CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

28…..

Faisal yace “Normal drugs na xaxxabi mana” El-ameen yace “Ohk, Allah ya bata lafiya” faisal yace “Ameen, idan Allah ya kai mu gobe xa a tafi da ita kudu” El-ameen ya d’aga kafada bai ce komai ba, faisal yace “Kayi wanka ka ci abinci sai ka sha magani xaka fi jin dadin jikin ka,” ba musu El-ameen ya mike ya shiga bathroom, faisal na ganin haka ya jawo wayarsa da sauri ya nemo number Junaid, cikin hanxari ya shiga rubuta masa text kamar haka “Ban yi tunanin akwai abinda ya isa ya shiga tsakaninmu da kai har ya hada mu haka ba, all the same Allah ya huci zuciyarmu, ba wai don ka hakura kuma na maka text din nan ba sai don in nuna maka ni babba ne….” Daga haka faisal ya tura text din sai da ya tabbatar ya tafi sannan ya maxa yayi deleting ya mayar da wayar ya ajiye, ko minti goma faisal bai kara a gidan ba yayi gaba. Junaid na xaune parlon Mumy yana cin abinci text din ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin sunan El-ameen, ya bude text din ya karanta content din, murmushi kawai yayi ya ajiye wayar, can ya mike ya dawo parlor ya d’an saci kallon Humainah dake kwance tana danna wayar fatima, karbe wayar yayi yace “Ke baki iya gaisuwa ba ne” mikewa tayi xata wuce daki ya fixgota, ta kusa fadowa kansa, turasa tayi kmr xata yi kuka tace “Ni ka kyaleni,” ya matso kusa da ita yace “Anki” ta bata fuska xata yi kuka, yayi murmushi yace “Abinda kika fi iyawa kenan ai” saketa yayi ya fita daga parlon ta bi sa da harara. Karfe takwas saura na dare El-ameen ya fito rike da makullin motarsa xai tafi clinic a bisa umarnin dad dinsa, bin sa da kallo Ummi tayi har ya fita, yana shiga motarsa driver din Abbansa ya karaso kusa da motar, xuge glass yayi yana kallonsa yace “Ya aka yi Umar?” Drivern ya d’an sosa kai yace “Yallabai dama, ji nayi Hajiya xata aika wasu xuwa can gidan ka, ina jin akwai fa binciken da take, xuwa anjima xa su je, nine ma xan kai su wai….” El-ameen ya firfito da ido yace “Gidana kuma, me tace maku xa ku je ku yi?” Umar yace “Wllh ban san me tace masu xa su je yi can ba, ni umarni kawai ta bani in kai su” El-ameen da hankalinsa ya gama tashi yace “Ohk ohk nagode kwarai Umar…” Umar din yace “Amma yallabai ka rufan asiri, naga kai din mutum ne mai kirki shi yasa nace bari in ankarar da kai, in ma da matsala ne sai ka gyara” El-ameen yace “nagode kwarai umar, kar ka ji komai” daga haka ya ja motar ya bar gidan, sai da ya fara tsayawa a atm machine ya cire kudi sannan ya nufi gidansa direct. Yana isa gidan yayi parking waje ya fita ya shiga ciki, murda kofar parlon yayi a hankali ya tura ya shiga, bbu kowa parlon sai Jasmine da plate din potatoe gabanta ta kifar kasa, mikewa tayi jin an bude kofa ta kalli kofar da sauri, ya tsaya ya rungume hannuwansa yana kallonta, a hankali ta shiga tahowa tana kallonsa itama har ta iso gabansa ta tsaya, murmushi ya sakar mata murya can kasa yace “Jewel!” Ita dai kallonsa kawai take, ya matso kusa da ita a hankali ya ja hancinta yace “Did you miss me” taba nasa hancin tayi a hankali ita ma, ya wara manyan idonsa yana ‘yar dariya sai ga mama jummai ta sauko daga stairs rike da jakunkuna biyu, ai tana ganin El-ameen tayi still, ya kalleta ya kalli jakar da mamaki, lkci daya murmushin dake dauke fuskarsa ya bace yace “Ina kuma xaki da jaka mama?” Ae sai ta fashe da kuka tace “Yo naji Ahmad na cewa gobe xai kai ta asibiti ta xauna a