CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske writers Association????
Captain Ahmad Junaid

_By Khaleesat Haiydar_✍????

24…..

Junaid ya juya shi ma ya bar wajen, Hajiya ta bi bayan khadija tana huci, a balcony ta tsaya ta tura kofar tana cewa “Kar ki bari in shigo parlon nan khadija, tun muna mu biyu ki fito ki wuce” tsayawa Junayd yayi yana kallon ikon Allah, Humainah dake xuge jakar kayanta da ta gama hadawa a parlor ta tabe baki ta mike, ta dauki remote din TV ta kure maganar gaba daya, Hajiya ta xaro ido tana kallonta, ji take kamar ta shaketa kawai ta huta, can dai tace “Ke wai ni sa’ar uwar ki ce kika raina ni haka a gidan nan, ina magana za ki kure min TV?” Humainah ta rike kugu tace “Ni ba dai uwata ba wllh” Sadiya ta karaso bakin kofar parlon tana cewa “Bata fito bane Hajiya” Hajiya ta fashe da kuka tace “Yanxu ni yarinyar nan take ma rashin kunya Sadiya, a haihuwar kaji ban yi jika da shegiyar ba” a fusace Sadiya ta shige parlon tayi kan Humainah, Junaid na ganin haka ya bi bayanta, ai tuni Humainah tayi dakin Mumy da gudu tana kwala mata kira, hakan kuma bai hana Sadiya bin ta ba tana kunduma mata xagi, wani tsawa Junaid yayi mata tun kan ta shiga dakin Mumy ya fixgota ya nuna mata kofa yace “Get out, ko a mafarki kika kuskura kika yi attempt din t’aba ta wllh sai na ba66allaki a gidan nan” kallonsa kawai take fuskar nan nata daure don tasan tana iya magana yanxu ta sha mari, Hajiya ta shigo parlon tana huci tace “Wllh Ahmad idan ka bari na saka ka gaba a gidan nan sai xaman duniyar nan gaba daya ta gagare ka, kayi hankali da ni ka bi ni a hankali, bani da kyau wllh, amma in dai ni ce mu je xuwa sai ka gwammace uwar ka bata haifo ka gidan nan ba, xaka san da ni kake” Mumy ta fito tana ma Hajiya wani kallo tace “Babu abinda kika isa ki masa wanda Allah bai masa ba, mu da Allah muka dogara, aniyar ki ta bi ki kuma” Hajiya tayi shewa tana murmushi tace “Toh mu xuba da ku,” daga haka ta juya fuu ta fice, Sadiya ta bi bayanta. Junaid ya girgixa kai ya juya ya fice daga parlon, shi gaba daya xaman gidan ma ya ishe sa kawai. Mumy ta kwalo ma Humainah kira ta fito, strictly tace “ina raba ki da mutanen nan baki ji ko Humainah, ina ruwan ki da su wai da har xaki dinga shiga tsabgarsu, kinsan Allah baxa mu shirya ba idan magana za ki dinga dauko min, so kike su sa ki gaba kema koh? To maxa gama hada kayan ki yanxun nan Ahmad ya tafi da ke inda xai kai ki kafin Abba ya dawo su kuma hada ki da shi” Juyawa Humainah tayi ta koma daki kamar xata yi kuka, Khadija ta fito daga daki tace “Mumy kiyi hakuri,” Mumy tace “Kinga idan kin yi laifi ki daina yo wa nan khadija, sai ki tsaya can ki basu hakuri” Khadija ta turo baki ta koma dakin su fatima. Junaid na shigowa bayan yayi wanka ya canxa kaya Mumy tace “Maxa kai ta gidan Aisha kan dare yayi Ahmad” ya kalli agogo don dama fita xai yi ya maida motar jiya, yace “Toh Mumy” Mumy ta kwalo ma Humainah kira tace “Dauko jakar ki da hijab” tana kumbure kumbure ta fito rike da ‘yar jakar kayanta da Hijab, Junaid ya mike yace “Sai na dawo Mumy” Mumy tace “Allah ya kiyaye, amma motar waye ka dawo gidan nan jiya da?” Ya d’an shafa kai yace “A frnd, idan na ajiyeta xan mayar ne ma” Mumy tace “Ohk,” ya fita Humainah na biye da shi a baya, Mumy tayi murmushi tace “Ba sallama Humainah” kamar xata yi kuka ta daga mata hannu ta fice, Mumy tayi dariya tace “Lallai Humainah” As usual Hajiya da Umma na balcony, duk suka bi su da hararan tsana, tsayawa yayi har Humainah ta karaso inda yake ya karbi jakar hannunta suka nufi parking lot, Umma ta kalli Hajiya tace “Ke wllh naga kamar sonta yake, dubi fa har da wani rike mata jaka, sai ya iya yiwuwa ma ya fito da ita a matsayin warce xai aura idan lokacin da Alhaji ya dibar masa yayi” Hajiya ta xaro ido tace “Ae ko da mun banu mun lalace, meye abun yi Bilki?” Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “ba mu ga ta xama ba,”
