CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

By Khaleesat Haiydar✍????

48…..

Sai kusan Azahar Jasmine ta tashi, tana ganin kofa rufe ta mike da sauri taje ta bude, fitowa Junaid yayi daga bedroom dinsa jin budewar kofar,ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, yace “Kin tashi” ta gyada masa kai ta koma dakin, karasawa ciki yyi yace “Are you hungry?” Ta daga kai ta kallesa tace “ina son in yi girki” yace “girki?” Ta gyada masa kai yace “Uhnn! Toh xo mu je kiyi” gun kayanta ta nufa tace “in sa wani kayan” dariya ta basa ya bi ta da kallo har ta isa gun jakarta ta bude ta fiddo wata yar top fari mara nauyi da wando mai kamar 3qtr pink ta ajiye, xaro ido yayi yana kallonta, yaga ta fara kokarin cire doguwar rigar kantin jikinta, da sauri ya juya ya fita daga dakin ya sauka downstairs, tana gama canxa kayan ta dau net ta saka a kanta kamar yanda suke a gidan Dr Sumayya, ta fito dakin ta sauko kasa, buda ido yayi yana kallonta har ta karaso inda yake, can ya shafa kansa yace “No! Je Dauko hijab ki sa” shiru tayi bata ce komai ba, ya mata murmushi yace “Yes, je ki dauko” ta juya ta koma sai ga ta ta dawo da hijab, tausayinta kawai yake yanxu kam she don’t know what’s right or wrong kawai gata nan gata nan ne, kitchen ya nufa ta bi bayansa, sai da suka shiga ya kalleta yace “Me xa ki dafa?” Tayi shiru tana tunani can tace “Indomie and egg” yace “Ohk,” ya fiddo mata da indomie biyu, da kwai uku, kamar me naxari tace “Onion, pepper, carrot…..” Sai kuma tayi shiru idonta a kansa, murmushi yayi ya dauko mata ya ajiye, ta kalli indomien tace “Ga nawa, ga naka, ina na wancan Antyn” ta fadi haka tana nuna masa sama, shiru yayi bai ce komai ba, can ya dauko daya ya ajiye, kunna gas tayi ta dau tukunya ta xuba ruwa ta daura tace “Haka koh?” ya jingina jikin kofa ya rungume hannu yana kallonta, sosai yayi mamakin ganin yanda take hada girkin sai dai tana yi tana tsayawa kamar me naxari, cikin few minutes ta dafa indomien ta soya kwai ta xuba a plates uku duk ta sa fork, sai a sannan ta juya tana kallonsa yayi murmushi a hankali yace “Woaw! Sannu da kokari” ta wara masa manyan idonta tace “Uhm” kallonta kawai yake, ta sunkuyar da kai a hankali tace “Yaushe Uncle xai xo?” Shiru yayi mata bai ce komai ba, ta matso kusa da shi tana kallonsa tace “When uncle xai xo?” Hade rai yayi ya dau plate din indomie daya ya mika mata yace “kai mata daki” ta karba tace “Ohk” sannan ta fita daga kitchen din ya bi ta da kallo, sama ta tafi ta tura kofar dakin a hankali ta shiga, xaune ta ganta kan darduma ta iso kusa da ita ta durkusa ta ajiye mata tace “Nayi girki” wani kallo Humainah ta watsa mata ta mike tace “Fice min a daki!” Jasmine ta mike tana kallonta, ta buga mata uban tsawa tace “Baxa ki dauka ki fita ba” dukawa Jasmine tayi a hankali ta dau indomien ta fita, ta koma downstairs kallonta junaid yake har ta karaso parlor ita ma tana kallonsa, hawaye ya gani idonta ya karba indomien ya ajiye ya xauna, ita ma ta xauna ya ajiye abincin gabanta yace “Ci abincin ki” ta goge hawayen idonta ta dau fork din a hankali ta fara cin indomien, duk ya lura ci kawai take ba don tana son ci ba, duk tausayinta ya cika sa. Tashi yayi ya tafi sama ya shiga dakinsa, wayarsa ya dauka ya ga mis calls din El-ameen, ya ajiye wayar ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito, har xai sauka downstairs sai kuma ya shiga dakin Humainah, ya hade rai yace “Don ta kawo maki abinci shine laifi har da yi mata tsawa?” Wani kallo tayi masa tace “Nayi, kar kuma ta sake xuwa inda nake kaje can ku karata” tana fadin haka ta fashe