CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
Captain Ahmad Junaid

  _By Khaleesat Haiydar_✍

13….

Junaid bai daga kiran ba ya juya yana kallon Khadija, Mikewa xaune tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace “Ni fa wllh ba chatting nake ba ya A.jay, ita Hajja bata san komai ba sai dai tayi ta magana” Junaid xai yi magana Humainah ta shigo palon fuskar nan nata a daure ta xauna gefen Hajja, Hajja tace “ke kuma fa? Ina aiken” Humainah tace “ko ba yi tayi kamar bata gan ni ba, kuma bata ce min komae ba sai aikinta take tana wake wake ta bar ni a tsaye” Junaid yace “Wa?” Ta kallesa tace “Anty sadiya mana” Hajja ta mike rai bace tace “Kambu!! Yaran nan sun raina ni wllh, don uwarta ni din sa’arta ce da xan aika tayi min abu ta share ki tana wake wake?” Kofa ta nufa kamar xata tashi sama, Junaid ya mike ya bi bayanta yace “Tsaya Hajja, me kika sata?” Tana huci ta juyo tace “Ca nayi ta min dafadukan taliya shi ke raina yanxu don Amina shinkafa tayi kamar ko da yaushe, ita bata da girki sai na shinkafa kullum” Junaid ya hade rai yace “Ita mum din tawa, Toh su wa ennan na palon naki me suke yi da baxa su maki ba” Hajja tayi tsaki tace “Xancen banxa, toh ban yi niyyan sa su ba, ko da yanda xaka yi da ni ne” tana kai wa nan ta nufi part din Hajiya da sauri, ya d’an tabe baki ya juya yana kallon Humainah yace “Sannu da hadi, ke baki iya taliyar ba sae kin je dauko magana koh?” Ta turo baki tace “Ae dai ba ni nace tayi ba, aikena aka yi” yace “Xaki yi bayani idan na kama ki ne” dauke kai tayi ya juya yayi wucewar sa, Khadija tayi dariya tace “Bari in je inyi kallo” Ana kiraye kirayen Magrib Junaid ya fito part dinsa sanye da jallabiya milk colour, dai dai nan Humainah da fatima suka fito daga part din Mumy, Humainah tace “Masallaci xaka ya Ahmad” Ya harareta yace “A’a office xan je” bae jira cewar ta ba ya kara gaba. Yana fito wa daga mosque bayan an idar da sllh ya tsaya da wani frnd dinsa da ke nan layin suna gaisawa, har sai da ya ga shigar Abba gida, snn yace “Abdul d’an ara min motar ka pls xan dan fita in dawo yanxu” Abdul yace “Toh mu shiga in baka key” junaid ya bisa suka shiga compound dinsu ya tsaya daga balcony har ya kawo masa makullin sannan ya nufi parking lot ya dau motar ya fita. Atm machine ya fara tsayawa ya cire kudi ya siya fruits nan wajajen sannan ya koma mota ya dau hanyar gidan El-Ameen. A waje yayi parking bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga gidan, Mama jummai na kwance Palo kasan tiles ta shimfida xani da ‘yar radionta a hannu tana saurare, ta mike xaune ganinsa tace “Sannu da xuwa Ahmad” xaunawa yayi yace “Yauwa mama ina yini?” Tace “Lfya lau, ya gidan?” Yace “Alhmdllh Mama, El-Ameen ya xo kuwa?” Tace “Ehh bae dade da fita ba, kuma yace min xai dawo” yace “Ohk, bacci take ne?” Mama jummai tace “Anya! Ina jin kamar idonta biyu” Junaid ya ajiye mata ledan fruits guda daya yace “Ga kayan marmari mama” godiya ta dinga masa ya mike ya nufi stairs ya haura sama. A hankali ya tura kofar dakin ya tsaya daga bakin kofar yana kallon cikin dakin, rakube ya ganta gefen gado ta sunkuyar da kanta, a hankali ya karaso cikin dakin yana kallonta har ya iso gabanta ya durkusa, sai a sannan ta dago kai tana kallonsa da dara daran fararen idonta, komawa baya yayi da sauri don ba kadan idanuwan nata suka bashi tsoro ba, ta wani kafe sa da ido ko kiftawa bata yi, sauke kansa yayi kasa ya bude ledan gabansa ya mike ya dawo kusa da ita ya duka a hankali ya dauki Apple daya ya mika mata, kallon Apple din take kamar me son gano abu a jiki, ya kai bakinsa ya gutsura a hankali ya fara ci yana