CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
⚓ Captain Ahmad Junaid ⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
3…..
Wani kallo Mumy tayi masa tace “Kaga ka kiyaye ni Ahmad, baxa ka gun El-Ameen din ba asibiti xa mu” shiru yyi yana kallonta sanin baxae taba convincing dinta ba, a hankali yace “Toh kiyi hkuri mumyna mu tafi asibitin” jakarta ta dauka tace “Sake ni mu tafi” saketa yyi dai dai lkcn da wayarsa ya fara ring, fiddowa yyi a aljihu yana kallon me kiran nasa ya ga El-Ameen ne, ya juya ya kalli Mumy ya ga kallon wayar take, d’agawa yyi ya kai kunne daga daya bangaren El-Ameen yace “ya ne captain, kana gida yau?” Junaid ya d’an saci kallon Mumy ya ga kallonsa take, yace “Noo! Don’t worry frnd Mumy tace mu tafi clinic kawae ba sai na xo ba” El-Ameen yace “What are yhu talking about guy?” Junaid yace “No ba komae wllh, kawae dae tace mu tafi asibiti ne” tsaki El-Ameen yyi yace “HeyJunaid are you ohk, wat are yhu sayin?” Junaid yace “Ohk Tnx for ur care frnd!” D’aga hka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya mayar aljihunsa yana sinne kai, Mumy tace “Don me xaka ce Mumy tace, maimakon kace Abban ka ne yace kaje clinic” Junaid yyi shiru yana kallonta, komawa tayi ta xauna ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh shknn, ka tafi can ya duba ka, amma yana prescribing maka magunguna ka dawo Ahmad, I repeat my self ka dawo” farin ciki ya lullubesa sae dae yyi kkrin boye hakan yace “Toh Mumy I promise” har bakin motarsa ta rakasa tace “Drive carefully” yace “Sure mum” tana tsaye har ya bar gidan snn ta juya xata koma bangarenta, xaune ta ga Hajiya Fatee da Hajiya Bilkee a balconyn Hajiya fateen suna kallonsu, Mumy ta karasa tayi masu sannu da xama, Hajiya Bilki kadae ta amsa da yauwa a dakile, juyawa Mumy tayi xata bar wajen Hajiya Fatee tace “Ynxu an ma hana d’an gwal din xuwa gaida mu tsabar mulki” juyawa Mumy tayi tana kallonsu tace “Ayya Bashi da lfya ne, ynxun ma gun likita xa shi” bbu wanda ya tanka ta cikinsu, ta nufi bangarenta ba tare da ta sa ma kanta damuwarsu ba. Junaid na isa ya tarda El-Ameen na clinic, bae so hkn ba amma bbu ynda ya iya hka ya nufi Babban asibitin Dad din El-Ameen din, don shima kwararren likita ne da yyi fice a Nigeria, da yake Nurses din sun san tsakanin Junaid da El-Ameen, bbu wanda ya dakatar da shi xuwa office din El-Ameen din, murda kofar yyi ya shiga babban office din, El-Ameen dake xaune yana dube duben files sanye da farin glass a idonsa ya dago yana kallon Junaid, ajiye pen din hannunsa yyi ya rike ha6a yace “Kan ka daya kuwa captain?” Dariya junaid yyi ya xauna kan table din office din yace “Kai da ban yi hka ba da Mumy bata bari na xo ba yanxu ai” El-Ameen ya girgixa kai yace “Mummy’s boy, na ga randa xaka girma ka samu freedom din kanka” murmushi yyi yana shafa kansa yace “Uhm am 30 ynxu kace ban girma ba, ae kila har in mutu baxan samu wannan freedom din gun momma na ba” El-Ameen yyi dariya yace “Idan kayi aure xa ka samu” murmushi Junaid yyi yace “Aure kuma” kallonsa El-Ameen yyi ya cire glass din idonsa yace “Amma ba ka jin ddi koh, you look weary?” Junaid ya lumshe ido ya bude da damuwa yace “Kinda frnd! Am just disturb, bani da kwanciyar hankali kwana biyun nn, M just nt my self…” Rike kai yyi ya kasa ci gaba, El-Ameen ya dafa sa yace “What’s wrong frnd, tell me ur problem, ‘Yan gidan ku ko?” Junaid ya d’aga kai yana kallonsa cike da damuwa yace “No! Wnn mahaukaciyar ban san ko laifi nayi da na kwace yaron nan a hannunta ba, duk na kwanta ita nake tunawa nake gani, k’asa