KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤Nigeria

Suraj neh zaune da Abban munay a parlour, Abbu yace
“Suraj abunda yasa nakeson magana da kai shineh a gaskia anzo mini da maganar yarinyan da kake so ka aura akan bata da tarbiya mai kyau, ban maka zancen ba har sanda nayi bincike mai kyau, kuma a binciken da nayi yarinyan yar maye ce, she’s a drunkard, and kuma ita kad’ai take zaune a gida ba uwa ba uba, bawai ina nufin banson auren ka da yarinyan nan ba, kawai ina fad’a maka aure ba abun wasa baneh, ka nemawa yayan ka uwa ta gari”, Suraj ji yayi zuciyan sa ya buga yace
“Abu nasan da haka, I knw everything about her kuma I completely trust her, nasan tana shaye shaye but that was then, kuma zama ita kad’ai da ake cewa Khairiyya bata ta6a zama ita kad’ai a gida ba, tana da masu aiki suna tayata kwana, Khairiyya kuma bata shigo da maza cikin gida Abbu, ka yarda dani”, Abu yace
“Ba komai Suraj, tunda you trust her ai shikenan, Allah kara shiryar da ita ya baku ikon zama tare da hakuri da juna”, Suraj yace Ameen Abu nagode

Tun ranar da akayi fixing date na auren Khairiyya Zilyadeen yaji labari, yana ta kiranta a waya but bata receiving call d’in, duk duniyan ta masa zafi ya rasa ganeh mei yake masa dad’i, Rumaysa ma tana cikin tashin hankali dan tun daga ranar Zilyadeen ya daina kulata, abincin tane kad’ai yake ci but baya mata irin wasa da dariya na da, ba abun da yake had’a ta dashi……………

Munay ce kwance akan gado sai dariya take ita da Mami, da alama duniyan ta mata dad’i tace
“Mami nifa ba wasa baneh just wait and see tik-tok goes da clock”, ta kara fashewa da dariya, Mami tace
“I trust you munay the beauty”, suka tafa abun su, Munay tace yanxu Wlhy Mami koh wani irin so yake ma Khairiyya I am pretty sure baxai aure ta, Mami tace nikam kinki kif’ada mini plans naki, Munay tace
“Kedai ki zuba ido kiga ikon Allah, ba auren saura two weeks ba yanxu, zuwa next week zakiji an fasa auren”, suka tafa suna shewa, Munay tace
“Opppps na manta wollah, munyi da Mabcie zata rakani gidan su KIM naganta”, Mami tace
“Haba toh tashi ki shirya mana, ki saka kayan da yafi tsada a kayakin ki, ina wancen lace da na siyo miki 45k, ki saka shi kinsan banso kiyi looking local, kuma ki d’au motar Abbu zan sato miki key d’in”, Munay tayi tsalle ta rungume Mami tace
“Mami ke yar garice wollah, I love you Allah bar mini ke, bara nayi wanka na dirza jikina”, Mami tace
“My munay the beauty ai ko bakiyi wanka ba kin had’u, but Hausawa sunce koh kana da kyau ka kara da wanka”, Munay tayi ihu had’e da tsalle tace yawwa Mami bara na shiga sai na fito

 Bayan ta fito a wankan ta saka lace da naji Mami tace 45k, bak'i neh da touches red, Gaskia kayan ya had'u ba karya kuma yayi fitting tsiririn jikin ta, jaka da gyale red tasaka sai flat shoe mai kyau bak'i da ja, tasha d'aure.. wayan ta galaxy S5 edge tacire a jaka takira Mabcie, tace