Humainah ta kalli motar da Junaid ya shiga tace “Motar waye wannan?” Kallonta yayi ya bude ido yace “Naki” ta hararesa ta xaga ta shiga, yana warming motar ya kira El-ameen, bugu biyu ya d’aga, Yace “kana ina ne Dr?” El-ameen yace “ina gida” Junaid yace “Ohk plss ka fito mu hadu kasan layin ku” El-ameen yace “Why?” Junaid yace “kai dai ka fito, it’s urgent, kuma ka taho da motarka” daga haka ya katse wayar, ya ja motar suka bar gidan, Humainah tace “Amma ya Ahmad gidan Anty Aysha aka ce ka kai ni fa xaka wani ce ku hadu a kasan layi, to yawo xaka yi da ni a mota” ba tare da ya kalleta ba yace “Ni tricycle ma zan je in saka ki yanxu ya kai ki” ta xaro ido tace “Ehh!” Yace “Yess!” yana isa layin su El-ameen ya hango motarsa ya isa gun motar yayi parking ya fito, xuge glass El-ameen yayi yana kallonsa a bit surprise yace “Whose car is dat?” Junaid yace “A good samaritan’s, jiya da ka yasar da ni a titi ka wuce….” El-ameen yayi tsaki yace “Kayi mugun bata min rai jiyan nan, don me yarinya xata shirga karya wai ta mance Atm card a gida ka yi amfani da kudina ka biya uban kayan da ta siya” Junaid yace “Ba dai na mayar maka da kayan ka ba, keep dat matter aside kar kayi provoking dina” El-ameen ya tabe baki yace “Ni Mama jummai ma na ba kudin da xata tafi daxu, and dat’s ur responsibility not mine” Junaid yace “Whatever, gidan Aisha xaka taimaka ka kai budurwar nan taka, ni ina son maida motan mutane ne kar ayi tunanin guduwa nayi da shi” El-ameen ya leka motar suka hada ido da Humainah, da sauri ya dauke kai ya bude ido yana kallon Junaid, Junaid yayi ‘yar dariya yace “Ehh ita din ce” daga haka ya juya yana kallon Humainah da ta hade rai cikin mota ya duka yana kallonta da kyau yace ” Oya fito saurayin ki ya kai ki ni…..” Kuka ta sakar masa tana yarfe hannu tace “Wayyo ni, wallahi kai aka ce ka kaini bbu inda xan bin sa” ya bude ido yace “Ke ba motata bace wannan, xan maida ma me shi ne” ta marairaice masa cikin sigar shagwaba tace “Plss mana ya Ahmad don Allah ka kaini” murmushi kawai yake yana kallonta, can ya mike ya juya gun motar El-ameen da ya wani hade ya daga kafada yace “Kaji wai tsoronka take ashe, don haka plss frnd just excort me in maida motar sai mu tafi gidan Ayshan da naka motar” El-ameen yayi masa wani kallo yace “I don’t have dat time, dama kiran da ka min kenan?” Junaid yayi murmushi yace “Toh shikenan, idan mun je can xa mu samu tricycle” daga haka ya xaga ya koma driver seat ya tada motar ya bar layin, tsaki El-ameen yayi ya bi motar da harara can ya tada nasa motar ya bi bayansa, Junaid na ganin haka yayi murmushi don dama yasan sai ya biyo sa. Cikin mintunan da basu wuce sha biyar ba ya iso layinsu Hafsat, yayi parking inda tayi jiya, ya fara kalle kalle don bai karbi numberta ba, Humainah tace “Ya Ahmad ina ne nan” yace “gidan su budurwata” kallonsa kawai take ya bude motar ya fita ya xaga ya bude mata ta fito, dai dai nan El-ameen ma ya fito ya rungume hannu ya hade rai yana kallonsa, murmushi Junaid yayi ya daga kafada ya nufi gate din gidan, yana danna bell maigadi ya leko, Junaid yace “Amm ina yini, Hafsat nake nema a gidan nan,” Mai gadin yace “Toh bari a mata magana” komawa Junaid yayi kusa da El-ameen ya tsaya yace “Da ma ka saki ranka kar Humainah tace ta fasa” shi dai El-ameen bai tanka sa ba, Humainah kam ko kallonsu bata yi ba, bude gate din gidan aka yi ta fito sanye da jan atamfa sai farin Hijab, xaro ido El-ameen yayi yana kallonta sai kuma ya kalli Junaid, murmushi tayi ganin Junaid sai dai lokaci daya murmushin ya bace ganin El-ameen gefensa da tayi, ta karaso kusa da su ta gaida su, Junaid ne kadai ya amsa don shi El-ameen juyawa ma yayi ya shige motarsa, banda kallonta babu abinda Humainah take, Junaid ya