KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Misalin karfe biyun dare Ammar neh yake ta juye juye a d’aki, duk ya kasa bacci, maganar da Khairiyya ta gaya masa ba karamin illa ya masa ba, Khairiyya ce zata ce masa ya tsane ta, ya fashe da kuka, yace Khairiyya ban ta6a tsanan ki ba, a kullum ina miki kallon matar da zan aura, na sani na 6ata miki rayuwar ki just because abunda na kulla a raina, but dan Allah kar kice bana sonki, ban ta6a Son wata d’iya mace sama da ke ba, i love you more than my own life itself, you’re my world KIM, you’re my everything…… Ya d’auka giya zai sha sai ya tuna da Khairiyya, baisan lokacin da ya d’auka kwal6en giyan gaba d’aya ya zubar dasu a toilet, alwala yayi yafara jera nafiloli yana mai kai kukan sa ma Allah, shineh baiyi bacci ba sai bayan Asuba……..
A kullum Suraj sai yazo wajen Khairiyya amma bai kara mata maganar soyayyar sa ba,Zilyadeen kullum sai sunyi hira da Khairiyya yana jan ta ajiki sosai, yana nuna mata illar shaye shaye, Allah yayi hani dashi kullum dai yana cikin mata wasa da dariya da wa'azi.................... Ammar kuma tun daga lokacin bai sake zuwa gidan ba, ya ramei yayi duhu, a kullum Ummi tana tambayar sa mei yake damun sa, sai yace mata ba komai, ba karamin damuwa Khairiyya tashiga ba dan rashin kallon Ammar, a kullum sai ta kirasa zai kai sau goma baya d'aukan wayar ta, ta tura masa text baya mata reply, Zainab koh wani bayan kwana biyu tana zuwa duba Khairiyya, idan tazo su zauna da Khairiyya da Suraj suyi hira .......
Ammar yana tuki ya tashi a wajen abokin sa zashi gida yaga Teema, tsai da motar yayi yace
“Teema ina zuwa da yamman nan”, Teema tace
“Wajen KIM Wlhy, kwana biyu ban samu na duba ta bah, yace toh shiga mota na ajiya ki” yana driving Teema sai masa hira take tana kakkashe murya amma koh kulata baiyi ba, tace
“Yaya Ammar baka da lafia neh na ganka ka canza”, shuru yayi bai kulata ba, ya shiga har cikin gidan su Zilyadeen yayi dropping nata, a lokacin Rumaysa tana parking space zata cire wayar ta a mota da ta manta, Ammar ya fito suka gaisa da Rumaysa, Rumaysa tace
“Ammar kwana biyu, tun lokacin da aka sallame Khair a asibiti”, yace
“Ina zuwa fa ban samun ki neh”, Teema ta wuce ta shiga cikin gidan, direct d’akin Rumaysa ta wuce,Khairiyya ce tana zaune tana game da wayar ta, ji take kamar muryan Ammar dai dai Teema ta shigo d’akin, Khairiyya tace
“Teema kamar muryar Ammar nake ji”
“Ehh shineh ya kawo ni ma”, bata san lokacin da ta wurgar da wayar taba tafita a d’ari, ji tayi ta buge mutum, ta juya da sauri taga ashe Zilyadeen ta buge tace
“Yi hakuri Yaya”, yace bakomai ina zuwa haka da gudu, tace naji kamar muryan Ammar neh a waje, Zilyadeen yace ohhh toh, da sauri ta fita wajen koh zata ganshi, Rumaysa kawai ta gani tana waya, tace
“Rumaysa ina Ammar d’in”
“Ya wuce yace gobe zaizo yanxu ana neman sa”, ji tayi hawaye yana sauka a fuskar ta, ta goge hawayen ta shiga cikin gida
Yau neh ranar da Khairiyya zata bar gidan su Zilyadeen, ita ta rasa ganeh kan Zil, sonta yakeyi koh kuwa, a yau tayi alkawarin zata fad’a mishi Sirrin dake Ranta, ji take idan bata furta masa ba zata iya mutuwa, zatayi loosing nashi, tace NOOOO i don’t wanna loose you Zil, I love you sooo much…….
