CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association????

[3/19, 9:22 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

56…..

Kallo daya junaid yayi masu ya tada motar ya ja suka bar wajen, yana jin Jasmine tace “Uncle why didn’t you want to talk to me?” Ba tare da El-ameen ya kalleta ba yace “Am meditating!” Ta wara ido tace “Ohh What’s that?” Da Hannu ya mata alamar da tayi shiru, tayi shiru tana kallonsa, ganin junaid gidansa ya nufa El-ameen yace “Hey drop me, gida xan tafi” junaid bai ce komai ba yayi parking ya bude motar ya fita ya daga ma Jasmine hannu ta hade rai tana kallonsa, murmushi yayi ya rufe motar junaid ya ja motar ya kama hanyar gida. Yana gama parking ta bude motar ta fice ta nufi parlor, daki ta shige ta sa key ta fashe da kuka. Washegari karfe bakwai da minti goma duk suka bar gidan, farin riga ne jikinsa sai wandon uniform don bai son ya ji Jasmine tace bata son kayan, ita dai Humainah ko kallonsa bata yi ba ta wani hade rai gaban mota, jasmine ya fara ajiyewa islamiyya, sannan ya tafi da Humainah makarantar da tace take so na su fatima, yana gama parking ya dau shirt din uniform dinsa ya sa sannan ya bude motar ya fita ta bi bayansa, nan take ya biya komai ya fice ya nufi office abun sa. Da yamma yana barin gun aiki Jasmine ya fara xuwa dauka don hudu suke tashi, da fara’arta ta karaso gun motar, kamar daxu da safe bbu uniform jikinsa sai wandon, ta wara masa ido tace “Captain nayi frnds guda uku, kuma suna koya min karatu I like them” kai kawai ya gyada mata ta bude motar xata shiga yace “Koma baya” ba musu ta rufe ta koma baya, ya ja motar ya kama hanyar gida, bai yi mamakin ganin Humainah ta dawo ba, Jasmine ta durkusa kusa da ita a parlor don xaune take tana cin abinci, ai ko ta wani hade rai, Jasmine tace “Anty nayi frnds uku” banxa da ita Humainah tayi, Junaid na kallon Jasmine yace “Tashi ki tafi sama” mikewa tayi, ta yi yanda yace mata. Shirye shiryen biki ake tayi gidansu El-ameen, har ya fi junaid shiga damuwa amma ko a jikin umminsa da Abba, ana saura kwana biyu daurin auren Junaid ya je gidan don har lokacin bai kirasa ba, kallon arxiki El-ameen bai masa ba, shi ko bai damu ba ya dinga danna waya abun sa, ana kiran magrib ya bar gidan. Ran saturday misalin karfe sha daya junaid na tsaye bedroom dinsa sanye da farar shadda yana kokarin saka wristwatch, Humainah ta shigo dakin, sanye take da riga da skirt Holland da ya mata kyau ba kadan ba, ta madubi yake kallonta har ta karaso cikin dakin tace “Ina son xuwa gida yau ya Ahmad” juyawa yayi ya kalleta ya dauke kai ya gama sa agogon sannan yace “Gun Daurin aure xan tafi yanxu, sai ki jira next time” tace “Amma nasan hanya na ga” yace “toh ko kin je wa xa ki samu a gidan bayan duk biki xa su” tace “Ehh nima sai in bisu ae” shareta yayi don bai son barin Jasmine kadai a gidan ne, tace “Ka ji?” Ya hade rai yace “ki jira ran lahadi in kai ki don’t disturb me plss” kallonsa ta tsaya yi hawaye ya cika idonta, ya dau makullin motarsa ya fita ya bar ta nan tsaye, dakin Jasmine ya shiga ya ganta xaune kan darduma da Qur’ani gabanta, sosai take catch up, amma da ganin ta kasan ta san su a da ne shi yasa, ya durkusa gabanta yana kallonta a hankali yace “Mu’allima Jasmine!” Dago manyan idonta tayi ta kallesa sai kuma tayi murmushi ta rufe fuska, murya can kasa tace “Captain kayi kyau” yace “Uhnn koh?” Ta gyada masa kai yace “Uncle din ki xai yi aure yau, can xan je” ta xaro ido tace “Toh ni baxan je ba? kuma ni bai gaya min ba” kamar xata yi kuka ta kare maganar, Langwabar da kai yayi yace “Maza kadai ke xuwa ai” shiru tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace “gobe sai na kai ki gidan ki ga amaryar” kai ta masa nodding a hankali tace “Toh” ya dago chin dinta yace “Tea’n ya ishe ki?” Tace “Uhm na koshi” yace “Ohk,” sannan ya mike ya daga mata hannu ya nufi kofa, bin sa da kallo tayi har ya isa kofa, a hankali tace “Kayi kyau” juyowa yayi da sauri sai kuma yayi murmushi yace “Ae kin gaya min” sunkuyar da kai tayi ya juya ya fita, har xai sauka sai kuma ya shiga dakin Humainah, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa, ya karasa kan gadon ya dagota ya ga kuka take, xaunawa yayi gefenta ya jawota jikinsa yace “Toh ba nace maki ran Sunday xan kai ki ba” ta fashe da wani sabon kukan, ya rungumeta yace “Toh yi hakuri, da yamma sai in kai ki by then su ma sun koma gida” shiru tayi bata ce komai ba, yace “kin ji” dago kai tayi tana kallonsa, ya buda mata ido ya ciro wayarsa ya shiga daukarsu hotuna, mikewa yayi daga karshe yace “sai na dawo” daga haka ya fita daga dakin, direct gun daurin auren ya tafi, El-ameen yi yayi kamar bai taba saninsa ba, shi kam ko a jikinsa don dariya ma yake basa, nan dai aka daura auren a kan sadaki dubu dari biyu, ko minti biyar Junaid bai kara ba ya bar wajen ya tafi gida abun sa. Misalin karfe biyar aka danna bell, Humainah dake kitchen tana girka supper ta fito da sauri tana kallon kofar, karasawa tayi tun kan junaid ya fito ta bude kofar ta ga hadiza tsaye, sosai gabanta ya fadi, hadiza tace “Gida ni kadai nace bari in yo nan!” Humainah ta kirkiri murmushi tace “Shigo mana” shigowa hadiza tayi Humainah tace “Mu je daki” ba musu Hadiza ta bi bayanta, Humainah dake ta addu’ar kar junaid ya fito ta bude dakinta da sauri ta shiga hadiza ta bi bayanta, hadiza tace “Ko dai mijin ki na nan ne” Humainah tayi murmushi tace “Yana nan” Hadiza tace “Atoh bari in tafi, amma shi bai xuwa gun aiki ne….” Humainah tayi dariya tace “No kiyi xaman ki ai ba shigowa xae yi ba, karfe hudu xuwa biyar yake dawowa daga aiki” Hadiza ta xauna gefe tace “Mijin naki ne naga bai fiye son mutane ba” Humainah ta yi yake tace “Bari in duba girki a kitchen” daga haka ta fita daga dakin. Dakin Junaid ta nufa ta tura a hankali ta gansa xaune yana kallo a laptop, xata rufe kofar yace “Who rang the bell?” Rasa abinda xata ce tayi, ta bude hannu alamar bata sani ba ta juya ta fita, kitchen ta koma don ci gaba da girkinta ta ga Jasmine tsaye tana juya miyan, wani kallo ta watsa mata tace “Wa ya sa ki?” Jasmine ta ajiye cokalin hannunta tace “Taya ki nake” Humainah tace “Fita!” Ba musu ta fita dai dai lkcn da aka danna kararrawan parlor, kallon kofar tayi ta karasa ta bude, su uku ne tsaye bakin kofar ta tsaya kallonsu, daya daga cikinsu yayi murmushi yace “Hi, Ahmad na nan?” Ta d’an bude ido tace “Waye shi?” Na gefensa yace “Junaid!” Ta kuma bude ido tace “Waye shi?” Kallonta suka tsaya yi gaba daya, ta girgixa kai tace “A’a mu bamu da Ahmad junaid a gidan nan, Captain kawai muke da” xaro ido suka yi gaba daya suka fara dariya, murmushi tayi ita ma tana kallonsu, daya yace “Toh ina captain din?” Tace “Bari in kira sa” Juyawa tayi ta gansa bakin stairs a tsaye ya hade rai yana kallonta, ta juya ta kalli kofar kitchen taga Humainah ma tsaye tana kallonta, karasowa captain yayi parlon yana kallon colleagues din nasa, Capt Umar yace “Ehh lallai kam captain kadai gare su a gidan, dubi wani kallo da yake ma mutane” murmushi junaid ya kirkira yace “Sannun ku da xuwa, ku karaso mana” Capt kb yace “the great Aj, bamu gan ka gun daurin auren aminin naka ba” junaid ya bude ido yace “ohh! Ae kam na je, kawai dai