KHAIREEYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Inna lillahi wa Inna ilayhir Raji’un Abba yaketa nanata wa, Abba idon sa yayi jazur, hankalin sa ya tashi yace
“Thank you Doctor, Ngd Sosai”
“Karka damu Alhaji, akwai wani friend nawa a can zan had’a ku, you don’t have to worry”, Abba yace
“Nagode”
Washegari an gama arranging komai, ba jirgin da zaibar Maiduguri amma ya biya kud’i sosai dan akaisu Lagos, da Abba, Ummi da Ammar suka d’aga zuwa Lagos, Ammar ba abun da yake sai kuka, tun Ummi tana lallashin shi har tagaji, Khairiyya kawai yake kallo, wanda take kwance kamar gawa bata koh motsi, sai Oxygen dake hanci da bakin ta
Zilyadeen neh a cikin Nakowa hospital ya birkice musu shi dole ina suka kai Khairiyya, duk doctors d'in sun nuna masa basu sani ba cos Abba yayi warning nasu kar kowa ya bada Information akan Khairiyya, Zilyadeen zama yayi a kujeran dake cikin reception Unit na asibitin yana hawaye yana cewa
“Khair kiyafe ni, nasan ni na jefa ki a wannan halin, i love you khair i am so sorry for not trusting you, but you mean everything to me, i promise na rantse da Allah idan kin samu sauki zan baki all the happiness khair, zan nuna miki tsantsan So da Kauna, zan baki farin ciki”
????????????????????????
Nana fa’ad En Eesha
[11/22, 11:49 PM] +234 806 524 6449: ????????♡♡♡♡♡♡
????????????????KHAIREEYYAH????
☆☆☆☆☆☆☆????
{Nov, 2016}
Written by Nana fa'ad En Eesha
[Page 69
]
India
New Delhi
Abba da Ammar neh zaune, kowa da abun da yake sakawa a ransa, ganin indicator bulb ya nuna green light na dakin da ake mata treatment da sauri suka tashi, Wani d’an India neh da labcoat a jikin sa da handgloves da gani doctor neh, Abba yace
“How is she Doctor”, Doctor yace
“Successful, can you please met me in my office”, Abba yace Sure, bayan kamar minti goma Abba ya samei Dr Mehra a Office nasa, Dr Mehra yace Zata iya samun sauki but akwai matsala, Abba yace menene matsalan, Dr Mehra yace
“Her Kidney is damaged”, Abba atake yayi gumi, Dr yaciga da cewa dole sai an mata Kidney transplant, dan duk gaba d’aya kidney ta sun samu matsala, idan ba damuwa za iya cire na Abba a saka mata, and kuma gaskia idan ta tashi ba lalle baneh tayi recognising naku cos she lost her memory, duk wannan maganan da turanci yake irin nasu na ‘yan India
Abba atake jikin sa ya d'au zafi, Inna lillahi wa Inna ilayhir Raji'un yake ta nanatawa yace wa Dr Mehra
“I wish I can donate her mine but unfortunately I can’t”, Dr Mehra yace
“But why, are you sick or something”, Abba yace koh d’aya, nima Kidney d’aya neh ajiki nah, yana fad’a yana hawaye, Dr Mehra yace karya damu zai duba if akwai wani available sai su siya, Abba ya masa godiya ya fita a office d’in
A daddafe yana dafa jikin bango har ya isa inda Ammar yake, Ammar ya rik’e sa yace
“Abba lafia, mei doctor yace”, Abba yana zub da hawaye yace
“Ammar Kidney (Qoda) ya samu matsala, and you know nima d’aya nake using I can’t donate her nawa”, Ammar zuciyan sa ya buga, yace
“Abba ka manta kana da ni, Khairiyya sister tace, ba abun da bazan iya mata ba, why not a duba ni sai a bata kidney na d’aya”, Abba ya girgiza kansa yace
“No baza muyi haka da kai ba Ammar, akwai kudi zamu samu In Shaa Allah”, Ammar yace
“Toh Abba yaushe zamu samu, idan har dagaske ka d’auke ni kamar d’an ka na cikin ka toh kawai ka yarda na bada nawa”, dakyar da kyar Abba ya yadda akan Ammar zaiyi donating nashi
Bayan an gama screening Ammar, duk wasu tests an masa and komai nashi is normal zai iya mata donating kidney shi, Operation akayi aka cire kidney nasa d’aya aka dasa mata and Alhamdulillah everything was successful sai dai har yanxu Khairiyya she’s in coma koh motsi bata iyawa, Ammar shi baiji sauki ba har sai kusan bayan wata biyu, yaji sauki sosai, kullum yana nan manne da KIM, addu’a yake mata safe rana dare
After 6 months