Yana zaune a mota yana jiran Khairiyya da Rumaysa, zuciyan sa sai tafarfasa takeyi, baiso ta tafi, ya saba da ita sosai, kuma ya tabbatar a ransa lalle shima ya kamu da sonta, a daidai lokacin Khairiyya ta fito sanye da habbaya bak’i mai uban kyau, tazo kusa da Zil tace
“Yaya please I can’t help it dole na fad’a maka, nasan is not right, bai dace ba abun da zakaji ya fito a baki nah but ba yanda na iya, idan ban fad’a maka ba zuciya ta zata iya bugawa, kar kace bani da kunya ina zaman ya mace but believe I can’t help it”yace
“Khairiyya just tell me,go straight to the point, menene “, daidai nan Rumaysa ta fito
Nana fa'ad En Eesha
????????????????????
www.narhnah.mywapblog.com
[11/8, 9:31 PM] +234 814 173 3262: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????
{Oct, 2016}
Written by Nana fa'ad En Eesha
Page 56
Mei yayi zafi Rumaysa, tunda bakison Khairiyya ai shikenan, share hawayen ki bazan aure ta ba har sai da yardan ki, har sai ranar da kika furta da bakin ki ehh kin amince, sai ranar da zaki zo gabana kice "Nural Hayat na amince Khairiyya ta zama abokiyar zama nah"....
Rumaysa tace “har duniya ta nad’e bazan ta6a amincewa ba, keep it at the back of your mind yaya Zil, bazan ta6a yarda ka aura Khairiyya ba, kar kace idan ka aure ni shikenan sai yadda kayi dani, ka sani koh da igiyan auren ka yana nan cas uku a kaina a ranar da ka auro Khairiyya toh zan bar maka gidan ka, ka sani yaya Zil, ka saka a ranka, lemme say it one more time keep it at the back of your mind bazan ta6a amince wa ba….
Zilyadenn Yace “naji future wife, zanyi yadda kike so kinji, bazan aura Khairiyya ba tunda baki son ta”, tace da ya fiye maka alkhairi, yace yanxu Toh tashi ki samu su Abba kice kin janye maganar yanxu zaki aure ni kinji, tana murmushi tace “toh”
Bayan kwana uku Khairiyya hannun ta ya warke zata fara shiga cikin makaranta dan anyi nesa sosai a lectures, duk tayi sanyi ba kamar da ba,Riga da skirt less ta saka da Hijab dogo har kasa brown colour da dogon takalmin ta da jaka shima brown, yau daga powder sai powder koh kajal bata saka a idon ta ba, daidai zata fita ta ja motarta sai ga Ammar shima zai fita, yace ahh Khairiyya bara na kaiki Makarantan mana, Khairiyya tace
“Ammar you don’t have to worry, I can drive”
“Are you sure Khairiyya, kibari na kaiki, umarni nake baki so just shut up your mouth”, ta shiga motar sa yaja suka bar haraban gidan, suna cikin tafiya kowa yayi shuru Ammar yace
“Khairiyya zanyi tafiya, zanje na samu su Abba a U.S sai na wuce wajen aiki nah ana nema nah, zan kai like wata shida In Shaa Allah kan na dawo, incase idan anyi auren ki bana nan zan tura miki gift don’t worry kinji”, sai ga hawaye shar a idon Khairiyya tace
“Ammar har wata shida, Toh ai ni kuma koh zanyi aure saidai mijin ya jiraka har ka dawo, dan bazan yi aure baka nan ba”, Ammar yace
“Shikenan My KIM, zanyi attending auren ki In Shaa Allah, share hawayen ki”, tana murmushi tace
“Mr Ego sunan nan KIM fa kai ka rad’a mini kuma gashi ya bini, dan nima inason sunan”, yayi dariya yace
