KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

"Sure Damsel Come In, fell free dear"
Tace "ohk"

Ta katse wayan, juyawa wajen su Kamalu tayi tace ku shiga bayan minti d’aya, suka ce an gama Kim
Tura kofan tayi ta shiga, ba laifi gidan tsab sai d’an warin toilet da yake tashiwa, washe hakora yake yana cewa
“Welcome Damsel, welcome”
Ya bud’e mata hannu alaman ta rungume sa
Kau da kai tayi tace “I am tasty”
“Ohhh sorry pls lemme offer you drinks but before then have a seat” nuna mata kujera yayi ta zauna ya bud’e fridge ya ciro faro water da Coke na roba, kan ya ajiye a gaban ta su Kamalu suka shigo gidan
Corper chris sai ganin maza karti yayi akan sa da kayan aikin su, muryan sa na rawa yace
“Who are you, What do u want? “
Kamalu neh ya amsa yace
“Uwaka da Ubanka neh”
Khairiyya ta fashe da dariya Coper chris ya juya yana kallon ta with suprise on his face yace
“Why Kim, Why? “

 Dariyan ta tacigaba tace 

“Ohhh Corper Chris you love catching Fun right, we gonna catch some fun now”
Muryan sa yana rawa yace “what do u mean by that, Please Kim I beg of you don’t do anything stupid”
Su Kamalu bad da yaransa suma sai dariya suke masa dan kusan duka basuji mai suke cewa ba

  Zaiyi ihu Kamalu ya kai masa bugu bakin sa, Khairiyya tace

“Ahswear Chris don’t you dare try that, bamu fara catching fun ba but you are already looking like a fish who has mental issues, ohhh you are such a frickle doodle”
D’aura shi sukayi da igiya mai karfi hannun shi da kafan shi, gum mai karfi suka manna bakin shi dashi
Khairiyya tace “Wow I’m gonna enjoy this”
Shiko duk an d’aure shi ga baki an toshe ba abun da yakeyi sai hawaye
Dukkan su dariyan sa suke Khairiyya tace
“We ain’t even started, save your tears for letter durling”
Zuwa wajen fridge nasa tayi ta d’auko ruwa masu sanyi ta watsa masa a jikin sa, sai shure shure yakeyi, gashin kansa daman yatara gashi irin na gayu Razor Kamalu bad yacire sabowa yasaka sabulu da ruwa akansa yafara masa aski, gabad’aya yabi ya 6ata masa kansa kaca kaca
Wani k’aton bulala Khairiyya ta d’auka ta fara zane shi da bulala tana cewa
“Ohhh I love this, this is fun, no more than that, ohhhh” sanda hanun ta yagaji ta barsa, tace Kamalu mu barsa haka atleast yayi catching Fun yanxu, kuma nasan bai ta6a catching Fun irin na yau ba en it will stuck in his brain forever
Corper dai sai hawaye dan kuka ma bazai iyayi ba dan an rufe bakinsa,Khairiyya tace
“Tell nobody, Idan kafad’a hmmm i’m gonna rip off your head en then feed it to your bitches” taja tsoki

Khairiyya da mutanen ta suka barshi a wajen suka shiga motar su, fitan su a gidan wani yagansu ya shigo da gudu yaga Chris a d’aure, neman wuk’a yayi ya kunce sa ya bud’e masa baki, yace
“Brother Chris what happen”
Kasa magana yayi Chris sai neman wayan sa da yake, yana samuwa ya danna wani numba an rubuta my brother, latsa number yayi yakira
Ana d’aukawa Chris ya fashe da sabon kuka yace
“Broh m finished, some people came en beat me up, don’t allow them out of the gate pls broh, don’t let them go” ya kara fashewa da kuka dan yaji zafin dukan da Khairiyya ta masa, ga naushin da Kamalu yamasa sanda bakin sa ya fashe
Yayan yace “what type of car Chris”
Chris yace “i don’t know lemme ask Gabriel”
Ya juya wajen Yaron da ya taimaka masa yana hawaye yace
“Abeg Gabriel what type of car do you see them with”
Wanda aka kira da Gabriel yana d’an tunani kan yace
“Yes the guys with Odesys en the babe with S-Cross”
A take ya fad’awa yayan nashi, yayanshi d’aga kai da zaiyi ya kalla motan sun kusan zuwa gate d’in, a take ya tashi yana ihu yana cewa
“Don’t let them out” da karfin sa, duk sojojin suka tashi suka tsaya bakin gate d’in sukayi cracking gun (gyara bindigansu) hankalin su atashe duk a zaton su an kawo musu attack neh
Su Khairiyya sai gani sukayi sojoji sun seta bindiga akansu, gaba d’aya sun tsorata

