KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

  Gida ya rikice, a yau neh za kai kud'in sadaki gidan yan uwan baban Rumaysa, Rumaysa ta rufe ido tace ita ta fasa auren, abun ya girgiza kowa, kaf kowa ya girgiza musamman Zilyadeen, su Daddy da Mummy suka sata a gaba dole sai ta fad'a musu menene dalilin ta na fasa auren Zil, tana kuka tace

“Kuyi hakuri mummy bazan iya auren yaya Zil ba, tun ma ba’ayi auren ba yana mini maganan kishiya”, Kishiya!! Duk suka fad’a a tare, Rumaysa ta cigaba
“Wlhy kishiya, kuma ba kowa bace illa Khairiyya “, salati duk sukayi, Daddy yace shi bazai tilasta mata akan abun da bata so ba, suka basu wuri da Rumaysa akan su tattauna, Daddy da Mummy suna fita Rumaysa tace
“Yaya Zil kaji na rantse da Allah, sai dai ka za6a koh ni koh Khairiyya”, tana mei zub da hawaye

Nana fa'ad En Eesha 

????????????????????????

www.narhnah.mywapblog.com
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

Page 57

       Suraj kam sai murna yake tayi, haka yayi dropping nata a gida ya juya ya tafi, itakam duk hankalin ta a jagule, ta rasa mei yake mata dad'i, da daddare da misalin karfe goma tana kwance a d'aki wayan ta ya fara ringing, da zumud'i ta d'auka dan ganin number Abba, bayan sun gaisa da muryan shagwa6a tace

“Abba yaushe zaku gama ku dawo neh”, Abba yace
“Baby nah ki kara hakuri har yanxu dai maganar case d’in nan neh ki kara hakuri in next two months In Shaa Allah zamu gama komai”
“What” tayi exclaiming da karfi tacigaba da cewa
“Har two months Abba, Gaskia ni zanzo na samei ku a wajen “, Abba yace Haba Babynah toh makarantan fa, be patient kinji, inda rai da lafia ai wata biyu kamar kwana biyu neh kinji, ga Ammar kuyi magana
Ammar yace “Hello KIM”, ta tura baki kamar yana kallon ta tace
“Mr Ego shineh koh ka kirani kace mini ka iso lafia, inata binka a raina”, Ammar yace So sorry KIM, but ina zuwa gida zan kiraki da number ta don’t worry”, Khairiyya tace
“Promise”, Ammar yace In Shaa Allah, Khairiyya tace tam shikenan, bayan sun gama wayar tana ajiyewa call na Zilyadeen yashigo, tana d’auka wa tace hello, Zilyadeen cikin muryan masifa yace
“Khairiyya tun d’axu nake trying number ki but number busy, na kusan awa d’aya ina dialing number busy, ke da wa kike waya haka tun d’azu”, ransa idan yayi dubu yatashi, kishi tsantsa, Khairiyya tace
“Nida Abba da Ammar neh fa”, wani dogon tsoki yaja, dan shikam a yanxu baya kishin Suraj kamar yadda yake kishin Ammar, dan kullum hiran ta Ammar, yace
“Keda Ammar dai bada Abba ba, kuma Ammar ba yana gidan ba”, Khairiyya muryan ta yana rawa tace
“Bayanan yayi tafiya yau”, “shineh har kin fara missing nashi koh, kuna waya kusan awa d’aya, duk hiran da kukayi before ya tafi bai ishe kuba” cewar Zilyadeen, maganar ba karamin 6ata mata rai yayi ba, bata san lokacin da ta katse wayan ba, haka ya ringa kiranta amma bata picking call d’in, ta 6angaren Zilyadeen kuma ya shiga damuwa ainun, yaga batada niyan picking call nashi ya tura mata Text message kamar haka
I’m sooo very sorry my dearest KIM, ina sonki sosai shiyasa nake bala’in kishinki, ina kishin ki sosai Khairiyya, banson wani namijin yaji sweet voice naki bayan ni, I sooo much love you, I love you alot Khair, do take care of yourself for me please….. 4rm ur future husband In Shaa Allah (kut!!! Ni nana nace Sunan Rumaysa yadawo kan KIM)
Ita bataga text d’in ba dan Suraj yakirata a lokacin, dad’ad’un kalaman sa sun sa ta mance da 6acin rai da Zilyadeen ya saka ta, ita bata gama wayar ba sai bayan minti talatin ahakan ma tace masa tana jin bacci, tana gama wayan taga text na Zil, ta karanta message d’in yafi sau goma, ba karamin dad’i text d’in ya mata ba, sai murmushi takeyi, tana cikin karantawa wani message yashigo, Captain Suraj tagani tafara reading kamar haka
falling In love with you is the second best thing in the world, Finding you is the 1st… with every beat of my heart, I love you, Until that last beat, I will love you… Goodnyt en swtdrms of mee
Hmmmm ta furta, ta kasa ma koh d’ayan su reply, addu’a tayi ta kwanta bacci bayan ta gama jiran call na Ammar amma bai kirata ba…..

a gurguje pls

   *Bayan wata biyu*....... 

