CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association
Captain Ahmad Junaid

 _By Khaleesat Haiydar_✍????

25….

Junaid yayi dariya yace “Of course haka nace ko nayi karya, ka fadi sisin da ka taba kashe mata in biya ka, kai yanxu har ka nuna mun ka fi ni damuwa da ita, wanda da na biye ka tun farko da baxa mu daukota ba ma, wani irin discourage dina ne baka yi ba, wani irin dariya ne baka min ba kan yarinyar nan…” El-ameen bai ce komai ba ya ci gaba da tukin sa, banda dariya babu abinda Junaid yake, ganin El-ameen hanyar gidansu ya nufa Junaid yace “Ohh ka fasa xuwa ka bata abincin ne?” Shi dai El-ameen bai tanka sa ba har ya isa bakin gate din gidansu, ya juya yana kallonsa yace “Idan kaga na kuma bi ta kan patient dinka, ka gaya min wanda ya fi wannan,” daga haka ya fice daga motar ya shige gida. Junaid yayi murmushi yana shafa kansa yace “Uhum wai fushi yayi?” D’aga kafada yayi ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, gida shi ma ya nufa abun sa. Washegari Junaid na gun aiki ya dinga kiran El-ameen ya ki d’agawa, shi dariya ma abun ke basa, don bai ga abun fushi ba daga fadin gaskiya, Karfe biyar ya baro gun aiki, ya canxa uniform din jikinsa xuwa mofti ya tafi can gidan nasa, a hankali ya tura kofar parlon, nurse din dake kula da ita na tattare biscuits din da yayi littering din tsakar parlon, ita kuma tana kwance nan kasa tana bacci, Junaid ya karaso ya amsa gaisuwar da nurse din ke masa yace “Dr El-ameen ya xo yau kuwa?” Ta girgixa kai tace “Bai xo ba, na kirasa ma he’s not responding” Junaid yayi murmushi ya xauna yace “Ohk, amma ta ci abinci?” Nan ma ta girgixa masa kai tace “tun jiya ma taki cin komai, kaga biscuit din nan ma na fiddo mata shima bata ci ba ta watsar, yanxun ma da kyar ta kwanta tun safe taki xama na rasa me take nema, duk ta ki yarda da ni” Junaid yace “Ohk, me yace maki ta fi so, I mean abinda take ci?” Tace “Kasan yace xai dawo jiya toh bai dawo ba bare ya gaya min, kuma duk yau ba a mata allura ba tunda bai gaya min yanda zan yi ba” Tabe baki Junaid yayi ya mike ya fice daga parlon. Gidansu El-ameen ya nufa Ummi tace ai tun safe yana clinic, ya mata sallama ya fito ya kama hanyar clinic din, Yana isa nurses din dake reception suka ce masa ai baya nan, yace “Ohk haka yace maku ku ce min idan na xo” kallonsa suka tsaya yi, ya haura sama ya tafi office dinsa, ya murda kofa yaji da gasken baya nan, tsaki yayi ya sauko ya fice daga asibitin, a mota ya dinga kiransa ya ki dagawa, shi ya rasa abun jin haushi a maganarsu ta jiya, daga fadin gaskiya, tsaki yayi ya tada motarsa ya tafi gida abun sa. Wasa wasa har 2 dayz El-ameen yaki xuwa can gidan, ya ma kashe wayoyinsa gaba daya, shi ma Junaid ya fita harkarsa bai kuma bin ta kansa ba, matsalarsa daya yanda Jasmine taki cin komai, gashi da ganinta xaka san abu na damunta, duk taki sakin jiki, though in yaje gidan da yamma ta kan je ta kwanta gefensa ko ta xauna kusa da shi, amma duk yanda xai yi da ita ta ci abinci bata ci, sai dai k’adan shi ma da kyar, in ya takurata tayi masa ihu, bini bini xaka ga ta kalli kofa ko taje can ta tsaya kamar dai tana jiran wani, on the third day Mama jummai ta dawo ya sallami nurse din, yasan yanxun xata fara cin abincin tunda ga mama jummai kila dama don