CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers association????
[1/14, 9:17 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

50…..

Washe gari ma kamar jiya haka suka wuni gidan, yana zaune d’akin Humainah da tayi kamar batasan da zamanshi ba,
Mikewa yayi ya fita daga dakin ya koma nasa, yana danna wayarsa yaji kamar ana sallama bakin kofa, tashi yayi ya isa gun kofar ya bude ya ganta tsaye, a hankali tace “Nace Assalamu Alaikum!” D’an murmushi yayi yace “Gud! Ya aka yi?” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Kin gama cin abincin?” Gyada masa kai tayi yace “toh mu je” fitowa yayi daga dakin ya shiga wanda take ta bi bayansa, ya xauna gefen gado ta karaso ita ma ta xauna daga kasa inda yake, yace “No dawo ki kwanta kiyi bacci” tace “I’ve not bathed” mikewa yayi ya shiga toilet ya hada mata ruwa ya fito yace “Toh tafi kiyi” ta mike ta cire hijab ta shiga toilet din ya bi ta da kallo, fita yayi daga dakin jin kamar wayarsa na kara ya shiga nasa dakin, 1st love ya gani jikin screen din, ya dau wayar ya xauna sannan yayi picking hade da yin sallama, Mumy ta amsa ya gaisheta ba tare da ta amsa ba tace “Ina Humainah” kallon kofa yayi yace “tana daki Mumy” Mumy tace “Aysha tace kuka kawai yake?” Ya d’an bude ido yace “Mumy ai kinsan yanda take behaving ni ban san me ke damunta ba” Mumy tace “Kai mata wayar” yace “Toh, xan kira idan na kai mata” daga haka ya katse wayar, da kyar ya mike gabansa na faduwa ya fita daga dakin ya shiga nasa, kwance ya sameta ta lullube gaba daya da bargo, ya karasa ya xauna kusa da ita ya yaye bargon yace “Humainah ga Mumy” kin bude ido tayi ya dagota ta buge masa hannu tana turasa, yace “Mumy ce xata maki magana” tana bude idon hawaye suka biyo baya, ta fada jikinsa tana kuka a hankali, rasa me xai ce mata yayi, ya dago kanta yana kallon fuskarta, murya can kasa yace “Humainah!” Kallonsa tayi bata ce komai ba hawaye na bin kuncinta, wayarsa ne ya soma ringing ya dauka yana kallon Screen din, can ya kalleta yace “Mumy xata yi magana da ke, plss ki bar kukan nan” bata ce komai ba ya d’aga ya kai mata kunnenta, daga daya bangaren Mumy tace “Humainah!” A hankali tace “Na’am, ina yini Mumy” Mumy ta amsa tace “What’s wrong with you kike kuka har yanxu?” Wasu hawayen ne suka xubo mata tace “Ba komai Mumy” Mumy tace “Ba komai kuma? Haka kawai kike kuka?” Shiru tayi bata ce komai ba, Mumy tace “Toh xan xo gobe” a hankali tace “Toh!” Mumy ta katse wayar, ya dago kanta da sauri yace “What did she say?” Komawa tayi ta kwanta tace “Nothing” ya dawo kusa da ita yace “Karya kike” k’in ce masa komai tayi, ya dagota yace “Baxa ki gaya min ba” turasa tayi tace “Let me” jawota jikinsa yayi yace “Ae sai kin gaya min” ta hade rai tace “Stop this, bana so” kallon bakinta kawai yake, ta fara kokarin sauka ya rikota, cike da masifa ta buge masa hannu xata yi magana ya dago kanta sai jin bakinsa cikin nata tayi, buda ido tayi tana kokarin turasa ta kasa ya kwantar da ita ya lumshe ido, tsorata tayi ganin ya fara wuce limit, lokaci daya ya kawar mata da tsoron ta sakar masa jiki kamar ba ita ba, yanda ya kwantar da kai ka rantse kace ba captain Junaid ba, murda kofar dakin aka yi, ya saketa da sauri ya koma baya ita kuma ta shige cikin bargo, Jasmine ce ta shigo dakin da hijab sai towel dake jikinta, kamar xata yi kuka tana kallonsa tace “Ni banga bag din kayana ba” kallonta kawai yake da rinannun idonsa, shiru tayi ita ma tana kallonsa, juyawa tayi ta fita ta tsaya daga bakin kofa a hankali tace “Assalamu Alaikum!” Lumshe ido yayi ya bude yana shafa kansa bai ce komai ba, sallaman ta kuma yi kamar xata yi kuka, amsawa yayi fuskarsa daure, ta shigo ta tsaya daga bakin kofa, sai dai ta kasa cewa komai ganin yanda ya tamke fuska, kallonta yayi yace “From now on idan kika sake shiga waje ba sallama I will slap you” hawaye ne ya cika idonta ta gyada masa kai ta juya a hankali ta fita, juyawa yayi yana kallon Humainah da tayi lamo cikin bargo, ya shafa kansa ya mike ya fita daga dakin ya shiga nasa, wanka ya shiga yayi, ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa yayi shafa’i da wutr, yana xaune kan darduma har Karfe sha daya can ya mike ya fita daga dakin, tsaye yayi bakin kofa yana kallon dakin da Jasmine take don kofar a bude yake, ya karasa ya shiga dakin, kwance ya ganta daga gefe kusa da bakin kofar tana bacci har lokacin Hijab da towel ne jikinta, durkusawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta, ya