shafa kansa yace “Ga motar ki, tnx a plenty, am grateful” ta kirkiri murmushi kawai tana gyada masa kai, ya mika mata makullin motar ta karba, ya kalli Humainah yace “ga kanwata can ku gaisa” karasawa tayi gun Humainah tana kallonta murmushi dauke fuskarta tace “Sannu, ina yini?” Humainah ta dauke kai babu yabo bbu fallasa tace “Lafiya” juyawa tayi ta bar wajen duk jikinta yayi sanyi, ta kalli Junaid tace “Toh nagode” yace “Ni ne da godiya” kallon Humainah yayi yace “Taho mu wuce” kamar xata tashi sama ta karaso ta bude bayan motar El-ameen ta shige, Junaid ya ciro wayarsa ya mika ma Hafsat yace “Sa man digit dinki mu dinga xumunci” karba tayi ta sa numberta ta mika masa suka hada ido da El-ameen dake kallonsu, da sauri ta dauke kanta, shi ko ya tabe baki, Junaid ya mata godiya ya xaga ya bude front seat ya xauna, El-ameen ya figi motar suka bar layin. Sai da suka hau main road El-ameen yace “Da nasan inda xaka kenan wllh ban xuwa, yaushe ka xama haka Captain, yaushe ka fara ware ma mace lokacin ka har da wani karban numberta, Tabdi” har suka iso gidan Aysha ana kiraye kirayen Magrib Junaid bai ce ma El-ameen komai ba, ya juya yana kallon Humainah yace “Toh gashi mun kawo, ki gaida ta” daukar jakarta tayi ta bude motar ta fice ta nufi gate, Junaid ya bi ta da kallo sai kuma ya bude motar ya bi bayanta, tsaki El-ameen ya ja ya danna masa horn, har gate Junaid ya shiga ya fixgota ta hade rai tace “Meye kuma” ya wara ido xai yi magana, ta fashe da kuka, kallonta ya tsaya yi, can ya d’ago kanta yace “What happen?” Ta fixge hannunta taki cewa komai, yace “Baki son xama gun Ayshan ne kuma?” Ta girgixa masa kai tana goge hawayen dake kuma sakko mata tace “To wace wannan yarinya” kallonta kawai yake sai kuma yayi murmushi ya ciro wayarsa daya a aljihu ya mika mata yace “Anjima xan kira ki in gaya maki wacece” juyawa tayi zata bar wajen ba tare da ta karba wayar ba, ya kuma dawo da ita ta fashe da kuka, murmushi yayi ya kama hannunta ya saka wayar, ya juya ya fita daga gate din don El-ameen ya danna horn ya kusa sau biyar, yana shiga motar El-ameen ya figi motar yana cewa “Wai meyasa kake min abinda ka ga dama ne Capt, ka wani shanya ni a mota kana biye ma karamar yarinya ‘yar cikin ka, ga baiwar Allah can ko abinci nasan bata ci ba….” Junaid yace “Budurwar ka fa na rako” El-ameen ya tabe baki yace “No, ni ban ce ina sonta ba kawai nace tana da kyau ne, kuma ni ba budurwa ta bace, warce nake so ma ta fi ta komai” dariya Junaid yayi yace “Xa ma ka fadi gaskiya ne, a ina ka samo warce kake son kai da kake tsoron mata” El-ameen yace “Am serious, ni bana son mace me tsiwa da jaraba, warce nake so is very gentle….” Junaid yayi dariya yace “Ita ma bata son mai tsoron mace” El-ameen yayi tsaki yace “Can gidan fa nake son in je don nasan baxata ci abinci ba sai naje shine ka wani bata min lokaci” Junaid ya tabe baki yace “Irin kamar ka damu da ita din nan koh” El-ameen yace “Of course na damu, nama fi ka, kai da baka da aiki sai na bada kudi, ni kuma lokacina gaba daya na bata, a yanxu haka I know her likes nd dislikes, duk motsin da xata yi nasan me yake nufi, I’ve studied her more than you can imagine, kai you are only showing dat you are a millionaire kana nuna kai kadai ma xaka iya kashe ko nawa ne ba sai ka nemi assistant ba, ni kuma….” Junaid ya ja tsaki yace “Aikin banxa kenan, don without that money you are talking about all this you are listing won’t come to action, kai da kake kyashin kashe mata naira biyar din ka, my frnd ka daina listing kan ka a wa enda suka taimake ta ma a rayuwa, you are only decieving ur self, coz I hired you and am paying you for the job, yau nace bana bukatan service dinka you are gonna quit!” Parking El-ameen yayi yana kallonsa yace “Haka kace Ahmad?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button