CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association
Captain Ahmad Junaid

_By Khaleesat Haiydar_✍????

23……

A hankali ya dago kanta yana kallonta, ya ciro handkerchief aljihunsa ya share mata idonta murya can kasa yace “Am sorry jewel” yana jin fitowar khadija daga kitchen yayi saurin dauke hannunsa a shoulder dinta ya koma baya, ta karaso parlon ta mika masa cup din ruwan, ya amsa ya ajiye sannan ya saukar da ita kasa shi ma ya sauko, dankalin da mama ta ajiye parlon ya jawo ya dauka ya hada da tomatoe ketchup ya kai bakinta, ta sa hannu ta karba ya sake mata, ta lashe tomatoe din, khadija tayi murmushi ta dawo kasa d’an nesa da su ta xauna tana kallonta, haka ta dinga shan tomatoe din kanta a kasa, ya tsura mata ido yana kallo, ta d’ago manyan idonta ta sauke kan nasa, dauke nasa yayi ya mike ya koma kan kujera yace “tafi kitchen ki hado mata tea khadija” khadija ta kama hanyar kitchen yana ganin haka ya kuma saukowa ya dawo ya xauna gabanta ya dau potatoe ya kai mata baki xata kauda kai ya rike kan ya hade rai ya tura mata dankalin yace “Eat!” taunawa ta shiga yi tana kallonsa tana yamutse fuska, ya kalli kofar kitchen sannan ya kalli ragowar ketchup din dake gefen bakinta, ya matso a hankali ya sa yatsa ya kwashe ketchup din ya lumshe idonsa ya kai baki, dai dai nan aka bude kofar parlon, ya koma baya da sauri yana goge bakinsa, Junaid ya shigo parlon, kallo daya yayi masu ya sunkuya ya shiga cire takalmi da safar kafarsa, El-ameen ya mike ya koma kujera yana shafa kai, karasowa cikin parlon Junaid yayi, yana sanye da trouser din uniform dinsa sai farin polo, El-ameen na kallonsa yace “Gud you came, so ya xaka yi da ita da nyt?” Xaunawa Junaid yayi bai ce komai ba, ta dauki plate din gabanta ta mike ta dawo kusa da shi ta daura kan kafarsa, murmushi ya d’an yi ya rike plate din yace “No! Thank you” El-ameen ya dauke kai hade da tabe baki, khadija ta fito rike da cup din tea ta ajiye tana kallon Junaid tace “Welcm bro” yace “Thank you, how about you telling Hajiya you will be spending the nyt at ur frnd’s place?” Shiru tayi sannan ta langwabar da kai ta xauna tace “Kasan Abba yana nan” shafa kansa yayi bai ce komai ba ya dauke plate din da ta daura masa a kafa ya ajiye kasa, El-ameen ya d’aga kafada ya mike ya haura sama, kallon khadija Junaid yayi, tayi murmushi tace “Wai yaya ka ban labarin inda Ku ka ganta mana, dama kun santa ne?” Junaid yace “I donno for El-ameen” tablets dinta El-ameen ya dauko a sama ya dawo parlon, sai da ya fara shiga kitchen yayi diluting dinsu sannan ya fito, ba musu ta bude baki ya juye mata tana yatsina fuska, Khadija tayi murmushi ta daura kanta jikin Junaid a hankali tace “I like her Ya A.jay” murmushi yayi bai ce komai ba, El-ameen yace “I will be going back to clinic yanxu, nan da thirty mins xata yi bacci, duk inda ta kwanta ki kyaleta kawai” a hankali khadija tace “Ni fa ina jin tsoro, tafiya duk xa ku yi ku bar mu” El-ameen ya harareta yace “An ce maki bata komai da’alla” Junaid ya tashi shima yace “Baxata maki komai ba sister, am also leaving” shiru tayi bata ce komai ba, El-ameen yayi hanyar kofar, Junaid ya bi bayansa, da sauri ta mike ta nufe su khadija ta bi ta da kallo gabanta na faduwa, gun Junaid ta nufa, El-ameen ya juya yana kallonsu, shima Junaid kallonta ya tsaya yi, tsaki El-ameen yayi ya xaro mata ido yace “C’mon koma kar in baki knock” kara ta saki kamar ta ji abinda yace, El-ameen ya fice daga parlon, Junaid