can, a gida ma ana yi bata warke ba sai wani asibiti can, ku bar ni in je a mata na gargajiya mana tun da ba a dace da na baturen ba, don Allah ni a bar ni da ita xan kula da ita har Allah ya bata lafiyan. Idan ya so sai in baku addreshin kauyena, ku yarda da ni baxan cuce ta ba…” El-ameen kallonta kawai yake da mugun mamaki, yanxu da Allah bai kawo sa ba tafiya da ita kawai xata yi, karasowa parlon yayi yace “Ehh wannan kuma gaskiya ne mama kin kawo shawara me kyau, Amma bari muyi shawara da Junaid din koh” tana matsar kwalla tace “Toh” xaunawa yayi yana kallon Jasmine dake ta binsa kamar xata shige jikinsa, yayi murmushi ya xaunar da ita ya jawo ragowar potatoe din da ta xubar ya dau daya ya kai mata baki, ta bude bakin ya saka mata, kallon Mama jummai dake kallonsu tana ‘yar murmushi yyi yace “Mama xaki d’an siyo mata fruits a bakin titi don Allah,” tace “Toh” ya fiddo kudi ya mika mata yace “Na dubu xa ki ce a baki” karban kudin tayi ta fita sabe da gyalenta, jasmine ta bi ta da kallo, mikewa yayi ya isa kofa yana lekan ko ta tafi sannan ya juyo ya kusa cin karo da Jasmine da har ta biyosa, murmushi yayi ya isa gun jakunkunan da mama jummai ta sauko da, ya bude yaga wanda ke dauke da kayan Jasmine din, duddubawa yayi ya fiddo da hijab ya sa mata, sannan ya dauki jakunkunan biyu ya rike hannunta suka fita daga gidan ya kulle da key, yana rike da hannunta ya nufi gun mai gadi, yace “Kana ji na Usman, xa mu dan yi tafiya ne amma baxa mu dade ba” ya fiddo kudi aljihunsa ya mika masa yace “Ga kudin ka na wannan watan, yanxu xaka tafi xan kulle gidan ne, sai ka tsaya bakin gate har mama ta dawo ka bata Jakarta da kudin nan ita ma, da xaran mun dawo xan neme ka” Mai gadin da ko kadan bai ji dadi ba yace “Toh shikenan yallabai, Allah ya kiyaye hanya, ya dawo da ku lafiya” El-ameen yace “Ameen, d’an je ka canja min wutan gidan xuwa na gen” ba musu maigadin yaje yayi yanda yace masa gidan ya dawo ba wuta gaba daya, ya dawo shima ya hada nasa kayan, suka fito gaba daya, El-ameen ya kulle gidan yace “Don Allah ka jira har tsohuwar ta dawo ka bata hakkinta da kayanta,” mai gadin yace “In’sha Allah yallabai” daga haka El-ameen ya nufi motarsa da ita da sauri yana rike da nata jakar kayan, ya bude front seat yasa ta shiga, ya ajiye jakar kayanta a bayan motar ya rufe, ya xaga ya shiga motar ya tada ya bar wajen, kafin ya isa titi ya ga Mama jummai na ta xabga uban sauri rike da ledan fruits, ta basa tausayi sosai, yasan tsakaninta da Allah take son yarinyar amma cutar dake damunta na asibiti ne ba na gargajiya ba, kuma tun da ta fara tunanin guduwa da ita wataran ko ba yanxu ba sai ta gudu da ita din, may be some other time xa su kuma nemanta, kallon jasmine yayi yaga yanda ta kafa ma glass din motar ido ko kiftawa bata yi tana kallon motoci dake tafiya kan titin kamar me son gano abu, yayi murmushi ya kamo hannunta yace “Jewel” kallonsa tayi da sauri, ya sakar mata murmushi, ta maida dubanta kan titi, sosai yake tausayinta don a yanxu dai bata da gata a duniya sai nasu, murmushi yayi tunawa da yayi axumi uku ya hau kansa fa. Tafiya kawai yake ba tare da yasan takamaiman inda xai kai ta ba ma, duk he’s just confuse, yasan ko ya kira Junaid yanxu ma ba fitowa xai yi ba yana can Mumy ta gama basa abinci ta lullubesa yayi bacci, tsaki yayi yana girgixa kai.

✍????
Haske Writers Association????
Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

29….