na bar gun da wuri ne” karasawa cikin parlon suka yi duk suka xauna, Tuni Humainah ta koma kitchen ta ci gaba da aikinta, Gaisawa junaid yayi da frnds din nasa, har lokacin Jasmine bata bar parlon ba duk da satan kallonta da yake yana hararanta, durkusawa tayi kusa da shi tace “Captain in kawo masu ruwa?” Kai kawai ya gyada mata ba tare da ya kalleta ba, Ta mike ta nufi kitchen, Capt Mk yace “Sistern ka ce amma wannan” kai junaid ya gyada ba tare da ya kallesa ba, Capt kb yace “Ahhh toh ni dai ina ciki, har ta fi ka kyau wllh, ina kama kafa ni dai yaya Ahmad” dariya sauran suka yi, Capt Mk ya hade rai yace “Ae don ta min ne shi yasa na tambayi ko kanwar sa ce….” Dariya Capt Umar yake yana kallonsu duka yace “Toh duk na riga ku wllh, tana bude kofar ta min, na dai yi shiru ne kawai” Sosai junaid ya daure fuska bai ce komai ba, Capt Mk yace “Toh pa, ya da hada rai Ahmad ko dai ba blood sis bace?” Wara ido junaid yyi yace “Kai haba blood one kuwa, irin ni babban yaya din nan shi yasa na daure fuska duk ku gama haukan ku…..” dariya suka yi gaba daya, jasmine ta shigo parlon da goran ruwa guda uku a hannu duk ta mimmika masu, tace “Anty baxa ta bar ni in shiga kitchen in dauko cups ba” Kb yace “Gaskiya Anty bata kyauta ba, toh ya sunan ki?” Ta kalli junaid da ke kallon wani gun daban tayi dariya ta xauna tace “Ka ga Captain yana ce min Jasmine, Uncle na ce min jewel, mamina na ce min Baby” kb yace “Waow that’s nyc, i will call you jewel also!” Ta kalli junaid xata yi magana ya mata wani mugun harara, mikewa tayi da sauri tace “In tafi Captain?” Yace “Ehh” juyawa tayi ta tafi sama, duk su ka bi ta da kallo, Mk yace “Uhmm! But ya aka yi ban santa ba Aj, fatima da khadija kawai na sani” Junaid yace “Ehh ba tare mu ke da ita ba” Humainah ce ta fito daga kitchen ta karaso cikin parlon ta tsaya daga bayan kujera ta gaida su, da fara’a suka amsa mata suna tsokanarta ta kara gaba abunta, dakinta ta shiga ta ga hadiza xaune har lokacin, ita har ta ma mance da ita, rufe kofar tayi tace “Kiyi hakuri girki nake ne” hadiza tace “Ba komai, nima nasan aunt dina kila ta dawo yanxu, tafiya xan yi” Humainah tace “Ki jira ki ci abinci mana, baki yayi a parlon yanxu xa su tafi” xaunawa Humainah tayi Hadiza ta fara mata hira ita dai sai uhn uhn take don bata son junaid ya ji muryarsu, shidda saura junaid ya raka frnds din nasa har bakin mota yayi masu godiya yace “Kun dai ki cin abinci” Mk yace “Kai kuma ka ki barin mu yi sallama da jewel, ni dai ina nan dawowa gobe” KB yace “kai ka ma kai shi har gobe, bayan isha ni ina nan xuwa” dariya suka yi gaba daya banda Junaid da yace “Ai duk kuna da ‘yan mata na ga” sun kusa minti sha biyar tsaye daga bisanni suka wuce ya koma ciki, Tuni Humainah ta sauka kasa ta debo ma Hadiza abinci jin fitarsu, yana haurowa sama dakin Jasmine ya bude, ya ganta tsaye bakin window tana kallon waje, hade rai yayi yace “From henceforth aka sake ring din bell kika sauka kika bude kofa I will slappp you, wani ya saki ne?” Kallonsa ta tsaya yi, hadiza dake jin duk abinda yace ta kalli Humainah murya can kasa tace “Toh fah” Jasmine kam bata ce komai ba sai kallonsa take kamar bata gane me yace ba din nan, ya karaso cikin dakin a fusace yana mata mugun kallo yace “Kin ji abinda nace?” Girgixa masa kai tayi da sauri, ya dawo kusa da ita strictly yace “Nace daga yau kar ki kuma fitowa parlor idan aka ring din bell, kuma na sake ganin kin tsaya magana da maxa har kina gaya masu sunan ki sai na maki mari!” Sunkuyar da kai tayi cikin tsawa yace “Kin ji?” Ta gyada masa kai hawaye cike idonta, juyawa yyi ya fice daga