BABBAN YARO BOOK 1 COMPLETE NOVEL
Fuskarsa na kalla naga ya sha kunnu sosai yace.” Saboda kina da lasisi a garin kano kin gagara kina da d’aurin gindi gorin shawagabbanin k’asa kike wannan ikirarin a kaina duk abunda zakiyi kije kiyi ina nan ina sauaran ki. Ya cigaba da cewa.” Ni duk abunda zanyi ado ne a gare ni ke kuwa fa? Ke zaki barwa kanki tarihin abun fada da ‘yayan ki da jikokin ki, babu ruwana ina zaune kika kawo min kanki har gidana kina rigima da Masu gadi dole sai kin shigo hakan bai ishe ki ba ki shigo min har bedroom.” Ya saki wani guntun murmushi yana dan shafa sajansa ya cigaba da cewa” tun farkon zuwan ki da abunda ya faru a tsakanin mu ina da vedion sa so tunda kin ce haka ma gobe idan Allah ya kaimu zan watsawa duniya su san ke wacece, in yaso sai kiji dadin d’aukar mataki.” Kuka na fashe da shi sosai tare da mik’ewa tsaye! Nace.” Idan baka futa da vidio ba baka kaunar Allah baza ka nuna min cewa kai d’an halak bane sai naga vedio nan na yawo a duniya sannan zan yadda da tacewar ka a fanni bariki,.” Na k’arashe maganar ina gunjin kuka lokacin ji nake ina ma zan samu abun duka Dana dunga dukan shi ko na samu zuciyata tayi sanyi daga azabar da ya gana mata. Gani nayi ya kwanta plate kan bed din yana lumshe idonsa Sam! Abunda nake ma be dame shi ba.” Da sauri na dauki pillow na jefa masa da k’arfi! Ya bude lumsassun idonsa yana kallona a zuciyarsa yake fadin” wannan yarinyar ‘yar bala’i CE, da alama tafi ni bala’i. D’aya pillow na d’auka na jefa masa da k’arfi nace.” Yau zaka San ka tab’owa kan ka bal’ai.” Dressing mirror d’insa na nufa ina rangaji ga bedshirt nan nad’e a jikina yana hard’e ni, kamar zan fad’i na fara d’ebo kwalayen turaran shi had’e da kwalabe robobin mayukan shi cream and lotin kamar wata mahaukaciya nayi kansa na fara jefa masa su ina aibata shi tare da cin alwashi a kansa iri-iri, in ka gani a lokacin zaka ce sai na rasa ruwan hawaye saboda yanda suke kwarara.
Da sauri ya mik’e ya dura daga k’asa dariya yake sosai yana Neman hanyar guduwa tare da fad’in”Lallai ashe da mahaukaciya nake zaune ban sani ba.” Kofar ya nufa da sauri yana lalube key jikin 3quoer din dake kasan jallabiyar jikinsa nan ya b’oye shi,, na bishi da gudu ina jifansa tare da fad’in” baza ka San da mahaukaciya kake zaune ba sai ranar da nayi maka illah a RAYUWAR ka.”
Da k’yar ya ciro key d’in ya bud’e d’akin ya futa, kafin ya ja kofar ya rufe ni nayi wuf!! Na futa, na cigaba da dukan shi da abubuwan da suke hannuna ina kuka kamar babu gobe, nace.” Dama kace sai ka sani kuka to ka sani kaji dad’i hakkina kuma da ka d’auka Allah ya isa ban yafe ba.” Kare jifan da nake masa yake da hannunwan sa, Sam!! Baya so ya kara kusanta jikinsa da yarinyar shiyasa ya kasa d’aukar mataki a kanta, amma yana ganin dole sai yayi hakan sannan zai samu ya shawo kanta, da sauri ya matse ta jikin kofar tare da kafe ta da lumsassun idonsa masu dagula wa mata lissafi, wani irin cool voice yayi amfani dashi gurin yi mata magana, Yace.” Kiyi mana shiru!! Ko bakin San dare bane? Hummm ok tunda ba kyaso in futa da vedio bazan futa dashi ba shikkenan, amma nima kar ki k’ara zuwa inda nake, ban sanki ba baki sanni ba, kowa yaje yayi sangar shi, kikara kara zuwa inda nake to ranar za muyi fad’an k’arshe dake kuma in futa da vedio na abunda ya faru a tsakanina dake, saboda haka babu ruwan ki dani.” Ya k’arashe maganar tasa tare da d’an hura mata iskar bakinsa a fuskar ta.
Asma’u ta shiga wani yanayi Wanda idan ba Allah ba babu Wanda ya isa ya futar da ita daga cikinsa sai shi Wanda yayi silar shigar ta yanayi Amjadu ko be fad’a cewar ta futa daga sabgar sa ba ya zama dole ta futa daga sabgar sa saboda ta gano tarayyar ta dashi bata da wani amfani dole tayi nesa dashi da rayuwar sa.
Miyau na kalato na tofa mishi ya sauka gefan bakinsa nace.” Ni sake ni ko ka kafad’a ko baka fada ba dole in futa daga sabgar ka, yanzu ma abunda ya kawo ni gidanka in dauki handbag dina shikkenan saboda tsabar mugunta ka kulle ni a daki a kori ‘yan uwana, kar ka manta da cewar nayi rantsuwar sai na dauki fansar abunda kayi min”.
Girgiza kansa yayi kawai yana sakin wani miskilin murmushi abunda yake gudu shi ya afku a halin yanzu babu abunda yake mutukar sha’awa illah yaga yana tsotsar bakinta shiyasa tun farko yak’i kusantar ta duk wasu zantukan ta da takeyi na shirme ne Sam basa gabansa yasan duk kuri take da nuna ita lallai kar yaga damarta don haka be dame shi ba.
