CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Uzuri! Uzuri
!! Uzuri!!! Yana
[1/14, 9:17 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
54……
Ko da nurse din ta xo kin bari El-ameen ya fita ya bar ta Jasmine tayi, ya fiddo wayarsa ya kira junaid har ya gama ringing bai daga ba, ya kuma kiransa nan ma no answer, kallon Jasmine da ke ta hawaye yayi yace “Nace maki am not going, yanxu xan dauko maki magani in dawo” tana girgixa kai tace “Noo” hade rai yayi yace “To bari in yi tafiyata…” Ta kamo hannunsa cikin kuka tace “Noo plss kar ka tafi” yace “Toh yanxu xan dawo” daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita, xaune ya ga junaid a balcony ga wayar a hannunsa, bai ce masa komai ba ya fita waje ya shigo da nurse din, ta gaida junaid ya amsa ba tare da ya kalleta ba suka shiga parlon tare da El-ameen, bai shiga dakin ba ya tura nurse din bayan ya mata bayani don yasan ba lallai ta yarda da nurse din ba idan ta gansa, tsaye yayi corridor din rooms din yana mamakin halin junaid, now a days the thing is just getting worst ma, tabe baki yayi yana nan tsaye har bayan kusan minti talatin nurse din ta fito tace “Dr bbu sanitary pad,” shiru yayi sai kuma yace “then sai na je hospital don shaguna basu bude ba yanxu” tace “Ohk, ka taho da injection da drugs” yace “Ohk” ya juya ya sauka ita kuma ta koma dakin, da ido junaid ya bi sa har ya shiga motarsa ya bar gidan. Bakwai saura El-ameen ya dawo ya kira nurse din ta fito ya mika mata ledan hannunsa ta karba ta koma dakin, yana nan tsaye har ta kuma fitowa tace “Tayi bacci Dr” yace “Ohk shiga dakin can” ta kalli kofar dakin da ya nuna mata tace “In yi me?” Yace “Bata da lafiya ita ma ki duba ta” bude kofar tayi ta shiga da sallama, ta karasa gun gadon tana kallon Humainah da ke kwance cikin bargo tana bacci, yaye bargon tayi wanda hakan ya farkar da Humainah ta mike xaune da sauri tana kallon nurse din, Nurse din ta mata murmushi xata yi magana idonta ya sauka kan gadon, shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi kofar da take tunanin bathroom ne, komawa Humainah tayi ta kwanta tana kokarin maida hawayen da ya cika idonta, ba a dau lokaci ba nurse din ta fito ta iso gun gadon tace “sannu sister tashi mu je bayi” bata mata musu ba ta cire bargon ta mike tsaye, kama hannunta nurse din tayi suka shiga bathroom din, Humainah ta kalleta cikin tsarkewar murya tace “Xan iya da kai na” nurse din tace “Toh shikenan” daga haka ta fito ta shiga gyaran dakin, tana nan har Humainah ta fito, nurse din ta tambayeta inda kayanta yake ta nuna mata ta bude ta fiddo mata da gown, cikin ‘yan mintuna ta gama shirya wa nurse din sai kallonta take don tasan daurewa kawai take, darduma ta shimfida mata ta bata hijab ta karba ta hau kan darduman ta tada sallah, nurse din ta fita don xuwa hado mata tea tasha kafin ta bata Magani, da mamaki ta kalli El-ameen dake tsaye har lokacin a corridor tace “Kana nan har yanxu Dr, ai da ka xauna parlor” yace “Am okay, ya jikin nata?” Tace “Da sauki I want to go nd make a cup of tea for her” yace “Are you sure she’s ohk?” Tace “Ka shiga ka duba Dr” yace “No ba sai na shiga ba, make the tea for her na taho mata da drugs” tace “Okay,” sannan ta sauka, ba a dau lkci ba ta dawo da cup din tea din ta kai ma Humainah, ba laifi ta karba ta sha, nurse din ta fito El-ameen ya bata magungunan sannan ya sauka downstairs, parlor ya ga junaid kwance yana kallo, El-ameen