      Nana fa'ad En Eesha 

    07034419520

????????????????????????
[11/8, 9:28 PM] ‪+234 814 173 3262‬: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????

   *[Sept, 2016]*


        Written by Nana fa'ad En Eesha????

{Page 17~18}

        Su kamalu sun tsure, fitsari neh kawai basuyi a wando ba, sai zufa suke duk AC da yake tashiwa a motar, dan su a rayuwar su suna tsoron sojoji balle sunga sunyi cracking bindigan su, d'aya daga cikin boys na Kamalu yace
"Wayyo Allah nashiga uku, wayyo Mamata idan sun kashe mu sun kashe banza fa Kamalu" 

Kamalu kam kasa cewa komai yayi duk jikin sa yana 6ari, ba abun da suke ambato wa sai “wayyo”

   Khairiyya ma tayi mugun tsorata, zuciyan ta sai tafasa yakeyi, sai "Inna lillahi wa Inna ilayhir Raji'un" take nanatawa idan sun har6e tama da sunan Allah a bakin ta

 D'aya daga cikin sojan neh ya tambaye broh na Chris yace

“O’boy what happen, who are they”
Yayan Chris yace
“Sun ma Chris duka” a irin hausan shi da baiyi kwari ba, wasu sojojin tsoki sukaja wasu kuma sun nufa wajen Khairiyya
Tsawa suka daka musu
“Oya come out before we shoot you”
Jikin ta yana rawa ta fito a motar ta su Kamalu ma suka fito, duk kallon ta sukeyi d’ayan yace
“Ba ke bace d’azu kika shiga”
Tace “Yes Sir”
Yayan Chris yace “All of you go on your kneels now”
Duk suka zube kasa, Khairiyya ce tayi karfin hali tace
“Bakusan mei yafaru ba kawai zaku d’aura mana laifi, ni gaskia ba wani kneel down da zanyi, kun san ni wacece?” ba karamin karfin hali tayi ba tafad’a, sai jinjina wa kanta take
Brother na Chris yace
“I don’t care who the hell are you just go on your kneels”
Wasu sojoji suna basa hakuri akan ita mace ce wasu suna zigasa ai ta raina su neh, su Kamalu har sun fara shan duka, wata bak’ar mota ceh had’adde da hilox biyu d’aya a gaba d’aya a baya ya dunno kai zuwa gate d’in, gaba d’aya suka tsaya ba matsowa suka sara wa motoci ukun
Sojan gaban cikin jeep ya fito ya bud’e bayan, wani saurayi neh mei jini ajiki wanda bazai haura shekaru talatin da biyar ba, baza kira sa dogo ba amma shi ba gajera ba madai daici mai faffad’ar kirji da gani yaci gym, kalan sa irin chocolate colour mai kyau, yana da ido daidai da hanci wanda ya dace da fuskar sa, ga bakin shi karami sai saje wanda ya kwanta luff a kyakkyawan fuskar shi, fuska a murtuke ya fito a motar yana kallon Khairiyya da sojojin yace
“What’s happening here”
Duk sun rud’e suka ce
“Nothing Sir”

Ya juya wajen Khairiyya yana kallon ta yace
"What are you doing here"
 Kallon sa Itama take, a jikin uniform nasa taga an rubuta *Captain Suraj a.a*, muryan ta yana rawa dan tayi matukar tsorata dashi tace
"Sir One of them try to rape me, a garin kare kaina shineh yaji ciwo and kuma shineh zasu mini duka nima"

