KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Nana fa’ad En Eesha

????????????????????????

www.narhnah.mywapblog.com
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 60]

   Yarinyan Alhaji Ibrahim Muhammad fu'ad, sunan ta Khairiyya cewar Mami, Munay ta zare ido tace 

“Dan Allah Mami, na d’auka wata talakace ai, toh yanxu yazamuyi”
Mami tace da hankali “beauty (sunan da take kiranta) the best solution kawai muje wajen malamin nan”, Munay ta 6ata rai tace
“Mami kin sandai ba abun da natsana a rayuwata duk iskanci na kamar zuwa wajen malami da boka koh, ki kawo wani shawaran amma ba wannan ba Cox gaskia bazan yarda da wannan shawaran ba”, Mami ta tureta tace
“Mtswww kefa banza ce, ana nuna miki hanya kina bijire wa, ashe dai ba Sonshi kike ba”, Munay tana shan kamshi tace
“Gaskia maganar gaskia tsakani da Allah ba wani sonsa nake ba, kawai dai inaso ana nuna ni ace ga matar GENERAL SURAJ, (yanxu dan an kara masa matsayi), shineh kawai Mami ana nunani ana cewa ga Matar sa, kin ganeh ai, kinsan ni Mami inason karya da respect, ina bala’in son kayan karya, duk wani cewa ina mutuwar sonsa fa I don’t really mean it, ina mutuwar son matsayin sa neh not shi d’in”, Mami tace
“Lalle beauty Toh ai shineh so d’in”, Munay ta girgiza kanta tace
“Mami nasan So, wanna baya cikin signs na So, a rayuwa ta mutum d’aya na So kuma kinsan wayeshi, tunda ya rasu ban kara jin irin feelings ma wani d’a namiji ba”, Mami tayi dariya tace
“Lalle munay the beauty, tunda bakison aikin boka da malami yanxu mei abunyi”, Munay ta tashi a kujera tace
“Yawwa yar gari, yanxu kike magana, kinsan mei Mami I will think of a solution, zan samo mana mafita ba boka ba malam, just give me a day, cikin kwana d’aya sai mu shirya aikin da yafi na boka koh malam”, Mami tayi shewa tace
“I trust you munay the beauty, Allah bar mini ke”, Munay tace Ameen

Wanene Suraj

Captain Suraj a.a wanda a yanxu General Suraj a.a, Asalin sunan shi Suraj Adam Abubakar, Yaron Mallam Adam Abubakar
Mallam Adam Abubakar ma’aikaci neh a UBA BANK, yan asalin garin maiduguri/kunduga baribari gaba da baya, sai matar sa malama Safiya ita yar asalin garin gombe, mutanen kirki neh sosai, Mallam Adam su biyu neh iyayen su suka haifa, shi da Alhaji Muhammad (mahaifin munay), iyayen su sun rasu tun suna kanana, haka suka tashi suna sana’ar hannu suna makaranta, bayan Shi Adam yagama ya samu aiki a bank yadauka nauyin kanin sa Muhammad a lokacin ya aura Safiya, bayan Muhammad shima ya gama marantan sa aka turasa service (NYSC) a Kano, a Kano ya had’u da Saude har suka fara soyayya, Muhammad yana da hankali sosai da sanin yakamata but amma Saude mace ce mai son duniya, tafifita duniya akan komai
Bayan shekara d’aya da aure Safiya da Adam ta samu ciki, bayan wata tara ta haifa d’an ta aka rad’a masa suna SURAJ, Suraj yana shekaru uku Muhammad shima ya aure Saude, Allah bai bata haihuwa ba sai bayan shekaru goma, inda ta haifa yarta aka rad’a mata Suna Munay……
Suraj yana shakaru goma sha hud’u mahaifan sa Mallam Adam da malama Safiya suka rasu a plane crash, inda Adam zaikai Safiya asibiti India dan tana da matsala da kidney nata za’a mata kidney transfer.. Toh tunda rasuwar mahaifan sa ya koma hannun kanin babanshi da zama wato Alhaji Muhammad (Abu ) ya rike sa tamkar d’an cikin sa shi ya haife sa, Saude (Mami) itama ta rikesa daidai balaifi, watarana ta musguna masa watara ta masa abun arziki, Suraj yana matukar kaunar su sosai kamar su suka haife sa, shi baima san Mami tana musguna mishi ba ya d’auka discipline neh take koya masa.. Yana bala’in kaunar su and he always abide by their rules, idan sunce bari toh har abada ya bari kenan, Mami tana yinsa dan ita a tunaninta ta juya masa kwakwalwa neh, a tunanin ta aikin bokan na ci batasan tsantsan biyayya baneh, Mami na matukar son yar ta Munay ta aura Suraj dan tasan koh bayan ransu zai kula da ita and most especially yana da kud’i… Munay kuma tun da tasan kanta basu ta6a zama tare sunyi hira ba danshi mostly baya zama a gidan ma, tun tana primary yaje school na soldiers, amma yana matukar burgeta, Munay yarinya ce mai Son girma, yarinya ce mai Son karya, Farko BSC Nursing suka bata a Unimaid ta canza zuwa environmental biology wai ya mata wahala she can’t stress herself…………………………. wannan kenan………….
Da misalin karfe takwas na dare bayan isha’i Suraj yazo gidan su Khairiyya, bayan sun d’an ta6a hira da Khairiyya yace
“Please ki sanar da Abba iyayena zasuzo next week akan maganar auren mu “, Khairiyya tayi murmushi tace
“Ba komai Allah nuna mana”, amma can kasan zuciyan ta ita kad’ai tasan yadda take feeling

a gurguje pls????????

