CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association????
Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

36…..

A hankali ta koma baya jin bai ce komai ba har lokacin idonsa na kanta, ta d’an bata fuska ta juya masa baya dai dai shigowar El-ameen ward din, da sauri ya karaso gun gadon yana kallonsa ganin idonsa bude, murmushi ne yayi escaping lips dinsa yace “Ohh Captain! You are back” Lokaci daya murmushin ya bace ganin yanda Junaid ke kallonsa, dukawa yayi a hankali yace “Ahmad!” Nan ma dai kallonsa kawai Junaid ke yi, El-ameen ya girgixa kai da sauri yace “No plss say something frnd, kana ji na…” D’aga sa yayi xaune yace “Ahmad talk to me” dafe kai El-ameen yyi a xuciyarsa ya dinga furta innalillahi…. Jasmine ta matso kusa da shi a hankali tana kallonsa, Dagowa yayi da kyar ya kuma kallon Junaid yace “Captain!” Dukawa tayi kamar yanda yayi ita ma cikin sanyayyan muryarta tace “Captain!” El-ameen ya juya yana kallonta, ta buda masa ido tace “Captain” juyawa yayi ya maida dubansa ga Junaid yaga kallonta yake, mikewa El-ameen yayi jiki a sanyaye ya nufi kofa, jasmine ta bi sa da kallo har ya fita sannan ta juya tana kallon Junaid tace “Captain” kallonta kawai yake, ta matso kusa da shi tana kallon shoulder dinsa a hankali tace “Ciwo!” Sai kuma tayi murmushi tace “Yana ma zafi?” Kallonta Kawai har lokacin ko kiftawa bai yi, shiru tayi kamar me naxarin abinda ta fada can ta rike kanta ta sulale nan wajen tayi k’ara tana cewa Umminta dai dai shigowar El-ameen da Abbansa sai wani Dr faruqh, Junaid ya lumshe ido ya bude, El-ameen ya karasa da sauri ya dagota yana kallonta, Abba ya girgixa kai tare da yin kwafa yace “When I say tomorrow I mean tomorrow” a sanyaye El-ameen ya maida ta kan gadon da take ya kwantar da ita har lokacin ta ki bude ido, Abba dake ta kallon Junaid ya duka gabansa a hankali yace “Ahmad?” Junaid ya dago ya kallesa sannan ya maida kansa kasa yace “Na’am” Abba ya juya ya kalli El-ameen da ya xaro ido yana kallon Junaid, da sauri ya karaso har lokacin idonsa a kansa, Abba yyi murmushi yace “Alhmdllh! Ina ke maka ciwo yanzu?” Junaid yayi shiru, a hankali Abba ya kuma cewa “Ahmad” ya dago ya kallesa yace “Ba ko ina Abba” Abba yace “Are you sure?” Ya gyada masa kai, Abba yace “Maa sha Allah, Allah ya tsare gaba bari a kawo maka tea yanzu sai ka sha drugs” daga haka Abba ya juya ya fita, Dr faruqh yayi murmushi yace “Allah ya kara kiyayewa Captain Junaid” Junaid yace “Ameen” daga haka Faruqh ya juya ya fita, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace “gaskiya kana da matsala junaid, ni meye nawa xa ka share ni” Junaid bai tanka sa ba ya sauka daga kan gadon ya nufi toilet, El-ameen ya bi sa da kallon mamaki, girgixa kai yayi ya juya yana kallon jasmine ya ga har ta fara bacci, ya karasa kusa da ita ya duka murya can kasa yace “Jewel” bude ido tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace “Sleep” cikin sanyin murya tace “Captain!” Yayi shiru yana kallonta kafin ya girgixa mata kai a hankali yace “Doctor!” Rufe idonta tayi bata sake budewa ba ya mike ya gyara mata kwanciya ya rufa mata bargon da ke kan gadon, junaid ya fito ya nufi gadon da yake, El-ameen ya bi sa da kallo yace “patient din ka ta samu lafiya” Ba tare da junaid ya kallesa ba yace “Naga alama” El-Ameen yayi murmushi yace “Hakan kuma ya faru ne ta dalilin accident din da ku ka yi, nd this clearly shows dat hatsari ne cause din haukanta, sai dai kuma ga dukkan alamu tayi loosing memory….” Wata nurse ce ta shigo da cup din tea ta karasa kusa da Junaid ta mika masa ya karba ya fara sha, ta ajiye magungunan hannunta ta gwada masa yanda xai sha ta bude fridge ta fiddo masa ruwa ta ajiye sannan ta fita, El-ameen yace “Ina magana xaka wani min shiru?” Junaid ya kallesa yace “Ai na ji ka, and am glad ta samu lafiya dama abinda nake so kenan, yanzu abinda ya rage shine in sama mata inda xata fara rayuwa har memoryn ta ya dawo…..” El-ameen yace “inda xa ka sama mata kamar ina?” Junaid ya kallesa sannan yace “Inda xata xauna ta ci gaba da rayuwa nace” El-ameen yace “Toh ai ban gane irin gun da kake fadi bane” Junaid yace “Ko mama jumman nan sai in sa a nemo min in damka mata ita ta rike har tayi recalling abubuwa ta nemi iyayenta” El-ameen yace “Haba, she still need medication har ynxu fa…..” Junaid ya kallesa yace “Nayi iya taimakon da xan mata a yanzu, idan mama jumman ma ta dauketa dole xan basu kudi that will be enough for der needs…..” El-ameen yace “No plss ba sai an kai ta kauye ba, ka bari ka cike ladan ka kawai” Junaid yayi masa wani irin kallo yace “Bana ketare maganar mahaifiyata, tace in maida ta inda na samo ta and dat’s wat am going to do…” Shiru El-ameen yayi na wani lokaci kafin yace “Amma baka mata adalci ba” Junaid yace “Look ka bar ni in ji da abinda ke damuna yanzu El-ameen, ban san da idon da xan kalli mahaifiyata ba, ban san ta wani sigar Abbana xai dauki batun nan ba, I’ve tried my best na mata iyakar abinda ya kamata tunda gashi ta dawo hankalinta….” El-ameen bai kuma cewa komai ba ya lumshe ido ya bude sannan ya fita daga ward din. Junaid ya jinginar da kansa jikin bango daga xaunen da yake ya lumshe ido, har kusan Karfe biyu El-ameen bai dawo dakin ba, ya juya yana kallon gadon da take kwance, saukowa yayi daga kan gadon da yake ya karasa nata gadon yana kallonta, lumshe ido yayi cikin sanyin murya yace “Na so taimakon da xan maki ya fi haka Jasmine, I can’t help, baxan iya tsallake umarnin Mumyna ba, am very glad kin dawo mai hankali, nasan you will cope da new environment din da xa ki samu kanki har tunanin ki ya dawo” ya kusa minti goma kusa da ita kafin ya mike a sanyaye ya koma gadonsa. Ciwon kai bai bar sa ya runtsa ba har Karfe hudu, yana nan kwance aka bude kofar El-ameen ya shigo, lumshe ido yayi kamar me bacci, El-ameen ya karasa kusa da shi yana kallonsa, ya daura hannunsa kan forhead dinsa ya ji da dumi sosai, kallon magungunan da ke gefensa yayi da mamaki ganin bai sha ba, ya jima tsaye kansa kafin ya juya ya koma gun jasmine, kwata kwata daren kasa bacci yayi sbda tausayinta, da ya tuna abinda Abbansa yace kan gobe bai son ganinta asibitin sai jikinsa yayi sanyi, in kuma ya tuno furucin junaid ma sai yaji tausayinta sosai, dukawa yayi yana kallon fuskarta, yaga ta bude ido da sauri, komawa baya yayi ta mike xaune tana mitstsika ido tace saw “Captain!”

Haske Writers Association????

Yau ma dai ba yawa, sorry.