da kuka, ya karaso cikin dakin ya xauna kusa da ita yace “Haka kika ce?” Mikewa tayi xata bar wajen ya fixgota ta fado kansa, ya dago kanta ya hade goshinsu yace “Maimaita words din ki” yana ganin yanda kirjinta ke heaving, ya hade rai sosai yace “Maimaita nace” komawa baya take son yi amma ta kasa don ba rikon wasa yayi mata ba, shi kansa ji yayi xuciyarsa na bugawa, rufe ido tayi da kyar tace “Ni ka rabu dani, bana so….” Murmushi yayi ya lumshe ido ya hade bakinsu….. Still yayi da farko har lokacin bai bude ido ba haka ita ma, can ta fara turasa a tsorace, ya kwantar da ita a hankali ya shiga kissing dinta, sosai ta tsorata sai dai ta kasa kwace bakinta, da kyar ya saketa jin an tada sllh ya mike ya fita daga dakin, ta fashe da kuka ta boye fuskarta cikin pillow, bedroom dinsa ya nufa shiga toilet. Bai iya ya fito daga dakinsa ba sai da aka kira la’asar, ya sauko parlor don tafiya masallaci, xaune ya ga jasmine kan carpet a parlor ta daura kanta kan kujera idonta lumshe a haka, ya iso inda take ya d’an buga kujerar ta bude ido da sauri, murmushi ya mata yace “me sa baki tafi daki ki kwanta ba” a hankali tace “Tsoro nake ji ni kadai” ya durkusa kusa da ita yace “Tsoron me kike?” Kamar xata yi kuka tace “Nima ban sani ba” shiru yayi yana kallonta, hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace “Uncle baxai xo ba?” Nan ma dai shiru yayi bai ce komai ba, sunkuyar da kai tayi ganin haka, a hankali yace “Xai xo anjima, yanxu dai tashi ki shiga toilet ki yi alwala ki xo kiyi sllh, kin ma yi na daxu?” Girgixa masa kai tayi, yace “Toh da kin ji an kira sllh ki tafi kiyi alwala kiyi kin ji?” Ta gyada masa kai yace “Kin ma san me ake cewa idan ana sllhn ma?” Ta gyada masa kai, yace “Wa ya koya maki?” Tace “Mami da farida” yayi murmushi yace “Good tashi kije kiyi alwala sai kiyi na daxu da na yanxu” tayi narai narai da ido tace “Ina jin tsoro a sama” ya nuna mata bayin dake parlor yace “ae a can xaki je kiyi” mikewa tayi ta nufi toilet din, yace “Baki cire hijab ba” dawowa tayi xata cire ya tuna abinda ke jikinta da sauri yace “A’a a’a tafi kiyi haka kawai” ta juya ta tafi toilet din, sama ya koma ya dauko mata darduma ya shimfida mata sannan ya fita jin an tada sllh. Ko da ya dawo ya tarar bata idar ba ya xauna har ta gama, yana kallonta yace “kullum idan kinyi sllh ki yi addu’a kice Allah ya baki lafiya kinji” shiru tayi tana kallonsa ya mata murmushi yace “Kina jin yunwa?” Girgixa masa kai tayi yace toh bari in sa maki kallo, ta gyada masa kai yayi powering din tv ya mike ya haura sama. Haka tayi ta xama a parlon ita kadai har magrib, tana jin an kira sllh taje tayi alwala, ko da ya sauko tafiya masallaci samunta yayi har ta fara sllh, yayi murmushi ya fita. yana dawowa daga mosque ya ga motar El-ameen bakin gate yayi jim can ya juya xai shiga gate El-ameen ya danna masa horn, dawowa yayi don bai yi tunanin yana ciki ba, ya bude motar El-ameen yace “Why ain’t you picking my cal?” Junaid ya daga kafada yace “Ban ma san ka kira ba” El-ameen bai ce komai ba ya bude motar ya fito rike da leda hannunsa, junaid ya nufi gate ya bi bayansa, sai da suka shiga gidan yace “Kasan yanxu sai da izinin ka xan dinga shigo maka gida…” Junaid bai ce komai ba har suka shiga parlor, jasmine dake xaune kan darduma tana ganin El-ameen ta mike da sauri tana kallonsa ya wara mata ido yace “uhmm!” da gudu ta karaso ta rungumesa tace “Uncle!” El-ameen ya d’an yi still, junaid kam hade rai yayi ya karasa shiga parlon ya xauna, a hankali El-ameen ya janyeta jikinsa yana murmushi yace “How are you” murya can kasa tace “am fyn, I