“Mabcie ki fito bakin gate yanxu zanzo na d’auke ki Kuma wollah Mabcie banda kwalliyan da zai 6ata mini time kinji, yanxu zan fita a gida” ta katse wayan, fita tayi taje d’akin Mami, Mami lokacin na kallon BBC, Mami ta kalle ta tace
“Munay the beauty kinsha kyau, saidai banji kina aman turare ba yadda nakeso, ga dressing mirror na kiyi spreading duk perfumes da suke wajen, ko fesawa gaba d’aya ma kinaso kiyi”, Munay tayi wani ihu tace
“Mami yar gari, gaskia kinje ghanas, thanks”, haka Munay ta fesa turaren gaban mirror na Mami har sanda taji itama ya isheta sannan ta bari, tace
“Mami ina key na motan”, Mami ta mika mata, Munay tayi wani ihun tace
“Anaa ahubbiki yaa Umma, take care bye”, ta mata kiss a goshi, Mami tayi dariya tace
“Allah kiyaye hanya the beauty”, fita tayi parking space ta shiga wata mota range rover had’adde blue colour, da alama shineh motan Abbu d’in
Ta fisga motar sai kofan gate na gidan su Mabcie, horn ta danna da karfe, nan da sec talatin Mabcie ita ma tafito tasha kwalliya, ta shiga motan, Mabcie ta bud’e baki tace
“Munay kefa yar wind ce, irin wannan kwalliyar da mota haka”, Munay tayi dariya tace
“Babban yarinya kikeji”, Mabcie tayi dariya tace
“Hmmm nayi shuru”, da gudu take Jan motar har takai gidan su Khairiyya, horn tayi mai gadi yafito, suka gaisa tace
“Umm baba wajen Zaynab nazo”, mai gadi yace ku kawayen tane
“Munay tayi murmushi tace eh”, mai gadi yace toh bara na kirata na sanar da ita
Munay tace haba baba baka ganeh mu baneh, koh munyi maka kama da yan danfara, Mai gadi yace
“A’a koh kad’an, bara na bud’e muku gate d’in toh “, Munay tayi masa godiya ta mika masa dubu biyu shima yana ta zuba godiya, bud’e mata gate yayi tashiga gidan, bud’e bakin ta tayi ganin tsarin gidan, a rayuwar ta bata ta6a shiga cikin gida irin wannan ba, wajen parking space taje dan Parker motar ta, anan ma tasha kallo dan duk cikin motocin da suke parker a wajen manya manyan motacine, sanda Mabcie tace
“Rufe bakin ki munay the beauty, wannan ma kadan kika gani”, hmmmm shineh kawai abun da Munay tayi suka fita a motar, kai tsaye cikin gidan suka shiga, da shigan su parlour duk suka bud’e baki, hanci, ido dan kallon gidan, Dije tana mopping parlor ta gansu tace
“Lafia kuwa”, Munay tace
“Ummmm lafia Khairiyya muke nema”, Dije tace ohk bara na mata magana,Munay tace
“amm bani number ki mana before kitafi akwai maganar da zamu tattauna”, Dije tace
“Lafia koh”, Munay tace lafian neh ya kawo haka ki kwantar da hankalin ki
Munay ta mika mata wayar ta Dije ta kar6a ta saka number ta, Munay ta mata godiya.. Dije ta wuce upstairs su munay suka zauna a kan kujera suka cigaba da bawa idon su abinci…… wajen Khairiyya kuma tana d’aki tana ta faman kiran number Ammar baya picking duk ranta a 6ace Dije tashigo d’akin, Khairiyya tace
“Menene kuma, just cook anything please”, Dije tace
“amm hajiya anzo wajen ki”, Khairiyya ta bud’e baki tace su waye, Dije tace
“Wasu yan mata neh”, Khairiyya tace ohk kice musu ganinan fitowa, Khairiyya ita duk a tunanin ta irin yan matan nan neh masu nace su zama kawayen ta irin su Eesha da sunga yarinya kyakkyawa da kud’i zasu so suyi kawance da ita, Khairiyya bata fito a d’akin ba sai kusan bayan minti arba’in, tun suna jira har suka gaji ga gaban su an cika musu da foreign drinks da snacks, Munay tace wa Dije wai baki mata magana baneh, Dije tace wollah na mata kuma bata so a mata magana sau biyu kuyi hakuri zata fito, bata ida maganar ba Khairiyya tana saukowa akan upstairs, kamshin turaren ta neh ya doshe hancin su, Munay zuba mata ido tayi tana kallon ta a zuciyan ta cewa take Allah yayi halitta, sai taji ta raina kyaun ta, yangan ta, jin kanta kai komai ma. Khairiyya tana murmushi tace
“So sorry na ajiye ku koh”, Munay tayi murmushi itama tace ba komai wlhy, suka gaisa sosai Khairiyya tace
“Sai dai ban ganeh ku ba”, Munay tace “ni sister na yaya Suraj ce wannan kuma kawata ce Mabcie”, Khairiyya ta bud’e baki tace
“Haba dai, ai da kun shigo d’aki kun samei ni tun d’azu, kuma shi Yaya Suraj bai sanar dani zakuzo ba”, Munay tayi dariya tace ba komai nima baisan zanzo ba and please karki fad’a masa, na kasa hakuri har ranar auren neh nace dole nazo naganki musan juna tun kan auren amaryar mu”, Khairiyya tayi dariya tace kai amma ngd, haka suka ta hira daga baya sukace zasu tafi Khairiyya ta rakasu, ta basu designers perfume da kayan make-up………

     General Suraj neh zaune da babban abokin sa doctor umar, kuma d'an uwan Hajiya saude (Mami), tare suka tashi tun suna yara kan kanana, docter umar likita neh a babban asibin UMTH, doctor umar sai zolayan sa yake yana cewa

“Ango kasha kamshi, Ango the Ango, yanxu sai wani feeling kanka kake kaga auren ka saura sati biyu”, Suraj yayi dariya yace
“Haba mana kabari please stop I don’t like it”, doctor umar yayi dariya yace
“Yanxu please bazaka kaini wajen amaryar ka na ganta ba” Suraj yace
“Toh yanxu ka tashi muje karka cika mini kunne”, Suraj yakira Khairiyya yace yana nan zuwa da abokin sa…….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button