Parking yayi a gefen titi yana tunanin inda xai kai ta, gidan frnds dinsa masu mata? girgixa kai yayi don yasan ba lallai basu yi thinking negatively ba, Hotel? Ya girgixa kai coz it’s not decent, to ina xai kai ta? Dafe kansa yayi cike da confusion, can ya dago ya juya yana kallonta ya ga ita ma shi take kallo, yayi murmushi a hankali yace “Ina xan kai ki jewel?” Dauke kanta tayi ta jinginar jikin glass din motar tana lekan waje, ya tada motar ya kuma hawa kan titi ya dinga driving din kamar bai son yi, cikin mintunan da basu wuce ashirin ba ya iso clinic, yayi parking a wajen da aka tanadar don ajiye mota, kalle kallen haraban hospital din ya dinga yi, ganin patients ne Kawai ya fito, ai tana ganin ya fita ta fasa ihu ita ma xata fito, ya juyo da sauri yace “Wait jewel yanzu xan bude maki” xagawa yayi daya side din ya bude motar ya fito da ita, kalle kalle ta shiga yi, ya rike hannunta ya shiga asibitin da sauri, bai saurari nurses din dake gaida sa ba ya haura sama da ita ya bude office dinsa suka shiga, key ya sa ma kofar sannan ya juya yana kallonta ya sauke ajiyar xuciya yace “We’ve got a good solution koh” kama hannunta yayi ya nufi bedroom din dake office din ya xaunar da ita kan gado yana kallonta, kwan kwasa office dinsa ya ji ana yi ya mike da sauri ya fita, mikewa tayi ita ma da saurinta ta bi bayansa, ganin ta biyosa yasa bai bude kofar ba yace “Who’s there?” Muryar nurse yaji tace “ur attention is needed at the theatre sir” a fusace yace “Toh da ban xo ba fa” shiru tayi yyi tsaki ya kama hannun Jasmine ya maida ta dakin, xaunar da ita ya kuma yi a hankali yace “Look jewel, yanxun nan xan dawo kar ki bi ni plss” ya kusa second goma yana kallonta sannan ya mike a hankali xai fita ita ma ta tashi da sauri, yace “Ohhw ina xan kai ki jewel?” Fita yayi ta bi bayansa, ya isa show glass din dake office din me dauke da magunguna da ruwan allurori ya bude ya dauki wani kwalban allura ya rufe, syringe ya dauka ya juya suka kusa cin karo, yace “Sorry!” kama hannunta yyi suka koma dakin ya sa ta xauna, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata a lap, ‘yar kara kawai tayi masa tana bata fuska, yayi kasa da murya yace “Sorry jewel!” sun kusa minti goma xaune yana yi yana kallon agogo, yaji an kuma kwankwasa kofa, ya mike da sauri ita ma ta mike sai dai da ganinta kasan duk jikinta ya mutu, rike hannunta yayi ganin yanda take layi ya fito office din yace “Yes!” Muryar Abbansa yaji yace “S’ako na bai iso gare ka bane, ka wani garkame office kana ce min yes” xaro ido yayi yace “Ohh No, kaya nake canzawa ne Abba gani nan xuwa yanxu” Abba bai kuma cewa komai ba, hakan yasa ya kama hannunta suka koma dakin, kwantar da ita yayi ta lumshe ido, ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya bude inda kayan shiga theatre dinsa suke, ya cire na jikinsa ya saka sannan ya lullubeta ya fito daga dakin ya rufe da key. Sha biyu saura ya fito daga theatre, yana komawa office ya bude dakin yaga bacci kawai take, toilet din dake nan ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kananun kayansa ya fito office ya xauna ya kifa kansa kan table don bacci yake ji, wata nurse ta shigo rike da cup din coffee ta ajiye masa kan table tace “Sir” dagowa yayi yace “Thanks” har ta kai kofa xata fita yace “Nurse Sharifah” juyawa tayi ta dawo tace “Sir?” Yace “Nan sama kike ko k’asa yau?” Tace “a nan nake duty” yace “good, akwai patient a dakina, i want you to stay with her throughout the nyt, mental disorder gareta, in case xata farka cikin dare ki rakata restroom” shiru tayi tana kallonsa tsoro bayyane fuskarta, murmushi yayi yace “She won’t hurt you, bata komai, just in case kar ta tashi ne yasa nace ki