kallonta, har sai da ya cinye sannan ya kai mata bakinta, kauda kai tayi da sauri, ya dawo gefenta ya kuma kai mata baki yace “Apple! taste ki ji” rike kanta yayi ya kai mata baki ta d’an bude bakin kadan ta gutsura, yana kallon yanda take kokarin hadiye Apple din ba tare da ta tauna ba yace “Wait, Wait!” Da sauri ya kuma gutsuran Apple din ya shiga taunawa yana kallonta ita ma haka, yanda ta ga yana yi haka ita ma ta shiga yi tana taunar Apple din a hankali, yayi murmushin sa me kyau yace “Good!” Tana hadiye wa ya kai mata baki kuma ta gutsura, karban Apple din tayi a hannunsa ta shiga ci da kanta, ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta, matsowa kusa da ledan ta shiga yi tana kallon ciki, ya dauki ayaba daya ya bare ya gutsura sannan ya kai mata sauran baki ta bude a hankali ya sa mata, taunawa ta shiga yi tana yatsine fuska, murmushi kawai yake yana kallonta, can ta dauki peel din bananan xata kai baki, ya karbe da sauri yace “No!” Tsuke baki tayi tana kallonsa, dariya yayi ya dauki wani Ayaban ya bude ya mika mata gaba daya, ta ajiye Apple din hannunta ta karba, cikin lkci kankani ta cinye ayabar, ya kuma bare mata wani shi ma ta cinye, haka ya dinga yi mata har ta ki karba kuma, ta dauki Apple din da ta ajiye tana kallo, karba yayi ya kai mata baki, ta dafe hannunsa da duk nata biyu ta gutsura a hankali tana taunawa, kallon hannunta kawae yake don duk haskensa ta fi sa nesa ba kusa ba, tana rike da hannunsa haka ta dinga cin Apple din, dai dai nan El-Ameen ya shigo dakin, xaro ido yayi ya rungume hannu yace “Tabdi! Me kke yi haka captain, she will bite the hell out of yhu wllh!” A hankali Junaid ya xame hannunsa daga nata, ta daga ido tana kallonsa, ya kamo hannunta ya danka mata Apple din sannan ya mike yana kallon El-Ameen, El-Ameen ya tabe baki yace “Ina raba ka da shisshige ma mahaukaciyar nan baka ji koh? Randa xata nuna maka halinta na hauka I won’t be around fah” Junaid bai tanka sa ba, El-Ameen yayi kwafa ya ajiye ledan drugs din hannunsa da fresh yoghurts ya dawo gabanta yace “Ashe kin iya cin fruits” bata kallesa ba sae cin Apple dinta da take, ya d’an yi murmushi ya nufi inda alluranta suke don hada wanda xae mata, Junaid ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi da sauri ganin haka, sae kuma ta bi bayansa, dai dai stairs yaji kamar ana binsa, ya juya ya ganta tana tahowa, kallonta ya tsaya yi, har ta karaso gabansa ta kama hannunsa ta saka masa Apple din, sannan ta daura nata hannun kan nasa ta kai bakinta ta fara cin Apple din, murmushi kawae yake yana kallonta, El-Ameen ya fito daga dakin ya rungume hannunsa yana kallonsu yace “Uhunm! It seems she’s getting use to yhu yanxu, kaga kawae sae ka tattaro ina ka ina ka ka dawo nan ka tsaya da ita sai ka cike Ladan ka” yana magana ne yana murmushi, Junaid ya xame hannunsa daga nata ya damka mata Apple din ya juya ya fara sauka stairs din, bin sa tayi da sauri, El-Ameen ya daka mata tsawa, a tsorace ta juya tana kallonsa, ya karaso inda take ya kama hannunta suka koma daki, xaunar da ita yayi gefen gado, ya bude yoghurt din da ya shigo da ya xauna gefenta ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, wani kallo yayi mata yace “I will slap yhu” kamar ta ji me yace bata sake yunkurin dauke kai ba, ya dafa kanta ya kai mata yoghurt din bakinta, a hankali ta dinga sha tana kallonsa, tari ta fara yi ya cire yoghurt din da sauri daga bakinta a hankali yace “Sorry,” ya dafa kanta ya kuma kai mata baki, ta dauke kai da sauri tana kokarin karban roban, sake mata yayi ta kallesa sannan ta fara tuttular da shi nan kasan dakin, fixge wa yayi da sauri yace “Ance maki idan aka koshi xubar da abinci ake?” Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya ja dogon hancinta yace “Da wani idanuwanta a wajen” jan hancin ita ma tayi yanda ta ga yayi, yayi murmushi yana kallonta, yoghurt din hannunsa ya rufe ya ajiye sannan ya mike ya nufi inda drugs dinta suke, diluting yayi mata a cup ya dawo gefenta ya xauna, matsawa ta fara yi daga kusa da shi, ya jawo ta ta fasa ihu, d’an buge mata baki yayi tayi tsit tana kallonsa, ya kai mata maganin baki taki budewa, sae da yayi mata tsawa sannan ta bude da sauri har jikinta na rawa, ya xuba mata maganin gaba daya, sai da ya tabbatar ta shanye snn ya mike yana kallonta, banda yatsine fuska bbu abinda take, yayi murmushi ya juya ya fita daga dakin, downstairs ya sauka ya samu Mama Jummai kadae palon, yace “Junaid fa Mama?” Tace “Ya fita ae” yace “Ohk, ki taso toh ki rakata baya tayi fitsari yanxu xata yi bacci tunda na bata magani” mikewa tayi tace “Toh, ae tana da tsafta yarinyar duk me xata yi naga tana shiga bayi” yayi murmushi yace “Kin dai yrda bata komai yanxu koh” yar dariya tayi tace “Ehh na yrda, don daxu ina xaune ta sauko, duk na tsorata ba kadan ba, ae ko in gaya maka sai gani nayi ta xauna gefe na ta mimmike kafa yanda taga nayi” dariya El-Ameen yayi yace “Ae wayo gareta, idan Allah ya yrda sama mata lfya baxae wani dau lkci sosai ba, kila daga nan xuwa wata hudu ko shidda in’sha Allah” Mama jummai tace “Toh Allah ya yrda, Allah ya ba Baiwar nan tasa lfya, gashi ‘yar yarinya da ita” yayi murmushi yace “Kina ga xata yi shekara nawa” Mama jummai tace “Kai baxata wuce sha shidda ba wllh, in ma ta kai kenan” yana murmushi yace “Ko kuma sha bakwai ba” Mama jummai tace “Allah sarki, amma dai ku dinga hada mata da Addu’a kunsan duniya bbu gaskiya, kar ayi ta na turawa nan kuma kila asiri ne” ya d’an yi shiru kafin yace “Anya kuwa, bana tunanin jifa ne, don da jifa ne ba lallai ta xama nutsatssiya haka ba, nd jiya naga tana ta observing wnn tumatir din cikin dankalin da na siyo kuma ta sha sosai” Mama Jummai tace “Toh Allah dai ya bata lfya amma dai ayi addu’ar ma” yace “Ameen, xa a hada mama” Sama mama Jummai ta nufa shi kuma ya xauna palon, bata mata wani gardama ba ta kai ta bayin. Ko da Mama Jummai ta sauko mikewa El-Ameen yayi ya koma sama, kwance ya sameta idonta lumshe alamar xata yi bacci, ya gyara mata kwanciya ta bude ido da sauri tana kallonsa, ya rufa ta da bargo, ya dawo dai dai fuskarta yace “Gudnyt” lumshe ido kawae tayi ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofa, yayi ma Mama Jummai sae da safe ya fice daga palon, xaune ya ga Junaid a balcony, ya d’an bude ido da mamaki yace “Thought ka tafi ai” Junaid ya mike yace “Sure! Yanxu xan tafi” daga haka ya sauka balconyn yayi hanyar gate, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki ya bi bayansa, kusan a tare suka fita compound din, El-Ameen ya kalli motar da Junaid ya nufa yace “Whose car is that?” Ba tare da Junaid ya kallesa ba yace “Abdul” daga haka ya bude motar ya shiga, El-Ameen ya karasa gun motar yace “Yhu are acting strange this dayz Captain, let it not be kai ma ka fara samun brain disorder’n ne fa, aikin sai yayi min yawa” El-Ameen ya kare maganar yana murmushi, junaid ma yayi murmushi yace “Sure!” Daga haka ya ja motar ya bar sa nan tsaye, El-Ameen ya bi motar da kallo yana murmushi yace “It’s Alwayz: ‘Yea! Sure! D’an rainin hankali, tasa motar shi ma ya nufa ya bude ya shiga ya bar anguwar yana tunanin yanda xai yi squeezing time dinsa gobe da safe ya xo ayi diagnosing dinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button