Bayan sati d’aya

Alhaji Muhammad Abubakar da sauran yan uwansa sukazo gidan Alhaji Ibrahim Muhammad fu’ad mai naira nemawa d’an su auren Khairiyya, sukayi fixing date sati uku mai zuwa, basu samei matsala ba kuma duk suna da kud’i a hannu.. Bayan tafiyan su Abba yashigo d’akin Khairiyya yasameita tana kuka, zama yayi yafara lallashin ta yace
“Baby nah idan bakison auren ki fad’a mini mana pls”, Khairiyya ta kwakulo murmushin dole tace
“I’m happy Abba, you don’t have to worry, wannan kukan da nakeyi na rubuwa dakai neh”, Abba yace
“Haba baby nah, koh aure bai rabamu ba ai mutuwa zata rabamu, balle ma I know you re used to it, inakai months bana kasa”, Khairiyya tayi murmushi tace
“Wannan daban neh Abba”, haka dai yata lallashin ta

~~~~~~

Munay tayi bincike akan Khairiyya sosai, duk wasu informations akan ta tasani, abun da tafi focusing akai shineh shaye shayen da Khairiyya takeyi, da kuma zama ita kad’ai a gida ba uwa ba ubu sai masu aiki. Tare take da kawar ta mei suna mabcie a cikin motar ta picanto tace
“Mabcie nifa haryanxu banga picture na Khairiyya ba”, mabcie tace
“Haba munay the beauty, duk zaman ki a maiduguri, duk wayayyun friends naki, duk fame naki amma bakisan KIM ba”, Munay taja wani dogon tsoki tace
“Toh ita sa’atace da zan santa, kinsan I am Off her level nafi karfin ta tunda kan shekaru”, mabcie tawani dariya tace
“Idan kince mini kin girme ta zan yarda, but tafiki qualities ahswear, kud’i komai”, Munay tawani murmushin mugunta tace
“Sai naganta tukun, pls ki nema mini her phone number”, mabcie tace kishiga Instagram nata mana, Munay tace kinsan User nata, Mabcie tace Eh
Haka munay tashiga IG nata koh zata gan pictures na Khairiyya,taga followers na Khairiyya kamar wata world Celeb kawai verified neh babu, bayan ya gama loading taga babu picture koh d’aya sai picture na Ammar, Munay tace
“Wow wannan had’addan dude d’in fa”, mabcie ta kar6a wayan tagani tace
“Ohh wannan cousin brother nata neh Ammar, sister na tace time da suke school Amr-d-player nickname nasa, mugun player neh, sai kiga yana fita da kawayen juna, kina mishi iskanci zai rabu dake, mata suna haukan sonshi”, Munay tace
“Ai dole, irin wannan kyau d’in mata ba dole suta mutuwa akan sa ba, ga kud’i ga kyau… hmmm ni mu mantar da KIM ma tunda inada informations akanta shikenan”

Nana fa’ad En Eesha

????????????????????

www.narhnah.mywapblog.com
[11/8, 9:31 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 61]

Russia

Ammar neh a wani had’adden mansion d’aki rike da hoton Khairiyya, he whispered
“You bae, I love you, why is it so hard to get over you and harder to stop thinking of you” sai hawaye sharr a fuskan shi, ya ramei yayi duhu, baida aiki sai tunanin Khairiyya, da hoton ta yake kwana dashi yake tashi, baya da wani magana sai na Khairiyya, idan ya d’au giya zaisha sai ya fasa………….. Khairiyya tana kiransa amma baya picking call d’in, sai da safe da ya bud’e mail nashi yaga message nata kamar haka
Thanks for everything Hot jerk, i dont know why you aint picking my calls… I soo much in need of your advice and prayers, please call me……. yagani baiyi reply ba, still takara tura masa message kamar haka
Aure nah next two weeks Ammmmar, I really don’t know what to do… kana hurting nah Ammar, I am soo much in pain, I really don’t knoe why you’re ignoring me but please I really wanna talk to you, ignoring nah da kakeyi zai iya saka ni hawan jini please and please Ammmar idan baza ka kirani ba please pick ma call
Jin auren ta dayayi yasa hankalin sa ya tashi, kuka yake sosai kamar karamin yaro, ga pictures nata a zube koh ina a d’akin sa, ba abun da yake fad’a kamar
“I love you KIM, I love you, I sooo much, I love you more than my own life, you mean the world to me” kuka yake sosai, nima harda d’an guntun hawaye nah???? kwanciya yayi a kasa yana kuka, Yaa Allah ka taimaka mini, ka cire mini son KIM a zuciya ta (ku tayani ce Ameen fans)..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button