CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kwana biyu da ya kama ran lahadi Humainah ce tsaye kitchen tana girkin lunch Jasmine na daga bakin kofar kitchen din tsaye duk ta cika ta da surutu ita dai aikinta take ba tare da ta tanka ta ba don da tace ta tafi xata dawo, junaid kuma na sama, danna bell aka yi Jasmine ta xaro ido tace “kila uncle koh Anty?” Humainah bata tanka ta ba ta fita daga kitchen din, jasmine ta bi bayanta da sauri, suka isa gun kofar a tare ta bude, wata yarinya da baxata wuce su ba ce tsaye bakin kofar Humainah sai kallonta take don bata santa ba, yarinyar tayi murmushi tace “Baki san ni ba koh, yi hakuri ruwan sha xa ki ban don Allah, na xo gidan aunt dina ne dake layin nan ne wllh wai ashe jiya da daddare suka yi tafiya da mijinta gashi duk na gaji bbu shagunan siyan ruwa nan kusa” Humainah tace “Ohk, shigo” yarinyar ta shigo tana bin ko ina na parlon da kallo ta samu kujera ta xauna, fridge Humainah taje ta dauko mata ruwa da drink ta ajiye mata, Yarinyar ta mata godiya tana murmushi Humainah ta koma kitchen, kallon Jasmine da ta xauna kasa kusa da ita tana kallonta yarinyar tayi tace “Sannu ya sunan ki?” Jasmine ta d’an wara ido tace “Uncle na kira na jewel, captain na kira na Jasmine, Mamina na kirana Baby” yarinyar dai sai kallonta take, Humainah dake kitchen tana jin su ta tabe baki ta ci gaba da girkinta, yarinyar tace “Waye captain, waye Uncle?” Jasmine xata yi magana suka ji taku stairs, shiru tayi tana kallon stairs din haka ma yarinyar har ya sauko, kallo daya yayi masu ya dauke kai, yarinyar tace “Ina kwana” ya ji bai ji ba ita dai bata sani ba don bai amsa ba ya shiga kitchen ya rufe kofar yana kallon Humainah yace “Wacece ta shigo min gida?” Humainah ta daure fuska tace “Ruwa xata sha” ya wani hade rai yace “Ruwa? Kika san daga inda take maxa fita ki sallameta kar ki sha mamaki” bata tanka sa ba ta ci gaba da girkinta, ya bude kofar ya fice, kallon Jasmine yayi yace “Come here” mikewa tayi ta bi bayansa don stairs ya nufa, yarinyar ta bi su da kallo, fitowa Humainah tayi ta xauna parlor ganin bata ga Jasmine parlon ba ta kalli stairs, yarinyar tace “Nagode kwarai ‘yar uwa, ni sunana Hadiza” Humainah tace “Welcome” yarinyar ta mika mata waya tace “Sa min number ki mu dinga xumunci naga kina da kirki” Humainah ta karba ta sa mata number ta mika mata, yarinyar tace “Suna fa?” Humainah ta gaya mata, tace “Allah sarki, amma kishiyar ki ce wannan da na gan ku tare” Girgixa mata kai kawai Humainah tayi, tace “Ayya, to ni xan koma xa mu ke xumunci” har bakin kofa Humainah ta rakata yarinyar sai murmushi take ta fita daga parlon, Humainah ta kulle, ta koma kitchen. Da yamma misalin karfe shidda motar El-ameen ya shigo gidan, Junaid dake daki ya mike yana lekensa ta window don tun ranan basu sake haduwa ba, ko parking din arxiki bai yi ba ya fito da ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, junaid ya fashe da dariya har da kyakyatawa ya sake curtain din ya koma kan gado ya dinga dariya, direct dakinsa El-ameen ya nufa don bbu kowa parlon, kwankwasa kofar yayi junaid ya mike xaune yace “Come in” ya tura kofar ya shiga yana kallon junaid dake ta kokarin danne dariyarsa, junaid ya mike tsaye yace “Ya aka yi na ganka haka besty, me ya faru” xaunawa kan gado El-ameen yayi ya rike kai, Junaid ya xauna gefensa yace “Talk to me mana” El-ameen ya dago da kyar yace “Kaga abinda su ummi ke shirin min sai kace wani mace, wllh not me” junaid yace “Me xa a maka?” El-ameen yace “Wai aure!” Junaid ya xaro ido sai kuma ya fashe da dariya El-ameen ya mike yana kallonsa, yayi mai isan sa sannan yace “Nima haka ka min” kofa El-ameen ya nufa junaid ya rikosa da sauri yana dariya yace “Wllh ramawa na yi nima haka fa ka min” da kyar ya lallaba El-ameen ya xauna, sannan yace “Toh kai yanxu kana da warce kake so ne da har xaka damu kanka, ba gashi nima haka aka min ba kuma ina xaune lafiya?” Shiru El-ameen yayi kafin yace “Ni ina da warce nake so” junaid yace “To wacece?” Da kamar baxai ce komai ba sai kuma ya shafa kansa a hankali yace “Baby!” Kallonsa junaid ya tsaya yi ko kiftawa bai yi, El-ameen ya mike yace “Kuma ita xan kai masu, in ma basu yarda ba ni sai na aureta don Allah xan iya hallaka warce xa a hada ni da” daga haka ya nufi kofa Junaid ya mike ya fixgosa yace “Wace babyn kake nufi?” El-ameen yace “Warce ke gidan ka” wani kallo Junaid ya watsa masa yace “Sai ka jira randa na maida ta gun iyayenta sai ka bi ta ka aureta, yanxu kam baka isa ba” murmushi El-ameen yayi yace “Koh?”

