KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Direct University Teaching Hospital Maiduguri yawuce, office nasa ya dubashi amma a rufe, ya kara fusgar motar shi zuwa gidan sa, da sa’an shi kuma yana gida, Suraj yace
“Haba Umar ya zaka mini haka, tell me meke faruwa”, Umar ya fusgar da iska mai zafi yace
“Suraj wannan itace matar da zaka aura”, Suraj yace Eh itace
Umar yace “KHAIREEYYAH Ibrahim Muhammad fu’ad koh”, Suraj baiyi mamakin sanin full name nata da Umar yayi ba, ko ba komai gidan is popular dan ana kwatance da gidan ma a gari, Suraj yace
“Tabbas sunan ta kenan, ka santa neh, idan kasanta ma a ina, meisa you look shocked daka ganta, please answer me”, Umar yace
“Zan amsa tambayoyin ka but first ina so ka mini listing halin ta, masu kyau da mara kyau”, Suraj yayi tsoki yace
“Badai zaka ce mini she’s a drunkard ba, ai nasani kuma zan aure ta a hakan”, Umar yace apart from ita drunkard yar maye, mei kasani gamei da ita
Suraj yace tana kwana da masu aiki shikenan, Umar ya girgiza kansa yace
“Suraj abokina, bazan iya fad’a maka ba, but ba abunda zance illa kaje kayi bincike akan ta mei kyau, but before kaje kayi bincike kasani KHAIREEYYAH patient nawa neh a asibiti, try and know ya tayi tazama patient nah, kayi bincike mei yake damun ta”, Suraj atake ya fara gumi yace “please tell me meye ke faruwa”, Umar ya girgiza kansa yace I can’t kaidai kaje kayi bincike sosai
Haka Suraj yabar gidan sa duk jikinsa yayi sanyi, da kyar ya iya driving zuwa gida, ya shiga d’akin sa ya kulle kofa, sai kiran Khairiyya yake a waya bata d’auka wa

Khairiyya bata bud’e d’akin ta ba sai bayan isha’i, time d’in ma Zaynab ce ta damei ta da knocking, tana bud’e kofan taja Zaynab cikin d’akin ta kara rufe kofa, tace a tsorace
“Zee wannan ba doctor umar ba, ya akayi yazama abokin Suraj, yanxu suna nan koh sun tafi “, duk wannan tambayoyin tana yinsu neh lokaci guda, Zaynab tace
“Haba mana calm down, calm down Khairiyya”, Khairiyya sai juye juye takeyi Zaynab ta rungume ta tace
“Just calm down Khairiyya sun tafi tun d’axu”, Khairiyya tace
“Are you sure”, eh KIM sun tafi, da kyar dai Khairiyya taci abinci, bayan hankalin ta ya d’an kwanta Zaynab tace
“Khairiyya ina kika sanshi, kuma mei ya ta6a had’a ku”, Khairiyya ta wani sauke numfashi tace
“Zaynab mu mantar da maganan nan please, ya wuce”
A ranar Suraj ya kasa bacci, sai tunanin maganan Doc Umar yake Khairiyya patient nawa neh a asibiti, try en know ya akayi tazama patient nawa, sai tunanin maganar yake zuciyan sa yana bugawa, gashi ya kirata bata picking na calls nashi, da kyar bacci yayi gaba dashi bayan yayi nafiloli

Ta 6angaren Khairiyya ma dakyar ta iya yin bacci, tunani da tsoro neh fal ya cika ta, haka da kyar bacci 6arawo yayi gaba da ita

