KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

   A d'akin Zilyadeen wayar sa neh a hannun sa, sai murmushi yakeyi, yace koh tana masifa her voice soo swt




       Please munyi resuming school, got alot to do, ga defence na SIWES Report ga Project wanda koh choosing topic banyi ba, before na kara posting sai na samu saiti.... ☹????




               Nana fa'ad En Eesha 

  07034419520 for corrections/comment

????????????????????????????
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

Page 54

  Washegari Khairiyya tana idar da sallan asuba ta koma bacci, ita bata tashi a bacci ba sai karfe sha d'aya, ta tashi gidan shuru ba kowa, Mummy ta samu a parlour tana kallon Arewa24, ta durkusa har kasa ta gaishe ta, Mummy da fara'a ta amsa mata tace 

“Khair yajiki”, ta amsa
“Da sauki Mummy, yanxu bana jin ciwo, damuwata kawai a kunce mini d’auren nan yana takura ni”, Mummy tayi murmushi tace
“Kar ki damu daughter nah, in next 10days zasu kunce, abincin ki yana d’aki hope kin gani”
“Eh nagani mummy sai nayi wanka zanci”
“Madallah, kiyi wanka a hankali fa, kina kula da hannun ki kinji”, Khairiyya tayi murmushi tace
“In Shaa Allah Mummy”,Khairiyya tace Mummy inasu Rumaysa
Sun tafi makaranta cewar mummy, Khairiyya tace ohk yayi kyau… ta wuce tsum tsum tashiga d’akin, duk farin ciki ya cika ta, da duk alama Mummy tana kaunar ta, koh dan ita tana da tabbacin zata samu ta aura Zilyadeen, wayyo dad’i, tunda mummy tana so nah ai komai yaxo da sauki, da farin ciki fal ranta ta shiga wanka
Bayan ta fito taji wayar ta na ringing, Captain Suraj tagani baro baro akan screen, da sauri ta d’auke wayan tace
“Hello yaya Suraj the great Soldier”, yayi murmushi mei sauti yace
“KIM yar rigima, ina guest room kizo please”, tace
“Ohk just give me 10mins kaji”
“Ba matsala sai kin fito”, yayi hanging off call d’in, dogon riga yar kanti armless ta saka da kyar, ta saka dogon hijabin Rumaysa da tagani saman kan gado, ta fesa designer turaren ta, ba koh shafa cream balle powder haka ta fito ta, kitchen taje ta samu mei aikin gidan jamila tace ta kawo mata abinci da drinks a guest room sai ta wuce guest room, da sallama tashiga ya amsa yana wage hakora, ta zauna kan kujera tace
“Cap Suraj, the Soldier, my sweet Yaya”, yayi dariya yace
“Duk ni kad’ai KIM, bai mini yawa ba”, tace a’a sai dai kad’an, yayi dariya, Jamila ta shigo da abinci da snacks da drinks ta dira a gaban Suraj, Suraj ya cire d’ari biyar sabbi fil guda uku ya mika mata tana ta zuba godiya, bayan ta fita a d’akin Khairiyya tace
“Yaya Suraj ga abinci kaci mana”
“Wlhy i’m ohk Khairiyya ciki nah dam yanxu nima naci abinci, sai dai nasha ruwa”, tayi tayi dashi yaci abinci yace shi sam a koshe yake, Khairiyya tace
“Soja tunda kai kaki ci ni zanci daman banyi break fast ba”, haka ta zuba abinci a plate chips da kwai taci ta koshi dam agaban shi ba kunya, tana shi tana masa hira, shi har mamakin ta yake, bayan ta gama ci tace
“Wai na koshi wollah, da ina tare da Ammar wollah bazai barni naci abincin nan da kyau ba”, shidai Suraj ya lura bata iya hiran minti goma bata ambato sunan Ammar ba, yace
“Kina ji da Ammar fa”, ta wani had’a rai ta tura baki tace
“Mtsww Allah sawwaka naji da Ammar, shi yake ji dani”, Suraj yayi dariya yace
“KIM kenan, yanxu mei abun 6ata rai dan na ce kina ji da Ammar eh”, tace
“Toh nidai gaskia baniso kace inaji dashi, ai da agaban sa ka fad’i haka ai da ka gama da ni”, Suraj yace toh Mss KIM so sorry kiyi hakuri kinji please, tayi murmushi tace ya wuce My soldier, dad’i yaji kaman mei da tace My soja, gyara zaman sa yayi yace
” Khairiyya akwai wani important magana da nake so muyi dake”, Khairiyya itama ta gyara zama tace
“Ina jinka, all ears Mr soja”, yace
“Khairiyya the very first time I saw you I fall In love with you”, ji tayi zuciyan ta yayi dum, jikin ta ya d’au 6ari ya cigaba da cewa
“You’re the woman I wish to spend the rest of my life , ina sonki Khairiyya, please dan Allah Khairiyya ki SO ni”, duk sanyin AC na d’akin tana gumi, bud’e baki tayi, mamaki neh fal a fuskan ta, Suraj neh ya sake cewa
“Please Khairiyya talk to me”, a take ta tashi akan kujera ta tsaya muryan ta yana rawa tace
“Yaya Suraj zanyi tunani ka bani time please”, yace
“Ba damuwa Khairiyya, zan iya jira, I can wait ko da in next 1000 years neh”, tayi murmushin dole tace
“Nagode”, a take ta fita a d’akin, Suraj kam zuciyan sa neh yake bugawa, yace yanxu idan Khairiyya tace bata so nah ina zansa kaina, nayi nesa da Sonki Khairiyya, please ki taimaka wa rayuwa ta, ya kusan minti goma tukun ya tashi ya wuce
Khairiyya tana fita a guest room d’akin su tawuce da gudu ta kwanta a kan gado, hawaye take sosai, tace a yau da ace bana son Zilyadeen da ba abun da zaisa na ki ka Suraj, bayan Zilyadeen kaine zuciya ta zata iya SO, I am sooo sorry Suraj you’re late, zuciya ta tariga ta kamu da Son Zilyadeen, saidai na maka addu’a Allah za6a maka mafi Alkhairi…. haka bacci yayi awon gaba da ita