Haske Writers association????
[1/14, 9:18 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

55…..

Wani kallo junaid ke masa ya sake sa ya koma baya yace “Yess! Me ya hana ka son auren nata lokacin da take hauka? You can call what ever prize you wish to for giving her your attention and I will pay you” El-ameen bai ce masa komai ba ya gyara kwalar rigar sa ya juya ya fita daga dakin, a stairs suka kusan cin karo da Jasmine, ta koma baya ta wara ido ganinsa tace “Uncle! When did you come” murmushi ya kirkirar mata yace “Am coming” ya bi ta gefenta ya sauka ta bi sa da kallo. Tana jin fitar motarsa ta bata fuska tayi daki da sauri xata fara kuka. Washegari monday Junaid na dawowa masallaci da asuba ya shiga dakin Humainah, ya sameta xaune kan darduma daga bakin kofar ya tsaya yace “You are resuming school today” tace “Na sani” juyawa yayi ya fita, ya bude dakin Jasmine, kwance ya ganta tana bacci cikin bargo ya cire bargon ta mike xaune da sauri yace “Tashi kiyi sallah, after that you brush ur teeth nd take ur bath” daga haka ya juya ya fita ya koma dakinsa, wanka Humainah tayi ta gyara bedroom dinta ta fito parlor nan ma ta share sannan ta shiga kitchen, ruwan lipton ta daura ta xuba kayan kamshi sannan ta fara peel din potatoe. Karfe bakwai saura junaid ya fito daga bedroom sanye da uniform dinsa don ranan sati biyun da ya dauka gun aiki ya cika, kitchen ya tafi ya tsaya daga bakin kofa yana kallon Humainah, ta juya tayi masa kallo daya ta dauke kai, yace “Xan yi tafiyata in kyale ki if you are not ready” tace “Toh ai dai ba xaune nake ba” bai ce komai ba ya karasa cikin kitchen din ya dau cup ya hada tea ya fita. Yana xaune parlor har karfe bakwai yayi Humainah ta fito ta wuce sama, can ya mike shi ma ya tafi saman, dakin Jasmine ya bude ya ga ta gama sa kaya yace “Fito ki ci abinci” shiru tayi tana kallonsa daga sama xuwa kasa yace “Baki ji na ne” komawa baya ta shiga yi a hankali har lokacin idonta na kansa sai kuma ta fashe da kuka tana girgixa kai tace “Ni bana son kayan nan captain” ya kalli farin shirt din uniform da navy blue trousers din dake jikinsa yace “Me suka maki kayan” ta kuma fashe wa da kuka tace “I don’t like it” wani kallo ya mata ya juya ya fice daga dakin, a hankali ta xauna gefen gado tana xaro ido kamar me son tuna abu, dakinsa ya koma ya dauki wayarsa da hularsa ya fito, dai dai lokacin da Humainah ta fito ita ma rike da cup, bai ko kalleta ba ya sauka downstairs ya dau makullin motarsa, ta bi bayansa tace “Toh baxa ka kai ni makarantar ba?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Sai kuma gobe am late” daga haka ya fice daga parlon ta bi sa da kallo kamar xata fashe da kuka, ajiye cup din hannunta tayi a parlon ta koma sama hawaye cike idonta. Jasmine na jin fitar motarsa ta sauko ta tafi dining ta debi breakfast dinta ta ci a nan ta koma sama. Da yamma misalin karfe hudu saura Humainah na dakinta bayan ta daura girki a kitchen ta ji an danna bell, mikewa tayi ta fito dai dai lokacin da Jasmine ma ta fito, ko kallonta bata yi ba ta sauka, bude kofar parlon tayi ta ga yarinyar jiya a tsaye, murmushi yarinyar tayi tace “Kin gan ni kuma koh, daxu aunt dina ta dawo na taho, yanxu ma gida xan koma nace bari in shigo mu gaisa” Humainah ta d’an yi murmushi ita ma tace “Toh sannu da xuwa” hanya ta bata ta shigo ta xauna parlon, yau ma kamar jiya ruwa ta kawo mata, yarinyar sai hira take mata kamar