bacci nake yanxu duk bani da sukuni” El-Ameen ya ja tsaki ya mayar da glass din idonsa ya jawo files din gabansa yana ci gaba da dubawa yace “Thought it to be something better ma, wai mahaukaciya” wani tsakin ya kuma ja, Junaid ya runtse ido ya watsar da files din yace “Haba Dr in ce maka bana iya bacci kace min yhu thought it was somethin better,” El-Ameen ya rike chin dinsa yana masa wani irin kallo da mamaki yace “Wae halan kana da dangantaka da mad woman din nn ne junaid” a fusace Junaid yace “Wa ya sani” wani dogon tsaki El-Ameen ya kuma ja yace “Kaga ka rabu da ni, I have meaningful things doing ynxu, aikin gaba na ma ya ishe ni stop bothering me plss da wata mahaukaciya can.” Kallonsa junaid ya tsaya yi na kusan minti biyu kafin ya sauka daga kan table din da yake ya dauki wayarsa da makullin mota ya juya ya nufi kofa, bin sa da kallo El-Ameen yyi kafin ya birkita lallausan gashin kansa a xuciyarsa yace “What’s wrong with Junaid da xae damu kansa ya damu wani da wata gagarumar mahaukaciya can” mikewa yyi da sauri tun kan ya fita ya kulle kofar office din yace “Look Captain, to ynxu me kake son ayi da rashin baccin naka, ko kuma dai kawai mu je ka ba mahaukaciyar hakuri?” Junaid ya kallesa yace “bude min kofa” El-Ameen na ‘yar dariya yace “Of course No baxan bude maka ba sae ka gaya min dalilin ka na xuwa gu na, which help do yhu want me to render yhu, mu je ka nemi gafararta mad woman din ne” tuni idon Junaid ya sauya kala, still behaving gently yace “Bude min kofa nace” El-Ameen yace “Noo!” Wani kara yyi ya cakumo sa yana huci yace “Bude min kofa Ahmad!” Murmushi El-Ameen yyi yace “Naki! ka xama Zaki a nn in ga” turasa da karfi Junaid yyi ya koma kan dogon kujera ya xauna ya rike kai, El-Ameen yyi dariya ya koma kan office chair dinsa ya xauna, sae bayan kusan minti goma Junaid ya dago kansa, ya kalli El-Ameen dake ta aikinsa, El-Ameen yace “Har iskokan sun sake ka kenan” Junaid bae ce komae ba ya kauda kai, mikewa El-Ameen yyi ya dawo gefensa ya xauna yace “Now tell me, ya kake son ayi?” Junaid ya sauke ajiyar xuciya cikin sanyi ya fara magana, “Frnd! May be tana son in taimake ta ne, shi yasa take bi na, she want me to help her” El-Ameen ya kwalalo manyan idanuwansa yace “Kayi me?” Shiru Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen ya girgixa kai yace “Yhu must be crazy Junaid, meye hadin ka da wata mahaukaciya can har kake tunanin taimakon ta, kai ka daura mata haukan, ko kasan me ya haukatar da ita? Wait! which help ma xaka iya rendering dinta tukun, taking her to psychiatry nd staying with her there ko yaya?” Junaid ya tabe baki yace “Ae dan Mumy da Abba baxa su yrda bne da nayi hkn wllh” El-Ameen yyi dariya sosai yace “Ehh lallai Junaid ka ja ma kanka” Junaid yyi kasa da murya yace “Listen to me plss Dr, ban da kai akwae wanda xan kai ma damuwar da na k’asa gaya ma mahaifiyata duk kusanci na da ita, why kake min hka frnd?” El-Ameen ya sauke ajiyar xuciya yace “Noo ba hka ba Junaid, ynxu tell me ya kake son ayi, hw did yhu want me to help in here?” Cikin kwantar da murya junaid yace “yhu are a Neurologist as well as a qualified MD, I knw yhu can cure her by the grace of Allah idan ka sa kanka, yhu neva can tell where one’s reward Lie’s” wani matsiyacin kallo El-Ameen ke yi masa kafin ya mike yace “Gaskiya ka janyo ma kanka fitina ka ja mana muma da muke tare da kai Ahmad, dama ban da abun ka me ya kai ka kama mahaukaciya kai da kake tuki a mota, Ohh My God! ga irinta nn ka tabo aljana, don Wllh yhu are not on ur right senses” Mikewa