yayi murmushi ya kama hannunta suka koma parlon ya xaunar da ita yana kallonta yace “Look Jasmine xa mu dawo anjima kin ji, khadija will be staying with you har mu dawo” Khadija tace “Waow yaya sunanta Jasmine?” Da sauri ya kalleta don ya manta gaba daya tana gun, yace “Ohh! Did I call her dat” khadija tayi dariya tace “Ehh mana” ya mike yace “No I didn’t” ihu ta fasa ta mike da sauri ganin ya tashi, Khadija ta langwabar da kai tace “Yaya ba ka baro gun aiki ba, stay with her plss, bata son ka tafi” yace “Am hungry, gida nake son tafiya in ci abinci” khadija tace “Ae Akwae food stuffs a nan ba sai in girka maka ba” shiru yayi sannan yace “Alryt ki min indomie kawai” tace “Toh” ta mike ta shiga kitchen, xaunawa yayi ya xaunar da ita gefensa yayi murmushi ya ja dogon hancinta yace “I will stay with you Jasmine” suna nan xaune har khadija ta dawo parlon rike da tray me dauke da indomie da fried egg a gefe sai roban ruwa da cup ta ajiye kasa tace “Gashi yaya” saukowa kasa yayi ita ma ya sauko da ita suka xauna sai kallon indomien take kamar idonta xai fito, murmushi yyi ya kalli Khadija yace “Ke baxa ki ci ba” ta girgixa masa kai tace “Na koshi” daukar fork din yayi ya debi indomie kadan ya kai mata baki bayan ya d’an huce, wani kara da yasa shi sakin fork din tayi khadija ta mike da sauri ta bar wajen, ta dinga ihu tana komawa baya tana kallon indomien duk ta ruda shi, ya riketa yana cewa “What happen jasmine, bakya so ne” ihu kawae take tana komawa baya, ya kalli khadija yace “Take it away” dauka tayi ta nufi kitchen da sauri, tsit tayi ta bi khadija da kallo, ta dawo kusa da shi ta xauna, shi kam kallon mamaki kawai yake mata, hannu ta sa ta taba long lashes dinsa, yayi murmushi ya cire hannunta yace “Indomie kike tsoro Jasmine” khadija ta fito tace “Yaya kila tsoron shi take ji, kaje kitchen ka ci” ya girgixa kai yace “no idan naje gida xan ci abincin” kallonta Junaid yayi jin ta jingina jikinsa ya ga bacci ya fara daukarta, ya mike ya kwantar da ita kan kujeran, khadija tace “Baxa ta fadi ba yaya?” Yace “Ehh, bari in tafi gida in dawo yanxu tun da tayi bacci” a hankali khadija tace “Toh amma ka dawo kafin ta tashi plss Allah tsoronta nake ji” Junaid yace “Ohk” yana fita ta dawo kusa da ita a hankali ta xauna tana kare mata kallo, doguwa ce yar siririya da ita, ta tsura ma kyakkyawan fuskarta ido da d’an karamin jan bakinta dake sheki, Khadija ta kama long fingers dinta a hankali tace “I like you sister, Allah ya baki lafiya” kallon hular kanta tayi ta dawo wajen ta d’an cire hular tana lekan kanta ta ga bakin gashinta sai sheki yake, fito da gashin ta shiga yi ta bude ido ganin tsayin gashin, ta lumshe ido tace “Waoww!” Haka tayi ta xama kusa da ita tana kallonta, komai na jikinta me kyau ne, mamaki ta dinga yi inda suka samota har suke son warkar da ita, to yan uwanta fa?? Mikewa tayi jin ana kiran la’asar taje tayi alwala tayi sallah, sannan ta d’an gyara gidan ta dawo ta xauna ta ci gaba da kallonta daga inda ta tsaya, bude kofa taji anyi ta juya da sauri, taga El-ameen ne, ya karaso parlon yace “Capt ya tafi ne” ta gyada masa kai, ya iso kusa da su yana kallonta yace “She’s still sleeping koh?” Ta gyada masa kai, ajiye ledan hannunsa yayi ya tada ta ya tafi sama da ita, khadija ta hade rai ta bi sa da kallo, haka kawae taji haushin abinda yayi, ta ja tsaki ta dauke kanta hade da tabe baki ta mike ta koma kujera ta xauna, ba a dau lokaci ba ya sauko, kallonta ya tsaya yi