lumshe ido ya bude murya can kasa yace “Jasmine” ganin bata motsa ba ya mike ya fita daga dakin ya sauka parlor ya dauko mata jakar kayanta ya dawo sama, ajiye jakar yayi ya bude ya fiddo mata doguwar riga ja mara nauyi, kiranta ya kuma yi a hankali bata tashi ba, ya d’an buga kafadar ta ta mike xaune da sauri tana mitsika ido tace “Uncle!” Ganinsa yasa tayi saurin cewa “Captain!” Bai ce komai ba ya mika mata rigar hannunsa yace “Tashi ki sa kayan ki” karban kayan tayi yana kallonta ta cire hijab din jikinta ta mike, dauke idonsa yayi daga kallon nata a nan wajen ta saka kayan da ya bata, ta dawo kusa da shi tace “Na sa” mikewa yayi ba tare da ya kalleta ba still ya nufi gado ya ce “Xo ki kwanta” tace “Kai ma xaka yi bacci nan koh?” Yace “Eh” karasowa tayi ta hau gadon ta kwanta har da matsa masa, lulluba mata bargo yayi ya xauna gefen gadon ya kunna Tv yace “Sai na gama kallo xan kwanta” har sha biyu bai ga alamar xata yi bacci ba, ya kalleta yace “Sleep mana” tace “Sleep captain” murmushi yayi ya gyada mata kai yace “Ke ki fara yi sai nima in yi” lumshe idonta tayi ya tsura mata ido yana kallo, bata sake bude idon ba kuma har daya saura, ya mike a hankali ya kashe Tvn, ya fita daga dakin ya bar kofar a bude ya shiga nasa dakin, kasa bacci yayi sai juye juye yake ya rasa dalili, daga baya dai ya gano dalilin ya kawar da shi daga ransa yayi forcing kansa yayi bacci. Washegari Monday yaji da ma kawai yayi resuming aiki duk da hutun sati biyu ya dauka but sbda Jasmine yasa bai yi haka ba, yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin Humainah ya ganta xaune kan darduma, juyawa yayi ya fita dakin ya shiga wanda Jasmine take, har lokacin ya ga bata tashi ba, dukawa yayi dai dai fuskarta yace “Jasmine” ta bude ido da sauri mikewa yayi yace “Tashi kiyi sallah” ta gyada masa kai ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet. Ya juya ya fita daga dakin. Karfe takwas saura Humainah ta fito ta sauka downstairs ta shiga kitchen, tsaye tayi tana tunanin abinda xata hada for breakfast, can dai ta fiddo Irish ta fara ferewa, ko da junaid ya sauko don siyo masu breakfast yayi mamakin ganinta a kitchen, ya tsaya daga bakin kofar kitchen yana kallonta, yace “Gud morning” ba tare da ta kallesa ba tace “Ina kwana” murmushi yayi ya juya ya fita daga kitchen din. Yana xauna parlo Jasmine ta sauko da alamar tayi wanka don ta canxa kayan jikinta, kusa da shi ta durkusa tana kallonsa cikin sanyin murya tace “Nayi wanka” ya gyada mata kai yana nuna mata kitchen yace “Tafi ki gaisheta ki taya ta aiki” tace “Toh” sannan ta mike ta nufi kitchen din ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya. Kallo daya Humainah tayi mata ta dauke Kai, ta karasa kusa da ita ta durkusa a hankali tace “Ina kwana” ba tare da ta kalleta ba tace “Lafiya lau” shiru Jasmine tayi can kuma tace “I want to help you” mika mata wukar Humainah tayi ta ta tafi gun gas xata kunna, jasmine ta dau dankalin daya ta rasa yanda xata fara fere shi, kallon Humainah dake kokarin dauko mai tayi sannan ta fara fere dankalin ihu ta fasa ta jefar da wukan jin wani xafi da ya ratsa taMikewa Junaid dake xaune parlor yayi yana kallon kofar kitchen din jin Ihun, Humainah ta ajiye man hannunta ta taho da sauri tana kallonta tace “Dama baki iya ba…..” Jasmine ta fashe da kuka q rikice tana yarfe hannu ganin jini a hannunta, Shigowa kitchen din junaid yayi ya hade rai yana kallon Humainah, hade ran ita ma tayi ta juya ta koma ta ci gaba da aikinta, Jasmine ta karasa kusa da shi tana kuka tace “Captain kaga blood din” kama hannunta yayi suka fita daga kitchen din Humainah ta bi su da kallo ta gefen ido. Sama ya tafi da ita xuwa dakinsa ya sa ta xauna bakin gado ya dauko tissue yana goge mata jinin dake ta xuba, ganin yanda take kuka yasa yace “Sorry!” Ta fashe da wani sabon kukan tace “It’s paining me” kallon yatsan nata yake, ido ya lumshe a hankali ya sunkuyo dai dai kan yatsan yana hura mata iska, itama lusmshe idon tayi tana jin d’umin iskar da yake hura mata, har ya d’ago idonta na a lumshe, cute face d’inta da eye lashes d’inta ke kwance ya k’urawa ido, a hankali itama ta bud’e manyan idanunta ta sauk’e kan face d’inshi, cikin wani irin murya yace “Does it still hurt?”, a hankali ta gyad’a mishi kai, spirit d’in da ya saka jikin wool d’in ya d’auko yasa mata kan yatsan, ido ta rintse ta saki k’ara tareda k’ank’ame mishi hannu tana haawaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button