Ammar tun da ya tashi a bacci shiri yake, ya rasa kayan da zaisa, daga baya ya d'au Farar shadda da hula bak'i ya saka kayan da sai sallah sallah yake sakawa, danshi koh ranar jumma'a toh kananan kaya yake sakawa, ba karamin kyau yayi ba, ya fesa jikin sa da turare designers kusan kala bakwai ya zara key na motarshi, daidai ya fito yaga Ummi tana zaune, Ummi ta bud'e baki tace 

“Ammar yau ba ranar sallah baneh kuma ba ranar jumma’a ba”, yana sosa keya yace nasani ai Ummi, tace lallai yau za’ayi ruwan sama da kankara, ina zuwa haka, yace emmm Ummi wajen KIM, Ummi tace lallai kam, toh yanxu ni ka kaini gidan Hajja bila (kawarta) a bayan CBN quarters idan ka kaini sai ka wuce wajen Khair d’in, ya wani kumbura fuska baiso haka ba shi da yake zumud’in zuwa wajen KIM nasa, yace
“Ummi toh tashi na kaiki”, Ummi tace toh bara naje na shirya, itace bata fito a d’akin ba sai bayan minti talatin, duk ya gaji yana ta kumbure kumbure, haka ya kaita ya wuce Gidan su Zilyadeen, yana shiga cikin gidan ya shiga parlour suka gaisa da mummy, bayan nan tace
“Ka shiga guest room zan mata magana”, Ammar yace bakomai zan kira ta ma a waya, tace toh shikenan, bayan ya shiga guest room ya kira ta a waya…….. m

Ringing wayan ta shi ya tashe ta a bacci, ba tare da ta duba taga wanda ke kiraba ta d’auka tace “hello”,da muryan bacci, can muryan Ammar yace
“Ki fito ina guest room”, tana yatsine fuska tace
“Nifa ina bacci mei dad’i ka wani tashe ni, gaskia sai nayi wanka nayi sallah idan zaka iya jira toh idan kuma baza ka iya jira ba ka kama hanya kayi gaba”,
“Ina jira”, kawai ya furta ya katse wayan, da kyar ta iya tashi tayi wanka, bayan ta fito ta saka doguwar rigan d’azu ta zura hijabi tayi sallah, bayan ta idar ta wuce guest room, ta zauna a kan kujera tana kumbure kumbure, ya sauko daga kujeran ya zauna a gaban ta a kasa a kan carpet, yace
“Na takura ki koh KIM”, ta zumbure baki tace
“Ina bacci nah ka tashe ni”, yace
“Sorry KIM, ya jiki”, tayi banza dashi yace munyi waya da Daddy, yace anyi releasing Abba a prison”,
“What!dan Allah, wow yanxu yaushe zasu zo”, Ammar yace in next 3weeks,tace Allah nagode maka, yanxu please ka kirasu muyi waya, Ammar ya kira daddy yace ya bawa Abba su gaisa da Khairiyya, Khairiyya ta kar6a wayan sai murna take, suka d’anyi hira da Abban ta har da guntun hawayen ta…. haka Khairiyya tana ta murna, tace
“Ammar you deserve something nice for the good news, mei kake so just mentione anything”
Ammar sai ya rufe idon sa, Khairiyya tace
“Ammar, Ammar are you ohk, lafia kuwa” tana bubbuga shi, dogon tsoki yaja yace
“When a guy closes his eyes, it means he wants you to kiss him”
Dukan shi na wasa ta fara tace
“Mahaukaci kawai mei ugly face, you’re a jerk”, shi kuma yana dariya yace Hot jerk ba, tace Ammar please ka tafi gida yanxu so nake nayi kwalliya nasha make up, Ammar ya 6ata rai yace “for who”
Tace for Zilyadeen tana mei kashe masa ido