sun dde da sanin juna, ita dai Humainah duk ta kasa sakewa, Jasmine ta shigo parlon tana kallon Humainah tace “Anty ki kira min Uncle” Humainah tace “Bani da waya” Jasmine tayi shiru bata ce komai ba, sai kuma ta juya ta koma sama, yarinyar da ta kira kanta da hadiza tace “Amma wacece yarinyar nan?” Humainah tace “Kanwar mijina ce” Hadiza tace “ohh, Allah sarki, amma basa kama ko dai ‘yar uwar na family kike nufi” a takaice Humainah tace “Eh!” Don duk ta kagu ta wuce sai kallon agogo take sanin hudu da wani abu junaid ke dawowa wani time, Hadixa tace “Toh dai ki kula” Kallonta Humainah tayi da sauri, hadiza tace “Naga yanda take wani shige masa jiya da na xo” murmushi Humainah ta kirkira bata ce komai ba, hadiza tace “Ae ba abun dariya bane, ni ma nan da kike ganina na kusa dawowa anguwar gaba daya gun aunt din nan tawa sbda damuwa da yayi mata yawa, in gaya maki wata yarinya mijinta ya ajiye wai yar uwarsa xata yi karatu a gidan, in kinga yarinyar very quiet har ni ke ce ma Anty fa’ixa ta dinga sake mata don Allah don ko kallonta bata yi, to yanxu xancen da nake maki Friday mai xuwa daurin auren mijin yayar tawa da yarinyar” kallonta kawai Humainah ke yi gabanta na mugun faduwa, hadiza ta dawo kusa da ita tace “Bari ki ga hotunan aunt din tawa da yarinyar har ma da mijin” kallon hoton kawai Humainah ke yi amma sam hankalinta baya jikinta, bude gate din gidan aka yi, hadiza ta bude ido tace “In ji dai ba mijin naki bane ya dawo” kasa ce mata komai Humainah tayi, Hadiza tace “A’a kin ga ki fa kwantar da hankalin ki, ai ba duka maxan suka taru suka xama daya ba kawai ke dai ki sa ido” Humainah bata ce komai ba still har junaid ya shigo parlon, daga bakin kofa ya cire takalman kafarsa ya bar bakar safar, kallonsu kawai yake a parlon lokaci daya ya hade rai, ya nufi stairs hadiza ta bisa da kallo ta d’an bude murya tace “Ina yini” a tunanin ta jiyan da ya shareta bai ji bane, ko kallonta bai yi ba bai kuma amsa ba ya haura sama, hadiza tace “Toh bari in wuce naga kamar mijin ki bai son baki” Humainah tace “Rabu da shi” dariya Hadiza tayi ta mike tace “Toh Hajiya Humainah kinga tafiyata, gobe ko jibi xan ma dawo anguwar baki daya” Toh kawai Humainah ta iya ce mata ta rakata har bakin kofa ta wuce sannan ta dawo ta tafi sama, tana shiga daki ta xauna gefen gadonta tana tunanin maganganun Hadiza, bude kofar dakin aka yi ya shigo fuskar nan tasa a daure ko uniform bai cire ba don fitina yace “Wace yar iskar ke xuwa gidan nan?” Ko kallonsa bata yi ba ta dauke kai, ya karasa ya fixgota yace “keh! Baxa ki gaya min wacece ita ba?” Fixge hannunta tayi tace “Mutum ce kuma ai ka gane ma idonka” yace “Koh? To wllh wllh ta sake xuwa min gida xan baki mamaki daga ke har ita” daga haka ya juya ya fice, kuka ta saki duk ta rasa me ke mata dadi sosai xancen hadiza ya xauna a xuciyarta, mikewa tayi ta sauka kasa ta kashe girkin da take ta koma daki. Har bayan magrib junaid na xaune daki duk abinda ya ma El-ameen jiya ya tsaya masa ya rasa yanda xai yi, ta yaya ma xai ce yana son Jasmine, wani irin so ma yake nufi, mikewa yayi daga karshe ya dau makullin motarsa ya fita, ana kiran isha ya isa gidansu El-ameen, sai da yayi sllh a masallaci sannan ya shiga gidan, xaune ya samesa a daki da faisal, faisal na ganin junaid ya bude ido yace “Captain junaid, ashe ana ganin ka” murmushi junaid yayi ya xauna yace “Kai ma ai ba ganin naka ake ba” hira suka d’an yi da