. Bayan Abdullahi ya gama jami’a yaje bautar kasa ya dawo, aka d’aura auren sa da Ramaadah, wanda ya gina musu karamin gidan su a Maiduguri, duk hutu tana gidan mijin ta, da an koma makaranta sai ta koma gidan kakar ta da ke kano, haka har ta kammala karatun ta
Sun haifa d’an su, suka saka mishi takwaran baban Mummy wato Zilyadeen Usman, daga nan duk cikin da ta samu baya zama haka suka hakura, Fatime kanwar Alhaji Abbdullahi (Daddy) tayi aure tana Jss3, ta dage sam ita aure takeso baza ta cigaba da karatun ta ba, da kyar Abdullahi da Alhaji Dahiru suka amince ta aura Hamman mijin ta, shi kuma kanuri da Shuwa neh, bayan auren su da wata tara ta haifa d’an ta aka rad’a masa suna Sabir, takwaran wan mijin ta Hamman (baban Teema), a lokacin suka fara samun sa6ani da mijin ta Hamman da yan uwansa, duk yan uwan mijin ta basu sonta, suka aura masa yar uwarsa Rukayya, Fatime ta kara samun ciki na biyu, kullum cikin wahala take ga yaro ga sabon ciki, kwatsam watarana tana zaune a d’akin ta ya mika mata takardar saki yace taje gida ya sallame ta saki biyu, haka ta tattara kayan ta taje gida da bakin ciki, bayan wata tara ta haife yarta a gidan iyayen ta suka rad’a mata suna Rumaysa, tun daga lokacin haihuwar ta Alhaji Dahiru ya rasu mahaifin su Daddy kenan, Daddy ya dage akan dole Hajja da Fatime su dawo gidan sa da zama, tun lokacin da fatime da zo da yaran ta biyu Sabir da Rumaysa, Zilyadeen Jinin sa ya had’u sosai da Rumaysa tun tana jinjira, shike mata komai da komai, su wanke kashi, fitsari da wanka alokacin shima yana da shekaru goma sha d’aya…. wannan kenan
Back to asalin labari

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button