A washegari da safe tun karfe tara Suraj ya shirya zuwa gidan su Khairiyya, Dije mai aiki tace masa ai sun fita da Abba zuwa asibiti, zuciyan sa neh ya kara bugawa, ya cire dubu goma ya mikawa Dije yace
“Please ki barni nashiga d’akin ta na duba wani abu”, Dije taki ta amince, da kyar da kyar ta amince ta kar6a kudin ya shiga main side na gidan, ta rakasa zuwa d’akin Khairiyya d’in ta fita, dube dube yafara a d’akin, tun daga cikin wardrobes nata har cikin drawers dasu kits, ba inda bai duba ba amma bai samu abun kirki ba, daga kayan karya sai su chocolates, can zai fita a d’akin idon sa ya hango wani karamin drawer a saman gadon ta, da sauri yaje ya bud’e, so much suprise on his face dayaga abubuwan da suke ciki, magani neh fal acike a drawer d’in, da sauri ya kwasa wasu a cikin maganin yasaka a aljihun sa yafita a d’akin, Godiya yayi ma Dije a lokacin Haule tana side na Abba tana gyara masa, Indo kuma taje kauye…. Ya shiga motar sa kenan sai ga motan Abba ya danno kai, ya jira sukayi parking Suraj yafito a motan ya durkusa har kasa ya gaishe da Abba, Abba ya amsa yana murmushi da tambayan sa ya mutanen gida, Suraj yace duk suna nan kalau, Abba yashiga ciki yabar sa tsaya da KIM, Khairiyya ma ta gaishe shi tace bismillah, ta masa iso zuwa guest room, bayan duk sun zauna Suraj yace
“Waye ba lafia naji kunje asibiti”, Khairiyya tayi murmushi tace
“Wlh Abba neh, kasan yana da BP shineh mukaje Yaron abokin sa ya duba sa a UMTH”, Suraj yace ayyah Allah kara sauki ta amsa da Ameen, bayan sun d’an ta6a hira yace
“KIM please tell me something, a ina kikasan Docter Umar”, ji tayi zuciyan ta ya buga tace
“A asibiti”, ya sake tambayan ta
“Why kika zama shocked da kika gansa”, Khairiyya tace
“ummm ammm ba komai fa, I don’t know why duk time da na gansa sai naji gaba nah yana fad’uwa”, Suraj yace
“Khairiyya please ki fad’a mini gaskia don’t hide anything”, tace gaskian kenan Nifa a asibiti nasan shi, lokacin ina d’an jin zazza6i shine yayi treating nawa, Suraj yace
“Ohk Toh shikenan” amma can cikin ransa bai yarda da abun da Khairiyya ta fad’a masa ba, ya tashi yace
“Ni zan wuce office”, tace ka tsaya kaci breakfast mana
“Karki damu KIM, naci kan na fito”, ta rakasa har mota ya tafi, ita kuma zuciyan ta neh yake bugawa sosai sosai…..

Yana fita a gidan su KIM direct ATAL MEDICAL CLINIC yatafi, dan sun saba da mai asibitin sosai, shineh family docter su, office nashi direct yawuce kuma yayi sa’a yana ciki, bayan sun gaisa doctor baanah yace
“Lafia General Suraj naga hankalin ka duk a tashe”
“Wlh ba lafia ba Doc baanah”, Suraj ya fitar da maganin da ya d’auka a drawer nah Khairiyya ya nuna masa, yace Please wannan maganin na mei neh”
Doc baanah with soo much suprise on his face yace
“What! “Yayi exclaiming, yacigaba
“Ai wannan anti-viral drugs neh, mei kakeyi dashi”, Suraj ransa yayi mugun tashi yace
“Mei kake nufi da anti-viral drugs, please ka mini da yaren da zan ganeh, in details please”, docter yace
“Hmmm Suraj kenan, wannan anti-viral drugs na Human Immunodeficiency Virus wato HIV kenan”, Suraj baisan lokacin da ya tashi a kujera da karfe yace
“What”, ya fara ja da baya yana girgiza kai yana cewa NO NO NO THIS CANT BE HAPPENING, hawaye sharrr yafara, Suraj tunda yasan kansa bai ta6a zub da hawaye ba idan ba lokacin rasuwan mahaifan sa ba, gashi yau yana hawaye, da sauri ya bud’e kofan yafita a office d’in doctor baanah na kiransa but koh sauraran sa baiyi ba, da karfi ya fisga motar shi har zuwa UMTH, office na Doctor Umar direct yashiga, lokacin doctor umar na tare da patient, ganin yanayin abokin sa yace wa patient d’in yajirasa a waje, bayan patient d’in ya fita Suraj ya kama kafan Umar yana kuka yace
“Please tell me ba Gaskia bane, Umar idan bacci nake please ka tashe ni”, Umar ya rungume sa yace
“Abokina nah ba mafarki kake ba, mugode wa Allah baka aure ta ba, mu godewa Allah ba wani abun da ya ta6a shiga tsakanin ka da ita, nine doctor nata, the 1st time da tazo ta fad’a mini bata da lafia, and the way take jin jikin ta nasa aka mata HIV test, sai kuma positive, and everyweek tana zuwa nan kar6an magani, yau ita da Abban tama sukazo”
Suraj kuka yake sosai yana cewa
“WHY KHAIREEYYAH WHY”

Nana fa'ad En Eesha

[11/8, 9:32 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

{Oct, 2016}

 Written by Nana fa'ad En Eesha

[Page 63]

