CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Da yamma Junaid na kwance palon Mumy bayan ya dawo aiki idonsa lumshe kamar me bacci sae dai ba baccin yake ba, Mumy kuma na kitchen tana ta girke girke don ranan Abba xae dawo, Bude kofar da aka yi ya sa shi bude ido, El-Ameen ya shigo palon da sallama, kallonsa kawae Junaid ke yi bae ce komae ba, El-Ameen ya karaso palon yace “Capt A.jay Murnai!” Da xolaya ya kare kiran nasa, Junaid ya mike xaune yace “Uhm!” Kitchen El-Ameen ya nufa ya tsaya daga bakin kofa yace “Ina yini Mumyna” juyawa tayi tana kallonsa tace “A’a Ahmad yaushe ka shigo?” yayi murmushi yace “Yanxun nan Mumy, ya gida ya aiki” tace “Alhmdllh, ya Hajiyar ka?” El-Ameen ya karasa shiga kitchen din ya mata side hug yace “Tana lfya Mumy, tace a gaishe ki” Mumy tace “Ina ta sa rana xan je can gidan ku Allah bae yi ba” El-Ameen ya sa hannu ya dauki daya daga kajin da take soyawa yace “Bari in d’an d’ana maki ko gishiri ya ji Mumy” dariya tayi tace “Naga alama” ya wara ido ya fice daga kitchen din yana murmushi, gefen Junaid ya xauna yana cin kaxar Junaid xae yi magana aka bude kofa, Hajja ce ta shigo palon da sallama, El-Ameen ya wara ido ya boye fuskarsa bayan Junaid yace “Kai yaushe Hajja ta xo?” Hajja ta cire glass din idonta tana leken El-Ameen tace “Wannan ba gantalallen nan me sunan ka bane Amadi?” El-Ameen yayi dariya yace “Ehh Nine Hajja, ashe kin xo, ae bae gaya min ba” Hajja tace “Toh ko ya gaya maka xuwa xa ka yi, kar ka manta turare ne fa yayi mani iyaka da kai, daga nace ka siyan turare na xama makiyiyar ka, toh Allah yayi mana tsari da irin ku” dariya sosae El-Ameen yayi, Junaid yayi murmushi yana canxa tashan tv, Hajja ta xauna tace “Har yanxu Muhammad din bae iso bane?” Mumy ta fito daga kitchen tace “Kila sae xuwa magariba Hajja” mikewa Junaid yayi ya kwashi wayoyinsa yana kallon El-Ameen yace “Mu je” El-Ameen ya mike, Hajja tace “Au don na shigo shine xa ku watse” Junaid ya balla mata harara yace “Da’alla! Rikicin tsufa ya maki yawa wllh” El-ameen yace “Kyalesa kawai Hajja ta so mu je kar ayi ba ke” Junaid yace “Allah kar ta xo min don rufe kofata xan yi” daga haka ya nufi kofa, El-Ameen ya bi bayansa yana dariya, ta tsuke fuska ta bi su da kallo tace “Wahalallu ko uwar me xasu ban da Allah bai ban ba, kuma naga dai gidan d’ana ne yau nace duk ya kora ku wllh ta xauna!” Mumy tayi murmushi ta koma kitchen. kwanciya El-Ameen yayi a palon Junaid yace “Kana ji na Capt?” Junaid yace “Ina jin ka.” “xa ayi diagnosing din patient din ka don in san irin neurological disorder dinta da treatment din da ya kamata in mata, nd dat’s money!” Junaid ya dauki remote din hannunsa yayi powering din Tv yace “Aiit! Nawa ake bukata?” El-Ameen ya mike xaune yace “ka turo dubu dari tukun mu ga” Junaid yace “Ohk I will transfer it ltr” El-Ameen yace “Gud! Ko gida xan sa a xo ayi diagnosing din nata, no need of taking her out” kai kawae Junaid ya gyada masa, “Kaga daga nan sae mu san irin uban kudin da xaka kashe” da xolaya El-Ameen ya kare maganar, Junaid yayi murmushi bae ce komae ba.
