CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
Captain Ahmad Junaid

_By Khaleesat Haiydar_✍????

26…..

Mikewa faisal yayi ya d’aga kafada ya nufi kofa, da sauri Sumayya ta bar jikin kofar ta shige dakinta rike da farantin jin takunsa, faisal yayi ma Ummi dake parlor har lokacin sallama ya fita daga gidan, El-ameen ya koma ya kwanta tare da lumshe idonsa. Suhaima ce ta shigo parlor rike da waya tana kallon Hajiyarsu tace “Hajiyarmu yanxu sumayya ta kira ni….” Da sauri ta kalli khadija da ke kwance parlon sai kawai ta juya ta koma daki, Hajiya ta mike ta bi bayanta, khadija ta tabe baki ta ci gaba da danna wayarta. Junaid na kwance parlon Mumy that same day, idonsa lumshe kamar me bacci kamar wanda ya tuna abu ya mike xaune yana kallon wayarsa ya dauka yayi dialing number bugu uku aka d’aga, bayan sakwanni 20 jin ba ace komai ba daya bangaren yace “Uhn how you?” Jin an ki cewa komai still, yace “sai in kashe wayata ne” kamar xata yi kuka tace “Toh ina ruwana ni nace ka kira” murmushi yayi yace “Ohk, sai anjima” da sauri tace “Noo Ya Ahmad don Allah ka xo ka dauke ni, gida nake son dawowa” yace “Anki, xaman ki a can ya fi maki, sai kiyi ta neman fitina da Jawahir!” Katse wayar yayi ya ajiye yana murmushi, can ya mike ya fita ya koma part dinsa don tun da ya dawo daga gun faisal yake kwance parlon Mumy ko uniform bai cire ba, yana bedroom ya fito daga wanka yana shiryawa yaji an murda kofar parlor, juyawa yayi yana kallon kofar dakin har aka bude, faisal ya shigo da sallama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace “Glad you came” faisal ya karaso ya zauna gefen gado yace “ka jira har El-ameen ya sauko Captain, yayi sama da yawa, beside ni ban….” Da sauri Junaid yace “Xuwa kayi ka samesa?” Faisal ya d’aga masa gira, Junaid yace “Ohhh shit! Why? Meyasa xaka min haka, why did you go faisal, gaskiya ka bata min rai, who’s he da yake tunanin without him Allah baxai bata lafiya ba, shi din banxa, bana bukatansa a lamari na kuma, bana bukata….” Faisal yayi murmushi yana girgixa kai yace “Haka kawai in sa baki daga karshe in ji kunya, da dai ban san ku bane, duk ku yi ku gama” Junaid yayi tsaki ya ci gaba da shirin sa, yana gamawa ya juya yana kallon faisal yace “Ka sama min psychiatry din ne frnd?” Faisal yace “Psychiatry me kyau sai Abeokuta or Lagos, but I will advice you to take haka to na Abeokutan ya fi, Neuro Psychiatric hospital Aro” Junaid yace “Har Ogun state? No plss samo min a nan north” faisal yace “Toh ai na can yafi komai ne, ga qualified neurologist…” Junaid ya xauna gefen gadon yace “Abeokuta kuma? Or kasan me I shud just look for a private neurologist for her….” Faisal yayi murmushi yace “That’s money frnd, hospital ya fi!” Junaid yayi shiru, sai kuma ya shafa kansa a hankali yace “Allah xai rufa asiri, just get me a qualify one” faisal yace “ohkk dats not a problem, duk dai yanda ta yiwu in na gidan in na hospital,” Junaid ya gyada kai yace “Toh shikenan” faisal yace “Sai da abu ya kwabe maku sannan xa a wani xo a sameni…. Ni kallonku kawai nake kai da El,” Junaid yayi murmushi ya mike yace “Kaga xan kai mata fruits can gidan yanxu, muje part din mumy sai inyi kamar rakaka xan yi” faisal yayi dariya yace “Plss do and get ur freedom captain! You are getting old fa Mumys boy!” Junaid yace “Uhum kaga in tafiya xaka yi ka taso mu tafi!” Mikewa faisal yayi ya bi bayansa yana dariya, suka nufi part din Mumy, faisal yayi mata sallama, Junaid na shafa kai yace “Mumy bari in rakasa!” Mumy tace “Toh sai ka dawo” fita suka yi faisal na dariya, Suhaima dake tsaye bakin tap ta bi su da kallo tana tunanin xancen da Sumayya ta mata a waya, ajiyar xuciya ta sauke tana tunanin ta ina xata fara binciken da Hajiya ta sa ta, wai Mahaukaciya, tab, har Allah Allah take washegari yayi! Suna fita gidan Junaid ya kalli faisal yace “Kaga ban fito da mota ba, da taka xa mu je can gidan daga can sai ka ga Mahaukaciyar,” faisal ya buda ido yace “Da