[1/14, 9:12 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

37/38

Murmushi El-ameen ya mata yace “Good morning” ita ma a hankali tace “Good morning!” Ya gyada mata kai yana murmushi har lokacin, duk abun nan da suke Junaid na kallonsu, yana ganin El-ameen xai juyo yayi saurin lumshe ido, El-ameen ya nufi kofa ta bi sa da kallo kafin ya fita tayi saurin cewa “Captain!” Juyawa yayi ya kalleta ya girgixa mata kai yana murmushi yace “No, Am doctor!” A hankali tace “Doctor?” Ya d’an bude ido yace “Yess” juyawa yayi ya fice. Saukowa tayi daga gadon ta nufi gadon Junaid ta duka tana kallon long eyelashes dinsa don har lokacin idonsa a lumshe yake, a hankali tace “Captain!” Ya bude ido da sauri yana kallonta, tayi murmushi tace “Good morning!” Mikewa xaune yayi ya mayar mata murmushin yace “Morning jasmine, how you?” A hankali tace “Am fine, and you?” Shiru tayi da sauri kamar me naxarin abinda tace, can ta runtse ido ta dafe kanta ta durkusa wajen, ya sauko da sauri yana kallonta, ta kusa minti biyar a haka shi dai bai dagota ba bai kuma san ma me xai ce mata ba, mikewa tayi a hankali tana rike da kan ta juya ta bar wajen ya bi ta da ido, xama tayi kan kujeran da ke kusa da gadonta ta kifa kanta ta inda ba ciwo, komawa yayi ya xauna har lokacin yana kallonta. El-ameen ne ya shigo dakin bayan an idar da sllhn Asuba, ya samu Junaid xaune kan darduma, ya ajiye ledan hannunsa ya ja kujera ya xauna yana kallonsa yace “Good morning captain, ya jikin?” Junaid yace “Alhmdllh” kallon magungunansa El-ameen yayi yace “Jiya baka sha drugs din ka ba ashe?” Junaid bai ce komai ba El-ameen ya tabe baki ya mike yana kallon jasmine dake xaune har lokacin kan kujera kanta kife kan gado, karasawa yayi yana kallonta ya ga bacci ma take a haka, ya dan duka yace “Hello!” Bude ido tayi da sauri tace “Hi” murmushi yayi yace “Good, tashi kiyi sllh” dago kai tayi da sauri tana kallonsa tace “Sallah?” Ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa kamar bata taba jin Kalmar ba, shi dai Junaid kallonsu kawai yake, El-ameen yace “Am coming” daga haka ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba ya dawo tare da wata nurse rike da hijab, ya kalli nurse din yace “Ki rakata bayi, ki gwada mata yanda xata yi alwala” nurse din ta kalli jasmine sannan ta kallesa tace “Ban gane ba sir” Yace “Yes alwala xaki yi tana gani tana bin ki” nurse din ta kuma kallon jasmine dake kallonta ita ma ta ajiye hijab din hannunta tace “Toh sir” El-ameen ya kalli Jasmine yace “Tashi ki bita kiyi duk abinda tayi kin ji” mikewa tayi tana kallonsa ya gyada mata kai yace “Yes follow her” tace “I should follow her?” Murmushi yayi ganin yanda take catch up da sauri yace “Yes follow her” kamar me tausayin kasa haka ta dinga bin nurse din a baya har suka shiga toilet din, nurse din ta rufe kofar tana kallonta tace “Do you want to urinate?” Kallonta kawai Jasmine take kamar me naxarin word din, a hankali tace “Urinate?” Matar ta gyada mata kai, girgixa mata kai tayi, matar ta dau kettle daya ta mika mata ita ma ta dau daya tace “Kiyi duk yanda ki ka ga nayi” a hankali Jasmine ta durkusa tana kallon nurse din runtse ido tayi jin xafi a kneel dinta, nurse din dai sai kallonta take har ta bude idon, sannan ta yi bismilla ta fara alwalan tana kallonta, jasmine ta wanke hannunta ita ma kamar yanda ta ga nurse din ke yi, haka tayi ta kwaiwayon ta har suka kare alwalan nurse din ta fito tana biye da ita a baya, har lokacin junaid na xaune kan darduma, El-ameen ma na xaune yana jiran fitowar su, mikewa yayi yana kallon junaid