Haske Writers Association
⚓ Captain_Ahmad Junaid⚓
_By Khaleesat Haiydar_
10….
Har Abba ya dawo bayan magrib El-Ameen na gidan, suna gama cin abinci da Junaid suka tafi palon Abba a tare don yi masa sannu da dawowa, Hajja na xaune palon da Hajiya da Umma, Humainah da fatima ma na xaune daga gefen Abba dake ta sauraran xancen da mahaifiyarsa ke masa, khadija da sadiya step sister dinta ma duk suna xaune palon, junaid da El-Ameen suka samu waje suka xauna, El-Ameen ne ya soma yi ma Abba sannu da xuwa ya gaishesa, Abba ya amsa murmushi dauke fuskarsa yace “Kana lfya son? Ya aikin?” El-Ameen yace “Alhmdllh Abba, ya hanya?” Abba yace “Alhmdllh mun gode Allah, jiya mun yi waya da Alhaji Mahmoud yace xae tafi Germany gobe” El-Ameen yace “Ehh gobe xae tafi” Abba yace “Maa sha Allah, Allah ya tsare” Junaid ya kalli Abbansa yace “Barka da dawowa Abba” Abba yace “Yauwa Ahmad, how yhu?” Junaid ya shafa kansa yace “Alhmdllh Abba, ya hanya?” Hajiya ta d’an tabe baki ta mike, Umma ma ta mike ta fice daga palon. Hajja ta bi su da kallo sannan tayi tsaki ta maida dubanta kan Abba tace “Ni dai Muhammadu matan nan naka basa min abun arxiki wllh, tun da na xo ko ruwan su ban gani ba sai daxu da safe, Amina kadae ce ‘yar arxiki take ta dawainiya da ni” siririn tsaki can kasa Sadiya ta ja tana hararan Hajja ta gefen ido ta mike ta fice daga palon. Murmushi kawae Abba yayi ya maida dubansa kan Humainah dake gefensa a kasa yace “ya karatu Humainah? Ss3 xaki yanxu koh?” Hajja ta karbe tace “Ehh ajin karshe xata, tana gamawa sae a hada aurensu da Amadidi sai taje can ta kare karatun a gidansa” da sauri Junaid ya kalli Hajja ya wani hade rae, ita ma Humainah kallon Hajjan ta ke kamar xata yi kuka, El-Ameen ya fashe da dariya, Abba kam murmushi yayi ya kalli Humainah da har hawaye ya cika idonta yace “Kyale Hajja dotana, wanda kike so xa a aura maki kin ji, kuma sae kin fara jami’a ma xaki yi auren,” tana goge hawayenta tace “Toh Abba” Junaid ya harari Hajja da ta sake baki tana kallon Abba ya dauke kai, Abba ya kallesa murmushi dauke fuskarsa har lkcn yace “Ae ni baxan ma ‘ya yana auren dole ba Hajja, duk abinda suke so shi mu ma xa mu so,” murmushi Junaid yayi ya mike yana kallon Hajja da ta wani hade rai, ya kalli El-Ameen yace “Tashi mu je” El-Ameen ya mike yana dariya suka yi ma Abba sallama suka fita daga palon, Hajja tayi kwafa tace “Toh zan ga ko kai ka haifeni kuwa,”
Bakin mota Junaid ya raka El-ameen yace “Gud nyt!” El-Ameen yace “Aitt, saura kar ka xo can gidan gobe!” junaid yayi murmushi bae ce komai ba, sai da El-Ameen ya ja motar ya bar wajen snn junaid ya juya ya koma gida. Part din Mumy ya shiga ya tarar tana bathroom ya fito ya nufi nasa bangaren.