Su Khairiyya a yau suka zana last paper nasu na first semister Maths102 na mallam mandara kowa sai complaining course d’in yake dan muguntan malamin, itadai Khairiyya shuru tayi dan daren jiya bata samu tayi bacci koh kad’an ba, ga karatun da tasaka a gaba ga kuma auren Zilyadeen da Rumaysa wanda za’a d’aura gobe, duk Zilyadeen ya rikitar mata da brain, a kullum yana kara jaddada mata shi har yanxu har gobe yana kan bakan sa, ya mata alkawari bayan auren su da Rumaysa da wata uku zai aure ta, ga wani mahaukacin so da yake nuna mata, Captain Suraj kuma shima kullum da nasa salon nuna mata So, shi Allah Allah yake Abban ta yazo ayi maganar auren su, yanxu kam yana cikin farin ciki dan Khairiyya ta fad’a masa Abban zai shigo Nigeria ranar Monday, saura kwana biyu kenan…… Ammar kuma tunda yace zai kirata har yau bai kiran ba, ta kar6a number sa wajen Ummi takirasa baya d’aukan wayar ta, koh da takira da wani number yana jin muryan ta zaiyi disconnecting call d’in, duk ta damu ta rame, Ammar shine kad’ai mutumin da take iya gaya masa matsolinta, gashi shima yana ignoring nata………., zata shiga motar ta kenan taja ta bar makarantar wata yarinya ce da bak’in kaya, socks baki, hijabi baki ga kuma wani bak’in nikaf a fuskar ta, a takaice dai daga sama har kasa bakin kaya neh a jikin ta, koh idon ta ba’a gani ta toshe da bak’in glass, Khairiyya da taganta sanda ta tsorata, yarinyan tace
“Khairiyya sannunki, ya exams”, Khairiyya zuciyan tane ya kara bugawa ji tayi kamar tasan muryan, Toh muryan wacece, yarinyan ce ta kara cewa
“Khairiyya farko da na had’u dake acikin makarantan nan naji ina kaunar ki, Khairiyya ina sonki shiyasa banso nayi kishi dake, ki taimaka wa rayuwar ki Khairiyya, inason Zil sosai, Naga taketaken sa, yana so bayan auren mu dashi ya aure ki, hmmmm shawara nake baki Khairiyya, idan kunne yajiii”, da kyar bakin Khairiyya ya iya furta
“R-u-m-a-y-s-a-h kece”

Rumaysa tace “nice Khairiyya, idan har kina son kiji dad’in aure Toh karki aura mini Miji Nah”, abun ba karamin mamaki yabawa Khairiyya ba, amma ta dake tace
“Rumaysa inaga kin manta Wacece Khairiyya, koh nace miki bakisan Wacece Khairiyya ba, bakisan Wacece KIM ba, kinyi babban kuskure da kikazo mini da wannan maganar, nasan inason Zil but auren sa yafita mini a kaa, but yanxu da kizo naji sha’awar auren sa, koh ba komai zan aure sa muje muta gwabzawa a gidan sa, muje muta catching Fun, kinsan I love catching Funs and kuma kidaina cewa mijin ki, mijin mu dai”, taja wani dogon tsoki tashiga motar ta, itama Rumaysa ta shiga motar Khairiyya gidan bayan dan abud’e yake tace
“Kina wani magana akan bansan Wacece Khairiyya ba, nasan ki mana Khairiyya farin sani ma kuwa, Khairiyya yarinya ce da ta zauna ita d’aya a babban gidan na shekara da shekaru, ai kinsan duk macen da ta zauna ita kad’ai a gida ba masu tsawatar mata Allah kad’ai yasan abunda zata aikata, Khairiyya itace yar maye, ba kayan maye da shaye shayen da batasha, Khairiyya batada friends sai maza, mazan ma yan daba yan ta’adda, kinga koh anan nafi karfin ki, kuma kin manta da wani abu guda d’aya Khairiyya, nifa yar gida ce, Zilyadeen ko mei na masa bazai ta6a ya saken ba, kefa bare ce”, Khairiyya tayi wani mugun dariya tace
“Hmmmm lalle Rumaysa, Rumaysah Rumaysa, kedai kije kiyi ta addu’a Allah sa kar Zilyadeen ya aure ni, dan a ranar da ya aure ni yakai ni gidan sa toh kisani a ranar kashin ki ta bushe, a ranar zaki kara tabbatar wa kanki cewa lallai mijin ki yar maye ya auro, zaki san cewa Yar shaye shaye ce kishiyarki, a ranar zaki sake tabbatar wa kanki cewa asalin yar daba ce kishiyar ki, a ranar zakisan cewa…… “bata karasar da maganar ba call na Zilyadeen ya shigo, baro baro akan screen nata Swt Zil tayi saving, d’aga wayar ta tayi ta nunawa Rumaysa tace kishiyas mijin mu fa yana kiranah, Rumaysah ranta neh yayi mugun 6aciwa tacewa Khairiyya
“Sai randa kika shigo gidana as kishiya ta zamu zuba”, tafita daga cikin motar, Khairiyya abun ma dariya yabata, kashe wayar ta tayi gaba d’aya dan yanxu haushin su duka takeji, ta bude glass na motar tacewa Rumaysa da karfi “jahila kawai”motar ta tafisga da gudu tabar cikin makarantan, tana zuwa gida tashiga d’akin ta da gudu ta kwanta a kan gado tafara kuka sosai kamar ranta zai fita, sai yanxu taji zafin kalaman Rumaysa, taji ta tsana kanta gaba d’aya, maganar Rumaysa neh yake yawo a kwakwalwar ta
Kina wani magana akan bansan Wacece Khairiyya ba, nasan ki mana Khairiyya farin sani ma kuwa, Khairiyya yarinyan da ta zauna ita d’aya a babban gidan na shekara da shekaru, ai kinsan duk macen da ta zauna ita kad’ai a gida ba masu tsawatar mata Allah kad’ai yasan abunda zata aikata, Khairiyya itace yar maye, ba kayan maye da shaye shayen da batasha, Khairiyya batada friends sai maza, mazan ma yan daba neh, kinga koh anan nafi karfin ki, kuma kin manta da wani abu guda d’aya Khairiyya, nifa yar gida ce, Zilyadeen ko mei na masa bazai ta6a ya saken ba, kefa bare ce

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button