bai bi ta kansa ba ya fita yayi xaman sa a balcony, nurse din na saukowa Junaid ya haura sama, kofar dakin da Jasmine take ya tura a hankali ya shiga ya tsaya daga bakin kofar yana kallonta, bacci ya ga take ya karasa kusa da gadon ya durkusa dai dai fuskarta yana kallonta, bude ido tayi a hankali ta mike xaune da sauri ganinsa, ya d’an koma baya yace “Cikin ya daina?” Kallon jikinta ta shiga yi, sai kuma ta gyada masa kai tace “Uncle ya tafi?” Hade rai yayi yace “Ban sani ba” tayi shiru bata ce komai ba, ya mike ya fice daga dakin, dakinsa ya shiga don yin wanka, Jasmine ta sauko daga kan gadon tana kalle kallen jikinta, a hankali ta dinga tafiya har ta fito ta sauko downstairs, hawaye ya cika idonta ganin bbu El-ameen, har xata koma sai kuma ta fita parlon, wara ido tayi ganinsa xaune yana danna waya, ta karasa da sauri ta durkusa kusa da shi tace “Uncle!” Yayi murmushi yace “Har kin tashi?” Gyada masa kai tayi, yace “Toh cikin ya daina?” Shiru tayi sai kuma a hankali tace “Eh ya daina, uncle wannan Antyn tace min am on my period, Meye wannan?” Ya d’an bude ido yace “Nima ban sani ba” shiru tayi sai kuma ta kalli jikinta a hankali tace “Uncle har yanxu fa yana yi” murmushi yayi yace “Xai daina, je ki duba min ko Anty ta tashi a sama” tace “toh” sannan ta mike ya bi ta da kallo har ta shiga parlon, dakin Humainah ta shiga ta ganta kwance tana kuka, karasawa gun gadon tayi ta durkusa kamar ita ma xata yi kukan tace “Anty menene?” Shiru Humainah tayi mata, hakan yasa ta mike ta fita ta koma gun El-ameen, hawaye cike idonta tace “Uncle kuka take, she don’t want to talk to me” yace “Captain din fa?” Tace “Yana dakinsa” mikewa El-ameen yayi ya shiga gidan ta bi bayansa, tsaye yayi bakin kofar Humainah yayi sallama har sau biyu bata amsa ba, Jasmine tace “Ka shiga tana ciki” bude kofar yayi ya mata alamar ta shiga, tana shiga ya bi bayanta, karasawa cikin dakin yayi ya tsaya d’an nesa da gadon yana kallonta yace “Ya jikin Humainah?” Mikewa xaune tayi amma ta kasa juyowa tace “Da sauki” yace “Ohk kiyi hakuri, Allah ya sauke kin ji” kai kawai ta gyada masa yace “Go to sleep xa ki ji sauki sosai” kwanciya tayi ya juya ya fita Jasmine ta bi bayansa, a hankali Jasmine ta kamo hannunsa tace “I hate that captain, he’s so mean” bude ido El-ameen yayi, sai kuma ta sunkuyar da kai a hankali tace “Though I like him also, he’s fine just like you” dariya El-ameen yayi yace “To naji tafi dakin ki” ta hade rai tace “Ina xa ka” yace “parlor” bude kofa aka yi duk suka juya Captain ya fito, suna hada ido da Jasmine ya watsa mata wani kallo a kan idon El-ameen kuma, xame hannunta tayi a hankali daga na El-ameen ta juya ta shiga daki, junaid yace “You are still around ashe, tot ka tafi” El-ameen bai tanka sa ba ya sauka kasa, junaid ya bude kofar Humainah ya shiga ya karasa gun gadon ya xauna yace “Good morning wife” rufe ido tayi da sauri, yayi murmushi xai dagota ta mike xaune sai kuma ta fashe da kuka, ya wara ido yace “Toh kuma, Allah ya baki hakuri just came to say ya jikin” daga haka ya mike ya fita, dakin Jasmine ya bude ya ganta xaune ta rungume hannayenta kiris ya rage ta fashe, yace “Ai kin iya dafa indomie koh?” Kai ta gyada masa a hankali, yace “Toh xo ki dafa mana” mikewa tayi ya juya ta bi bayansa, indomie hudu ya fiddo mata tace “Har da Anty?” Yace “Eh” kujera ya dauko ya xauna kitchen din yana kallon yanda xata yi girkin, har ta gama bayan kusan