bata saba da nurse din bane amma sai yaga otherwise don yi ma tayi kamar bata taba ganin mama jumman ba, ta kuma ki cin abincin still, da mama jummai ta tambaye Junaid El-Ameen ce mata yayi, yayi tafiya ne, duk abinda mama jummai tasan tana so sai da ta yi ta bata duk taki sai ketchup da take ta sha, duk baiwar Allahn ta rame. Yau Junaid na barin gun aiki ya nufi gidansu Faisal, yayi sa’an shi ma dawowan shi daga aiki kenan, Faisal yayi mamakin ganinsa barin da yaga ko canja uniform din jikinsa bai yi ba. Junaid ya xauna bayan sun gaisa yace “Ina son muyi wata magana da kai ne frnd” Faisal ya maida hankalinsa sosai yace “Am ol ears” Junaid ya shafa kai a nutse ya soma basa labarin mahaukaciyar tun daga farkon haduwarsa da ita, Faisal ya kwalalo ido yana kallonsa baki bude, har Junaid ya kai karshen labarin yana murmushi, Faisal ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace “Babban magana, but El-ameen bai kyauta ba, kuma ni ban ga abun fushi a nan ba, sabon da tayi da shi ne ya hanata sakin jiki da bata ganinsa, shiyasa take kin cin abinci!” Junaid ya tabe baki yace “Yanxu dai you are a Doctor, so nake plss ka gaya min yanda xaman psychiatry yake, is it advisable in kai ta can babu matsala?” Faisal ya kuma sauke wani ajiyar xuciyar yace “Gaskiya ina ga na gida kamar yanda El-ameen ke mata ya fi, kuma gashi har ta saba da shi samun lafiyarta ba lallai ya dau lokaci ba, yanxu dai kar ka damu xan je in same sa, nasan…” Junaid yace “No! no bana bukatan sa kuma, he shud hold on to his medication, idan taje psychiatry din suma xata saba da su” murmushi Faisal yayi, Junaid ya mike yace “Plss ka binkitar min psychiatryn da ka ga is ohk… I might come back later ko kuma in kira ka. Don yanxu Mumy xata fara kirana its almost six o’clock” Faisal ya bi sa da kallo har ya fita sannan ya shafa kai yace “Lallai Junaid da El-ameen, mahaukaciya kuma???” Mikewa yayi shi ma ya dau makullin motarsa ya fita xuwa gidansu El-ameen din, Ummi ce da Sumayya xaune parlor, ya gaida Ummi, ta amsa da fara’a tana tambayarsa mutan gida yace “Duk Suna lafiya Ummi, El-ameen na nan kuwa” tace “Ehh yana daki” dakinsa ya nufa ya tura kofar ya shiga da sallama, Ummi ta kalli Sumayya tace “Ki kai masa drink, ki tambayesa ko xai ci abinci” mikewa tayi ta nufi kitchen, kwance faisal ya sami El-Ameen da laptop a gefensa sai dai wayarsa yake dannawa, El-Ameen ya mike xaune ganinsa, Faisal yana murmushi ya karaso ya xauna gefensa yace “Yane the great Dr Ahmad El-ameen” El-ameen yayi murmushi shi ma ya mike xaune yace “Daga ina haka da yamma?” Faisal na kallon fuskarsa ganin yanda manyan idanuwansa suka fito yace “You look pale, are you ohk?” El-ameen ya lashe lebbensa yace “Stress ne frnd, ya aikin?” Faisal yace “Alhmdllh, Ya captain naka….” Dai dai sanda Sumayya ke kokarin shigowa dakin da faranti me dauke da drink da ruwa jin an ambaci Junaid ta tabe baki ta tsaya jikin kofar, El-ameen yace “Yana gidansu!” Faisal yayi dariya yace “Kuna nan har yanxu kamar ‘yan biyu abun ku” El-ameen yayi murmushi yace “Sure!” Faisal yace “Uhmm!” El-ameen na kallonsa yace “Ya aka yi?” Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace “Bana tunanin akwai abinda ya isa ya hada ka da Captain…” Sumayya ta gyara tsayuwa da kyau ta baxa kunnuwa, El-ameen yace “Ban fahimta ba” Faisal yace “Daxu ya xo ya sameni ya kuma ban labarin baiwar Allahn da ku ke kokarin ganin kun ceto rayuwarta daga…..” El-ameen ya katse sa yace “No! Da yake kokarin ganin ya ceto rayuwarta dai” Faisal yayi murmushi yace “Haba Dr, bayanin da Captain yayi min is not enough ace kayi fushi haka, kuma naga kun saba haka a tsakanin ku, kar ka manta lada ba kadan ba xaka samu idan yarinyar nan ta dawo hankalinta” El-ameen yace “No ni bn yi fushi ba faisal, just dat nayi quit ne, ya nemi wani likitan ko ya kai ta psychiatry…” Faisal yace “No pls, kar kace haka Dr, ba don Junaid xaka yi ba don Allah xaka yi….” El-ameen yayi murmushi yana girgixa kai yace “You know what?” Faisal ya girgixa kai, yace “Wllh wllh ban yi kuma, I’ve quit, he shud take her to the psychiatry, ka dai ji rantsuwar musulmi na maka, but babu damuwa xai iya ci gaba da amfani da gidana” Sumayya dake jikin kofa har lokacin duk tayi confuse ta rasa gane kan maganar, to wace yarinya suke magana a kai, yanke shawaran kiran Suhaima tayi tasan xata bata labari, El-ameen ya mike yace “kaga am going to clinic yanxu faisal” faisal ya sauke ajiyar xuciya yace “Ban ji dadin rantsuwar da kayi ba El-ameen, don Allah xaka yi ba don Junaid ba” El-ameen ya koma ya xauna yace “Look faisal, kullum! I mean everyday, karfe bakwae na safe baya karasawa nake barin gida in tafi gun yarinyar don akwai injections din da nake mata a lokacin, before leaving kuma sai na tabbatar tayi breakfast dat’s around to eight, ina barin gidan xan kuma dawowa nan gida inyi wanka in shirya inyi breakfast snn in tafi clinic, a can clinic duk abinda nake da xaran sha daya da rabi yayi xan bari koma meye kuwa in tafi gun yarinyar don bata drugs dinta, in tilasta ta taci abinci sannan in kuma komawa clinic, duk abinda nake Karfe uku da rabi xan bari in kuma komawa gun yarinyar don bata drugs, sannan in sake komawa asibiti, Karfe bakwai da rabi a gidana yake min don a wannan lokacin ma tana da injections, baxan kuma bar gidan ba sai after ten don kafin ta kwanta Akwae drugs da xata sha, kasan sau nawa Junaid ke xuwa gidan?” Faisal yayi shiru yana kallonsa, El-ameen yace “Sau daya! shi ma sai da yamma ko kuma after magrib, kuma da ya xo xaka yi tunanin tsikararsa ake a gidan da kayi magana yace maka Mumy, ni ne ban san dadin tawa Mumyn ba, kasan matsalar da nake fuskanta yanxu gun parent dina kan yarinyar nan kuwa? yace ko biyar ban taba kashe mata ba I agree kuma dat is as a result of yana nuna shi me kudine, baya bukatan assistant din kowa, kasan dai yanda yake abubuwansa na girman kai, ni kuma kallonsa kawai nake don in kudin account dinsa sun yi wuta wllh basu wuce million uku ba in ma sun kai, kuma medication din hauka ba karamin kudi mutum xai kashe ba, yau da gobe yana cire dubu Dari dubu hamsin dubu dari biyu, dole kudin xai yi kasa, at dat time ko waye ubansa dole xai ce min i shud help ni kuma hakan nake jira dama, don kai kanka kasan waye ni idan baka tambayeni ba wllh baxan baka ba, in ko ka tambaya ko last card dina ne xan baka, kuma yace inyi excluding kai na a wa enda suka taimaketa a rayuwa tuni nayi hakan, don haka ka rakasa ya kaita psychiatry kawai frnd”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button