Washegari ya kama Sunday Junaid na gida baya duty, kwance yake palon sa misalin Karfe goma da rabi na safe Khadija ta shigo palon, kasa ta xauna kusa da kujeran da yake tace “Gud morning ya A.jay” yace “Morning baki je islamiyya bane” tace “daxu ae anyi yayyafi shine Abba yace in bari gobe,” yace “Keep quiet ba cikin ruwan fatima da Rabi’a suka tafi ba, ina ga gishiri ce ke koh, continue deceiving ur self” shiru ta dan yi tana turo baki sae kuma tace “Ae da yamma xan je” bai tanka ta ba, tayi kasa da murya tace “Yaya dama plss 5k xaka ban xan siya wani takalmi ne plss” wani uban harara ya watsa mata yace “Tashi ki bar min Palo, ke baki da aiki sae dae a baki kudi, beside kije ki samu Abba mana, get out my frnd” marairaice masa tayi tace “Don Allah fa yayana” xae yi magana aka bude kofa Suhaima ta shigo palon cikin wasu shegun English wears lokaci daya wani shegen kamshi ya bade palon, mikewa xaune yayi yana kallon Khadija yace “Naji! naji tashi ki tafi” Khadija tayi murmushi tace “Yauwa ya A.jayy nagode” ta mike ta hade rai tana kallon Suhaima tace “Toh ae sae mu je koh” wani kallo Suhaima tayi mata tace “Wa kike gaya ma haka” Khadija ta ja tsaki tace “Duk inda mutum yayi sae ayi ta bin sa da’alla” bata rufe baki ba Suhaima ta fixgota ta sauke mata mari, Khadija ta dafe kunci tana kallonta, mikewa Junaid yayi ya karaso ya bude kofar ya fixgo Suhaima ya wulla ta waje cikin kakkausar murya yace “Kada ki sake taba ta” Umma dake balconyn ta xaune tare da Hajiya ta mike da sauri ganin abinda ya faru, Hajiya ta bi bayanta da sauri ita ma, a fusace ta karaso bangaren Junaid tana huci tana kallon Junaid dake tsaye bakin kofa har lokacin tace “Kai Ahmad uwar me tayi maka xaka jefota haka kamar pillow?” Suhaima ta fashe da matsanancin kuka, hakan ya kuma harxuka Umma cike da masifa da bala’i tace “Ba magana nake maka ba” kallonta kawai yake bai ce komai ba, idonta ya kankance don fitina ta juya tana kallon Suhaima tace “me ya faru, me kika yi masa?” Suhaima na matsar kwalla ta gaya mata, Umma ta xaro ido tana kallon Khadija dake tsaye bayan Junaid a tsawace tace “ke har abun farin cikin ki ne bare yayi ma ‘yar uwar ki wannan cin mutuncin Khadija, to don uwar ki fito kar in karya ki palon nan, Shegiya me halin banxa, fito nace” Hajiya tace “Ke dae sallamammiya ce wllh khadija, munafuka wawiya kawai” Hajja ce ta leko jin surutai, ganinsu tsatstsaye part din Junaid ta fito da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru, ko kallonta su Umma basu yi ba, Umma na kallon Khadija tace “baxa ki fito ba sae na maki lahani a palon nan?” A fusace Hajja tace “Yau na ga bala’i, ta ya xa ki ce ta fito palon d’an uwanta, ke kin isa ki shiga tsakaninsu?” Hajiya ta tabe baki ta dauke kai, Hajja ta karasa balconyn tace “Me ya faru khadija?” Khadija tace “Wae fa Hajja Suhaima ce ta mareni shine ya Junaid ya koreta palon, shine fa take kuka haka” Hajja ta xaro ido tace “Ta mare ki? Toh Muhammadu ya fito ayi ta ta kare yau, duk ko wannensu ya kwashe agololinsa a gidan nan don ba gidan ubansu bane nan din, shima maganinsa knn da auren xawarawa, haka kawae xa a sa mashi ‘ya ya a gaba, kuma bari kiji abinda baki sani ba Bilki, wllh