yace “Pray mat malam” junaid ya tabe baki ya mike ya koma kan gado, El-ameen ya shimfida ya kuma dauko wani ya shimfida a baya, ya dau hijab ya mika mata yace “Ki saka” karba tayi tana kare ma Hijab din kallo, ya mata alama da tasa, kokarin sakawa ta shiga yi ta kasa don bata san ma yanda xata saka din ba, ya karaso yana murmushi ya karba ya saka mata, Junaid ya kauda kai hade da tabe baki, El-ameen ya nuna mata inda xata tsaya kan darduman yace “Kiyi duk yanda kika ga nayi” shiru tayi tana kallonsa, yace “Kin ji?” A hankali ta gyada masa kai, ya koma darduman gaba ya tada sllh, haka ta dinga binsa sllhn tana yin duk yanda taga yayi da kyar sbda kneel dinta, har suka idar ya juya yana kallonta, jini ya gani Hijab dinta ya dawo kusa da ita da sauri yace “Ohh!” Hannu yasa xai daga hijab din ta koma baya sauri tana masa wani kallo, komawa baya yayi cikin sanyin murya yace “Yi hakuri,” mikewa yayi ya fita, ta juya tana kallon Junaid da ke kallonsu, dauke kanta tayi tana nan xaune har El-ameen ya dawo da nurse, nurse din ta duka kusa da jasmine tace “Sannu” daga hijab din tayi tana kallon kneel din, kayan aiki El-ameen ya miko mata nan ta fara gyara mata wajen, rufe idonta tayi da ganinta kasan daurewa kawai take, El-ameen ya durkusa kusa da ita yana mata sannu, har nurse din ta gama, a hankali ta bude idonta da ya kada, yace “Sannu” ta kallesa sannan ta sunkuyar da kanta, mikewa nurse din tayi ta fita da kayan aikin, tashi yyi ya dauke darduman da yake kai ita ma ta mike ta dauke dayan, Junaid ya dauke kai tun kan su kallo inda yake, ledan da El-ameen ya shigo da ya nufa ya bude ya fiddo da sabbin toothbrushes da toothpaste, ya ajiye ma junaid daya ya bude daya ya matsa toothpaste ya mika mata yace “Tafi ki wanke bakin ki” karasowa tayi ta karba tana kallonsa, murmushi yayi sanin bata gane ba kenan, yace “Follow me” da sauri tace “Follow her” dariya ta basa yace “No, follow me dai” daga haka ya shiga toilet ta bi bayansa, yana kallonta yayi mata alama da hannu da ta wanke baki da brush din, saka brush din tayi a baki ta tsaya, yace “Toh wanke bakin” tsotsan toothpaste din tayi ta cire brush din tana yamutse fuska, yace “No ba haka ba” ya mika mata hannu alamar ta basa ta mika masa ya kai brush din baki, nan ya shiga gwada mata yanda xata yi sannan ya mika mata, yanda taga yayi haka tayi yana kallonta har ta gama sannan ya nuna mata gun xuban ruwa yace “Wash ur mouth,” karasawa tayi tana kallon wajen, yayi murmushi ya karaso ya bude mata ruwan ya tara da hannunsa ya kai bakinsa ya kuskure ya xubar sannan ya kalleta yace “Haka xa ki yi” tara hannunta tayi ita ma, ya tsura ma fararen hannun nata ido har ta kai ruwan baki ta kuskure kamar yanda ta ga yayi” murmushi ya mata yace “Good gal” juyawa yayi yace “Mu tafi” ta bi bayansa suka fito, bai yi mamakin rashin ganin junaid dakin ba, yana lafiya ma ya aka kare bare yanxu, kujera ya nuna mata ta xauna yace “Am coming” sannan ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. Ba a dau lokaci ba ya dawo da bowl me dauke da apples, ya jawo table karami ya ajiye kusa da ita sannan ya daura bowl din kai yana kallonta yace “Eat” kallon bowl din kawai take, can ta sa hannu ta dau apple daya a hankali ta kai bakinta, bude kofa aka yi duk suka juya, gabansa ya fadi ganin Abbansa, Abba ya karaso dakin yana kallon gadon junaid yace “Where is my patient” El-ameen yayi saurin cewa “Ya d’an fita ne yanxu Abba” Abba yace “Ya fita da sassafen nan ya je ina?” El-ameen da gabansa ke faduwa yace “Ina jin ya fita ne, no cewa yayi xae fita ya sha