faisal, shi dai El-ameen wayarsa kawai yake dannawa, daga bisanni faisal yayi masu sallama yace xai tafi clinic ya fita, Junaid ya kalli El-ameen da ya ki kallon inda yake yace “Har da wani pretending baka gan ni ba?” Ba tare da El-ameen ya kallesa ba yace “Ai mun gaisa” Junaid ya d’an shafa kai yace “Look, am sorry about what happened yesterday, I don’t know what came over me…..” Katse sa El-ameen yayi yace “It’s ohk, I also don’t know what came over me, i was just confused, I couldn’t help it… May be dat was y I uttered those words” shiru junaid yayi yana kallonsa ganin he was so serious, El-ameen yace “Yess!” Junaid yace “No idan ma sonta kake da gaske ai ba komai bane, just pray memorynta ya dawo a maidata gun iyayenta nd then you can go on….” Shiru junaid yayi don jin maganar yayi wani iri a bakinsa, El-ameen yace “Noo, ni an min mata ai” Junaid bai kuma cewa komai ba sai bayan kusan minti uku yace “Ohk gobe da yamma ka raka ni ayi enrolling dinta a islamiyya, she so need it yanxu, ita kuma Humainah is resuming school” El-ameen yace “Ohk” junaid na kallonsa yace “akwai shirye shiryen da xa ayi ne na bikin?” No kawai El-ameen yace masa. Washegari Tuesday junaid bai bari Humainah ta je school ba don bai son barin Jasmine ita kadai a gida sai sunyi registering dinta a islamiyya, haka Humainah tayi ta kumbure kumburenta ya wuce aiki abun sa, kwata kwata ranan bata sake ma Jasmine ba, sai taji ina ma Hadiza xata xo ranan ma amma har Junaid ya dawo bata xo, bai damu da girkin da bata yi ba don sai ya ci abinci yake dawowa, Karfe biyar saura ya shiga dakin Jasmine ya ganta kwance tayi jigum, tana ganinsa ta mike xaune yace “Sa hijab din ki ki fito” ba musu tai yanda yace ta fito parlor, sai ga Humainah ma ta sauko ta tsaya bakin stairs tana kallonsu ta wani hade rai, Ko kallonta junaid bai yi ba yana kallon Jasmine yace “Mu je” ta bi bayansa xa su fita Humainah ta rufe kofar tana masa wani kallo sai kuma ta fashe da kuka tace “Ni wllh xan hada ka da Abba na gaji haka kuma” Jasmine dai sai kallonta take, junaid ya fixgota yace “rashin kunyar ki ta da ne xai dawo koh?” Bai jira cewarta ba ya turata one side ya kama hannun Jasmine suka fita ta fashe da kuka sosai ta haura sama da sauri, Junaid ya kira El-ameen ya fi sau biyu kafin ya daga, bai damu da hakan ba ya gaya masa islamiyyan da xai taho ya samesu, ya fi minti talatin yana jiransa kafin ya xo, a tare suka shiga babban makarantar suka yi duk abinda ya dace junaid ya bada kudi, aji hudu aka sa ta bayan yayi bayanin ailment dinta, shi dai El-ameen kallonsu kawai yake, suna fitowa makarantar xa su shiga mota junaid ya hango Hafsat sanye da uniform din makarantar da hijab, tuni El-ameen ya shige mota Jasmine ma ta bude bayan motar ta shiga tana kallonsa, Hafsat bata lura da Junaid ba xata wuce yace “Hafsat!” Juyowa tayi da sauri tana kallonsa, murmushi yayi yace “kwana biyu” dawowa tayi ita ma tayi murmushin tace “Alhmdllh” yace “Nan kike knn” kai ta gyada masa, ganin duk tayi wani iri yana kallonta yace “Baki da lafiya amma koh?” Murmushi ta kirkira tace “Am getting married ne” ya d’an bude ido yace “Ohh really, when?” kamar baxa ta ce komai sai kuma tace “Friday” Junaid yace “Toh Allah ya sanya alkhairi, but shine bbu gayyata” bata ce komai ba, ganin kamar bata son maganan yasa yayi mata sallama tayi wucewarta ya shiga mota.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button