minti goma idonsa na kanta bai ma san ta gama ba, ta karasa kusa da shi ta duka a hankali tace “Captain!” Rufe ido yayi ya bude da sauri ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace “Jasmine” bude ido tayi a hankali tace “Na gama” mikewa yayi a hankali har lokacin yana rike da hannunta yace “Ohk dear, dauka daya ki kai ma Anty sai ki dauka kema ki ci” toh tace ya sake hannunta ya juya ya fita. Da yamma nurse Salima ta kuma dawowa duba Humainah da Jasmine kamar yanda El-ameen ya umarce ta. Da magrib junaid ya shirya ya tafi gida, gabansa sai faduwa yake don bai san yanda xa su kwashe da Mumy ba, part din Abbansa ya fara shiga don gaidasa, ya tarda Umma da Hajiya a parlon, xaunawa yayi kasa ya gaida Abba ya amsa yana tambayarsa gida, yace “Alhmdllh Abba” juyawa yayi yana kallon Su Umma ya gaida su, duk suka amsa masa da fara’ar da bai kai ciki ba ana tambayarsa amarya, Hajiya ta mike ta fice daga parlon bayan ta ma Abba sallama Umma ta bi bayanta, ya d’an jima xaune parlon Abba sannan ya mike yace masa xai je gun Mumy, kamar munafuki ya xauna kasa ya sunkuyar da kai yana gaida Mumy, ta amsa masa bbu yabo bbu fallasa, rasa abun cewa yayi haka ya karashi xaman sa Mumy nata harkan gabanta ya mike yace xai tafi tace “Allah ya tsare” ya fita parlon, bai yi mamakin ganin su Hajiya da Umma xaune a spot dinsu ba, ko sallama bai yi masu ba ya fice, Hajiya tayi murmushi tace “Komai dai ya kusa xuwa karshe in da rai da lafiya, sai mun cusa ma iyayenka tsanarka” gidansu El-ameen junaid ya nufa bayan ya bar gidan, yayi mamakin ganinsa xaune waje, ya xauna gefensa yace “kai kuma xaman waje ka fara yanxu kenan” El-ameen ya shafa kai yace “Yafi min alkhairi ne, kawai Ummi ta dau fushi da ni kan abinda bansan komai kai ba, ni wllh ban san kayan me take nufi ba” junaid yayi shiru can yace “Toh ka tambayi Abba mana,” El-ameen yace “He also don’t want to say anything about it to me” junaid yace “Toh tashi mu je mu samu ummin sai mu tambayeta” El-ameen yace “A’a ni baxan je ba, wannan Kanwar Abban nawa na ciki” mikewa Junaid yayi ya shiga gidan, Small mum din El-ameen ce xaune parlon da Ummi, Ummi ta hade rai ganinsa ya d’an shafa kai ya karaso ya xauna kasa kusa da Ummi ya gaida ta ta amsa bbu yabo bbu fallasa, ya gaida Anty dake parlon ita ma ta amsa masa haka, yana shafa kai yace “Ummi mu fa bamu san kayan me ake cewa ba” Anty tace “Eh ai baxa ku sani ba munafukai, irin yanda aka maka haka xa a masa shi ma kwanan nan” ko kallonta Junaid bai yi ba ya kalli Ummi ya marairaice yace “Allah Ummi ba mu sani ba” Ummi tace “kayan auren mutum ku ke hadawa a boye ko na me” junaid ya xaro ido yace “Kayan aure kuma Ummi, wani kayan auren?” Ummi ta tabe baki tace “Na sha gaya masa yanda aka yi maka a gida haka shi ma xa a masa yana xaton fadi nake kawai koh, to xaku sha mamaki daga kai har shi” junaid yayi shiru can yyi murmushi yace “toh ayi masa hakan kawai Ummi, don nima ina masa maganan aure baya saurarana, ni ba gashi ina xaune lafiya da matar ba” Ummi tace “To tafi daki ka ga kayan sun yi” junaid ya d’an bude ido yana kallonta, sai kuma ya mike ya nufi bedroom dinta, ko da ya fito dariya kawai yake yace “Wllh sun yi sosai Ummi, Allah ya saka da alkhairi” junaid bai ce ma El El-ameen komai ba da ya fito kawai dariya yake bakin rai, El-ameen yace “Meye haka?” Junaid yace “Nothing, na shawo kan Ummi ta hakura wllh” kallonsa kawai El-ameen yake bai ce komai ba.