“Shineh lecturer da kika ce mini kina sonsa koh”, atake Khairiyya tace
“Ehhh fa shineh Ammar, ina sonshi sosai,more than anyone idan kacire Abba nah, ya had’u koh Mr Ego”, ji yayi kamar an zuba masa gawrashi a zuciyar sa, da kyar ya iya bud’e baki yace
“Khairiyya kina sonsa more than me, kin manta how you used to love me before, kin manta irin son da kike mini tun kina yar karama, kin manta the second person in this world that cares for you, mutumi na biyu a duniya da ya nuna miki tsantsan So da Kauna”, Khairiyya tayi wani murmushin ciwo tace
“Ammar I can never forget that, You are the second person in this world that show’s me care and you are the person dakayi ruining life d’ina, ka nuna mini hanyan da bata dace da rayuwa ta ba and you see because of banzan halayyar da ka koya mini ban tsaman Zilyadeen zaiso ni ba, i’m not saying that baka so nah kana so nah and at the same time you hate me, baka so nah baka kauna ta, ai duk wani mai son ka bazai ta6a saka ka a hanya da badai dai, a gur6atacciyar hanya……. I can’t say you love me nor to say you hate me, bansan wanne daga ciki ba”, ji yayi gaba d’aya duniyan ta masa zafi, kasa furta komai yayi, can bayan kamar minti hud’u yace
“You are my 1st love KIM, I love you, now that I love you, I can’t love again, Ever again, banga laifin ki da kikace bana sonki ba, I know i made a very big mistake in my life, I know ban kyauta wa rayuwar ki ba just because of my selfish interest, m such a pathetic loser”, zubar da hawaye yake kamar mace, ita duk maganar ta kasa fahimta, zuciyar tane yake yawo da his last magana “all because of my selfish interest, I’m such a pathetic loser”
Yace but I want you to know that I love you soo much, ban ta6a Son wata d’iya mace a duniya ba kamar yadda nake sonki, You are my life Khairiyya.. Yana gama fad’an haka ya tashi ya fita, fashewa tayi da kuka tace
“I am sooo sorry Ammar, you are my brother, zuciya ta Zilyadeen take so, I only love him”, sosai tayi kuka, bayan ta gama kukan ta tashiga cikin main gida, Mummy ce a parlour tace
“Khair ke da abokin fad’an ki koh”, Khairiyya tayi murmushi tace eh mummy ta wuce d’aki, tana shiga d’aki ta kwanta kan gado, ta rasa tunanin wa zatayi, Zil neh, Suraj neh, koh Ammar.. bata ankara ba taji ana kiran sallan Asr, tashiwa tayi tayi sallah ta fad’a toilet tayi wanka, bayan ta fito ta shafa mai ta saka doguwar riga atamfa cotedvoir pink da touches blue, ta zauna a gaban mirror tana tsara kwalliya da hannu d’aya, ba karamin kyau tayi ba, zaman jiran Zilyadeen da Rumaysa tayi, sune basu dawo gida ba sai karfe biyar, Khairiyya har ta gaji da jira, tana jin horn na motar Zilyadeen a take ta fita a d’akin, parlour taje ta zauna, da sallama suka shigo cikin parlourn, Khairiyya ta amsa, kallo Rumaysa ta zuba mata tace
“Khairiyya lalle kinji sauki, irin wannan kwalliyan haka”, Khairiyya tana murmushi ta gaishe da Zilyadeen wanda ya zuba mata ido, suna had’a ido ta sunkuyar da kanka alaman kunya, ba karamin kishi Rumaysa taji ba ganin Zilyadeen yana kallon KIM, Rumaysa taja ta d’aki tace zo kiji wata labari Khairiyya, Khairiyya ta bita cikin d’aki
Bayan sallan Magrib Rumaysa taje ta samei Zilyadeen ranta a 6ace tace “Yaya Zil wani irin kallo d’axu naga ka keyiwa Khairiyya, wlhy har naji na daina kaunar ta”
“Haba future wife, mei sa zaki fad’a haka, kinsan dai ina sonki, yau zan fad’a miki gaskia”, haka ya labarta mata tun farkon had’uwar shi da Khairiyya a Mall, da kuma zuwa mishi aji da tayi a maye, amma ya 6oye mata tana sonshi, yace
“Rumaysa so nake na ja ta jiki, Rumaysa ba karamin lada zamu samu ba idan har muka had’a kai da ni da ke muka shiryar da ita, muka sata a hanya meikyau, ki yarda dani Rumaysa ina sonki, bazan ci amanar ki ba”, Rumaysa ta tausaya wa Khairiyya ainun, bata ta6a kawo a ranta akan Khairiyya tana shaye shaye ba, har ma abun nata yayi nisa tana shan giya, tace
“Ka yafe mini Nurul Hayat, In Shaa Allah na baka goyon baya, nima zanyi iyakan kokarina na ganin mun sata a hanya wanda ta dace”, Zilyadeen yayi murmushi yace Ngd Matatah Allah bar mini ke, tace Ameen Nural Hayat…. Bayan sallan isha’i duk suka taru a dinning suna cin dinner, Zilyadeen da Rumaysa sai janta suke da hira, tun bata sakewa dan Zil har tazo ta sake suna ta hiran su….. Bayan sun gama ci suka zauna a parlour suna kallon Indian Film Love games, su basu gama kallo ba sai sha d’aya, daga nan suka wuce d’akin su dan bacci……….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button