dakin. Hadiza tace “Toh fah, don Allah ki gaya min yanda kuke da yarinyar nan” Humainah ta tabe baki kamar baxata ce komai ba sai kuma tace “Yar uwarsa ce” hadiza tace “Tabdi toh Meye kuma na hanata magana da maxa, aurenta shi xai yi ko me?” Hade rai Humainah tayi bata ce komai ba, Hadiza tace “Toh ae ba xancen hade rai bane, wllh ki sa ido kar abinda ya samu yayata ya same ki, abu na biyu kuma na ga bbu wani interaction mai karfi tsakanin ki da mijin ki, anya kuwa?” Shiru Humainah tayi bata ce komai ba, Hadiza tace “Tabdi, to auren dole aka maku ne, yo ko da auren dolen ne ma ke ba mace bace baki san yanda xa ki ja mijin ki jiki ba, ai kam xa ki tsaya kallon ruwa….” Ita dai Humainah har lokacin bata ce komai ba, Hadiza tace “Ya ina magana xa ki share ni, ni tun randa na ganki naji Allah ya dora min san ki banda haka wannan ai ba hurumin da xan shiga bane, batun gaskiya Humainah da sake a xaman auren ki, ga mijin ki hadadde me kyau da shi xa ki tsaya wasa wata ta kwace maki, lallai ma” mikewa tayi tace “Kin ga tafiyata abincin ma ya ishe ni” Humainah da duk jikinta ya mutu tace “A’a don Allah ki kara…” Hadiza tace “Tafiya xan yi” daga haka ta nufi kofa fuu irin tayi fushi din nan ita, Humainah ta bi ta da sauri don ita tsoronta kar junaid ma ya ganta, tuni hadiza ta fice daga gidan gaba daya, Humainah ta sauke ajiyar xuciya tana naxarin maganganun ta, xama tayi bakin gado tayi tagumi hawaye ya cika idonta, to ita ta ma san yanda xata yi da junaid, da kyar ta iya mikewa ta shiga bayi ta dauro alwala don yin magrib, ta jima xaune kan darduma daga bisanni ta mike ta fita daga dakin ta sauka kasa, kitchen ta tafi ta hada masa abincinsa a tray, ta gama xata fita Jasmine ta shigo kitchen din ta tsaya daga bakin kofa tace “Anty abinci na” ba tare da Humainah ta kalleta ba tace “Ban yi da ke ba, ki shiga ki dafa” Jasmine tace “Na’am” juyawa Humainah tayi ta fice daga kitchen din ta bar ta nan tsaye. Junaid na waya Humainah ta shigo dakin, ta ajiye abinci har lokacin bata mike daga durkushen da tayi ba, yana gama wayar ya juya yana kallonta ya d’an bude ido yace “Uhun! Yau kuma” hade rai tayi, yayi murmushi yace “Toh na gode, kin ba Jasmine na ta?” Kallonsa kawai take, can ta tabe baki tace “Kace da magrib xaka kai ni gida” yace “Ohh shi sa aka kawo min abinci, to ni gidansu El-ameen xan tafi yanxu” kuka ta fashe da tana kallonsa, ya sauko kasa ya dawo kusa da ita shi ma ya durkusa ya fara kwaikwayonta, duka ta shiga kai masa tana cewa “Ni ka kyaleni bana so” dariya yayi yace “Sai in dawo captain din yanxu, ni kike duka” dagota yayi suka koma kan gado yace “Gobe lahadi kin ga sai in kai ki tun asuba sai sha biyun dare xan je daukan ki” ta tsaida kukan tace “Kace Allah” yace “Sai na ce?” Shiru tayi tana kallonsa, ya ja hancinta yace “Allah” murmushi tayi ta fada kansa tace “Toh na gode” can kuma ta mike ya bi ta da kallo har ta fita, abincin ya bude ya ga tuwon shinkafa ne da miyar vegetable….. ” ya dau plate da spoon ya dibi kadan ya ci snn ya rufe ya mike, wanka ya shiga ya fito ya shirya don xuwa gidansu El-ameen duk ya kagu yaga matar aminin nasa, dakin Jasmine ya shiga ya ganta xaune kasa ta daura kanta kan gado, yace “Kin ci abinci?” Ta girgixa masa kai, yace “Bata baki bane?” Ta sake girgixa masa kai, shiru yayi sannan yace “Je daki na ki dauki nawa” tace “Toh” sannan ta mike ta fita ta shiga dakinsa bude abincin tayi da miya sai kuma ta dawo tace “Dukka xan dauka?” Yace “Ehh” komawa tayi sai ga ta ta dawo da tray din, murmushi yayi ya juya ya fita daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button