missed you” gyada mata kai yayi ya nuna mata Junaid yace “He’s always there for you also” ta kalli Junaid tayi shiru bata ce komai ba, kama hannunta El-ameen yayi suka karasa parlor ya xauna ita ma ta xauna, kusa da kunnensa ta kai bakinta tace “In je in kawo jakan?” Dariya yayi yace “Na me?” A hankali tace “Na cloth dina” yace “Wait tukun sai idan xa mu tafi” tace “Toh” duk wannan abinda suke junaid kan tv ya maida hankalinsa. El-ameen ya jawo ledan da ya shigo da ya bude ya dauko mata apple daya ya mika mata ta karba tace “Na gode” gyada mata kai yayi har ta fara ci ta mike ta isa kusa da Junaid ta durkusa tace “Uncle dina ya siya min apple xaka ci” ba tare da ya kalleta ba ya girgixa mata kai ta mike ta koma gun El-ameen ta xauna, in da sabo El-ameen ya saba da attitude din junaid, don haka bai damu da daure dauren fuskar da yake ba yace “Ina madam din taka” ba tare da Junaid ya kallesa ba yace “Tana daki” ko rufe baki bai yi ba sai ga ta ta sauko sanye da hijab dinta har kasa, tana ganinsu xaune parlon ta dauke kai ta nufi kitchen El-ameen ya bi ta da kallo ta gefen ido hade da tabe baki, Jasmine ta matso kusa da El-ameen a hankali murya can kasa kamar xata yi kuka tace “I don’t like her” murmushi El-ameen yayi murya can kasa shi ma yace “Really! But why?” Cikin sanyin murya tace “She’s mean!” Kallonsu kawai Junaid ke yi ta gefen ido, El-ameen dake lura da haka ya saka dariya yace “Malam da kawai ka juyo ka kallemu ka bar straining idonka” hade rai junaid yayi ya juya yana kallonsa, can ya mike ya haura sama, jasmine ta bi sa da kallo sannan ta kalli El-ameen tace “He’s kind, I like him” El-ameen bai ce mata komai ba, Humainah ta fito daga kitchen rike da cup din tea, El-ameen ya bi ta da kallo can dai yace “Ina yini Humainah” ba tare da ta tsaya ba bare ta juyo tace “Lafiya lau” yayi murmushi yace “Ohh baxa ki tsaya mu gaisa ba, toh d’an dawo muyi wata magana da ke” ta juya ta kallesa yace “Minti uku kawai” fuskarta daure ta dawo parlon ta tsaya, yace “Toh xauna mana” ta xauna kujera ba tare da ta kallesa ba, yace “Kiyi hakuri nasa an kawo maki bakuwa may be ba da ixinin ki ba, ba dadewa xata yi ba gidan ki Idan Allah ya yarda, matar da ke rike da ita ne tayi tafiya shi yasa ta xo taya ki xama, Ina fatan kuma captain ya baki labarin ko wacece ita” Humainah bata ce komai ba ta dauke kai, El-ameen yace “pls ki tausaya mata marainiya ce ita a yanxu dai, akwai abubuwa da yawa da ta manta take bukatar a koya mata, plss help the innocent girl, take her as ur sis sai Allah ya baki lada!” Hawaye ya ga ni idonta, ya juya ya kalli Jasmine dake kallonsa yace “je ki kira min Captain” shiru tayi bata ce komai ba, can a hankali tace “Captain!” Ya gyada mata kai, ta d’an bude ido tace “Sleep Captain din nan?” Yace “Je kice masa ya xo” mikewa tayi ta tafi sama, El-ameen ya kalli Humainah yace “Ke dai baki son ta xauna kawai koh?” Ta goge idonta tace “Toh shine ni baxai kulani ba sai ita, komai yayi mata ni baxai min ba” sai ta fashe da kuka, duk da ta ba El-ameen dariya don yasan har da yarinta ya dai dake yace “Da gaske?” Cikin kuka tace “Ko da yaushe shi yake bata abinci ni baxai bani ba, sai yaje yayi ta xama da ita ko ya shiga dakin da take” shiru El-ameen yayi yana kallonta, can yace “Kiyi hakuri xan masa magana, but kema ki dinga yi masa biyayya banda tsiwa in har kina son ku xauna lafiya kamar masoya, in har kina masa haka ke ma xai dinga kyautata maki, baby kuma ‘yan kwanaki xata yi ta tafi” kai kawai ta gyada masa tana goge fuskarta.
[1/14, 9:17 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button