ganin yanda ta hade rai yace “Ke in kin gaji ne tashi ki tafi gidan ku” mikewa tayi ta dau Jakarta ta fice fuu, yayi tsaki ya dau wayarsa da ke ring. Tana fita ta kira Junaid yana d’agawa yace “Ta tashi ne?” tace “Wani tashi? Bayan ya wani ce wai in tafi” Junaid yace “Wa?” Tace “Ya El-ameen mana, wai wani in tafi gida” shiru ya d’an yi kafin yace “Saboda me?” Tace “Oho masa, ya wani dauketa ya kai ta daki bayan bacci take” mikewa Junaid yayi daga zaunen da yake parlon Mumy yace “daki kuma, ke kina ina?” Khadija tace “Ehh mana, ni na riga na fito ma tafiyata xan yi” katse wayar yayi kawai ya ajiye, Mumy dake ta kallonsa tace “Wani dakin? Kuma da wa kake waya” Kallonta yayi da sauri don ya mance tana wajen yace “Ohh dama, dama na aiketa ne, shine… no wai ce min tayi yayarta ta kulle ta a daki, khadija ce” Mumy na masa wani irin kallo tace “Karya kake” ya xaro ido yace “Mumy karya kuma” ta girgixa kai tace “Ahmad am beginning to suspect you this days, behaviours dinka sun fara canxawa, i notice kana boye min wani abu, but be careful” daga haka ta shiga bedroom, Humainah dake xaune parlon ita ma tana gyada kai tace “ta tashi ne? uhnn ko waye ya tashi oho, daki kuma? Uhnn ko wani dakin yake nufi oho, ke kina ina? Uhn ko wacece haka oho, hmm we are beginning to suspect you this days Captain be careful” wani harara ya watsa mata ta mike tayi masa gwalo tace “In tayi tsami ma ji dai” da sauri ta shige dakin Mumy ita ma. Ya shafa kansa a hankali don yasan ko hauka yake baxae bari Mumy taji xancen mahaukaciyar nan ba, tabdi! mikewa yayi da sauri ya dau makullin motarsa ya fita, waje ya fita don bai shigo da motarsa compound ba ya hau motar ya nufi gidan El-ameen, cikin few mins ya isa, yana Parkin ya fito ya shiga gidan, xaune ya tarda El-ameen balcony yana waya, ya tsaya yana kallonsa har ya gama ya hade rai yace “Y did you send khadija away?” El-ameen yace “Haka tace maka, to let me get hold of her” Juyawa Junaid yayi jin an bude gate, wata mace da baxata wuce 27 ba ta shigo, ta karaso balcony ta gaida Junaid, ya gyada mata kai kawai, mikewa El-ameen yayi yace “Welcm, ki shiga daga ciki” ba musu ta shiga parlon, El-ameen yace “we are hiring her for 2 dayz kafin Mama ta dawo, sai ka biyata 10k, old nurse din clinic din mu ce” Junaid ya daga shoulder yace “Anyhow” juyawa yayi yace “sai gobe, na tafi” El-ameen yace “Wato xuwa Kayi ka ga what I was up to da nace khadija ta tafi koh?” Junaid yayi murmushi bai ce komai ba yayi gaba abunsa, El-ameen yayi kwafa ya shiga parlon. Karfe shidda da wani abu Junaid ya shigo gida, ya ga khadija tsaye nesa da balconynsu, Hajiya da Umma na xaune sai Sadiya da Suhaima, Sadiya sai cewa take “Kawai ki bar min komai a hannuna Hajiya idan na lallasa ta xata fadi inda taje wllh” Umma tace ” Ni tun da ta fara mu’amala da shegiyar ‘yar da aka kawo gidan nan Humainah take kowa, dabi’un ta suka canxa, ke har kin kai matsayin da xa Kiyi karyan xuwa gidan kawa ki fita tun safe sai yanxu kike shigo mana gida don Kazan ki” junaid ya karasa wajen ya gaida su yace “Hajiya tare muka fita, ta rakani ne” Umma ta watsa masa wani kallo tace “Da yake ba Aysha bace ko Fatima dole ka kareta mu bar ta ta lalace” Juyawa khadija tayi fuu ta nufi part din Mumy, Hajiya ta shiga kwala mata kira tana cewa “Kika kuskura kika shiga wajen nan mai raba ni da ke sai Allah, kuma wllh kin ji na rantse sai kin fadi daga inda kike”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button