Khadija ta fi kusanci da Ahmadu a kan da warcan bakar yar taki a gidan nan, don uba daya ba wasa bane” ae sum sum Hajiya Fatee ta bar wajen, Mumy ce ta fito jin hayaniya ta karaso da sauri tana tambayar abinda ya faru, Hajja ta shiga mata bayani cikin fada, shiru Mumy tayi tana kallon Junaid, Umma ta fixgi hannun Suhaima suka bar wajen tana huci, Hajja tace “haka kawae, xata kawo mana agola a gida ta adaddabe mu, ita ma wancan mai kama da kutaren ma haka ta kawo nata agolar, duk an cika masa gida da agololi,” juyawa tayi tana kallon Khadija tace “Toh wllh ki rike d’an uwanki, don shine dolen ki kuma kun fi kusanci da shi akan wancan bakar don uba daya ba wasa bane” tana kai wa nan ta nufi bangarenta kamar xata tashi sama, Humainah dake tsaye balcony tana kallon film din sae dariya take, Fitowa Khadija tayi daga palon ta bi bayan Hajja don tasan ko hauka take baxa ta nufi sashinsu yanxu ba, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta karasa cikin palon Junaid ya bi bayanta, a hankali ta soma magana tace “Ahmad ina raba ka da shiga tsabgan mutanen nan baka ji koh, ba sonka suke ba kai kanka ka sani, ina ruwanka da shiga tsakanin Khadija da ‘yar uwarta?” Junaid yace “Marinta fa tayi Mumy” Mumy tace “koma dai meye ni dae ka kiyaye su bbu ruwanka da su, tsakanin ka da Khadija daban tsakanin Khadija da Suhaima daban” yace “Toh shknn Mumy kiyi hakuri,” juyawa tayi ta fita daga palon, ya koma ya xauna yana kallon agogo don duk ya kagu ya fita xuwa gidan El-Ameen. Har bacci ya fara daukansa yaji ana buga kujerar da yake kwance kai, ya bude ido da sauri ya ga Humainah tsaye kansa, mikewa xaune yayi, ta rufe bakinta da hannu tana ‘yar dariya tace “Dama haka kake bacci baki bude” shafa kansa yayi yyi saurin fixgota ya xaunar da ita kasa, kara tayi tana kiran Hajja, ya hade rai yace “me ya shigo da ke Palo na?” A rikice tace “wllh Abba ne yace in kira ka” yace “A bude kika ga baki na?” Da sauri tace “A’a wasa nake” daga hannu yayi kamar xae kai mata duka ta boye fuskarta tana kiran Hajja, ya saketa yace “Ashe fitsarar ta karya kike yi” shiru tayi bata ce komae ba, ya mike ya nufi kofa, ta bi sa da harara, yana fita ta sa dariya, mikewa tayi tana kare ma palon kallo ko ina tsaf kamar na mace ga kamshi ya kama palon sosai, bedroom dinsa ta nufa, nan ma very neat ta rike kugu tana bin ko ina da kallo ganin how over tidy it is ga kamshi me ddi dake tashi, ta nufi gaban madubi tana kallon turarruka masu tsadan gaske dake jere gaban mirrorn, daukansu ta shiga yi da daddaya tana fesawa don jin irin kamshin su, kala biyu ta dauka ta fito daga dakin da sauri ta fita daga palon ta ja masa kofa, part din Hajja tayi da saurinta. Junaid na xaune kasan lallausan rug din palon Abbansa yana kallon Abban nasa da mamaki jin abinda yake cewa, juyawa yayi ya kalli Umma da ke xaune ta sha kunu palon ga Suhaima ma xaune kasa, Junaid ya lumshe ido don ko kadan bae son a laka masa sharrin abinda bae yi ba a hada sa da mahaifinsa, cikin fada Abba yace “Kana jina kayi shiru Ahmad?” Bude ido yayi a hankali yace “Kayi hakuri Abba hakan baxae kuma faruwa ba in’sha Allah” Abba yace “kasani daga yau matsayin Suhaima daya da na khadija