take neman hada aminai biyu ba!” Junaid ya tabe baki yace “No bata hada mu ba, frndship din ne ya xo karshe dama” dariya kawai faisal yake, Junaid ya karbi makullin hannunsa ya shiga motar ya tada. A hanya suka siya fruits sannan suka kama hanyar gidan El-ameen, mama na sharan parlon suka shigo, ta mike tana masu sannu da xuwa, Junaid sai kalle kallen inda xai ganta yake, mama jummai ta lura da hakan ta nuna masa gefensu tace “Ga ta can” juyawa yayi ya ganta xaune ta jingina da bango ta d’an dukar da kai alamar bacci take, xai yi magana Mama jummai tace “Babu yanda banyi da ita ta bar wajen nan ba ta ki, kuma ta ki kwanciya, ni dai na rasa gane kan baiwar Allahn nan, ko abinci taki ci, dama Aminu kadai yasan kanta, rashin cin abincin nan ba karamin daga min hankali yake ba, toh ko dai bata da lafiya ne” Junaid ya tabe baki bai ce komai ba, faisal kuwa kallonta kawai yake, duk da ba ganin fuskarta yake ba, Junaid ya kallesa sannan ya karasa kusa da ita ya duka kamar me rada yanda bbu wanda xai ji sa a hankali yace “Jasmine!” D’ago kanta tayi da sauri ta bude ido tana kallonsa, a hankali faisal ya dinga komawa baya yana kallonta ko kiftawa bai yi har ya isa jikin kofa bai sani ba, kalle kalle kawai take sai kuma ta mike tana kallon kofar jin alamar mutum, da sauri ta nufi kofar Junaid ya bi ta da kallo, tana isa bakin kofar ta tsaya tana kallon faisal, still yayi a wajen ko kwakkwaran motsi bai yi, har lokacin idonsa na cikin nata, juyawa tayi a hankali ta dawo kusa da Junaid ta xube gabansa ta xauna, kallo daya xaka mata ka ga ramar da tayi, mama jummai ta fara dariya tace “Wayyo, ca take Aminu ne baiwar Allah, to ko don bata ganinsa yasa taki sakin jiki ne? Kasan fa ko mara hankali dole ya gane me kyautata masa” Junaid ya lumshe ido ya bude ya ajiye mata ledan fruits din hannunsa ya bude, kallon fruits din kawai take, a hankali ya 6alli ayaba guda daya a bunch dinsa ya mika mata, karba tayi tana ta kallon ayabar kamar me son gano abu, can dai ta sa hannu a hankali ta shiga cire peel din yanda ta ga El-ameen na mata, Junaid dai kallonta kawai yake, tana gama cirewa ta mika masa, ya karba ya kai mata baki ta ki ci, duk yanda yayi da ita kin ci tayi ta kwanta nan wajen, Mama jummai tace “Wai yaushe Ahmad din xai dawo ne, ina jin fa yarinyar nan sabon da tayi da shi yasa ta ki sake jiki rashin ganinsa, tausayi take ban wallahi” mikewa Junaid yayi bai ce komai ba, ya nufi kofa, faisal dake wajen har lokacin yana kallonta ya basa hanya ya fice, sannan shi ma ya juya ya bi bayansa, xama Junaid yayi a balcony ya fito da wayarsa yana jujjuyawa, faisal ya sauke ajiyar xuciya yace “Me ka fahimta game da reaction din yarinyar….” Tsaki Junaid yayi yace “kaga Kawai na yanke shawarar tafiya da ita Abeokutan, xai fi! Maganar ta saba da wannan ta saba da wancan bai taso ba yanxu” faisal dai kallonsa kawai yake, Mikewa yayi yace “Xan koma gida kafin…..” Faisal ya katse sa yace “Haba Captain kana jin ance tun safe bata ci komai ba sai kace xaka tafi, ko da milk ne ka siyo a gwada bata mana” Junaid yace “Yea! But I don’t want my mum to start calling me, bayan bakin gate kadai nace xan raka ka, do me a favour by buying the milk and bringing it to them, ga Atm card dina” kallonsa kawai faisal ke yi, har ya fiddo card din ya mika masa, can ya girgixa kai yace “Nima yanxu Mumyna xata kira ni” Junaid yace “Ohk then! Let me send the gate keeper!” Daga haka ya nufi gun mai gadi, faisal ya girgixa Kai ya koma parlon, ai tana jin an tura kofa ta mike da sauri, faisal ya rungume hannayensa yace “Poor you!” Komawa tayi a hankali ta xauna. Ya juya ya fita daga parlon wani tausayinta na shigarsa, anya ba asiri bane wannan, ban da haka me yayi mata xafi haka har ya kai ta ga hauka at her young age!” Ko da ya fita har Junaid yayi masa gaba da motarsa, tsaki kawai yayi ya nufi titi don hawa tricycle, ko waye bai son uwarsa???

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button