Lumshe idonsa yayi had’e da tallafo fuskar ta babu zato taji bakinsa cikin nata. Damtse bakina nayi tare da cije hak’orana ina ture shi. Hannusa ya zura cikin bedshirt din yana shafo mazaunai na, take na bude bakina, zan kurma ihu! Hakan ya bashi damar cafko harshen ya ya fara tsotsa kamar Wanda ya samu sweet.
Bedshirt din ya silale ya fad’i k’asa jikina yayi lub’us babu jarumta ta ko ta kwabo a tare dani, ina ji ina gani ya d’auke ni cak ya shiga dani bedroom din ya shimfid’e ni kan bed tare da yi min rumfa da faffad’an k’irjinsa ya jigaba da yin kissis dina, ni kuma nakasa tab’uwa kaina komai domin in kwaci kaina lumshe idona kawai nayi ina jin shigar wani yanayi me wahalar fassawara a jikina.
Amjad ya gane abunda yake damun yarinyar kenan shiyasa ta gaza hakuri take ta neman fituna dashi, ya lura yarinyar tana da mutukar k’arfin sha’awa Wanda irinsu ne idan basu samu jajurtattun maza ba suke shiga wani hali, ya zame masa dole yayi nesa mutuka da ita saboda a zuciyarsa na mutukar tausaya mata lura da yayi da rashin galihu gami da taulaci a tare da ita, idan wani Abu ya afku a tsakanisa da ita mahaifiyar ta tana iya shiga wani hali,ita kanta yarinyar tana iya shiga wani hali yanzu k’uruciya CE kawai take damunta Babban abunda ya fi kamata da ita shine kawai tayi aure ta huta Idan ba haka ba rayuwar ta tana iya shiga cikin wani irin hali.
Kissing din ta yayi sosai ya rage wa kanshi zafi sannan ya sakar mata bakinta gami da sauka daga bed din ya futa daga dakin ma gaba d’aya ya kulle ta da key, ya gwammace ya kwana a parlor domin gujewa abunda kan iya zuwa ya dawo.
Nafi minti goma tun bayar futarsa ban iya d’aga ko da Dan yatsa na guda ba, idona a tsaye k’am! Yana kallon rufin dakin. Na ma rasa wane irin tunani zanyi, jiki a sanyaye na mik’e zaune ina duba jikina babu komai sai briziya itama da ita gwara babu tunda duk ga nonowana nan a waje sun fito pant kuwa dama tuni an share babin sa, wato d’azu bedst din na saki a kasa ban sani ba, wasu hawaye suka zubo min masu zafin gaske, muryata na karkarwa nace.” Ka zame min annoba a rayuwa ta, ya zama Dole inyi nesa da kai ya zama dole Ubangiji ya bimin hakkina daka d’auka nayi da na sanin saninka a rayuwata yau nayi dana sanin zuwana wannan duniyar, Ya Allahu ka yafe min, astagafirullahi Allah.”!!!!!!
Na k’arashe maganar ina sakin wani marayan kuka na tsantsar tausayin kaina.
Sai da nayi kuka me isata sannan na mike a daddafe na shiga toleit d’insa na hada ruwan zafi sosai na fara Wanka tsarki inayi ina kuka tare da nadamar abunda na aikata nace” Ubangiji kai ka hallice ni kasan ba laifina bane Kaine ka hallice ni da wannan hallitar ya Allah ka saukaka min, Wanka nayi sosai da soso da sabulu na futo ina matse fuska tsayuwa nayi tsakiyar dakin ina tunani rigata dai ya yaga min, tunani na ya bani in bude cikin kayan shi ko zan samu irin duguwar rigar da ya bani farkon zuwana gidan shi, wardrobe din na nufa na fara kici-kicin budewa tana budewa na fara ware ido kaya ne ko ita ina na lura ko wane kayan sawarsa a kwai b’angaran sa, da k’yar na hango wasu tarin ledoji daure wasu kan wasu na fara birkitosu Allah ya bani sa’a na ciro wata a baya irin ta mutan Saudiya bata da ado sosai sai kad’an kamar bubu take na zura a jina na dauki sabon hijab me hannu had’e da nikaf shima na farke daga ledar sa, kan dadduma na nufa domin yin sallahr magariba da isha Wanda suka wuce ni. Bayan na idar sosai na kaskantar da kaina gaban Ubangiji INA rokonsa da ya yafe min kuma ya yaye min damuwa ta, kwanciya nayi kan abun sallah ina lumshe idona tare da tunanin ko a wane hali su Mimi suke ciki oho dadin da naji kawai Mimi bata koma gida ta koma gidan su Munnu nasan k’aryar da zamuyi wa Umma cewar a gudansu Munnu muka kwana. Haka na dinga sak’e sake gami da zancan zucci har aka fara kiran sallahr asubah na mike da hanzari ina shirin shiga toilet din naji yana k’okarin bude kofar dakin, komawa nayi na kwanta had’e da takure jikina na rufe idona ruff nayi rantsuwar har in bar gidan magana tafarar baki baza ta kara hadani da shi ba, ya shigo a hankali INA jinsa ya tsaya a kaina tsawon minti biyu sai naji wucewarsa na bude idona a hankali naga ya nufi toilet nasan alwala zai dauro, motsin ruwan da yayi yawa ne yasa na fahimci cewar Wanka yake, minti goma yayi ya futo da sauri jin ana k’okarin tada sallah wasu sabbin kayan ya sanya jallabiya da gajeran wando ya futa daga d’akin nasan masjid ya nufa, nace” kullum cikin tsoron Allah amma a gefe guda ana aikata sab’on Allah.”