iska” wani kallo Abba ke masa sannan ya kalli Jasmine dake kallonsa yace “Bana son in sake shigowa in ga yarinyar nan a nan Ahmad” kallon Abban nasa yayi a sanyaye yace “Toh Abba” Abba yace “Mutumin banxa kawai, kuma maxa kaje ka dubo min patient dina yanxu” daga haka ya juya ya fita, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine, murmushin karfin hali ya sakar mata yace “Eat your apple” sunkuyar da kanta kawai tayi, ya juya a sanyaye ya fita daga dakin. Babu inda bai duba ba a asibitin amma bai ga junaid ba, abun yayi mugun basa mamaki kar dai gida ya wuce, dawowa sama yayi bai kuma yi gigin xuwa gaya ma Abba bai gansa ba don yasan baxai ji da dadi ba, office dinsa ya fara tafiya ya dau makullin motarsa sannan ya tafi ward din da jasmine take ya ganta har lokacin rike da apple din bata ci ba, ya karasa kusa da ita yace “Eat mana jasmine” bata kallesa ba ya kama hannunta xai dago ga ta fixge hannun tana masa wani kallon da ya fadar masa da gaba ya d’an koma baya a hankali yace “kiyi hakuri” ya gane bata son a taba ta kenan, mikewa tayi tsaye, ya fara tafiya yace “Mu je” har ya isa bakin kofa ya juyo yaga bata biyosa ba, yafito ta yayi sai gashi ta fara tahowa, Suna tafe yana juyowa yaga ko tana binsa har suka fito haraban hospital din ya nufi parking space da ita, gaban mota ya bude mata ya mata alamar ta shiga, still tayi tana kallon motar kamar warce ta tuno abu, can kuma ta kallesa kamar xata yi kuka, accident dinsu na jiya ne ya fado masa lokaci daya ya gane abinda yasa taki shiga, girgixa mata kai yayi yace “babu abinda xai faru jewel, shiga” kin shiga motar tayi still, ya xaga ya bude driver seat ya shiga ya tada motar kallonsa kawai take daga waje, can ta fara kalle kallen asibitin, a hankali ta shiga daga karshe yayi murmushi ya rufo motar, yana gama warming ya ja motar suka bar haraban asibitin bayan an bude masa gate, driving kawai yake ba tare da yasan inda xai kai ta ba, duk tausayinta ya cika shi, a hankali yace “Ina xan kai ki Jewel?” Kallonsa tayi ba tare da ta ce komai ba, Kanwar Abbansa ce ta fado masa kawai ya yanke shawarar kai ta can gidan, Karfe takwas da wani abu suka isa gidan, ya bude motar ya fito ya xaga ya bude mata ita ma ta fito, yana gaba tana biye da shi a baya suka shiga gidan, bbu kowa parlon ya nuna mata kujera ta xauna, cousin sis dinsa ta fito daga kitchen da mamaki take kallonsa tace “Toh fa, yaya daga ina haka?” Yayi murmushi yace “Gida, kira min Mumy” daki ta tafi tana cewa lallai yau akwai ruwa da kankara, Hajiya salmah Kanwar dad dinsa ta fito parlon tana kallonsa tace “Kayi batan hanya ne Ahmad?” Yayi murmushi yana shafa kai yace “A’a Mumy ina kwana” ta tabe baki ta amsa tana kallon Jasmine, sunkuyar da kai jasmine tayi, El-ameen yace “Mumy na xo neman alfarma ne a gun ki pls” tana kallonsa tace “Na me fa Ahmad” yayi kasa da murya ya shiga mata bayanin Jasmine, kallonsa take baki bude har ya kai karshe tace “Ehh lallai Ahmad, wato kai ne baka jin maganar naka iyayen koh, kai ne baka san darajar su ba, to wllh maxa ka maida masa ita shi da ya jajubo ta, maganar banxa kawai, shi me wayo yaji maganar tasa uwar sai kai ne da baka san darajan naka uban ba koh…..” Mikewa El-ameen yayi bai kuma sauraranta ba, Jasmine na ganin ya tashi ita ma ta tashi da sauri, ya nufi kofa ta bi bayansa, small mum din tasa ta bi sa da harara tace “D’an rainin hankali kawai, mara wayo, kuma wllh sai na kira yaya na gaya masa yasan baka dauke sa bakin komai ba.” Har ya fice daga parlon bai tanka ta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button