Junaid yyi shi ma yace “Stop this El-Ameen, meye illar taimakon Baiwar Allah da xa mu yi? Haba idan wani yace min xaka yi hka I won’t believe wllh,” El-Ameen yyi shiru yana kallonsa baki bude, cike da mamakin aminin nasa, Junaid ya juya ya nufi kofa rai bace, girgixa kai El-ameen yayi yace “listen Captain” ko sauraransa Junaid bae yi ba ya fice daga office din, ya birkita kansa ya bi bayansa da sauri, a tare suka isa inda motar Junaid yake, El-Ameen yace “Haba frnd listen to me, ynxu mu koma ka min bayani sosai yanda zan gane abinda kake nufi don wllh am confuse” hararansa Junaid ya shiga yi yace “Ka dae san ba kai kadai bane abokina likita ba koh?” El-Ameen ya d’an yi murmushi yace “I know” hannunsa ya rike suka koma asibitin dae dae lkcn da wayar Junaid ya shiga ringing, fiddo wayar yyi yaga Mumy ce ke kiransa, El-Ameen yace “Mummy’s boy” d’agawa Junaid yyi daga daya bangaren Mumy tace “Ka kyauta Ahmad” Junaid ya marairaice yace “Ohh Ummata, drip karami yake kara min ne fa, nd am feeling much beta ynxu har na ci abinci kuma” Murmushi Junaid yyi bayan ya gama sauraranta yace “in sha Allah mum” daga hka ya katse wayar suka nufi office din El-Ameen.
El-Ameen ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yana kallon Junaid yace “ina jin ka, Allah sa ka dawo senses dinka yanxu, ya kake son ayi kace?” Junaid ya lumshe ido ya bude yace “Wae da cure dinta nake son kayi ko nawa ka bukata xan biya ka” El-Ameen yyi murmushi yace “Ohh i see, A can kan bola xan dinga tafiya ina samun ta kenan” Junaid ya ce “Noo of course, dauko ta xa mu yi” El-Ameen ya bude ido yace “Mu kai ta ina? Gidan ku?” Hararansa Junaid yyi yace “Plss frnd be serious, a gidan ka xa mu ajiye ta, ni idan nace xan ajiyeta a nawa gidan dole sae su Mumy sun sani, barin ma ni da nake da ‘Yan sa ido, kai kam bbu me sa maka ido” El-Ameen ya buga table din gabansa yace “Wnn ne kuma baka isa ba Malam, I can’t keep a mad woman in my house, the house that’s meant for my wife!” junaid yyi shiru yana kallonsa, a hnkli yace “Ohk let me rent an apartment” Tsaki El-Ameen yyi yana Mamakin Matsalar Junaid, anya kuwa kansa daya, Junaid yyi murmushi yace “I knw u are thinking if am alryt at all, tausayi ne ba wani abu ba frnd, naga yarinyar is too young ace hakan ya sameta duk da ba a ja da ikon Allah, baka san inda rayuwa xae yi da kai ba wataran frnd, it really pays to be kind, and you neva can tell where one’s reward lies! ni xuciyata daya nake son taimakonta saboda Allah, I will pay yhu wat ever amount yhu require for the bill, ni dae fatana ta samu lfya ta nemi ‘yan uwanta” wani dariya El-Ameen yyi yana tafe hannu yace “Toh governor Ahmad Junaid, don this is the government’s job not urz” mikewa Junaid yyi yace “What ever, ynxu dae let me start lookin for an apartment” El-Ameen ya daga kafadarsa yace “Left to yhu, amma ina guje maka reaction din yan gidanku idan suka ji shirmen da kake shirin aikatawa” Junaid yyi tsaki yace “Ni dae nemo plaster ka sa min a hannu am leaving, gobe I might come back idan na sami apartment” El-Ameen ya mike ya dauko plaster ya mika masa yana kallonsa cike da mamakinsa, a tare suka fito, El-Ameen yace “Yi Dropping dina a gida kawae, na mance key a office” a hanya El-Ameen ya kwashe da dariya yace “Tabdi wa ya ga Capt Junaid da taimakon mahaukaciya, but idan taimako kake son yi Why not kaje orphanage home kayi ne” share sa Junaid yyi, yana parking kofar gidansu ya juya yana kallonsa fuskarsa daure yace “Sae da safe” El-Ameen yyi dariya ya bude motar ya fita sanin har ya ji haushi ne.