Ammar zaune akan kujera a d’akin da akayi admitting Khairiyya, tun lokacin da tayi hatsarin har yanxu bata farka ba, jin motsin da yayi yasa ya bud’e idon sa, Khairiyya ce ta tashi sai kokarin cire drip da aka sa mata take, da sauri ya matso kusa da ita yace
“KIM ki bari karki cire kinji please”, zare ido tayi tana kallon sa, shi kuma a take ya danna emergency call yace I need help help please, call the doctor
Khairiyya kallon sa take koh kifta ido batayi, Doctors neh da Nurses suka shigo d’akin suka duba ta, bayan sun duba ta suka ja Ammar gefe d’ayan Doctor yayi congratulating nashi yace yanxu ta tashi ba matsala sai dai tayi loosing memory’n ta but zuwa few months zata zama normal, Ammar ya musu godiya suka tafi
Zuwa yayi ya samu Khairiyya, kallon sa still take tace
“Who are you”, Ammar yayi murmushi yace
“Ni yayan ki neh”, girgiza kai tayi tace
“Kai ba yaya na baneh”, sai ta fashe da kuka, daidai nan Abba yashigo d’akin, da murnan sa yashigo yace
“Baby nah sannu”, kallon Abban take shima, tace
“Who are you”, Abba baiyi mamaki ba yace
“I am your father, your Dad, Abban ki”, Kawai sai ta fashe da Kuka tace
“Father kaga wannan ba”, tana nuna Ammar da yatsa, Abba yace
“Mei yamiki”, Khairiyya tana tura baki tace
“He said that shi Yayana neh”, Abba yayi murmushi yazo kusa da ita ya shafa fuskan ta yace
“Yayan ki neh mana, bakiga kuna kama ba”, zaro manyan idon ta tayi tace
“You mean ina kama da this Monster”, Kawai sai ta fashe da kuka, tace
“Father wlh bana kama dashi, kace bana kama dashi”, Abba yace
“Shhh baby nah, bakya kama da wannan Monster d’in kinji”, ta sauke numfashi tace
“Thank God, Father see his long face, bulky eyes, colourful lips, nose like like”, ta rasa abun fada sai ta nuna dogon yatsan hannun ta, tace his Nose like wannan long finger nah, he is a monster father
Abba yace “yi shuru baby kinji”, Ammar shi kallon ta kawai yake, ya zagaya ya fita a d’akin kawai sai hawaye, yace
“Bazan iya kallon ki a cikin wannan halin ba KIM, I love you”, haka ya gama kukan sa ya koma d’akin, a lokacin Khairiyya tayi bacci, Abba yace take care of her Ammar, tafiya ya kamani zuwa Dubai, Zaynab ma tana hanya yau zata shigo India,Ammar yace In Shaa Allah Abba
Wasu Nurses neh suka shigo d’akin suka cire mata duk wasu drips na jikin ta suka kara mata allura, d’aya daga cikin nurses din tace wa Ammar yanxu kam tasamu sauki In Shaa Allah, Ammar ya musu godiya
Washegari da safe
Khairiyya ta bud’e idon ta a hankali, sai kalle kalle take, cak ta tsaya da ta kalla Ammar da yake kwance, ta tashi a hankali har ta iso inda Ammar yake, kallon sa take sosai ba koh kifta ido, tun daga dogon bak’in gashin kansa, gashin giran sa bak’i wanda ya kusan had’ewa, dogayen eye lashes nashi, dogon hancin sa, pink lips nasa, da sajen sa, hannun ta ta d’aga ta shafa fuskan shi, ta kara kai hannun ta taja dogon hancin sa, da hankali ya bud’e idon sa, ganin ta da yayi baisan lokacin da ya tashi ba, itama taja baya, Ammar yace
“KIM mei kika mun”, ita kuma sai ja da baya take tace
“So sorry monster”, Ammar ya girgiza kansa yace
“Ni ba monster baneh, come close”, sai ta kara ja da baya, ya kara cewa
“Bazan miki komai ba, ni ba monster baneh come dear”, sai ta kara ja da baya, Zaynab ce ta shigo d’akin da sallama, da gudu taje ta rungume Ammar tace
“Yaya Ammar wata takwas, eight good months ban ganka ba, gaskia nayi missing naka sosai”, yayi murmushi yace
“I miss you too”, Zaynab juyawa tayi taga KIM, da gudu taje ta rungume ta tace
“I miss you sis, I miss you soo much, ya jiki”, Khairiyya tana kallon ta baki bud’e tace
“Ce miki akayi bani da lafia, who are you ma”, Zaynab ta kama hannun ta tace
“Kin manta Zaynab ce, your durlin Sis”, Khairiyya ta tura bakin ta tace
“Ya kina kama da that Monster”, juyawa Zaynab tayi ta kalla Ammar sai ta fashe da dariya tace
“He is not a Monster, he’s your brother KIM”, Ammar yace
“Yawwa yanxu kin yarda”, Khairiyya ta d’aga kanta alaman Eh ta yarda