“Gashi kuwa sunan ya biki, Instagram celeb ba, KIM can you remember lokacin da nake Mexico muna competition wayake da highest followers a Instagram, but nafiki followers, matan Nigeria da son karya, sunga fine boy gashi kuma suna ganina cikin snow kullum da tsadaddun jackets kawai suta following d’ina”, Khairiyya ta fashe da dariya tace
“Mr Ego wlhy nafika followers, nifa macece, yanxu ma haka inada 56K followers”
“Ni kuma inada 58K followers”cewar Ammar, Khairiyya tace ita sam bata yarda ba karya yake mata, sanda yayi parking mota a gefe suka d’auka wayan sa suka duba, kuma ehh hakan neh ya fita followers, tace
“Kaii mata dai sunji kunya, da sunga namiji ya had’u ga kud’i kuma suna ganin hotunan shi a kasar waje sai su rikice gaba d’aya suta following”, Ammar yayi dariya sosai yace
“Yau ke da bakin ki kike ce na had’u, wayyo naji dad’i”
“Kar ma kaji dad’i Mallam, ironically nake nufi, opposite idan baka san meaning na ironically ba” yace mata “whatever gurl”, haka ya ja motar ya shigar da ita har cikin school, ta bud’e motar ta fita kenan Ammar shima ya fita a Motar yaje daf kusa da ita yace
“Khairiyya jirgi na zai tashi karfe sha d’aya, but karkiji komai zan dawo soon, nasan Abba yana zuwa maganar auren ki za’ayi, I am very happy for you KIM, I must say that you’re so very lucky, wanda kike kauna shima yana kaunar ki, baki son masu wani, the one you love also love’s you back, Allah kara had’a zuciyan ku KIM, Allah barku tare, Allah sa alkhairi neh, I can’t hide to you, bazan 6oye miki ba, I must have to say this, I’M GONNA MISS YOU ALOT KIM, DO TAKE CARE OF YOURSELF, GOODBYE
Yana gama fad’an haka ya shiga motar sa da sauri ya fisga motar da gudu yabar wajen, ta kasa gaba ta kasa baya sai zubar da hawayen da takeyi, tace da karfi kamar mahaukaciya I will Miss you more Mr Ego, m gonna miss you more more more more, more than words can say, kowa ya juya a wajen yana kallon ta, cire handkerchief tayi a Jakarta ta share hawayen ta, ta d’au wayar ta takira Teema, Teema batayi picking call d’in ba, tsoki taja, motar Zilyadeen neh ya tsaya a gaban ta, bud’e mata kofa yayi yace tashiga, ba musu tashiga motar ta gaishe shi ya amsa fuska asake, yace
“Yajiki, da alama kamar kin warke”, eh na warke ta amsa mishi
Zilyadeen yace “Khairiyya akwai very important magana da nake so muyi dake, but muje office nawa sai muyi maganan acan ” Khairiyya ji tayi zuciyan ta ya buga tace “ohk bakomai”
Bayan yayi parking motar a parking space na staff suka wuce office nasa direct, bayan sun shiga ya bata drinks tasha suka d’an ta6a hira sama sama, Zilyadeen ya gyara zama yace
“Khairiyya maganan da nake so mu tattauna akan Rumaysa neh, Rumaysa taki ta amince, bansan ya abun zai kasance ba But karki damu Khairiyya inda raina zan aure ki, inda raina Khairiyya matar Zilyadeen ce, Inda Raina zamu kasance tare har karshen rayuwar mu….. (ZIL-KHAIR), Khairiyya tace Allah za6a mana mafi alkhairi, karka ji komai yaya zil, koh da Rumaysa bata amince ba zan iya hakura
“Shhhhh Khairiyya karki kara fad’an haka, koh da ke zaki iya hakura ni bazan iya hakura ba, yanxu naji nafara sonki, So na hakika”
Khairiyya tayi murmushi tace “ni zan tafi, inada da lectures bye”, yana kiran ta amma koh tsayawa batayi ba tafita a office d’in