Kuka sosai yakeyi, sai cewa yake

“Khairiyya why, you betrayed me bayan kinsan I love you with all my heart, why Khairiyya, I soooo much hate you now, I hate you I hate you”, Doctor Umar sai cewa yake
“Cool down, Easy guy wannan ba girman ka baneh, kana zaman babban Soja, General Suraj Adam Abubakar, Haba Haba karka bada maza mana please Easy Man”, Suraj yace please kabani file nata Umar
Umar yace “mei zakayi dashi”, Suraj yace da tsawa
“Nace kabani file nata” ran soja ya 6aci, a take Umar yacire file d’in ya mikawa Suraj, Suraj ya kar6a da karfi yafita a office d’in, direct parking space yaje ya shiga motar shi ya fisga ya bar asibitin sai gidan su Khairiyya, a lokacin Abba kuma yafita meeting, cikin main house d’in yashiga, lokacin Haule ce take zaune a parlour, da tsawa yace mata
“Ina Khairiyya”, Haule duk ta tsorata jikin ta yana kakkarwa muryan ta na rawa tace
“Tana d’aki”, da gudu ya hau upstairs zuwa d’akin ta direct, lokacin Khairiyya ta fito a wanka daga ita sai towel guntu iya cinya, bud’e d’akin yayi da karfi har ta tsorata, ganin sa datayi fuskar shi a murtuke idon sa jaa zur yakara tsoratar da ita, neman hijabi tafara dan rufe jikin ta, da sauri tacire hijabin ta a wardrobe zata saka kenan ya warce hijabin a hannun ta, yana mata kallon tsana, Khairiyya wanda tariga ta gama tsorata tayi karfin halin cewa
“Yaya Suraj mei haka, please ka barni kar ka lalata mini rayuwa, mei na maka please yaya Suraj”, tana mai kare jikin ta, da karfi ya zare towel dake jikin ta Allah yasota already tasaka Pant da Bra, yana kallon ta daga sama har kasa, kallon tsantsan tsana, ita kuma Khairiyya sai faman sunkuya wa take, ya rik’e ta gam yaki barin ta tafi, d’aga wa tayi ta wanke shi da mari ji kake Taassssss, tace
“Are you stupid, are you out of senses, How dare ehn, how dare you touch me with your stupid filthy phalanxes you son of the bitch” a take ya saketa, ransa yakara mugun 6aci idon sa yakara jaa zur, yayi wani mugun murmushi yace
“Kin taka sa’a Khairiyya Ibrahim Muhammad fu’ad, you are lucky, kinyi sa’a bana dukan mata, wlh wlh idan badan bana ta6a mace ba da sai na lahira yafiki jin dad’i, kina wani rufe jikin ki, mei zan gani a surar ki, Allah kiyaye, Allah mini tsari da mutane irin ki, Allah ya mini katangan karfe da irinki, kin d’auka wai bazan san gaskia baneh, abun duniya yana 6uya neh, ai koh tona rami kayi ka rufe kanka toh wlh sai yafito, kin bani kunya kin bani mamaki, Khairiyya da kin fad’a mini gaskia da abun ba haka baneh, you betrayed me, I hate you Khairiyya, I sooo much hate you”, Khairiyya wanda tagama zurma hijabin ta har kasa ta juya tana kallon sa ranta idan yayi dubu ya6aci, tace
“Just tell me straight to the point, cin fuskan ya isa haka”, ciro mata file d’in yayi a aljihun sa ya nuna mata, yace
“Mei wannan”, zuwa kan gadon ta yayi ya bud’e drawer da yake saman gadon ya fara cire mata magungunan, ita kanta ta tsorata, tayi looking shocked, bud’e baki tayi tama kasa magana dan abun yabata mamaki, Suraj yace
“Khairiyya kenan, kin d’auka gaskia bazai fito bako, you are mistaken KIM, ki fad’a wa Abbanki gaskian yafito kuma nafasa auren, Hmmm HIV positive indeed, kin gama yawo, kin gama bin maza, at 1st I trusted you completely, na toshe kunne na duk abunda za’azo mini dashi akanki,ashe sune my true friends ke kuma a dushman(an enemy) kinyi sa’a kin taka sa’a,bye Khairiyya bye”, yafita a d’akin ita kuma she was speechless bakin ta ya mutu, duba papers d’in tafara, sunan tane complete da kuma HIV TEST POSITIVE, ga maganin da duk anyi marking har dates

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button