tsaya da ita” a hankali tace “Ohk sir… Let me explain to…” Katse ta yayi yace “No! Xan je in mata bayani” daga haka ya mike ya fita. Ta lallaba ta isa kofar dakin ta tura a hankali ta leka ta ganta tana bacci cikin bargo, a haka ya dawo office din yace “Ki shiga baxa ta maki komai ba nace” gyada masa kai tayi ta shiga dakin, ya dau coffee dinsa ya sha bayan ya huce sannan ya mike yayi kwanciyarsa kan kujeran dake office din. Can misalin Karfe uku ihunta ya farkar da shi ya mike da sauri ya nufi dakin dai dai lokacin da nurse din ma ta fito da gudu, shiga dakin yayi ya ganta tsaye sai ihu take, ya karasa da sauri ya rike hannunta yace “Jewel!” Tsit tayi tana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya ya xaunar da ita gefen gado, ya juya xai fita ta mike ta bi sa da sauri, nurse din na tsaye bakin kofar fita office har lokacin yace “Taho ki rakata restroom nace babu abinda xata maki” da kyar ta karaso ta shigo dakin, shi ya kaita toilet din, ya juya yana kallon Nurse din ta karaso a hankali ita ma ta shiga toilet din ya juya ya fita. Da asuba yana kwance idonsa lumshe bayan ya dawo daga mosque yaji mutum kusa da shi, bude ido yayi da sauri ya mike xaune yana kallonta, murmushi ya sakar mata yace “Good morning jewel” dagota yayi ya xaunar da ita gefensa, remote ya dauka ya kunna mata tv, wani kallo ta dinga yi ma TVn kamar idonta xai fito, dariya ta basa ya mike ya shiga daki yaga nurse din rakube kasan gado tana bacci, yace “Nurse Sharifa” mikewa tayi da sauri tana murxa ido duk da ganinta kasan a tsorace take, yayi murmushi yace “Kin yi sllh?” Tace “Yes sir” yace “Good” toothbrush da paste dinsa ya dauko ya mika mata yace “Xaki wanke mata baki” ta karba tana kallonsa, ya fito ya dagota taki tashi idonta kyar kan TV ko kiftawan kirki bata yi, dariya ta basa sosai ya kuma dagota ta fasa masa ihu har lokacin bata dauke idonta kan kallon ba, ya dau remote ya kashe tvn, sai a sannan ta juya ta kallesa, yayi murmushi ya dagata ta mike ya shiga daki da ita, kin yarda nurse din ta wanke mata baki tayi, hakan yasa ya wanke mata da kansa, ganin hadiye komai take yasa bai mata amfani da ruwan toilet din ba, ya fita ya dauko table water ya bude ya bata ta sha ya kama hannunta suka fita, ya kalli nurse din yace “Tea xaki je ki hado min plss” ba musu ta fita sai ga ta ta dawo da cup din tea ya karba yace “Thank you, kafin ki tafi ki dawo” tace “Ohk sir” sannan ta fita, jasmine ya shiga ba tean, ta sha kadan taki shan sauran da alama tea bai dameta ba, mikewa yayi ya tafi ya wanke bakinsa toilet, juyawan da xai yi ya ganta tsaye bayansa, murmushi yayi ya kama hannunta suka fito office, ya xaunar da ita sannan ya shanye sauran tea’n, TV ya kunna mata don yana son fita ya gaida Abbansa, ai ko ta nutsu sosai tana kallon mutanen dake yawo a tvn, ya mike a hankali yanda baxata lura ba ya fita ya haura last floor xuwa office din Abbansa, wani aikin Abban nasa yasa sa, ransa bai so ba amma bai yi musu ba ya shiga yi, yana cikin yi aka yi interrupting power, ya xaro ido sanin kila yanxu xata fara ihu, da sauri ya dinga signing files din, cikin minti sha biyar ya gama ya fice, ya sauka xuwa office dinsa, yana budewa yaga wayam daki ya nufa ya tura nan ma wayam, ya xaro ido ya shiga toilet nan ma bbu ita, wani mugun tashi hankalinsa yayi ya fito da sauri ya dinga dube dube ya sauko har downstairs yana kallon nurses din yace “wata patient bata sauko ba yanxu” bai jira cewarsu ba ya fita haraban asibitin da sauri, ya dinga dube dube bai ganta ba, gun masu gadi ya nufa da sauri ya tambayesu suka ce basu ga kowa ba, komawa reception yayi ya dinga yi ma nurses din masifa basu ga wata ta sauko ba yanxun nan, nan suka