 "What! Ya juya yana kallon su" duk hankalin su ya tashi, ya kara juyawa yana kallon ta, ita kuwa sai zare zaren ido takeyi, yana ganin ta yasan sharri take musu dan shi yana iya ganeh gaskiar mutum da wuri
Yace "you can go now"

Ta juya wajen su Kamalu wanda suka d’an sha bugu tace tashi mu tashi
Ta 6angaren captain Suraj kuma mamaki yakeyi, wannan wace irin yarinya ce karama batajin magana tasa kanta acikin masifa bata tsoron abunda yan iska sojoji zasu mata yace
“Zamu raka ki gida”
Ya juya wajen sauran sojojin yace
“Idan nadawo zakuyi explaining abun da kuke so ku mata, stupid”
Aka bud’e masa mota ya shiga, su Khairiya ma suka shiga motar su, bayan ta suke bi, dan su Kamalu sunyi hanyan su daban, ita Khairiyya zuciyan ta na tsinkewa wai meisa dole sai ya biyo ni neh koh bai yadda da ni baneh, haka dai har suka karaso anguwar su wanda yake Circular Road, daidai tazo gate ta tsayar da motar, ta fita aciki shima Captain Suraj aka bud’e masa kofa yafita
Ya samei ta a inda take tsaye yace
“Ke daughter’n Alh Ibrahim Muhammad fu’ad mai naira neh”
Tace “Eh”
“Be carefull next time dan bakisan da irin mutanen da zaki had’u ba, dan daga ganin ki nasan ke kika ta6o su”
Khairiyya tace
“Nifa ban ta6o suba su suka fara” tana tura baki, hakan da tayi ba karamin kyau ya mata ba, kallon ta kawai yakeyi baya kifta ido, azuciyar shi cewa yake
“Yaa salaam Allah mai iko, irin wannan halittar”
Haka ta karashe maganar yana kallon ta, ita kuwa da ta lura haka ta buga masa hannu tace
“Hea you Suraj, what are thinking”
Yadawo hankalin sa yace
“Nothing, zan na zuwa dubaki In Shaa Allah duk time da nake maiduguri, do take care of yourself please”
Tana murmushi a fili amma can cikin zuciyan ta cewa take mtsw Mallam yi sauri ka tafi dallah na tsana shishshigi, tace
“Ohk I will, bye”
Ya juya zai tafi Itama zata shiga motar ta yace
“emm please can I have your digits”
Tace”sure why not”
Ya mika mata wayar sa ta saka numban ta, a take yayi dialing yashiga, yace save my number please
“Don’t worry I will, thanks” ta shiga motarta ta danna horn da karfi aka bud’e mata gate, shiko yana so ya tambaye sunan ta amma yakasa
Tana shiga gida ta fad’a parlour ta zauna akan kujera tace
“Wayyo Allah what a Day! munyi catching Fun sosai wow” sai dariya take idan ta tuna da Corper Chris da Kamalu yadda suka tsure da sukaga sojoji sunyi cracking bindiga, darawa take kamar wata zararriya, can bayan tagaji tafara ihun kiran masu aikin ta dan da tashigo bata gansu ba, atake duk su ukun suka fito, Khairiyya tace
“Wai bakuji na shigo baneh baza kuzo ku mini sannu da zuwa ba, tukunna ma uban mei kukeyi a ciki”
Duk sun tsorata dan kallon film sukeyi aciki wanda ya d’auke hankalin su basu san lokacin da tadawo ba, Haule neh tayi karfin halin cewa
“Hajiya kiyi hakuri kallo mukeyi bamuji ba”
Kallo ta watsa musu kan tace
“Ya muku kyau toh, Dije mei kika dafa”
“Hajiya pepper fish da soyayyan doya”
“Bana so bazan ciba, had’a mini hamburger da pickles kafin nayi wanka nafito”
“Toh Hajiya angama” cewar Dije
Khairiyya ta juya wajen Indo tace
“Ki gyara mini d’aki nah na upstairs zan koma can yau so kikai mini duk abun da is important can d’akin nagaji da kwana a kasa”
“Toh Hajiya” cewar Indo
Ta kara juyawa wajen Haule tace “had’a mini ruwan wanka yanxu” itama Haule ta fice

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34Next page

Leave a Reply

Back to top button