wajen ka, kar in kuma jin wannan shirmen, ashe baka da hankali ban sani ba” a hankali Junaid yace “Kayi hakuri Abba” Abba yace “Xancen banxa kake yi, kuma ka bata hakuri yanxun nan” juyawa yayi yana kallon Suhaima da idonta ke kansa ko kifta wa bata yi yace “Kiyi hakuri” tayi kasa da kai tace “Ya wuce” Abba yace “Tashi ka ban waje” mikewa Junaid yayi xuciyarsa na kuna ya fice daga palon. Part dinsa ya nufa yana shiga Palo yasan an shiga bedroom dinsa, ya karasa bedroom din ya kalli gaban mirror ya ga an dauka turare, kayan jikinsa ya canxa xuwa blue jeans da farar T shirt ya feshe jikinsa da turare ya dauki car key da wayoyinsa ya fice daga dakin. Kulle part dinsa yayi da makulli sannan yayi bangaren Mumy, bedroom dinta ya karasa ganin bata Palo ya sameta tana gyara kayanta a closet yace “Mumy xan dan fita sae na dawo” Mumy ta kallesa sannan ta ajiye kayan hannunta ganin mood dinsa tace “Me ya faru son?” Shiru yayi da farko sae kuma yace “Wae shine xa su samu Abba su ce na doki Suhaima, meyasa idan basu yi karya ba basu ji ddi ba ‘yan gidan nan?” Mumy tace “Ae tun ba yau ba na sha fada maka ka daina shiga hurumin da ba taka ba, to yanxu gashi sun hada ka da Abban ka ae” ya fuzar da iska yace “Na tafi Mumy sae na dawo” tace “Ina xaka?” Yace “Gidansu faisal xan je” Mumy tace “Toh shknn kar ka dde, and drive carefully” yace “Ohk Mum” har bakin mota ta rakosa, su Umma dake xaune da Hajiya suka bi su da kallo suna tabe baki, ko kallonsu Mumy bata yi ba har Junaid ya ja motarsa ya bar gidan, Mumy ta koma part dinta, Hajiya ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Wannan Yaro ya xame mana babban obstacle a gidan nan wllh, komae sae yanda yace ma ubansa, idan ba ina bakin ciki da numfashin da yake a duniya ba Shegiya nake” Umma tace “Uhm ke ko ni, da da yanda xanyi da shi da tuni ni dae nayi wllh, don ko uwarsa bata isheni kamar yanda ya ishe ni a gidan nan ba, na tsane shi wllh wllh, ko ‘ya yan mu fa Hajja bata ji da kamar yanda take ji da shi wae don yana namiji mu kuma mata gare mu” Hajiya tace “Toh shine kike kokarin ganin yanda xa ki cusa masa Suhaima ya aura kuma” Umma tace “Toh ae ke ma da xae auri Muhibba so kike naga” Hajiya tace “Da kenan ba yanxu ba don nasan hakan ma baxae taba yiwuwa ba, bari mu shiga ciki ki ji shawarar da na yi a kan matakin da xamu dauka kan Ahmad a gidan nan” Umma tace “Toh me muke a nan, mu shiga kawae ki ban in sha” mikewa suka yi gaba daya suka yi palon Hajiya. Gidan El-Ameen junaid ya nufa, yana gama parkin a waje ya shiga ciki, wanki ya tarar mama nayi a compound din na kayansu, ya karasa inda take suka gaisa sannan yace “El-Ameen ya xo ne mama?” Tace “Eh ya xo daxu da safe” yace “Ohk, bacci take yi ne?” Ta girgixa masa kai tace “A’a idonta biyu sae dae ya kulle dakin,” cikin gidan ya nufa ya haura sama, sae dae ya kasa bude dakin, ya kusa minti biyar tsaye sae kuma ya murda key din a hankali, bayan kusan second talatin ya murda handle din kofar, tsaye ya ganta jikin window tayi baja baja da gashinta tana sanye da doguwar rigar kanti pink colour da blue nd black flowers jiki, kallonsa take tana bobboyewa jikin bango, yayi murmushi ya rungume hannayensa yana kallonta.