shiga dube dube su ma cikin ward,haka aka yi ta nemanta cikin asibitin har da likitoci da cleaners, wasu na tunanin anya kuwa Dr El-ameen dai dai kansa yake ganin yanda ya wani rikice nurse Sharifa ma duk hankalinta ya tashi barin da tasan ba mai hankali bace patient din, har Abba sai da ya sauko jin wai ana neman patient daga bakin wani likita, kallon d’an nasa kawai yake yana son sanin wace patient ce wannan wanda shi kadai yasan da ita a asibitin, Salatin da Dr Ibrahim wanda office dinsa ke kallon na El-ameen yayi ya ja hankalin nurses da wasu likitocin, da hanxari duk aka karasa wajen aka gansa tsaye bakin office din yana kallon ciki da mamaki, El-ameen ya karasa shima yana kallon office din, tsaye take a office din duk tayi kaca kaca da uban files din dake kan table dinsa, ta bude show glass duk ta watsar da magunguna da allurorin dake ciki, El-ameen ya d’an saci kallon Abbansa da ya rungume hannu yana kallon ikon Allah, daga likitocin har nurses din kallonta suke su kalli El-ameen, hakan ya bata tsoro sosai ganin yanda aka taru bakin kofar ana kallonta, ta fasa wani shegen ihu da karfi tana kallon El-ameen, sunkuyar da kansa yayi, ta dinga ihu can ta tafi bayan glass da gudu ta labe har lokacin ihu take, da kyar ya dago kai yana kallon Abbansa yace “Abba… Brain disorder gareta, I..I… She’s under medication ne Abba, jiya da xan xo na taho da ita…” Wani mugun kallo Abba ke masa yace “Asibitina yayi kama da na mahaukata?” Sosa kai yayi xai yi magana Abba ya masa wani uban tsawa yace “Uwar ka xaka gaya min, wasu mahaukatan iyayen ne suka baka ‘yar su ka sata under medication har kake yawo da ita?” Ya lumshe ido ya bude a hankali yace “No, A gida nake mata treatment din Abba, dama…dama akwai injection da nake mata da daddare ne to kuma ka kirani clinic shi yasa na taho da ita… Yanxu ma xan maida ta gidansu…” Abba yace “Amma arnaye ne iyayenta koh?” Shiru yayi bai ce komai ba, Strictly Abba yace “Ka maida masu ‘yar su ka basu shawaran su kai ta asibiti, na kuma hanaka aikin nan daga yau, in ma kana son concentrating a field dinka na neurology ne yanxu you can go and apply for work a psychiatry ba ka dinga yawo da mahaukata ba har kana kawo min su asibiti suna min barna” daga haka Abba ya juya ya bar wajen, nurses din ma duk suka juya, jiki a sanyaye El-ameen ya karasa cikin office din ya kamo hannunta suka fita, sai wani shisshigewa jikinsa take a tsorace, likitocin dake gun suka bi sa da kallo, hijab dinta ya sa mata suka fita xuwa gun motarsa yasa ta shiga ya tada mota yyi warming ya bar haraban hospital din. Hotel ya nufa da ita don dat was the only option a lokacin, yana parking a haraban hotel din kiran Junaid ya shigo wayarsa, yayi mamakin ganin kiran don yasan bai xuwa can gidan da safe bare ace yaje ne ya gani a rufe, ya kalli agogo yaga bakwai da wani abu, daga kiran yayi daga daya bangaren Junaid yace “I saw ur text jiya, kuma I hail you da ka nuna kai babba ne” El-ameen yace “what’s he talking about” Junaid yace “Really! There’s no need of pretending, kana ina yanxu” El-ameen ya kalli inda yake sannan ya gaya masa, Junaid yace “Me kake a hotel” El-ameen yayi shiru sannan yace “Why are you even asking?” Junaid yace “Magana xa muyi, shud I come over…” El-ameen yace “aikin fa?” Junaid yace “Na dau hutun sati daya…” El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace “Good! Taho ka same ni yanxu” daga haka ya katse wayar, junaid ya sauke ajiyar xuciya ya dafe kansa don maganar da faisal yayi masa jiya ya tsaya masa, so yake yaji mai El-ameen xai ce game da shawaran faisal, in har shima ya basa go ahead xai jaraba ya ga ko me yiwuwa ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button